Chapter 16
CHAPTER 5
بسم الله الرحمن الرحيم
Ganin ya shanye tea ɗin tas ya saka na janyo food flask ɗin na zuba ma shi joloup ɗin taliyar da akaiwa tsarariyar dahuwa sai turirin ƙamshi ta ke, a nutse na bashi ya ci, ba laifi ya ɗanci sosai, ruwa na bashi me gauraye da magani, sannan na gyara ma shi kwanciyar na tashi na shiga toilet na ɗauro alwala, ficewa na yi daga ɗakin ina neman ɗakin da na sauka ɗazu gami da ƙarewa babban parloun gida kallo ina yaba kyau da tsarin da ya yi, bayan na gane ƙofar ɗaki na shiga tare da zuwa wajen da aka tanadar dan yi sallah wanda aka shimfiɗa prayer mate da cazbaha harsa al'ƙur'ani me girma sai ƙaramin littafin azkar.
Bayan am fito da Zuka daga kogin azaba wasu aljannun suka ɗauke shi suka yasar a can ƙarahen baƙin daji, sukai tafiyarsu suka barshi ba tare da tausayin halin da yake ciki ba, da kyar ya daure azabar da yake ji ya ɓace zuwa kogon da boka ya ke ciki, boka na zaune ya na haɗa magungunan surkullensa kawai ya ji faɗowar abu ya na nishi gami da fitar da hucin azaba, ga wani irin zafi da ya fara mamaye kogon, cike da razani boka ke kallon yanda zuka ke fitar da numfashi ga jikinshi duk yayi fari alamar ƙonuwa, zai buɗe baki kenan yai magana kawai Zuka ya feso ma shi wani baƙin hayaƙi daga wawakeken bakinshi, nan take ya faɗi a wajen kamar gawa, cikin matsananciyar azaba Zuka ya kamo hudar gashin bokan ya shiga zazzage ma shi cutar da azabar da ke cikinshi, sai da ya gama juyewa bokan ciwon jikinshi tas sannan ya tashi a galabaice ya bi ta jikin bangon dutsen ya ɓace ɓat yabar boka kwance cikin mawuyacin hali.
ABDFA GROUP OF COMPANY.
Su biyu ne masu tsananin kama da, duk iya kokonton mutum ba zai iya banbance su ba sai dai idan su ne suka nemi a gane su, fararene tas masu matsakaicin kyau sai, amma fuskokinsu cike suke da haiba da kwarjini, hannuwansu sarƙafe da juna, hatta takon ƙafafuwa tare suke saukewa kuma au ɗaga a tare, idan suka haɗu da wanda suka sa ni sukan ɗaga ma shi hannu tare da sakar ma shi tattausan murmushi, gaban jibgegiyar motarsu suka nufa, ɗayan ya kai hannu na yaɗewa ɗayan, a maimakon ya shiga shima sai ya koma can ɗayan ɓarin ya buɗewa ɗaya, murmushi suka saki atare dare da zagayowa kowa ya shiga ƙofar da ɗan uwansa ya buɗe ma shi, babu ɓata lokaci driven motar ya ja da wani irin spich suka fice daga companyn.
"My bee, zamuje mu duba jikin friend, kwana biyu kenan bamu je ba, kuma akwai wasu magunguna da nike so in gwadawa Pahpah ya gwada yi ma shi amfani da su za'a dace da yardar Allah."
Ɗayan ya faɗi fuskarshi da damuwa, numfashi ɗayan ya sauke shima fuskarshi na zancaza zuwa tsananin damuwa dannan ya ce.
"Ok My bee, mu biya mu gaida shi ɗi."
Babu wanda ya sake magana a cikinsu sai tunani da kowanensu ke yi.
