Babi na ɗaya
by @dijensy
*SHI SO DABAN YAKE*
_Khadija Ado Ahmad(dijensy)-
*Da sunan Allah mai girma,mai rahama ,mai jin 'kai*
*Ban yadda wani ya sauyamin labari ba ta hanyar mai dashi audio ko AI video ba tare da izini ba,wannan littafin ban yi shi don iya nishaɗi ba darusa sunfi ƙarfi a ciki ba kuma ina da manufar ɓatawa kowa rai ba,ayi karatu lafiya*
Arewapen
Wattpad
Youtube channel domin samun audio ku shiga link na ƙasa
500 kacal a biya ta Opay *** Khadija Ado Ahmad
Free page
*Wasu mutane suna shiga rayuwarka su zama mafarki, amma ƙaddara ta rubuta su a matsayin darasi. Soyayya ba ta tambayar matsayin mutum zuciya ce kawai take zaɓa*
[Mafari]
1
Madaidaciyar parlour ce an ƙawata ta da kujeru da labulaye ratsin ruwan madara da ruwan ƙasa mai turuwa masu kyawun gaske sai plasma TV manne a bango gefen kusurwa fanka ce a tsaye ke busawa ba sautin da yake tashi sai shesheka kukan matashiyar da ke zaune dunƙule waje guda cikin mayafinta ruwan toka baka ganin fuskarta daga kan kujera mahaifiyarta ce zaune ɗaya gefen ƙanwar mahaifiyarta daga daya 'bangaren 'yan uwan Babanta mata suke zazzaune muryarsa suka tsinkayo daga tsakar gidan "Toh mene ake jira da bazata fito ba?! Cikin ɗaga murya yayi maganar mai kama da yana cikin ɓacin rai.
Rushewa ta sake yi da kuka tana fara birgima a tsakar parlourn ɗaya daga cikinsu ta tashi tana riƙota "Jidda mene haka?"
"Ni bazan je ba ,dan Allah dan annabi ku roƙi baba a fasa aurennan wlh mutuwa zanyi idan naje gidan bazan iya ba Ummana ku sa baki "Ta ɗago fuskarta da ta damile da hawaye da majina baba da ke jiyo kurma ihunta ya shiga ɗaki yana ɗakko doguwar wayar charger ya fito yana shigowa parlourn kamar daga sama suka ganshi ya shigo yayi kanta ya fara shauɗa mata a baya ta shiga birgima tana ihu tana riƙe bayanta sai da bulalar ta tsinke a jikinta cikeda takaici ya fara dukanta da hannunsa yana kai mata gula da 'kafa yana fatali da ita ɗaya daga cikin kannensa ta durƙusa har 'kasa tana riƙo kafafunsa "Yaya don girman Allah kayi haƙuri wallahi zata tashi yanzu a aikata karka ji mata rauni".
"Tohm ai gwara in ji mata rauni ni idan mutuwa tayi ma ai hutawa kawai zanyi ko akwai wani abu da yayi saura?da nasan haka zata yi a duniya ba gwara ban haifeta ba ma".Rufe baki sukai maganar tashi na girgiza su ta cure jikin kujera tana gunjin kuka.
Haƙuri suka cigaba da bashi Ummanta bata ce komai ba ta tashi tana barin parlourn 'kanwar mahaifiyar tata hawaye na gangarowa daga idanunta ta taso tana kamo hannuta ta gyara mata mayafinta "Tashi mu fita Jidda ki yi shiru ki dena gardama ba abinda zai canja karki bari ya faɗi wani abu mara kyau akanki mahaifinki ne shi ki guji sake 'bata masa rai".
