Chapter 20
CHAPTER 9
بسم الله الرحمن الرحيم.
Da ƙyar na kawar da tunanin Mama na wajen ya ɗauka da haka har muka gama karyawa a tsanake cikin tsari da burgewa.
Bayan kowa ya gama ne muka ɗunguma zuwa wajen duba jikin Fauzan, sai da kowa ya gama shiga sannan na shiga daga ƙarshe ina ɓuya bayan Hajjo.
Idanuwansa a kulle suke amma jin wannan sanyin me saka ma shi nutsuwa ya saka shi saurin buɗe rinannun idanuwanshi, haƙiƙa wannan sanyi rahama ne a gareshi, wannan sanyi ya na taka muhimmiyar rawa cikin rayuwarshi, sannan bugu da ƙari tun daga jiya bai huta ba koda na second ɗaya daga tunanin tsari da zubin halitar wacce ta taryeshi hannu biyu a matsayin mijin aurenta wanda ya ke a mawuyacin hali, haƙiƙa ya yabawa jarumta, haƙuri gami da tawassali irin nata, a halin da yake ciki yanzu haka shi yasan ba kowa zai so shi ba sai dai aji tausayinshi.
Ɗaya bayan ɗaya suka shiga gaisheshi su na yi ma shi ya jiki, ya na amsa su da kai, da haka har aka zo kaina, yayinda a sanyaye na matsa kusa da shi ina kin wani abu da ba daidai ba a wajen, cikin sanyin murya na buɗe baki na ba tare da na kalleshi ba na ce.
"Barka da safiya, ya ƙarfin jikin, Allah ya bada lafiya."
Bai amsa ba kuma bai daina kallona ba, a hankali na yi niyyar matsawa, amma sai naji saukar hannu me ɗumi ya riƙo nawa hannun, wani irin tsale duka ƙirjina ya yi, yayinda na ɗaga idona ahankali na sauke akan na shi hannun wanda babu komi sai ƙasusuwa da fata, amma sosai na yi mamakin yanda ya riƙe ni da ƙarfi sosai.
"Kai Fauzan cika ma ta hannu manah, baka ganin aikin zuba maka magani za ta yi." Mommy ta faɗi ganin yanda nike ta kiciniyar janye hannuna amma na kasa.
Da wani irin sauri na juya tare da sakin baki galala, ba ni kaɗai ba harsa su Hajjo sun cika da mamakin jin abin da na ji.
"Uhumm, Mommy ina son ɗumin jikinta, pleasw ki ce ma ta karta tafi ta barni."Fauzan ya faɗi cikin wata iriyar haɗaɗiyar murya me daɗin amo, nutsuwa, kamala gami da shagwaɓa duka muryar tasa ta haɗa, nan take na ji wani abu ya tsaga ta cikin jinin jikina, yayinda sautin bugun zuciyata ya sauya ta koma dokawa a hankali cikin sanyi.
Da sauri Mommy ta taso tazo gabana ta kama hannuna tare da matsawa kusa da Fauzan idonta na tsiyayarda hawayen farin ciki ta damƙa hannuna a cikin nashi ta na faɗin.
"My lovely son🥹, indai har zaka samu lafiya ka dawo cikin farin ciki kamar yanda muke a baya, to ga Mubaraka nan na damƙa ma ka ita amana, ka ƙarfafa zuciya da gangar jikinka wajen hana ciwo yin galaba akanka, ga kwarara zuciyarka ta hanyar sakawa wannan baiwar Allar me zuciyar zinare da mafificin alkairi kamar yanda ta sadaukar da farin ciki da ƙuruciyarta ta amince da aurenka sannan ta amince da jinyarka alhalin ko mu da muke makusantanka bamuyi maka wannan sadaukarwar ba, tabar ƴan uwanta da danginta harma da rayuwarda ta saba ta zo cikinmu ta zauna dan kawai ta faranta mana rai ta hanyar kulawa da kai, ga Mubaraka nan na damƙa maka ita ɗin matarka ce kuma amana a wajenka da mu baki ɗaya."
Mommy ba ta ƙarashe faɗin abin da za ta faɗa ba wani irin raunananen kuka ya ci ƙarfinta, wanda hakan ya saka ta ƙanƙame hannuna da nashi wajen ɗaya hawayenta na sauka akan hannuwan namu, Phapha ne ya taso cikin sanyi jiki ya janyeta daga wajen tare da rungumeta ya fice fuskarshi da damuwa, Hajjo ma jan hannun Sulaima da bakinta ya mutu murus dan tsabar murna ta yi suka bar wajen, ficewa sukai suka barni daga ni sai Fauzan wanda ke ƙanƙame da hannuna kamar wani zai kwace ma sa ni.
