Chapter 14
CHAPTER 3
بسم الله الرحمن الرحيم
Yayinda baƙin cikin halayar Abba da Umma ya mamaye zuciyarta har ta na jin kamar ta tashi ta barmusu gidansu kawai, tunda dama da ita da babu du ɗaya ne, sunan ta na zaune ne kawai amma zaman haƙuri da jure halin Abba kawai ta ke.
Umma kuwa kwantar da kai ta yi ta lallaɓa Abba ya bita ɗaki, can sukai lissafinsu ba tare da sun nemi Mama ba, sai da daddare da lokacin cin abinci ya yi aka aiki Yaya Sumayya ta kirawo ta, da farko kamar ba za ta je ba dan tunanin halin da nike ciki ya ƙi barinta, Abba bai sanar ma ta na warke daga makanta ba, amma ko mi ta gani sai kuma ta tashi ta je, tun da tai sallama ta kai dubanta inda su Abba ke zaune da tarin kayan kwalam da makwalashe a gabansu ta jinjina lallai ba ƙaramar duniya Abba ya samo ba, kaji ne ƙosasshi aka banƙare tare da yi musu kyakkyawar gashi sai sheƙi da ɗaukar ido suke, kusan guda biyar aka jere a ƙaton faranti, sai lemon jarka kaloli shina an jere sai kuma robobin take away da yogofura.
Mama bata ce komi ba ta shiga ta zauna ba tare da ta kula kowa ba, Abbama bai kulata ba dan ta bashi tsoro yanda yaga ta ɗauki lamarin da zafi, bayan anzubama kowa abin da yake so suka shiga ɗibar daɗi babu me tunawa da ni sai Mama.
⭐⭐⭐
A slow na lumse manyan fararen idanuwa masu ɗaukar hankali, sai kuma na sake buɗesu warrrr na watsasu akan Fauzan wanda har yanzu bai janye idanuwanshi daga gare ni ba, da yake Pahpah ya yi ma shi bayani akan matsayina sai ya shiga tunani a zuciyarshi.
'Ita kuma wannan kyakkyawar halittar zunubin mi ta aikata da za'a haɗata aure da ni, amma dai gaskiya ba'ayi ma ta adalci ba sam, kuma wannan ai san kai da tauye haƙƙi.'
A hankali na tashi zaune ina jin ko ina na jikina na yi min ciwo, jingina na yi a jikin bangon glashin ɗakin, a hankali cike da tsoro da kuma tsananin tausayin halin da ya ke ciki na sake dubanshi sannan na ce.
"Sannu bawan Allah, Allah ya baka lafiya ya sa zakkar jiki ce."
Lumshe idons ya yi yayinda sanyi da daɗin sautina ya ratsa har cikin kanshi, kamar ba zai amsa ba sai kuma ya sake dubana sannan ya ce cikin harshen turanci.
"Thank you".
A taƙaice, kuma bai janye idonshi daga kallona ba.
Kamar daga sama na sake jiyo amon raunanniyar muryarsa wacce ta ke fita a hankali kuma can ƙasa sosai ya na faɗin.
"Dan Allah ki taimaka min da ruwa d lemo a cikin wancan fridge ɗin".
Ya sake faɗa da turanci.
Ban musa ba a hankali na tashi tsaye ina ji na kamar bazan iya tsayuwarba saboda rashin kuzari, amma na daure na tilastawa kaina tsayuwar harma da fara takawa dan cika umurninshi, ina zuwa gaban fridge ɗin kai na yai wa ta irin sarawa, tsikar jikina na mimiƙewa ta na yamm yammm amma haka nai addu'a tare da buɗe fridge ɗin, lemon da ya faɗa min sunanshi na sauke idona a kanshin, amma sai zuciyata ba ta kwanta da shi ba, dan haka sai kawai na sauke hannuna akan wa ta robar lemon tare da ɗauko wa na ɗauki ruwa na kulle murfin da ƙarfi.
A gaban ɗan table ɗin da ke wajen na ajiye tare da ɗauko cup na shiyaya ma shi ruwa, kallonshi na yi ina faɗin.
"Ga su ammafa da zaka daure ka tashi zaune da sai ka fi jin daɗin sha."
Ɗan waro idanuwa ya yi jin abin da na ce, sai ya yi murmushi kawai tare da miƙomin ƙonannen hannunshi alamar in taimaka in tada shi.
Kamar ba zan yi ba, sai kuma na kama hannun na shi wanda ke fitar da ƙarni da warin ƙonuwa, a hankali na ja hannun da niyar in tada shi, amma sai na ji bai ko motsaba, hakan ya saka na yanyo ɗayan hannun shima na janyo shi da tsananin ƙarfi, sai da ya saki nishin azaba, dan na yi nasarar tada shi zaune daga wajen da shi kanshi ya mance rabon da ya ganshi an tada shi, ko mi za'ayi ma shi sai dai a yi ma shi shi daga kwance.
Saura kaɗan in sake shi inyi baya dan tsoro, duka manyan idanuwana na waro waje ina karanto addu'o'i a fili tare da kawar da kaina gefe ina bawa hawayen da na bansan da taruwarsu ba damar fitowa.
Ƙarni da wari ne kawai ke tashi a wajen ga fatar bayanshi nan tanƙare a kan glasa bed ɗin, sai tsutsotsi da ke ta faman sintiri a wajen, da mugun hanzari na kalli bayanshi wanda ya sille ya saluɓe tas babu ko fata sai sauran tsokar da ta rage a jikinshi itama tai jajur ga tsutsaotsi nan manya da ƙanana su na sunturi akai.
Wani irin sanyi me sanya nutsuwa ne ya ke safkarwa Fauzan, ga wani irin daɗi da ya baibaiye shi jin na raba shi da wannan azabar da yake ciki, yasan za'a iya samun fiye da abin da na gani dan kuwa shi kaɗai ya san mi yake ji a jikinshi, sannan wannan sanyin da tun zuwana ɗakin ya baibayeshi daga azabar da yake ciki sai yanzu ya gane daga gare ni ya ke.
Cike da ƙarfin zuciya da tsananin tausayi na lallaɓa na janyo shi zuwa ƙasa, sai nishi da shesheka ni ke yi, na yi ina ƙoƙarina wajen ganin na zaunar da shi, amma abin ya ci tura, ban san lokacin da na cire hijabin jikina ba na ɗauki gorar ruwan sanyin da na ɗauko na tsiyaye shi akan hijabin tas, wasu ƴan tuntaye na gani a gefe da su na yi amfani na shimfiɗasu agefe sannan na shimfiɗa hijabina a ƙasansu, cike da dabara na kwantar da shi na gefe tare da tare shi da wannan tuntayen gudun kar ya kwanta ta bayan.
A jiyar zuciya ya sauke me ƙarfi tare da lumshe ido ya na jin sanyin abayata na ratsa ƙonannen jikinshi.
Ƙoƙarin zare hannuna daga na shi na yi, amma ya hana hakan faruwa ta hanyar riƙe nawa hannun da kyau, saurin kallonshi na yi sai naga idonshi na kan ruwan da na zuba a cup, ni na manta shaf wallahi, dan hankalina sam baya jikina ganin irin halin da yake ciki, da ɗayan hannuna na yi amfani wajen ɗauko ruwa, a hankali na zauna agabanshi na fara yin tofin ayatul shufah a cikin ruwan sannan na yi bisimilla tare da kaiwa ga busashen bakinshi...✍️