Tana shesshekar kuka ta ke kallanta ta sake fashewa da kuka ta jata tsaye 'kannen baban suka nufi inda take kamar gurguwa suka haɗu suka fitar da ita 'kofar gida motar da ke tsaye honda accord suka nufa suna sakata ciki har lokacin kuka take mai sauti 'kanwar mahaifiyarta ta shiga gidan gaba d'aya daga cikin 'kanwar baba ta zauna kusa da ita a gidan bayan.Tafiya mai nisan gaske sukai cikin wata unguwa a gwammaja ghetto ce ajin farko mai tuƙin motar kansa sai da ya raba 'kafar motar don kwata ce tsakanin layin har aka isa gidan,ɗan 'karamin gida ne da tsohon fenti duk ya dusashe alamar tsufa su kansu 'yan rakiyar kallon gidan suke a sanyaye suka buɗe motar gidan baya "Anty Mairo dan girman Allah kar ku min haka ki tafi dani gidanki amma kar a barni anan Anty Baby bazaki ce komai ba?"Ta shiga tambaya tana ɗago rinannun idanunta ta kalli 'kanwar Ummanta Anty baby ta kamo hannunta ta jawota "Kin dai ga dukan da ya maki a gida ba abinda zai hana ya sake miki wanda ya fisa ko a gaban mijin naki ne".Anty Baby ta furta Jidda ta sauke 'kafarta waje tana fitowa tana kallon dandamalin gidan da zasu shiga da ita sai a lokacin ta lura da kalar gidan Anty Baby ta riƙota suna hawa dakalin ta na riƙe da ita suka shiga tana yin ƙasa da kanta.Sallama Anty baby tayi aka amsa daga ciki wata matashiya ta fito daga ɗaki bazata wuce shekara talatin ba gabaɗaya.Fuskarta ɗauke da faraa ta ke musu sannu da zuwa ta na musu iso ta shigar dasu ƙaramin ɗakin da kujeru ne a ciki ƙananan set ruwan bula ƙasa kapet ne malale ruwan hadari sai labulaye sun shiga da kujerun da ganin yadda ko ina yake tsaftace zaka san matar gidan mai tsafta ce ƙamshin turaren wuta sai tashi yake ba ta bari sun zauna ba sai da ta shimfiɗa musu abin sallah mai laushi da gani sabo ne suka zauna Jidda kanta na sunkuye.
"Ina yini".Ta gaishesu fuskarta ɗauke da murmushi Anty suka amsata suma suna ƙalo murmushi "Fatan mun same ku lafiya ya yaran?"Anty Mairo ta faɗa tana kallon yarinya ƙarama da ta leƙo daga uwar ɗaki.
"Lafiya lau an gode Allah".Ta furta.
Anty Mairo ta dafa Jidda dake durƙushe "Ga ƙanwa mun kawo miki muna fatan zaku haɗa kawunanku in sha Allah Jidda ƙanwarki ce muna fatan zaki zama yayarta kema ubangiji ya baku zaman lafiya ni ƙanwar mahaifinta ce wannan kuma ƙanwar mahaifiyarta ce"Anty Mairon ta furta ta ga tayi murmushi har haƙoranta ana gani tace "Ni ai matar yayansa ce Hassan bai taɓa aure ba ,sunana Ruƙayya yarana uku shekara biyu da rasuwar yayan nasa".Ta furta a kunyace Anty Mairo ta murmusa Allah sarki Allah ya rahama masa".Anty baby ma kusan haka ta faɗa Anty Ruƙayyan tace "In sha Allah ba za ku ji kuka daga wajen mu ba bazata samu matsala daga garemu ba Mungode sosai ayi hakuri dan Allah wasu abubuwan sai daga baya abin ne yazo ba shiri haka Allah ya tsaro in sha Allah zamu kula da ita da karfin ikon mu".Anty Ruƙayya ta faɗa suna amsawa da ameen ta tashi tana ɗauko musu ruwa a tray ruwan fiyawata mai sanyi da zoɓo ta ajje musu ta rasa ina zata sa kanta gani take kamar karamcin ya musu kaɗan sukayi godiya shiru na biyo baya.