Cikin sassanyan sauti me taushi na kalleshi tare da falin.
"Ammm,,, ɗan cika min hannu zan haɗa magani."
Na faɗi ina ƙifta manyan idanuwana dan kuka ne ke neman kwace min.
"Ni bazan cika ki ba gaskiya😩."Fauzan ya faɗi a shagwaɓe ya na janyo ni gaba ɗaya, saura kaɗan in faɗa jikinsa amma na hana hakan faruwa ta hanyar dafe ƙasa da hannunawa, fuskata na fuskantar ta shi fuskar wacce tai baƙi saboda maganin da na shafa masa jiya.
Bazan iya banbance halitar fuskarshi ba amma yanayin yanda naga gashin kanshi ya kwanta luf baƙi wuluk sai hakan ya saka nike tunanin ko yayane zai kasance cikin sahum maza ƴan kwalisa.
Sauke fararena na yi a cikin nasa, wani irin abu me ƙarfi ne ya ke haɗuwa a cikin idanuwanmu, saurin sauke kaina ƙasa ƙirjina na luguden duka.
Zare jikina na yi na ja baya tare da tashi cikin rashin kwarin jiki, tashi na yi tare da zuwa wajenda aka ajiye waɗannan ledojin da baƙin jiya suka kawo jayan dubiya, raɗau nike ganin shatin yatsun wanda ya riƙe ledar na fitar da baƙin hayaƙi, sannan wani irin wari marar daɗi na tashi, gabana na faɗuwa haka na buɗe ledar ina leƙen abin da ke ciki, sai naga kayan fruit ne wasu duk sun ruɓe wasu kuma nunanun sai walƙiya suke da ɗaukar ido, waɗanda suka ruɓe kuma sai wari suke fitarwa tare da wannan baƙin hayaki, saurin ɗaukar ledar na yi na fitar da ita daga ɗakin, a bakin ƙofa na ajiye ta ina jin tsikar jikina na tashi, juyowa na yi na koma ɗakin sai naji yanzu yamin daidai, ajiyar zuciya na sauke sannan na shiga gyara ɗakin duk da ba wani datti yai ba, kuma yau da sauƙin ƙarnin ba kamar jiya ba, bayan na gama na koma wajen Fauzan ɗauke da ruwan magani wanda Phapha ya bani akan agoge ma shi jiki da shi, ruwa na haɗa masu sanyi sannan na ɗauki tsaftatacen towel fari ƙar na saka a cikin ruwan maganin, ba tare da na ce da shi komi ba na matsa kusa da shi na fara aikina, idonshi ƙur a kaina ya na kallona kamar wanda zai haddace kamanin fuskata, bayan na gama goge ma shi fuska da hannuwa na koma kan wuyanshi zuwa cikinshi, duk inda na ɗaura towel ɗin sai wajen ya kwalje amma banji komi ba haka na ci gaba sa goge ma shi jiki, yau ba kamar jiya ba dan yau ko ina sai da na goge ma shi a jikinshi da maganin sannan na na barbaɗa wanda na barbaɗa ma shi jiya, abin gwanin ban tausayi dan kuda fatar jikinshi ta saɓule tai jajir, ban gaji ba na sake kaɗa ma shi na sha, nai bisimilla tare da kaina saikin bakinshi, kamar me jira haka ya buɗe bakin na shiga zuba ma shi maganin, sai da ya shanye tas sannan ya lumshe ido, ina tsaka da tattare kayan wajen zan tashi naji ya riƙo hannuna da ƙarfi, kafin inyi wani yunƙuri tuni ya shiga kelaya amai kamar dai jiya, sai dai na yau harda jini da wani abu kamar saɓa, duk dauriyata sai da nai kuka dan ba kaɗanba ya bani tausayi, a hankali na dafa kafaɗarshi gudun kar in fama ma shi ƙunar na samu na kwantar da kanshi akan pillow sannan na zare hannuna ina jera ma shi sannu, lumshe ido kawai ya yi tare da sake min hannu, a hankali na tashi daga wajen tare da kwashe kayan sannan na gyara wajen tsaf, bayan na gama ne na koma gefe na rakuɓe nai shiru ina tunanin duniya da irin ƙalubalen da ke cikinta, haka wani kalar nannauyan barci yai gaba da ni.
