Chapter 18
CHAPTER 7
بسم الله الرحمن الرحيم
Ba'a ɗau lokaci ba Abubakar ya sanar da Usman akan ya je ya ga Halima su daidaita, Usman matashi ne me biyaya ga umarnin na gaba da shi, hakan ya saka bai ja da nisa ba ya je ya ga Halima, kallon farko ya afka cikin kogon sonta dan kuwa Halima takai a so ta a kallon farko, ta haɗa duk wani abu da namiji me hankali zai buƙata a wajen mace, ga nutsuwarta wacce tai bala'in tafiya da shi, shi mutum ne me son nutsuwa, a ɓangaren Malam Sa'idu ma ya sanar da Halima da zatai baƙo, cike da ladabi ta amsawa mahaifin na ta, bayan zuwan Usman sai ta ga ya kwanta ma ta sosai saboda mutum ne me nutsuwa da kamala, sam bashi da hayaniya irinta samarin zamani.
Bayan komawar Usman gida ya samu yayanashi Abubakar ya sanar da shi ya na son Halima dan ya yaba da hankalinta, idan babu damuwa aje kawai ai magana ba sai anja lokaci ba.
Sosai malam Sa'idu ya ji daɗin maganar sa abokinshi ya zo ma shi da ita, bai ja da nisa ba bayan ya koma gida ya nemo Halima ya tambayeta akan shin ko ta amince, abinka da mace me kunya da tarbiya bata amsa ma shi ba sai duƙewa da ta yi ta gagara ɗagowa ta kalli mahaifin na ta, ya ji daɗin wannan abin da ta yi dan haka ya sallame ta ta tafi ya zanta da mahaifiyarta.
Bayan kwana biyu aka tsaida maganar aurensu nan da wata ɗaya, saboda wani aiki da ya tasowa Usman ɗin zai je wanj couse a ƙasar waje, kafin aure wa ta iriyar ƙaƙarfar soyayya da shaƙuwa ce ta ƙulu tsakanin Usman da Halima, sun yarda da junansu sun tsara rayuwa me tsari wacce take cike da soyayya, sai de su na tasu Allah na tashi, tsarinsu kawai suka sa ni, basu san tsarin Ubangiji me kowa me komi ba, shi yasa ake so ɓu rage buruka da shagala da duniya, domin duniya ba matabbata bace, babu wanda ke sa shaida ko alamar dawwama da ratuwarshi, ita mutuwa bata sallama ko aike, idan ta zo ɗauka kawai ta ke, dan haka dan Allah ƴan uwa musulmai mu rage burika, mu dinga tunawa da mutuwa a cikin al'amuranmu, kada rayuwar ko ruɗin duniya su shagaltar da mu, Allah ya kyautata ƙarshen mu amin.
BAYAN WATANNI BIYU.
Bayan auren Usman da Halima da wata ɗaya suka tarkata zuwa chaina dan Usman zai gabatar da wani aiki wanda aka ɗaukesu su uku a companyn da ya ke aiki, tare da halima suka tafi, acan suka gudanar da rayuwa me tsafta da tsari, sai da sukai shekara ɗaya da rabi sannan suka dawo Nigeria, sosai ƴan uwa da abokan arziƙi waɗanda ke kusa sukai murnanar dawowarsu tare da tarin nasarori, ɗaya bayan ɗaya suka dinga zaga gidajen ƴan uwa na kusa dana nesa, a lokacin Halima na ɗauke da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe, Usman sai nan nan ya ke da cikin dan kuwa yanzo baya jin nauyi ko junyar kowa wajen bata kulawa, ko da gidan Malam Sa'idu suka je haka zai manne ma ta babu ruwanshi da ganin idon surukai.
