Hs 30
by @legendspen
_Page 30_
"Okay to shi ke nan." Daga haka Bhatool ta kashe wayar, ta kira Jannah daga nan ta kira Suhaima, ranta a ɓace da Jannah, wai dan ta ce mata zasu tafI Dubai shine zata ce wai ta dinga riƙw sirrinta, to me take nufi da ita Mahaukaciya ko me?, Haka Bhatool tayi ta mita yinin ranar. Sai can yamma ta sake kiran Amrah, bayan sun gaisa ne ta ce. Wai Amrah kin san me?."
"Sai ki! faɗa Bhatool."
"Hhm, wai ni Janna zata ce na dinga riƙe sirrina."
"Banganeba, wane sirri?." Amrah ta tambaya. "Daga na ce mata zamu tafi Dubai, na ce mata na faɗamiki zan faɗawa Suhaima shine wai na riƙe sirrina."
"To me take nufi dan ubanta, mu munafukai ne ko me?." Amrah ta faɗa a fusace. "Oho ita ta sani."
"Ke Nifa daman tun a biki naga kamar tana baƙin ciki, mussaman da ta yi saurayi cikin abokan Senate, sa ta wani kame gefe." Amrah ta faɗa. "Ita ta sani, ni dai ta yi da 'yar halak wallahi." Bhatool ta faɗa, daha nan ta yi alƙwarin ba zata sake faɗawa Jannah abinda ya shafe ta ba tun da haka take, Amrah kuma ta yi ta famfata.
Haka Rayuwa ta fara tafiyarwa Bhatool da Senate, kullum cikin sabuwar soyayya, kullum cikin sabuwar shaƙuwa. Da ka taɓa Senate zai ce Bhatool, daka ta ɓa Bhatool za ta ce Senate ko da yaushe suna tare cikin gida, yau su yi hirar can gobe su yi ta can. Girki da aikin gida komai tare suke, yana taya ta yana mata hira, a kowacce ranar da sabuwar soyayya suke ƙara ta shi, kowa yana nisa cikin zuciyar ɗan uwansa.
"Yau tun safe Senate yake ta faman yi wa Bhatool tambayoyi game da rayuwarta, ya tambayeta can, ya tambayeta can.
"To amma ranar da kika fara gani na me kika ji?." Miƙewa ta yi sanan ta ce. "Bara na fara duba abinci na dawo?."
"To ɗagoni mu ta shi." Ya faɗa yana miƙo mata hannu, kama hannu ta yi ta ja amma kamar ba ta ja ba. "Kaga kawai ka tashi, ba zaka ƙarar mun da ƙarfina ba." Dariya ya yi sanan ya ce. "Ki ɗagani dan Allah."
"Hannu ta kai ta ƙara ja, amma me makon ya tashi sai ita ta faɗo kansa, dariya ya yi sanan ya ce. "Zauna ni zan duba."
"Ai baka isa ba, ka je ka ƙara zamɓaɗa mana maggi kaman jiya."
"Allah ni zan duba." Ya faɗa yana ta shi ya fice, miƙewa ta yi ta bi bayanshi tana faɗin. "Allah ka tsaya na duba, bazaka lalatamun abinci ba." A cikin kitchen ɗin ta tarar da shi yana buɗe tukunyar, tsayawa ta yi ya buɗe ya jujuya sanan ya ce. "Ta dawo."
"Mugani." Ta faɗa tana ƙarasawa kusa da girkin. "Wanan ne ya dahu?." Ta faɗa tana karewa abincin kallon. "Ni to yunwa nake ji." Ya faɗa fuskarshi a shagwaɓe. "Duk yunwanka ai bazaka ci ɗanye ba."
Ficewa ya yi ya koma falo ita kuma ta rage gas ɗin sanan ta dawo falon, lokacin yana zaune yana danna waya, zama ta yi sanan ta ce. "Mun fara noticing kana bibiyamun a garden, amma Amrah ta ce muja steez ɗin mu kar muje bamu kake bibiya ba." Dariya ya yi sanan ya ce. "To kinji so a kallo ɗaya da ake faɗa?."
"Ni banji ba, kawai dai kyanka ya ɗauki hankalina."
"Ni kuma kin san me?." Girgixa kai ta yi, shi kuma ya ɗora da cewa. "Tun da na shiga gate ɗin makarantarku na ji, heart beat ɗina ya sauya, yana yi da wani ƙarfi abun har tsoro yabani fa."
