Chapter 1
by @aisha2310
✨✨ Rasheedah✨✨
By
A'ishah Abdulkareem
Bismillahirrahmanirrahim
Page 1️⃣
Misalin karfe hudu na yammaci garin yayi sanyi saboda ruwan sama daya doki ƙasa ga iska Mai dadi dayake kadawa wani dattijo ne dazai haura shekaru hamsi yake kokari shigar da mashin dinsa cikin zauren gidansa dawowarsa daga kasuwa kenan wani matashin yaro ne ya shigo da sauri yana kwalawa mahaifiyarsa Kira tun daga bakin kofar gidan
Inna! Inna!!
Matashin yaron bai kula da wanda ke cikin zauren ba dattijon dake kokarin gyara parking din mashin ɗinsa yatare hanzarinsa dacewa lafiya kabiru mai ya faru kashigo kana kiran innan ku haka sai sannan ya dubi dattijon yace sannu dawowa baba Saida ya jingina da mashin din kafin yace lafiya kalau menene yake faruwa kabiru yasosa ƙyeyarsa kafin ya hado abinda zai fadamasa saboda yasan halin mahaifin su bakowacce maganace ake fiskantar sa dashi ba baba yasake dubansa yace Ina tambayarka kamini shiru sai sannan ya fara kame-kamen cewa uhmm uhmm baba dama "Rasheeda" ne naganta.....bai karasa Fadi ba sai ga mahaifiyar tasa dayake ƙira yayin shigowar sa wato (Inna) tashigo zauren tare da katseshi dafadin Ina ruwanka da ita kabiru bana hanaka shiga abinda bai shafe kaba amman tsabar baka daukar magana ta da mahimmanci saida ka cigaba da shishshigewa rashidan nan bane tacigaba dacewa nasan bazai wuce dalilin ta bane yasa ka birkita kanka kake kwaɗamin ƙira tun daga ƙofa mai zaka faɗamin wanda bansani ba ina ruwana da abin datake yi a waje dazakazo ka faɗamin gani uwarta ko
Ko kallon ta dattijon da kabirun ya kira da baba baiyi ba yace Ina Rasheedan take kabiru yace naganta a kwanar layin su ladi mai markade ita da su barna umurni dattijon ya bashi daya kirata kabiru na fita baba ya cire hular sa daya sanyawa leda saboda ɗan yayyafin da ake dazu Inna ce tace malam sannu da dawowa sai lokacin ya kalleta yace aww sai yanzu kikaganni bayan kin gama shiga tsakani ƴan uwa nide kullum Ina fadamuku ku zaiyiwa ciwo wata rana gyara dauri zaninta tayi dauri kirjin ne da ita tace malam yabazan shiga tsakanin suba Kai kasan rashinjin ta ƴan waje ma kokarin raba 'ya'yansu suke da ita haka kawai taje tabatamin yaro tabarni da kunci.
Ɗayar matar gidan ne wanda yaran gidan ke kira da Mama datun dazu tazo take tsaye a baƙin ƙofar zauren bayan taji bararan da Inna takewa kabiru batasa musu baki ba tace to Allah ya kyauta tashige cikin gidan malam bai tankawa inna ba ya daura hularsa saman mashin ɗinsa tareda taukar daron dayake sawa tunkiyarsa abinci ya shiga cikin gidan yabarta tsaye itama shigowar tayi Tana hura hanci saboda Bata samu damar zazzage abinda ke bakin taba.
Wannan shine "GIDAN MALAM HAMISU KAMALUDDEEN"
Dake garin Gombe cikin unguwar nasarawo madaidaicin Gida ne gini bulok dake dauke da ɗakuna ciki da falo guda biyu da Kuma ɗakuna falle guda uku sai madafi da Kuma bandaki ɗaya da madaidaicin tsakar gida ga babban zaure mai ɗauke da dakuna har biyu malam Hamisu haifefen jihar Gombe ne cikin garin dukku local government iyayensu Fulanin dukku ne su goma iyayensu suka haifa maza takwas mata biyu malam hamisu shine na biyar a gidan su a yanzu haka shine babba acikin ƴaƴan mahaifinsu yayyunsa maza uku Kabiru, Usmanu da Buhari duk sun rasu daman addarsu babba Khadijah tun tana budurwa ta rasu yanzu su shida suka rage shi hamisu da imamu, ɗalhatu, Nasiru, Hannatu da kuma autansu yahya mahaifinsu malam hamisu wato malam kamalu ya kasance manomin rani da damina matarsa ɗaya har ya bar duniya wato mahaifiyarsu malam hamisu mai suna Ramatu wanda suke kira da yelwa wanda a yanzu bata duniyar shekara ɗaya da rasuwar ta kenan.