Wa ta rana bayan dawowarsu daga gidan Abubakar da daddare naƙuda ta tasowa Halima, wanda ya saka Usman ya kira gida ya sanar sannan ya tashi ya ɗauki mota ya tado me aikin da ya samo ma ta suka nufi asibiti, sai dai basu samu isa ba Allah yai nashi ikon, a daidai lokacin da wa ta ƙatuwar mota wacce akayo lodin shanu burkinta ya kwanta ta daki motar Usman, a lokacin ne Halima ta samu nasarar sauke abin da ke cikinta zuwa wannan duniyar me cike da tarin al'amurra masu kyau da maras kyau, a lokacin da jinjirar ta saki kukan godiya ga Ubangiji, a lokacin ne numfashin Usman na ƙarshe ya fice daga ƙirjinshi bayan ya yi nasarar karanto kalmatusha shahada a rarrabe.
Halima bata san abin da ya faru ba dan tsoro da firgicin abin da ya faru ne ya saka ta haihu ba tare da ta sa ni ba, sai farfaɗowa ta yi ta tsinci kanta akan gadon asibiti ƙarƙashin kulawar likitoci, tun da ta farfaɗo ba ta cewa kowa komi ba sai kallon likitocin da ke ta aikin bincike akanta ko akwai wa ta matsala, amma cikin ikon Allah babu matsalar komi, hakan ya saka suka sallameta kawai.
Lokacin da suka koma gida babu wanda ta kula dan sam batai magana ba, amma duk wanda ya ambaci sunan Usman ko hatsari tofa za ta kafe shi da ido ta na kallo babu ƙaƙƙautawa.
Halima bata dawo daidai ba sai da ta kwashi tsawon watanni uku, babu irin maganin da ba'a nemo ma ta ba amma ko ina maganar ɗaya ce lafiyarta ƙalau kawai ta shiga halin ruɗu ne wanda ya mantar da ita komi, amma za ta dawo daidai da yardar Allah, hakanan iyayenta suka zubawa sarautar Allah ido su na taya ta da Addu'ar samul lafiya.
A wata rana Mama da Zulaha suka ɗauki Halima da jinjirarta wacce ta ci suna Fatima, zasu kaita asibiti saboda zazzaɓin da ta ke fama da shi, akan hanyarsu ta dawowa sun tsaya jiran go slow ya rage wani ɗan ƙaramin gatsari ya auku, inda mashina guda biyu suka yi karo da junansu suka faɗi, wa ni tartsatsi ne ya gifta ta cikin kan Halima, yayinda aka tariyo ma ta yanda sukai hatsari ita da Usman, nan take ta fasa ƙara tare da kwalla kiran sunan Usman ta ƙarfi sai kuma ta faɗi a sume.
CIGABAN LABARI.
Saurin ta shi Mama ta yi jin amfara kiran sallar asubahi, ta na jinjina irin daɗewar da ta yi ta na tunanin rayuwarta ta baya, sake tashi ta yi ta je ta ɗauro alwala ta sake jero wasu sallolin kafin a tada asubahi.
Zarya ya ke ta faman yi a cikin makeken ɗakinshi, yayinda ya ke dunƙule annayenshi duka biyun ya na saiwa iska naushi a haukace, sai faman huci ya ke kamar kumurcin maciji.
"Waye wannan wanda ke wasa da rayuwarshi ta hanyar shiga gonata, wallahi ko wanene sai naga bayanshi tunda har yai gangancin shiga hurumin da ba nashi ba, dole ko waye zai biya wannan bashin da rayuwarsa."
Ya na gama faɗin gakan ya juya da sauri ya nufi wajen wasu manyan lokoki ya buɗe, ya janyo wa ta jaka, buɗe jakar ya yi ya shiga fito da wasu ƙullin abubuwa ƴan ƙananu, zuwa ya yi bakin door ya kulle tare da batin key ɗin a jiki, sai ya nufi wajen labulaye ya sakesu duka, kashe wutar ɗakin ya yi sannan ya kunna hayaƙi tare da yin tsirara haihuwar uwarshi, sannan ya shiga kirari ya na kwalla kiran sunan ZUKA.
Duk abin da ya ke Zuka na tsaye jikin gini ya na kallonshi, sai da ya galabaita da sosai wajen kiranshi sannan ya buso wani ɓakin hayaƙi me wari sannan ya bayanna a sufar jegare me amon wuta.