"Tsoro kuma?." Ta tambayeshi. "Eyh tsoro." Ya faɗa yana gyaɗa kai sanan ya ɗora da cewa. "Na dawo gida na faɗawa Mom, na ce i'm scared, su Anas su ka ce Aljanna na gani, and kinsan me ya ƙara ban tsoro?." Girgiza kai ta yi, shi kuma ya ce. "The Next day, na fito daga gym kawai na ji heart beat ɗina ya ƙara sauyawa, direct na fito sai kawai na ganki kin shiga gidan Yaya Karima, i was like ko dai aljanna ɗin ce?." Dariya Bhatool ta yi mussaman yanayin da ya yi magana kamar yanzu yake jin tsoron. "Dagaske fa Bhatool, son ki ya wahalal da zuciyana wallahi, fatana kawai ki yi ta sona har abada kamar yadda nake fata nima."
"Zan soka Senate, zan so ka so na har abada, zan rayu da sonka ina fatan na mutu da sonka." Rungumo ta ya yi jikinsa sanan ya ce. "Ina alfahari da saninki, ina alfahari dake a matsayin matata, ina godiya sosai da soyayyarki gareni Bhatool." Sun ɗauki lokaci tare suma bayyana soyayya ga junansu kafin ƙaurin da ya fito daga kitchen ya katse musu daddaɗan yanayin dasuke ciki, ita ta tashi ta shiga kitchen ɗin bayan 'yan mintuna ƙalilan ta fito da abinci ta kai kan dinning suka fara ci.
~~~~~~~~Nyan'ya.
Hayaniyarsu Ɗan-ladi da ta Gaggo Larai ce ta karaɗe gidansu Bhatool. "Wallahi tun da yaran nan sunce nan zasu zauna, Larai sai an bar su." Iliyasu ya faɗa, dan shi yana ganin 'yarsa ta hau matakin da zata sami miji mai kuɗi, haka ma Ɗan-ladi, amma Goggo Larai ra fitike akan sai sun dawo, su kansu yaran sun ce babu inda zasu. "Ni fa ki gama abinki babu inda zani, a yanzu nakai matakin samun Addmission a kwalleji, zan zama 'ya kamar kowa shine zaki ce na baki?."
"To Fure ki sani dai ubanki ba zai iya biya miki kuɗin karatu ba, tun da dai kinsan karatun akwai kashe kuɗi mahaifinki kuma faƙirin talaka ne." Goggo Larai ta faɗa, shi kan shi Iliyasu jikinsa ya yi sanyi da yaji ancw karatu. "ai mijin Karima ya ce zai dauki nauyin karatunmu shi da Abdul." Habi ta faɗa. "Kunyi baƙar asara, kwalamammu." Goggo larai ta faɗa, tana bakim ciki da wanan abun ita a kullum burinta ta ga 'ya'yan Ahamd a hulakance sai ga shi yau za a ce albarkacinsu 'ya'yan 'yan uwanta zasu ci.
Umma dai na zaune ba ta tanka ba, ita dai Furee da Hari ba ta da matsala da zamansu kuma idan za'abar mata su tana so, amma fa bazata buɗe baki ta ce abarsu ba, duk yadda suka yanke tsakaninsu sun fi kusa. "Ɗan-ladi, kuzo mu shawarta." Goggo Larai ta faɗa, ba musu suka bita suka yi waje. "Kunga yaranan sun fara samun abun arziƙi, a yanzu haka suna da sanari a hannu idan muka barsu nan wallahi komai aka kawo ita zasu bawa, mu muna can ɓasho, ko mazajen nasu ma sai sun fi ganin mutuncinta a kan mu, idan ko muka karɓesu komai mu za a kawo wa."
"Da ɗan gaskiyya fa a maganarki Larai." Iliyasu ya faɗa. "Nima na fara ganin haske fa." Ɗan-ladi shima ya faɗa. "To kumga mu ɗauke su, bakwa ganin ita munafukar ta yi shiru ƙus ta barmu muci kanmu." Goggo larai ta sake faɗa. "Nima duk shine haushina." Daga haka suka yanke shawarar ɗaukan 'ya'yansu su tafi.
