ZAFIN WUTA

Chapter 17

by @maryamstar248

Version:1.0 StartHTML:0000000156 EndHTML:0000096399 StartFragment:0000000469 EndFragment:0000096391

        CHAPTER 6 

بسم الله الرحمن الرحيم 

 

  'Mike shirin faruwa ne, waye ya sakama Fauwa wannan maganin, shin wai tayaya hakan ta faru, ina Zuka da alƙawarin da yai min???.' 

 

Haka yai ta jera tarin tambayoyi a zuciyarshi, amma babu amsa. 

 

Bacin sun gaisa da su Pahpah suka aje ƙatuwar ledar da suka kawo kayan dubiya tare da yi ma shi fatan samun lafiya sannan suka tafi fuskokinsu da jimami. 

 

Albarka su Hajjo suka shiga saka musu tare da  yabama karanci irin na su. 

 

 

 

 

 

AGEGE 

ABBA 

 

Durƙushe ya ke a gaban wani gini da aka yi shi da zallar zinariya, ga kudaɗe na ta shawagi a ata ko ina, Ni kuma ina zaune a saman kuɗin ina ta sakarwa Abba murmushi, gefe ɗaya kuma wani ƙaƙƙarfan farin mutum ne me ƙira irinta sadaukai tsaye a can bayana ya na aika min da kallon irina so da ƙauna, yayin da wa ta wuta ke tahowa ta bayanshi har ta iso ta mamaye shi gaba ɗaya, wani irin kukan kura na yi tare da dirkowa daga kan katangar na isa wajen wutar sa dugu na janyo mutum ina kakkaɓe ma shi wutar da ke ƙona shi ina kuka, yayin da na sauka daga kan katangar wasu mutane masu tsananin kama su biyu suka ɓillo ɗaya daga cikinsu na nufo inda ni ke ina kuka tare da yayyafawa wannan mutumin ruwa ina kakkaɓe ma shi wutar, ya na isowa ya shiga taimaka min muka kashe wutar a tare, yayinfa Abba da ɗayan suka nufi wajen katanfar da aka gina na gold suka haye tare da juya manah baya. 

 

A mugun firgice Abba ya farka daga mafarki da yayi, yayin da ya shiga sakin shehseka tare da ajiyar zuciya me ƙarfi, kallonshi ya kai wajen jakar kuɗinshi, sai yaga an canza ma ta yanayin ajiya ba haka ya ajiye ta ba, da sauri ya diro daga kan kadon ƙarfen Umma ya na sakin ashar. 

 

  "Uban ɓarawo ya zurma ya afka ya hwaɗa ya zumduma cikin satar min ƙudi, na rantse da kabarin kakana bazan yarda ba."  sai ya buɗe iyakar muryarshi ya kwarara uban ihu tare da nufar jakar ya buɗe ta, ilai kuwa an ɗibi kuɗin sai dai ba sosaiba, ɗaurin dalla ɗaya kaɗai aka ɗauka, ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfi tare da rataye jakar a hammata ta shiga kwalla kira har sai da ya  tada kowa na gidan. 

 

Zuciyar Umma ce ta hau luguden duku da ƙarfi, sai sharce gumi ta ke, yayinda ta tura hannunta can bayan gado ta saki ɗaurin kuɗin da ta sha baƙar wahala wajen satowa, da kyar ta aro baigon jarumtar ɓoye halin da ta ke ciki ta tashi ta na murza idanu kamar me barcin gaski. 

 

     "Abba wai lafiya zaka tashi mutane a tsohon darenan, wani abu ya faru da kulinne." 

 

"Inafa lahiya Umma ana neman a yashe ni tsaf, wallahi babu zaman lafiy ga duk wanda ya taɓa kuɗinan dan wallahi gidan wannan abokin me dallar Me rauhanai zanje a binciko min wanda ke farautar rayuwata ta hanyar barazanar taɓa min dukiya, na rantse da sittin ta Ubangiji bazan bar ko waye ya zauna lafiya." 

 

  Wa ta iriyar tusar tashin hankalice ta kuncewa Umma, yayinda dana sa nin ɗaukar kuɗin Abba ya baibaye ta, ta manta da waye Abba akan kuɗi, Abba zai iya tuɓe riga ya daku da uban kowa akan kuɗinda basu taka kara sun karya ba, nadama ce baibaye ta yayinda zuciyarta ke luguden duka. 

 

 "Ahaf ai dole ne kiyi hutu Ummakatiti kina can ki na barci za'a yashe ma ki tattalin arziƙin miji, Allah kaɗai yasan irin haɗarin da na tsallake wajen samun kuɗinan, amma wani banza ƙaramin ɓatawo me fama da bakin uwa ya zo zai yashe ni, nasan abin da zanyi wallahi bazan zauna hakanan sake ba." 

