Chapter 19
CHAPTER 8
بسم الله الرحمن الرحيم
Tashi na yi na shiga toilet ɗin ɗaki wanda ya gaji da haɗuwa, Allah na gani toilet ɗin ya tashi kaina, ƙauyanci ko ba'a magana, sai dai intaɓa nan in taɓɓa can inata jin daɗi, ni kaina nasan banada yawan fara'a bare murmushi, idan kaga murmushi ko dariyata to ina gaban Mama ne muna fira, amma wallahi zuwana gidannan jiya na yi murmushi sau babu adadi, iya kalon kayan ƙawar da aka ƙawata gidan kawai ya isa ya saka ni murmusawa bare kuma yanda aketa ririta ni.
FAUZAN
Tun bayan da muka gama firar dare muka yi ma shi sallama tare da fatan samun lafiya, kallona kawai ya ke, ga amsa kuwar muryata da ke ta faman yi ma shi gizo a kunnuwa, maganata biyu tun da Hajjo ta ja ni zuwa ɗakin, duk da su na ta saka ni a firar amma sam na ƙi sakin jiki inyi firar, ganin yanda fuskokinsu suka washe da fara'a kawai ya isheni farin ciki, ga Mommy da duk motsin da zanyi sai ta tambayeni ko ina buƙatar wani abu ne, ko ta sakar min murmushi tare da yimin godiya, yanda naga su na ji da Fauzan sai abin ya burge ni na ji inama ace nima haka nawa Iyayen sa dangi ke so na.
Fauzan tun da muka tafi ya ke ta tunanina, kuma ya lura idan ina waje to wannan sanyin wanda ke sakar ma shi da kasala ya kuma saka ma shi nutsuwa yana wajen, amma da zarar na tafi sai ya dainajin sanyi, ji ya yi kamar ya tsaida ni duk da ba magana ni ke ma shi ba, amma kuma sai ya kasa yin hakan, ya na ji ya na gani na fice banko waiwayeshi ba.
Bayan na gama ƙauyancin na tara ruwa a baho na tuɓe kayana na afka ciki, wani mugun daɗin ruwan ne ya baibaye ni, aiko na sake nutsewa ina lumshe ido gami da wasa da hannuna da ruwan cike da nishaɗi, na ɗauki tsawon lokaci a haka kafin daga bisani na yi wankan na fito ina zuba ƙamshin turaren wanka, banga towel ba dan haka na maida kayanda na saka na zumbula hijabina na fito.
Sulaima ce zaune a bakin gado su na gaisawa da Hajjo cikin harshen turanci, mamaki ne ya kama ni jin yanda Hajjo ta lamkwashe harshe kamar baturiya ta na zayyano turanci tiryan-tiryan a bakinta.
Jin sallamata ne ya saka su duka suka juyo su na kallona fuskokinsu da murmushi.
"Ƙanwata harkin fito kenan, tun ɗazu na shigo Hajjo ta ce min kin shiga wanka ba ki fito ba."
Sulaima tai maganar ta na tashi tsaye cike da kulawa ta miƙo min jakar hannunta ƴar madaidaiciya me kyau.
"Ih wallahi na shiga wanka ne shi yasa na daɗe ban fito ba."
Na bata amsa tare da miƙa hannu na karmi jakar.
"Kayan da za ki saka ne, kiyi sauri muna jiranki a main parloun zamuyi breack."
Tai maganar ta na duba tsadadiyar agogon diamond ɗin da ke ɗaure bisa tsintsiyar hannunta.
Kallonta na sake yi cike da burgewa, dan Allah ya sa ni ina matuƙar son mace me gayu da ado, shi yasa ko a gida tamu bata zo ɗaya data Umma ba, dan ƙazama ce ta bugawa ajarida, yayinda Mama kuma ta kasance mace me tsananin tsafta, gashidai bata da kayan ƙawa da ada irin na Umma, amma idan ta yi wanka ta caɓa ado kai ka ce ba matar Abba ba ce, dan sam Mama bata yi kala da matar da Abba zai aura ba, kalar matan Alhazawan masu kuɗi ne.
Har na aje jakar nufina inje mu karya sannan in dawo in saka, sai kuma na yi gudun kar ace dokar gidance haka, tun da ƴan gayu ne ƙila sai anyi ado da kwalliya sannan ake zama cin abinci, ɗaukar jakar na yi ina buɗewa sai naga atamfa ce ɗinkakkiya wacce ta sha guga a linke tsaf, fito sa ita na yi dan insaka, ban san lokacin da n doka tsallen murna ba, Allah ya sa ni ina natuƙar son inyi gayu musamman ace sababin kaya na samu, amma ba damar hakan dan Abba bai damu da yimin ɗinki ba daga sheka sai shekara, haka zanga Yaya Sumayya na caɓa ado abinta, ni ko inta sha'awarta ina binta da kallon burgewa, idan na isheta da kallo kuma tayi ta hantarata ta na zagina wai na isheta da kallo sai kace mayya.
