ZAFIN WUTA

Chapter 15

by @maryamstar248

Version:1.0 StartHTML:0000000156 EndHTML:0000083853 StartFragment:0000000469 EndFragment:0000083845

 

           CHAPTER 4 

بسم الله الرحمن الرحيم 

 

Da sauri ya amsa tare da zuƙe ruwa, janye cup ɗin na yi ina tsananin tausaya ma shi, kafin in dire cup ɗin na ji wani irin kakari gami da nishi, sauri juyo da kaina na yi, aiko nai arangama da shi ya na sheƙa uban amai, ruwan da ya sha, ya amaye tasss tare da wasu irin abubuwa marasa kyan gani masu fitar da wani irin wari. rasa abin yi na yi sai kawai na fashe da kuka me ƙarfi da sauti, har lokacin ina riƙe da hannunshi cikin nawa. 

 

Mommyce ta yi taga-taga kamar za ta faɗi, dan dukkan abin da ke faruwa akan idonta, ji ta yi anyi saurin taro ta, buɗe rinannun idanuwanta waɗanda suka rine saboda kuka ta yi tare da kallo tsakiyar nashi idanuwan waɗanda ke cike da zallar ƙauna da matsanancin tausayinta, sake shigewa jikinshi ta yi tare da fashewa da kuka me sauti, rarrashin ta yayi tare da kwantar ma ta da hankali, gefe ɗaya kuma ya na jinjinawa ƙoƙarin da nayi, dan shima tun lokacinda yaga tahowarta ya biyo bayanta dama  ya tsaya wajen bada umarnin a dafawa Fauzan shari da abu me ruwa wanda zai iya sha, da kanshi ya tsaya ya taho da basket ɗin bayan an gama haɗa komi, shine ya tsaya kallon irin ƙoƙarin da nike yi shima. 

 

Kamo hannun Mommy Pahpah ya yi tare da ɗaukar basket ɗin ya shigo da iya ɗakin. 

 

Har yanzu kuka nike na rasa yanda zanyi, kaina gaba ɗaya ya kulle da tausayin halin da Fauzan ke ciki, jin sallamar su Pahpah ya saka na ɗan tsahirta daga kukan amma ba dainawa na yi ba. 

 

Mommy ce ta ƙaraso tare wajena itama ta na zubda hawaye, ba ta jira komi ba ta rungume ni tsam a ƙirjinta ta na shafa bayana, mun daɗe rungume da juna kafin daga bisani ta sake ni ta na kissin face ɗina tare da jero min godiya da addu'a cikin harshen turanci. 

 

Pahpah ma sannu ya jera min tare da saka min albarka sannan ya miƙomin wani ƙullin magani tare da basket ɗin hannunshi, bayani ya yi min akan yanda zanyi amfani da maganin sannan ya janyo Mommy da ke zubda hawaye har lokaci suka fice badan ta so ba. 

 

A je kayan hannuna na yi tare da bin wa ta madaidaiciyar ƙofa da na gani a buɗe, ina shiga naga ashe toilet ne ƙerarre amma na glashi sai dai shi ba'a iya ganin cikinshi, amma wanda je ciki zai iya ganin abin da ke waje. 

 

Ruwa na tara cikin wani butiki da na gani, na ɗauki wani towel da aka shanya a jikin hanger, sannan na ɗauki detergent powder tare da freshner na zuba da moper na fice. 

 

Fauzan tun da na tashi daga wajen na shiga toilet ya dainajin wannan sanyi wanda ke saukar ma shi da nutsuwa, a hankali ya fara jin wannan zafin me kama da ZAFIN WUTA ya na tasowa a hankali a hankali har ya fara baibaye dukkan ilahirin jikinshi, runtse ido ya yi yana sauraren yanda azabar zafin ke saƙe konashi. 

 

Tun da na fito daga toilet na dinga jin wani huci na me haɗi da zafi ya baibaye ɗaƙin, ina tafiya ina jin yanda hucin zafin ke nesa da ni, ina ƙara matsawa ya na ɓacewa har ya ɓace ɓat, wa ta iriyar wawiyar ajiyar zuciya Fauzan ya sauke lokacin da sanyin da ke tattare da ni ya baibaye duniyarsa ya na saukar ma shi da wa ta iriyar kasala da nutsuwa. 

