ZAFIN WUTA

Chapter 23

by @maryamstar248

Version:1.0 StartHTML:0000000156 EndHTML:0000079613 StartFragment:0000000469 EndFragment:0000079605

 

         CHAPTER 12 

بسم الله الرحمن الرحيم. 

 

 

Ta na ganin dishi-dishi haka ta miƙe ta saɓi mayafinta da carkey ta fice zuwa parking lot ta ɗauki motarta ta fice da mugun gudu ta na sharɓar kuka, ga fuskarta kaca-kaca da jini, sai da tai gudu sosai ta tabbatar da ta fita daga garin Abuja sannan ta nemi waje tai parking tare da kwanciya ta baya akan kujerar. 

 

 

 

 

SADIYA 

Tsaye ta ke ta na bawa masu aiki umurnin yanda zasu shirya abinci, fuskarta gwanin kyau domin kuwa kwalliya ta caɓa kamar me shirin zuwa gasar ado da kwalliya, ta na gama sallamarsu ta fice zuwa main parloun inda ya ke cike da baƙi ƴan barka da taya murnan sake samun rabo bayan tsawon shekaru da ta kwashe bata sake haihuwa ba. 

 

      "Ai Sadiya baiwar Allah ce, ga kirki da tawassalin ɗaukar ƙaddara, yo idan wa ta ce aka sacewa ƴaƴa har karo biyu ai ba zata sake zama da mijinba, musamman yanda ake ta raɗe-raɗe akan wai shike sadaukar da ƴaƴanshi ga dodon tsafi." Wa ta dattijuwar mata ta faɗa cike da gulma, yayinda wace ke kusa da ita itama ta caɓe da faɗi. 

 

     "Ai babu wai, yo ai daganin wannan farin jini da tarin dukiyar ta Alhaji Umar ku kunsan ba banza ba, a yanda ake faɗi fa yanzu shine na bakwai a jerin ƴan kasuwa masu kuɗin Nigeria." 

 

 Sallamar Sadiya wace ta rigada taji dukan firar da suke, ita ta katse Iya Laraba daga zancen ƙanzon kuregen da ta ke, sai kuma tahau burin kunya gami da ƙaƙalo fara'ar dole ta yaɓa akan fuskarta. 

 

      "Kaga Halimatus Sadiya uwar gida me pacasity a gidan Alhaji Ummaru sarkin ƴan kasuwa, yau dai Allah ya nufa bayan tsawon shekaru ashirin kin sake ganin kwanki a duniya, ni  Balaraba ina tayaki murna, Allah ya rasa akan sunnar Ma'aiki." 

 

Murmushi kawai  Hajiya Sadiya ta yi, fuskarta babu alamun komi ta gabatar musu da lemo kafin abinci ya sauka, babu kunya suka naɗe lemon a jaka, su na faɗin sayiwa yara guzuri da shi, da yake Baba Laraba ƴar uwar Sadiya ce kuma anan ƙauyen abuja take da zama itada mijinta, sanin halin Alhaji Umar na son baƙi da talakawa ya saka bata kwashe wata guda cir ba tare da tazo gidan ba, idan ta tashi zuwa haka za ta ɗibo gayyar mutanen arziki ta taho da su dan samun abin duniya, dayake karamci a jinin Alhaji Umar ya ke, hakanan yake zagewa ya saki bakin aljihu yayiwa Baba Laraba da tawagarta kyauta ta bajinta da ban girma. 

 

A wunin ranar haka Sadiya taita karmar baƙuncin ƴan uwa da abokan arziƙi, musamman matan abokan kasuwancin Alhaji Umar da ƴan siyasa, yara kuma sunsha kyaututuka sosai a wajen ƴan barka, sai dare Sadiya ta samu kanta, ta je ɗakin barcinsu ta taradda Alhaji Umar na sana'ar ta shi wato tunani, idan ta kalleshi sai zuciyarta ta tsinke saboda yanda ya zama abin tausayi, yayi wani sukuku da shi kamar marar laka a jiki, har yanzu Sadiya bata saba da wannan yanayin  nashi ba, ta lura yanzu abin na shi gaba yake sake yi, domin kuwa kullum sai ta lura da wani sabon canji a tare da shi, yanzu bai damu da yayi komi da kanshi ba sai shiga toilet, da kuma zuwa gaban photon yaransu da suka rasa yai tsaye ya na kallonsu ya na kuka, alamomi da yawa a bayyane suke waɗanda  daga gani tasan ba lafiyar mijinta lauba. 