Ɗas ɗinkin goduwar rigar ya zauna a jikina, yayinda gaba da bayan rigar ya ci ado da stons masu sheƙi da walwali, wani ƙarin abin burgewa shine atamfar da ɗinkin sun amshi jikina sun zauna ɗass, da ya ke atamfar me ɗan duhu ce sai ta sake fito da ainahin hasken fatata wanda rashin kyara ke barazanar disashewa, ban iya stayle na ɗaurin kallabi ba hakan ya saka na kama gashina na gyara na ɗaure shi da ɗan ƙaramin ribon wanda na siyo a shagon kusa da shagon Abba wanda ni ke tsarewa.
Da kyar na tattare gashin saboda silɓi da tsawonshi sai de bai cika irin yawannan cinkus ba, yafi tsawo sosai amma babu yawa.
Ganin yanda gashin gaban goshina ya kwanta luf ya saka na ɗauki wani mai gaban miro wanda nike tunanin na gashi ne na zuwa a hannuna sannan na shafe goshin nawa, aiko sai gashin ya sake kwanciya ya lafe tare da yin ƙyalli gwanin burgewa, ban shafa komi ba sai iya turare da na malala saboda ina son ƙamshi, sai na shafa lips glow me danƙo wansa ya taimaka wajen fito da ainahin pink lips ɗina, sake ɗauko jakar da Sulaima ta bani na yi na zazzage, saiga mayafi me shara-shara marar nauyi ya faɗo, tare sa takalma plate masu kyau, ɗuka na yi na safa a saman kai tare da gyala shi ta kafaɗata sai na zura takalmin wanda ya zauna a ƙafata ɗas gwanin sha'awa.
Juyi na yi tare da ƙara juyawa ina ganin yanda na yi bala'in kyau, ni kaina nasan yau na yi kyan da ban taɓa yin irinshi ba tun tasowata, wani sassanyan murmushi ne ke fitowa a fuskata na tsananin murna da jin daɗi, yayin da a zuciyata nike ta yiwa su Pahpah da Mommy addu'a dan wallahi na ji daɗi sosai da sosai.
"Ma sha Allah laƙuwwata illabillah, wallahi kinyi azabar kyau Mubeenah."
Sulaima da ban san lokacin da ta shigo ɗakinba na ji ta faɗa gami da takowa inda nike, ban ce komi ba sai murmushi da na yi najin daɗin yabon da tai min, kama hannuna ta yi muka fice tare da haurawa sama mukai wajen dinning ta na ta yaba kyawun da na yi.
Fuskarsu a sake suke kallona yayinda muka isa wajen na zame hannuna daga cikin na Sulaima na tsugunna ina gaidasu a jimlace, cikin kulawa suka amsa min tare da tambaya ya baƙunta, bance moki ba sai murmushi da na yi, wajen Hajjo da aka shimfiɗa ƙaton lallausan carpet, ancija gabanta da kayan kari na nufa, zaunawa na yi tare yi ma ta tata gaisuwar cike da bata girma.
"Hajjo barka da safiya, antashi lafiya, ya gajiya."
"Lafiya ƙalau Mubaraka ya gajiyarki, ai kece da gajiya ƴarnan, sannu jiya kinsha fama da marar lafiya, mun gode sosai Allah yayi albarka."
Hajjo ta faɗi ta na janyo ni zuwa gabanta.
"Hajjo ki kyaleta hakanan ta samu ta karya za ta bawa Yaya Fauzan magani."
Sulaima ta faɗi ta na dire plate ɗin hannunta wanda ta zubo soyayyar doya wacce ta yi caɓa-caɓa da kwai da vegetables da yanyanka ƙanana a cikin kwan, sai ɗaukar ido soyayyar doyar ta ke, ga sous da aka zuba agefe da kechop harda yankaken carbege, yanda aka jere komi a cikin farantin kwanin sha'awa, sai kunun cous-cous wanda ya wadatu da madara sai ƙamshin flavor ya ke, ajiyewa ta yi a gabana sannan ta tashi ta ɗauko tea flask ta ajemin tare da janyo min kwankwanayen kayan tea.
"Bisimillah, ki yi ki ci kar surutun Hajjo ya cika miki ciki."
Sulaima ta faɗi tare da zama itama ta haɗa nata kayan garin.
Murmushi kawai na yi ina hasaso inama ace tare da su Mama zanci wannan kayan alfarmar, duk sai na ji jikina ya yi sanyi, kewar Mama na sake bijiromin ina tunanin yanzu ko mi ta ke yi, ko wane hali take ciki.