 

A hankali na duƙa kusa da inda ya ke na shiga gyara wajen ba tare da na damu da warin da aman ke fitarwaba, ina yi ina tazbihi gami da godiya ga Allah da ya wadata ni da lafiya, tsaf na gyara wajen sannan na kwashe kayan na kai toilet na zubar da ruwan na kunna shower ta wanke wajen, tap ɗin ruwan zafi na kunna na sirka ruwa daidai misali sannan na fito da su zuwa inda Fauzan ya ke, ba tare da jin ko ɗar ba na duƙa gabanshi na dinga saka ƙaramin towel ɗin cikin ruwa ina matsewa, na shiga goge ma shi fuska ba tare da na damu da yanda jikinshi ke fitar da ƙarni gwanin kyankyami ba. 

 

Tas na goge ma shi fuskar wajenda ya kwalje kuma na saka maganin da Pahpah ya bani, komawa na yi wajen hannuwanshi suma na durje su tasss sukan ba laifin sun ƙone sosai gaskiya dan kusan duka fatar na darje tare da barbaɗa maganin sannan na tashi na canzo wasu ruwan amma wannan karon harda detol na saka a ciki da kuma sumfi na farkon yawa, komawa bayanshi wanda ya caɓe babu kyan gani na yi, tsayawa tunanin ta inda zan fara na yi, dan harga Allah bayan na shi bayu kyawun gani, hakanan na karanto bisimilla tare da aro bargon juriya da haƙuri ina tuna saboda aikin jinyarshi aka kawo ni gidan kuma aka aura man shi ba'a son raina ba, ina tilastawa kaina dole na yi aiki tuƙuru kodan biyan bashin maƙiden miliyoyin kuɗin da Abba ya tafi da su. 

 

A hankali na naanaa ma shi towel ɗin tare da gogawa, wa ta irin ƙara marar sauti ya saki tare da jujjuya kanshi ya na sakin numfarfashin wahala da azaba, cike da tsoro na ja da baya ganin yanda na ɗago da towel ɗin yayi caɓa caɓa da jini da kuma danƙararriyar dauɗa wace ta  manne da ƙananun tsutsotsi, kamar ba zan iya ba na aje towel ɗin sai kuma na sake ɗauka na ɗauraye a cikin ruwan na kuma mayarwa akan bayan ba tare da na kalli wajenba, sake wankewa na yi amma wannan karon a hankali ba da ƙarfi ba, sau uku na wanke bayan badan ya fita ba na barshi hakanan sai dan saboda warin da ƙarnin da suka addabe ni, cikin sauri na tashi da kayan na kai toilet tare da sakarma bukitin ruwan shower dan bazan iya wanke su da hannuna ba, na ga worshing machine amma rashin iya amfani da shi ya saka banyi gigin zuwa inda yake aje ba, wanke hannuna nayi sosai sannan  na koma na ɗauki maganin na saka audiga na dinga goga ma shi a hankali a wajen. 

 

 

A jiyar zuciya na sauke lokacin da na gama saka magananin, sosai na yabawa kaina dan kuwaba kowace mace ce zata iya yin abin da na yi ba, wajen basket ɗin na koma na ɗauko madaidaicin cup na shiyayi ruwan tea ɗin da aka zuba a ƙaramin flasck wanda ke ta tashin kayan ƙamshi, na buɗe gwangwanin madarar da aka saka da vornbiter na zuba nai haɗin kauri, babu sugar saboda haka nai amfani da zumar da aka sako cikin wani ɗan ƙaramin cup, juya tea ɗin na yi da tea spoon har na tabbatar da babu zafi sosai sannan na sake matsawa inda ya ke kwance kamar gunki nai bisimilla tare da nufar bakinshi da cokalin da na zuba tea ɗin, bai musamin ba ya buɗe bakin cikin sauri, ganin ya amshi wanda na bashi ya saka na yi dabarar saka mashi cup ɗin abaki dan sauƙaƙama kaina wajen bashi, aiko tunda ya kafa kai bai tsaya ba sai da ya zuƙe tea ɗin tas, da yake da yawa na zuba mashi ba laifi.....✍️