Anty baby ta duƙa tana raɗa mata "Kiyi haƙuri Jidda kiyi haƙuri zaki ga ribarsa da izinin Allah kuma baba zai yafe maki in sha Allah kar ki sa damuwa sosai a ranki kiyi haƙuri a duk yadda komai ya zo miki a sabuwar rayuwar da zaki tsinci kanki sannan ki riƙe azkar da sallalloli Allah zai shige miki gaba ki kula kuma da haƙƙoƙin da suka rataya kanki".
Anty baby daga haka ta tashi suka mata sallama don tun a gida su Anty Mairo sun mata nasu faɗan dukda kukanta take ba wani saurarawa tayi ba ko da ta ga zasu tafin ma ƙaro saurin kukan tayi suka tafi suna barinta ba tare da sun sake waiwayarta ba.
LABARIN JIDDA
Kan dandamalin wani gida take zaune tana wasa da 'kafafunta da basu ƙarasa kaiwa ƙasa ba tana sanye da uniform ɗin makaranta ruwan sama ta ja tsaki tana katse nisan tunanin da take cikin aljihun jakar makarantarta ta cusa hannunta tana ciro niece biscuit ta buɗe ta fara ci sai da ta cinye tass ta sauko daga kan dandamalin tana rataya jakarta a kafada tana fara tafiya ta ji murya daga bayanta "Jidda wallahi na ganki kin karya azumin ki sai na fadawa Ummanki".Ta waiwayo a fusace tana ganin yarinyar makotansu ta nufeta da gudu ta ruga a guje tana falfalawa hanyar gidansu Jiddan tayi ƙwafa.Kai tsayae ta tura 'kofar gidansu bayan ta ƙarasa tana shiga ciki ta ga Ummanta da Anty baby sun zuba mata ido a yayinda suke tsaka da aiki Ummanta ta kalla tana tsintar wake "Jidda daga ina kike?"
Baki ta turo tana cilli da jakar a tsakar gida "Uwar gulma ta kawo Munafunci ai ba karya azumin nayi ba da kanshi ya karye "Ta faɗa tana shigewa ɗaki ta fito ta cire hijab dinta kai tsaya kitchen ta shiga tana buɗe tukunya tasan akwai abincin gandaye ta ɗebo ta fito ko ɗumamawa batayi ba ta bararraje a tsakar gidan tana fara loma Umman ta kalleta ta girgiza kai.Yarinyar da ta kawo rahotan ta karya azumi ta kalla ta gwalalo mata ido "ko yawunki zai dalalo bazaki ci ba munafuka fita kuma in na ganki kin zo da shan ruwa sai na ci kan *warki".Daga Umma har Anty Baby sai da suka ɗago "Kunun sadakarma an dena bawa Salame(sunan uwar yarinyar)".
"Jidda kar in kuma jin zagi a bakinki haka abinda kuke koya a makarantar boko kenan?"Ta kalli mai maganar tana cuno baki "Wai ke Anty Baby yaushe zaki aure in huta da sa ido?" ta fada tana Jan majina don ta cika yaji a shinkafar da waken ga mai kamar zai magana "Sanda Allah yayi mara kunya".Anty baby ta faɗa Jidda ta taɓe baki "Inda kin yi haƙuri da Aminunki da ba haka ba ki...."Bata karasa ba Umma ta cire silifas ta jefa mata ta kauce tana kyalkyala dariya ta tashi tana shure kwanon da 'kafa har bakin rariya Anty baby ta kalleta ta kafa baki a fanfon ruwan na kwararowa har ta 'kirjin rigarta kafin ta kashe fanfon ta zo inda Umman take "Ina wayarki?"Ta tambaya tana tsaye a gantsare.
"Me zaki da ita?"Cewar Umman.