 

         Kife kanta tayi a kan gado wani irin kuka na rashin mafina na kwace ma ta, sai da tai kuka sosai kamar ranta zai fice, naman ƙasan idonta yai jajur, su kansu idanuwan na ta sun kaɗa sun koma launin jah, sai ta ke jin kamar abin ya mata nauyi ba zata iya ɗauka ita kaɗai ba, da gaskiyar Malam da yace akwai rikitattun al'amuura da zasu fuskato rayuwarta masu kama da ZAFIN WUTA, wanda suk juriyarta ba zata taɓa iya jure su ba, dole ne za ta nemi taimako, abin da ta ke yiwa kallon shirka da kanta za ta nemi a aimaka ma ta da shi, ba zata taɓa mance kaifafa maganganun da ya watsa ma ta ba kafin ya tattare kayanshi yai tafiyarshi. 

 

      Zumbur ta tashi kamar wacce aka zabura, sai kuma ta shiga laluben wayarta, bayan ta ganta a saman pillow sai ta shiga neman number da ta ɗauki shekaru ta na dannawa delete amma ta saka gogewa, saboda batasan mi gobe za ta haifar  ba, da ace ta goge number da tashin hankalin da zata shiga sai ya ninka wanda take ciki. 

      Gabanta ne ya shiga luguden suka, wa ta iriyar kunya ta baibayeta, sai ta ji duk ta muzanta, ita ta koreshi daga rayuwarta, kuma itace ta nemoshi kamar yanda ya ce zata nemeshi idan al'amurra suka rikice, wa ta iriyar hantsalowa zuciyarta ta yi kamar zata faso ƙirjinta ta fito lokacin da ta cinkayi sallama daga muryarshi, ba zata iya fasalta halin da take ciki ba, sai cintar kanta da ta yi tana faɗin. 

 

     "Malam!!! Malmam,, Malam na sare, ƙarfina ya ƙare, zuciyata ta karaya bazan iya ɗaukar komi ni kaɗaiba, ina buƙtarka a kusa da ni, ina buƙatar  taimakonka atare da ni, bazan iya ɗaukar nauyin ba, na raunana yanzu na yi rauni zuciyata ta karaya, badan ni ba badan halayyata ba ka taimaka ta dawo, na yi imani da Allah kaima na yi imani da maganganun da ka gaya min a baya, tabbas wa ta jarabtar ba lallai mutum ya iya jureta ba duk kuwa ƙarfin imani da zuciyarsa, na haɗa ka da girman Allah Malam."  

Kukan da take riƙewa ne ya kwace ma ta ya shiga rero kanshi, yayinda acan ɗayan ɓangaren Malam ya yi shiru ya na sauraren kalamanta, sai wani murmushi ya kwace ma shi, yasani ba zata iya ɗauka ita kaɗai ba, abin yayi  ma ta yawa, ko a bayama yaga mugun ƙoƙarinta, kuma ya yaba ma ta, ya jinjina da irin ƙarfin da zuciyar mace take da shi, sai ya sauke numfashi yana jin kukanta na ratsa kunnuwanshi, a hankali cike d rarrashi ya ce. 

 

      "Haƙiƙa kinyi namijin ƙoƙari, na yaba da ƙoƙarinki Halimatu, kin neme ni da kanki bayan tsawon lokaci, ki saka a ranki matsalolinki zasu fara warwarewa tun daga tushen da aka soma gina su, komi ya zo ƙarshe, yanzu yaƙin namu ne, kuma da izinin Ubangiji mune da  nasara, zamuyi nasara akan mugaye kuma azzaluman mutane, waɗanda suke azabtar da ruhin ƴan uwansu da ZAFIN WUTA, zan zo gare ki Halimatu.".