Sauke numfashi ya yi tare da ɗagowa ya na haki kamar wanda ya tiƙi uban gudu sannan ya ce a galabaice.
"Ya zakai min haka! ba haka mukai da kai ba Zuka ba haka mukai yarjejeniya ba, na riga da na gama yi maka dukanin abin da kake so, na sadaukar maka da jinin waɗanda suke da muhimanci a rayuwata ta yaya zaka yi haka, waye wa warware aikin, da idona na ga anzuba ma shi magani, kuma yanzu har iyayenshi na can zaune tare da shi su na hira su na raha, bama wannan ne babban abin da ya dameni ba, shin ko kasan har yanzu babu wani ci gaba a company har yanzu banga alamar wancan tsohon banzar zai miƙa ragamar komi a hannuna ba, na gaji! na gaji!!! na gajiiiiiiiiiiiii."
Yai maganar da ƙarfi jijiyoyin jikinshi na firfitowa yayin da idanuwanshi suka koma launin jah.
Cikin amo marar daɗin saurare gami da firgitawarta Zuka ya fara magana a suffar dabbah.
"BA DAGA NI BA NE, SU NE SUKA LALATA AIKIN DAGA WAJENSU, YANZU HAKA TASIRINA YA RAUNATA SABODA SUN ƘONANI DA RUWAN KOGIN HUKUNCI, A HALIN YANZU BA ZAN IYA KOMI BA DOLE SAI NA YI JINYA ME TSAWO, SAI DAI KA SA NI BA KOWA NE ZAI IYA IRIN AIKIN DA NA YI MAKA, MUSAMMAN YANZU DA SUKE DA DANGANTAKA DA SARAUNIYA ZUBIDIYYA ƳAR SARKIN RUWA, KUNE KUKA JEFANI A HALIN DA NIKE CIKI YANZU, SABODA HAKA ZAN RABA JINYAR TARE DA KU."
Ya na gama faɗin haka ya huro iska me ƙarfi daga bakinshi zuwa jikin matashin, sai da ya suma dan azaba, ya na suma Zuka ya saka hannunshi ya dafa bayan matashin, nan take wasu abubuwa suka shiga fitowa daga jikin Zuka da ke a suffar Jegare ya na sauka akan bayan matashi.
Bayan ya gama juye ma shi cutar ya tashi ya fice da sama ba tare da ya sake bi takan matashin ba, sai dai ya tattara kayan ya maida a ma'ajiyarsu tare da buɗe ɗakin.
Barci nike ina juyi cike da nishaɗi, sanyi AC da lallausar katifarda aka shimfiɗe akan gadon na sake taimaka wajen saka ni nannauyan barci me cike da nishaɗi, tun bayan da na yi sallar asubahi na koma na sake kwanciya, dan Allah na gani ina mutuwar son yin barcin safe amma sam bana samun damar yi lokacin da nike gida.
Ba ni na farka ba sai wajen sha ɗaya na safe, shima Hajjo ce ta tada ni dan tare muka kwana da ita a ɗakin sai dai kowa gadonshi daban.
Hajjo dattijuwa ce me tsananin kirki da sanin darajar ɗan Adam, sam banyi tunanin samun karɓuwa a wajen mutanen gidan har haka ba, iya jiya kaɗai sun nuna min gata, kulawa gami da godiya akan bajintar da nayi wajen kulawa da lafiyar ɗansu, yanda suke nan nan da ni kaɗai ya tabbatar min da su ɗin na daban ne ko a cikin masu kuɗi, kuma na ji zan iya jure ko wace iri wahala wajen ganin na hidimta musu da gangar jikina, na ɗaura ɗamarar bautata musu ba tare da gajiyawa ba, indai har zasu dawwama su na nuna min kulawa kamar wanda sukai jiya, na taso cikin rashin kulawa a gidanmu, babu me kukawa da ni sai Mama ita kaɗai, to itama wani lokacin ba cikakkiyar lafiyace da ita ba, ina daga cikin mutane masu son kulawa koda ba za'ayi min duka abin da nike so ba matsawar za'a kula da ni to ambiya ni duniya da lahira.....✍️