Malam hamisu yakasance mai sana'ar awun hatsi a babbar kasuwar Gombe wanda ya farone asali ne daga tushen su wato dukku wanda ada yakan noma hatsinsa ne duk ranar kasuwar dukku yake fiddawa yana siyarwa wanda daga baya ya fara kawowa cikin Gombe ranar da take cin kasuwa daga haka harkokinsa suka kara bunkasa harya kan siya hatsin a wajen abokansa manoma ya shigo dashi gombe wanda takaishi ga kafa rufa a kasuwar dalilin da yasa ya nemi shawarar iyayensa yanason ya siya fili a Gombe ya fara ginin gidansa saboda a lokacin sana'ar sa tafi ƙarfin a Gomben suka amince masa yayi aurensa na fari a dukku kafin daga baya ya tattaru yadawo gombe bayan rasuwar mahaifinsu saboda kasuwar tafi karfi anan matarsa ta farko wato uwargidansa itace inna sunanta Aminatu asalinta bafulatanar dukku ce wanda sukayi auren saurayi da budurwa da malam Hamisu itama yar asalin dukkun ce sai kuma matarsa ta biyu mai suna shafa'atu wanda yara ke kiran da mama ita kuma yar Gombe ne bayan dawowarsa nan da zama ya auro ta suna zaune lafiya da Inna a zahiri kafin ya auro shafa'atu Innaa bata taɓa samun haihuwa ba wanda sunyi shekara biyar da aure kenan sai bayan auro mama suka samu ciki a lokaci guda zokaga murna wajen dangisu daga lokacin haihuwar tabuɗewa malam hamisu daga nan kuma suka fara gasar haihuwa Inna ta haifi 'ya'ya biyar maza biyu da mata uku Kamaluddeen shine babban ɗanta suna kiransa da yaya Abba sai mai binsa Khajida suna kiranta da Adda Nana tayi aure a cikin garin dukku yaranta biyu yanzu sai hindatu da hannatu sune yan mata a gabanta yanzu sai auta Kabiru wanda ita anan haihuwa ta tsaya mata sai mama mai 'ya'ya shida maza hudu mata biyu Haruna shine babban sai Nasiru mai binsa sai Bashir daga shi sai Ramatu ana kiranta da Ummi sai suwaiba da kuma autan ta salihu suna kiransa da Ammar.
Fasalin Cikin gidan yakasance ciki da falo na Inna ne da mama sai dakin malam hamisu falle ɗaya sai fallen ɗakuna biyun Kuma na yara matane a yanzu Wanda ada ɗaya daga ciki yakasance ɗakin mahaifiyar su mlm ce da yadaukota bayan jinya yacim mata tasha doguwar jinya har Allah ya karbi rayuwarta sa'anan akwai rumfa a gaban dakunan su mama gefen hanyar bandaki Kuma mlm ya kewaye shine Dan kiwon dabbobin sa yakasance ma'bocin son Noma da kiwo Amma kamar kiwon Bata karɓe shi ba Dan yanzu tunkiya dayace ta rage masa yana nomansa na hatsi har yanzu a damina amma tayi sanyi ba kamar daba sannan sai dakunan dake cikin zauren guda biyu na yara maza ne wa 'yanda suka tasa.
Malam hamisu yakasance yanada sauƙin hali ga sanyi sanyi a lamarinsa ga rashin baya sakewa da mutane hatta 'ya'yansa baya sakewa dasu gashi bai cika tsawatarwa yaransa ba sai abu ya tsananta tukuna zakaga yayi magana akai sai ya zamana yaya Abba shine mai tsawatarwa a gida gaba daya yaran gida suna tsoronsa saboda shi yanada zafi mai sunansa ya gado wato kakansu malam kamalu shima haka yake malam hamisu mutum ne mai rufin a asiri da zuciyar yi duk da a yanzu kasuwar tayi sanyi ga gidansa yasake nauyi Amman yana kokari saboda a gidansa ba a rasa ci da sha ƴaƴansa duk suna zuwa boko na gomnati da islamiyya.
Gidan malam hamisu kenan da tushesu a takaice.......✍️