"Baba zan kira ya siyo min Rufaida da tsire ".Ta furta tana dage rigarta cibiya a waje tana goge fuska "Ajjiyar kudi kika basa Jidda? da baki ake siyo tsiren ke ba kya tausayin babanki ne ba jiya kika karɓe masa kuɗi ba na sake uniform da jaka?ba kya tunanin rayuwa ke kam kodayake shi ya ɗaure miki gindi kike duk abinda kike so je ciki ki cire uniform ki kai min markaɗe kafin ki je islamiyya".Umman ta faɗa tana tashi ta turo baki "Ai de ance mata suna cin abi me kyau idan suna haila ɗaya yake da mai ciki ni wallahi gidan Yagwalgwl zan koma an tsaneni a gidannan".Ta furta tana fakar ido ta ɗauki ƙaramar wayar ta ganta gefen kujerar da Umma ta tashi tana ɗauka ta shige ɗaki tana kiransa ya ɗauka ta faɗa masa abinda take so haɗi da faɗa masa ya taho mata da auduga tata bata da yawa ta gama wayar ta fito tana ajjewa ta koma cikin ɗaki ta kwanta bayan ta matso da fanka sabuwa da baba ya siya mata sabida zafin da ta masa ƙorafi ta sama ta mata kaɗan.Tunda ta baje kan gadon bacci ya ɗauketa sai bayan asr ta taso tana hamma ta shafa mara don ciwo take ji fita tayi ta shiga ɗakin Anty baby tana tsaye kanta tana karatun Al qurani a kan sallaya "Ina hulba ɗinki da kika ban rannan ki sake bani cikina zai fara ciwo kuma kinsan in na fara kowa sai yaji dai to karki ce min ta 'kare ni bazan sha ruwan ɗumi ba".Duk cikin numfashi ɗaya tayi maganar sai da Anty baby ta kai ayar ƙarshe ta ɗago ta kalleta tana mamakin shirme da gaɓunta na Jidda shekarta sha huɗu amma tana abu kamar yar shida nuna mata locker tayi tace ta ɗiba ta dawo mata da ita ta buɗe tana cirowa ta fice ta ɗiba dayawa a roba ta mayar mata da ragowa ta koma kitchen tana ɗora ruwan wanka cikin babbar tukunya kan gas ɗin ta ɗakko kofi ta zuba hulbar ta sa ruwan ɗumi ta fita zuwa ɗakinta.
Malam Haruna ɗan asalin Jos ne tashe tashen hankali ya dawo dasu Kano da daɗewa bayan ya gama jamia ya haɗu da Amina wadda ta kasance 'yar asalin adamawa amma tashin garin Kano ce ,Malam Haruna aikin gwamnati yake na jiha albashi na sa na da ɗan tsoka kuma dai dai gwargwado suna da rufin asiri don ba da iya albashi yake dogaro ba yana kasuwanci manyan shaguna biyu ne dashi na kayan hatsi sai provision kafin auren Amina ya taɓa yin aure matar ta rasu ta bar masa yara maza biyu sabida haka bayan auren Amina ta riƙe yaransa Ibrahim da Abubakar suna zaune cikin kwanciyar hankali da Amina matarsa haihuwa ce basu samu ba har tsahon shekara bakwai kafin kwatsam Allah ya basu yarinya mace ya raɗa mata sunan mahaifiyarsa Hauwau ake ce mata Jidda tunda suka haifeta Mal Haruna ya ɗora mata jarabar so duk wani abu da take so sai ya yi mata ba a isa a daketa ba ya dinga faɗa kenan mahaifiyarsa ma ganin an mata takwara itama ta ɗora da nata son haka idan ta je hutu wajenta kamar ƙwai haka take kula da ita Umma tayi ƙoƙarin ganin ta tarbiyantar da ita da kyau amma sun rinjayeta da ta gyara zasu ɓata a gabanta zai sa Umma a gaba yana faɗa don me zata hanata abu yasa Jidda ta raina kowa na gidan ana haka sai da ta shekara biyar aka mata ƙani namiji bayan shekara biyu Amina ta sake yin namiji bata kuma haihuwa ba ta ɗauka fifikon zai ragu Umma amma dukda an mata ƙanne baba bai daina lelata ba sau nawa zatayi laifi amma ƙarshe ta ja musu duka musamman su Ibrahim yasa tunda suka taso suka fita harkarta tun daga aji uku suke boarding jamiar ma hostel suke zama banda Umma bata nuna musu banbanci da wasu ma zasu ce janye musu mahaifi tayi.Anty baby ƙanwar Umma ce da ta samu jinkirin aure har yanzu mijin aure bai zo ba bayan rasuwar iyayensu ta komo gidan yayarta da zama.Wannan kenan.