 

"Ah..ih...eh wallahi Abba ya kamata asan abin yi tun kafin lamarin yai nisa, ko kuma muje banki gobe da sahe mu binne kuɗin a can babu wanda yaji bare ya gani." 

 

Umma ta yi maganar ta na ƙyafta idanu yana shege lahira. 

 

Mama kuwa duk abin da suke ta na jiyo su, amma ba ta nuna tasan su na yi ba, dan zuwa ta yi ta ɗaura alwala ta fara jero salloli ta na kaiwa Allah kokenta, tare da roƙon Allah ya shiryar da Abba akan hanya madaidaiciya, sannan ta jero min addu'ar kariya da taimakon Allah aduk inda nike, ba ita ta gama sallar ba sai da ta ɗauki tsawon lokaci sannan ta shafa tare da tashi ta naɗe kayan da ta yi Sallah ta adana sannan ta haye kan gadonta tana tunanin ranar da zaren ƙaddara ha haɗa ta da Abba har ya janyo ta zuwa ga wannan rayuwar me cike da son kai. 

 

FLASH BACK 

 

IKORODU 

 

Anan ne unguwarda Malam Sa'idu ya sauka tun bayan barowarshi daga ƙauƴen Kura, ya sauka a unguwar tare da iyalinshi gaba ɗaya, inda suke rayuwa cikin sauƙi kasancewar ya taho da guzurinshi bayan rasuwar mahaifinsu da aka raba gado aka bashi kasonshi, ya na da mata ɗaya me suma Zulai da ƴaƴa uku Halima ita ce babba sai ƙanwarta Zubaida da ƙaninsu Sagiru, Malam Sa'idu mutum ne me tarin ilimin addini, a ƙauyen Kura shine limami a ungursu wanda ya ke jan su sallar juma'a, abin da yai sanadiyar barowarshi daga Ƙauyen har ya shigo duniya shi ne, mahaifinsu na da mata uku sannan akwai ƴaƴa masu yawa kusan ƴaƴa talatin da ɗoriya, Balarabe shine mahaifinsu, mutum ne me tarin dukiyar noma da kiwo, yana ɗaya daga cikin manyan attajiran da ake ji da su a kaf ƙauyen, to kafin rasuwarshi ya bar wasiyya akan abawa Sa'idu babbar gonarshi wacce yake  noman shinkafa a cikinta, sannan ya ware wasu daga cikin shanaye ya ce lallai idan ya riga Sa'idu barin duniya to abashi nashi ne halak malak basu cikin gado, nan akai rubutu Balarabe ya rantaɓa hannu akan takarda sannan akabawa me garin garin ya aje a wajensa, babu jimawa Balarabe ya kamu da ciwo wanda ya sha jinya sosai har daga ƙarshe ya riski ajalinshi, bayan sadakar arba'in ƴaƴanshi suka hura wuta akan rabon gado wannan yasa me gari ya zo da kanshi ya warware takarda ya karanta kuma yabawa kowa ya duba, nanfa aka shiga tashin hankali, domin ƙiri-ƙiri saura suka nuna rashin amincewa da hukuncin, me gari bai bi takansu ba ya saka malaman fada suka raba gado sannan aka bawa Sa'idu kasonshi da kuma wasiyyar mahaifinshi, tofa wannan wasiyya sa aka bashi ta zama tashin hanƙali ƙiri-ƙiri ƴan uwanshi suke neman rayuwarshi, hakan ya saka yaje wajen me gari ya damƙa amanar gonarshi da abin da za'a noma tare da isassun kuɗi wanda zasu isa ayi komi, ya tattara sauran gadonshi ya sayar ya haɗo kan iyalanshi ya yo kudu dan tsira sa rayuwarshi da ta iyalinshi. 

 

Halima yarinyace nutsatsiya ta na da hankali sosai ga tarin ilimin Mahammadiya da samu wajen mahaifinta, bata zuwa ko ina kullum su na gida zaune abinsu,   amma wani lokaci takanbi  mahaifinta kasuwa inda ya ke saida kayan gwari. 

 

Ta na shekara ashirin da biyu wani abokin kasuwanci Malam Sa'idu yaganta ya yaba da halayyarta da nutsuwarta, nan take yai wa ƙaninshi sha'awar aurenta, bai yi nauyin baki ba ya tari Malam da maganar, ya nuna jin daɗi sosai kuma ya bada goyon baya ɗari bisa ɗari dan ya yaba da karancin Usman ƙani ga abokinshi Abubakar...✍️