"Gaskiyya yanzu mun yanke shwarar tafiyar da yaran mu." Ɗan-ladi ya faɗa. "Haba Baba Ɗan-ladi, dan Allah ku barmu mu zauna mu yi karatun nan." Furee ta faɗa, kamar zatayi kuka. "Harira, Furaira." Umma ta kira sunansu. "Na'am." Suka amsa a tare. "Tun da sum takura sai kun koma to kawai ku koma ɗin, idan da rabon karatun naku sai ku yi, zan yi magana da shi Mijin Karima sai ɗauki nauyin karatun naku." Kuka su ka fara, amma Umma ta fara ba su haƙuri har suka haɗa kayansu suka bi iyayensu.
~~~~~~~~New bra bra.
Zaune suke kan dinning suna ci abinci, cike da soyayya senate ya bata a baki, itama ta ba shi a baki. Suna taɓa hirar sama-sama. "Bhatool." Ya kira sunanta. "Na'am." ta faɗa. "Kinsan ina son sunan fiye da komai?." Murmushi ta yi sanan ta ce. "Sunan yafi daɗi a bakinka fiye da bakin kowa."
"Daman ai bazaiyi daɗi ko ina ba, sai bakin mallakinshi."
"Bhatool, wallahi ina sonki."
"Wallahi nima ina sonka mijina." Ƙarar kiran waya ne ya katse musu hirar ta su, ɗauka tai ta duba taga sunan Amrah. "Hello Amrah." Ta faɗa bayan ta ɗaga wayar. "Na'am Bhatool, ya gida?."
"Alhamdulillah Amrah, ya makaranta."
"Lafiya kalau, yau zan shigo daga schll."
"Okay, ke da Jannah?."
"A'a ai Jannah bata shigo ba ma."
"Okay Allah ya kawo ki."
"Amin na gode."
Bayan ta sauke wayar ne ta ce. "Amrah ce zata zo."
"Yau?." Ya tambaya. "Eyh, daga makaranta."
"Okay, Allah ya kawo ta lafiya."
"Amin ya Allah." Ta faɗa tare da ci gaba da cin abincin. "Kin san wanan ƙawar taki Jannah, tana da saurayi ne?."
"A'a, wani dai cikin abokan ya ce yana sonta ko?." Bhatool ta ba shi amsa. "Eyh, ya dage fa dagaske a yanzu so yake ya tura iyayensa aje ayi magana fa."
"Kai Ma sha Allah! Am so happy, Allah ya tabbatar mana da alheri." Bhatool ta faɗa a fili, a ranta kam tana mamakin yadda Jannah ta ɓoye mata komai.
Bayan sun kammala cin abincin ne ya fara shiri zai fita. "Wai ina zaka?."
"Zanje wajen Mom, sanan zanje wajen abokaina." Haɗe fuska ta yi sanan ta ce. "Ka fara zuwa wajen abokan naka, daga nan sai kaje wajen Mom nasan ita ba zata barka ka yi dare ba, su kam babu ruwansu." Dariya ya yi sanan ya ce. "Ko ina naje ba zanyi dare ba, in sha Allah."
"Allah yayarda." Ta faɗa tare da tashi ta rakashi zuwa waje, ɗaya cikin tsadaddun motocin dake harabar gidan ya shiga ya fice, ita kuma ta dawo cikin gida.
Tana zaune falo tana kallon TV, gaba ɗaya gidan ya yi mata faɗi sabida babu senate a cikin gidan, so take ma ta zaga cikin gidan amma ta kasa. Wayarta ce ta fara ƙara alamun kira na shigowa, ɗagawa ta yi tare da faɗin. "Amrah kin ƙaraso ne?."
"Eyh, na ƙaraso Bhatool."
"Okay ina zuwa." Bhatool ta faɗa tare da tashi, wani abu ta danna ya yi ƙara; ƙarar da ta sanar da mai gadin cewar tasan da zuwan mutumin dake waje. Ƴan mintuna kaɗan Amrah ta sake knocking ƙofar falon. "A buɗe take shigo." Bhatooɗ ta faɗa. "Kai ni wanan gida naku tsare-tsarensa ya yi yawa." Amrah ta faɗa bayan ta shigo ciki, dariya Bhatool ta yi sanan ta ce. "Dan fa mai gadin bai ganeki ba ne, amma da ya ganeki bazai miki haka ba."
"Bawani nan." Amrah ta faɗa, tana zama. "Bhatool Amarya." Amrah ta sake faɗa. "Uhm wai kin san me?." Bhatool ta faɗa. "Faɗi ina jinki."
ku yi following page dina, domin samun update akai akai, jazakallahu khairan
Legendspen
***