Yau asabar ba boko ta tashi daga baccin safenta goma da arbain wandon baccine a jikinta da ya wuce gwiwa sai riga da bata kawo cinya ba tana yawo tsakar gida tiɓi tiɓi don wata sura ce da ita kamar matan rwanda ba gama zama cikakkiyar mace tayi ba amma wani irin hips Allah ya bata ga girman baya kuma ba kiɓa ce da ita sosai ba Jidda ba fara bace amma baza ta shiga layin baƙaƙe ba Sai dai a ce mata wankan tarwaɗa mai haske Umma har ta gaji da maganar shigar da take yi da Kayan bacci ta buɗi baki tace ai ba 'yan maza gidansu suna makaranta Yaseer da Abdallah yarane baba ne kawai kuma shi ubanta ne ai ta shiga lissafawa Umma karatun islamiya na muharramai da wanda ba muharramai ba Umma ta kyaleta.Kitchen ta shiga tana ɗauko ƙwai guda uku ta fashe ta zuba albasa da maggi tana daukan ashana zata kunna gas wuta ta taso a guje tafito tana ihu baba da ke kwance yau bai fita ba baya jin dadi sosai ga azumi a bakinsa yaƙi ajjewa ya fito da gudu ya shiga kitchen ɗin da take nuna masa da dabara ya kashe wutar Anty baby ta fito Umma daga banɗaki ta jiyo ihunta ta fito tana zura hijab ta sameta a tsakar gida tana dafe ƙirji haɗi da zare ido sai da baba ya fito yace mata "Matsoraciya".Ta fashe da dariya tana riƙe ciki "Baba ashe lafiyarka lau".Baba kansa dariya ta bashi don da bai san dariyar da take yi ba Anty baby tayi murmushi Umma ta girgiza Kai tana tsaki ta koma ciki "Baba Toh ya zanyi yanzu ƙwai zan soya fa?"
"Uwar masu gida ba sai na soya maki ba".Ya faɗa yana komawa kitchen ɗin ya kunna yana ɗora kasko ya soya mata ya kwashe a faranti "Uwar masu gida zo ki karba to"Ta fito daga ɗaki da brush a bakinta duk kumfa ta ɓata gaban rigarta ya mƙo mata "Babana na kaina yasa dik nafisonka a gidannan".Ta furta tana rungumesa ta gefe yayi dariya.
"Ragowar bread Umma ta bani"Ta faɗa tana zunɓuro baki bayan ta karɓi ƙwan ya kama ƙugu "Kice kwantai ta baki tun shekaranjiya fa na sayo shi a bawa almajiri mana ".Ya furta yana ciro dubu ɗaya a alhiju ya bata "Su Yaseer su siyo miki je ki kirawo su".
Ya bata kuɗin ta karbe tana zuwa bakin ƙofar ɗakinsu ta tasosu ta ƙarasa fanfo ta wanke bakinta kafin su dawo ta yi haɗin kauri suka kawo mata ta sa a gaba sai da ta ci ta rage ta basu saura ta fito da kwanukan ta ajje bakin rariya don bata wanke wanke tunda ta taɓa yin wani mura ta sha wuya ai baba yace pneumonia bazata shigeta ba Sai dai su sami me aiki ko suyi sharar ma bayi take ba daga makaranta sai bacci sai cin abinci.'Daki ta koma tana tunanin gobe da azumi zata tashi inama kwana goma take yi.Ta faɗa a ranta tana jawo littafinta karami ta bude tana ɗaukan biro ta fara rubutun aji duk yawan wasanta Jidda tana da ƙoƙari a karatun boko da islamiyya J S 3 take a boko a yayinda a islamiyya sauransu hisbh ashirin su kammala saukar Alƙurani mai girma.......
Arewapen
Dijensy