Sarauniya Zubudiyya ce zaune akan bango ta na kallon dukanin abin da muke yi, yayinda tausayina da na Fauzan ya sake kamata, ita ɗin hallita ce me tsananin tausayi, sam bata son zalinci kuma bata shiri da duk wani me aikatashi, daga inda take ta na ganin inda Zuka yayi ajiya a jikin Fauzan, wanda hakan ke taimakawa wajen sake tsananta ciwon na shi, daga inda take zaune ta ziro hannu ta tattaro ajiyar kakaf, hakan yayi daidai da lokacinda na bashi maganin sha, shine ya amayar da sukanin ajiyar, sai ya ji wasai cikin cikinshi kamar an ɗauke ma shi wani nannauyan dutse, cikin sanyin da ta saka min ta huro ma shi iska wace ta saka shi barcin rahama da salama.
ABUJA NG.
MAITAMA.
Tsaye ya ke agaban makeken frem ɗin da ke ɗauke da hotunan kyawawan ƴan mata guda biyu masu tsananin kama, babbar ba zata wuce shekaru huɗu ba alokacin da akai hoton, ɗayar kuma jinjirace fara sol kyakkyawar gaske.
Idonshi na zubda ruwan hawaye ya ke kewaye daidai fuskar jinjirar ya na shafawa.
Wa ta kyakkyawar ma ta ce me kama da laraba ta shigo ɗakin inda mutumin ya ke, taɗan jima a bayanshi ta na kallonshi, fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa irin wacce tafi ƙarfin a bayyanata a baki, tabbas ta na cikin matsananciyar damuwa, amma hakan bai hana ta yi tawassali da Allah ba, domin tasan dukan abin da ya samu bawa to yana rubuce a jikin littafin ƙaddararsa, kuma babu me gujewa ƙaddara face ta biyo shi da mugun gudu, irin gudun da idan har ta cimma masa to kuwa sai ta Allah kawai, ita ɗin mahaifiyace kuma me rauni, akwai raunin da yakai a raɓa uwa da ƴarta tun bata gama tantance iskar duniya ba, akwai raunin da yakai a raba uwa da ƴarta lokacinda ta gama wahalar shayarwa da reno, ita tasan me rauni ce gaba da baya, amma batabawa zuciyarta damar raunana har ta kaita ga samun matsala ba, ta riga da ta dangana, ta bar komi a wajen Allah, mudin rana na fitowa ta na faɗuwa tasan wannan ranar za ta zo, ranar da duk wani ƙulli zai warware kansa da ƙarfin ƙudurar ubangiji, ko da bata raye tasan ta yi babban tanadin zuwan wannan ranar, abu ɗaya kawai take jira, shine wanzuwar ikon ubangiji ta hanyar bankaɗo duk wa ta ajiya da aka bizne a cikin baƙin duhu.
Cike da ƙwarin gwuiwa ta taka zuwa inda mutumin yake tsaye ya na ta faman sharɓar kuka tare da shafar fuskokin jikin photon.
"Bansan har zuwa yaushe gwarzon jarumina zai yi tawassali da ƙadararda ta daɗe da yanke wannan damɓarariyar ƙaunarba, ha isa hakan, ya isa!! yanzu ba lokacin yin kuka ko nuna damuwa bane akan zarenda ƙaddara ta daɗe da yankewa ba, yanzu lokacin farin ciki ne da nuna godiya ga Allah da akan manya-manyan kyaututtukan da ya bamu, zo muje muyi tafiyar da za ta sada mu da farin ciki madawwani wanda bazai yanke ba da izinin Ubangiji."
Ta ƙarashe maganar ta na janyo hannuwanshi duka biyu kamar ƙaramin yaro me koyon tafiya, haka ta dinga janshi ta na tafiya da baya-baya harta cimma ƙofar wani ɗaki, buɗe ƙofar ta yi da ƙafarta sannan ta shiga har lokacin bata saki hannuwanshi ba, a gaban baby bed guda biyu ta tsaya tare da dafo kafaɗunshi ta juyar da fuskarshi ta na faɗin.
"Yanzu lokacin farin ciki da godiyar Allah ne da ya azurta mu da wannan gagarumar kyautar wacce muka daɗe muna jira, ga makwafin yaranmu da muka rasa Allah ya dawo manah da su, MUBARAKA da MARYAM sun dawo gare mu, kallah!!! kallafa!, kalesu Alhaji."
Ta yi maganar ta na ɗago da jariran yaran ɗaya bayan ɗaya ta na nuna ma shi, fuskarta faɗaɗe da yalwatacen farin ciki, wanda ya kasance na gidoya ga Allah da ya ake azurtata da ƴaƴa mata waɗanda ta ke fatan su kasance ma ta sanyin idaniya, kuma su mamaye wawakeken ramin da ke zuciyarta na rashin ƴaƴanta da ta yi, waɗanda ba mutuwa sukai ba, kawai ƙaddarace da jarabawa ta Ubangiji ta nesanta tsakaninsu.