Bayan na gama sallah tare da karatun azkar wani irin nannauyan barci ya kwashe ni, barci nike yi sosai, ga sanyi AC da rashin hayaniya da ya sake taimakamin wajen yin barci cikin daɗin rai, ban samu farkawa ba sai daf da kiran magrib, shima dan ban saba barci lokacin sallah ba, koda kuwa barci ya ɗauke ni babu jimawa aka kira sallah, tofa haka zan tashi in kakkaɓe barcin, dan sam bana wasa da lokacin sallah, addu'ar ta shi daga barci na yi, gamin daga bisani na tashi na cire hijabin da ke jikina na nufi toilet, ba da niyyar yin wanka na shiga ba, amma dana gwada zuba ruwa a bahon wanka naga sun taru gwanin sha'awa sai na ji ina so inyi wankan, dan haka sai na ɗauki wasu robabi da ake aje turarukan wanka na bulbula sosai a ciki, sannan na cire rigata na sulala ciki, kai arziki rahama, na faɗi a zuci yayinda daɗin ruwan da ƙamshi ya ratsa ni, sai na nemi kasalar da nike ji ta barci na rasa, yayinda na shagala ina wasa da ruwan ina murje lallausar matata wacce na ji ta sake yin laushi dana shiga ruwan, sai ji na yi in kwalla kiran sallah a masallcin da nike da tabbacin daga cikin gidan ya ke, da hanzari na kammala wankan na fito ba tare da na tsiyaye ruwanba, towel na gani ɗan ƙarami sai na ɗauke shi na ɗaura cikin hanzari, rigar da na cire kuma na jefata a cikin bahon wankan, acewata idan na gama Sallah zan dawo in wanke ta, a gaggauce na yi alwala na fito, turus na tsaya ina tunanin yanzu ya zanyi ga shi banga jakar kayana ba, sai na yanke hukuncin zan ari ɗaya daga cikin waɗanda naga ankawo ɗazu an aje, ban tsaya wata-wata ba na buɗe sif ɗin na zaɓo wani lallausan manterial me taushi, na antaya rigar a jikina sannan na shafa mai tare da fesa turare ina ji na yau wasai.
Hajjo, Pahpah, Mommy da Sulaima su ne zagaye da Fauzan su na ta yi ma shi fira, fuskokinsu cike da farin cikin ganin sauye-sauye da dama, sai shi mani albarka suke tare sa gasgata lallai ni ɗin alkairi ce, da yake Pahpah ya basu labarin bayanin da me magani ya yi mashi, akan indai aka samu me irin baiwata tabbas zai rabu da lalurar gaba ɗaya, tunda dama sihiri ne akai ma shi da ɓakin aljani.
Fuskar Mommy yau wasai babu kuka sai mumushi wanda ya ƙi yankewa daga fuskarta, ita ko hajjo abin ba'a magana iya arziƙin zama lafiya lau ba tare da wannan tururin ya addaba musu ba kaɗai ya isheta farin ciki, a dah daurewa kawai suke su zo duba shi amma Alla-Allah ta ke su fita saboda zafin da ke mamaye ilahirin ɗakin wanda ke hanata nutsuwa.
Su na ahaka su na firar duk da Fauzan barci ya ke amma basu tafi ba, hakanan sukai zamansu zagaye da shi, ana cikin haka ne me kula da shigowar baƙi ta sanar da zuwan wasu baƙi, basu damar shigowa Hajjo ta yi, anan ne suka shigo hannuwansu sarƙafe cikin na juna, ga fuskokinsu faɗaɗe da murmushi.
"Ah lalle marhaban da zuwan Al-Hassan da Al-Hussain, kune tafe da yamma haka, ku ƙaraso daga ciki." cewar Hajjo cike da murnar ganinsu.
Wa ta iriyar mummunar bugawa zuciyar ɗayan ta yi, ganin Fauzan kwance a ƙasa ga magani a jikinshi, sannan babu wannan tururin da ke fitowa daga jikinshi, wa ta iriyar muguwar ashar ya kutuntuma acikin zuciyarshi, yayin da a fili fuskarshi ta ke normal kamar yanda ta ɗan uwanshi ta ke.....✍️