FreeArewaPen original
SHI SO DABAN YAKE
- 1views
- 19chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Writer Imaginator Dreamer Writing create my own world🥳 Marubuciyar Waqt,Tagayyara,Kadangaren bakin tulu d.s
Sample · Babi na ɗaya
*SHI SO DABAN YAKE* _Khadija Ado Ahmad(dijensy)- *Da sunan Allah mai girma,mai rahama ,mai jin 'kai* *Ban yadda wani ya sauyamin labari ba ta hanyar mai dashi audio ko AI video ba tare da izini ba,wannan littafin ban yi shi don iya nishaɗi ba darusa sunfi ƙarfi a ciki ba kuma ina da manufar ɓatawa kowa rai ba,ayi karatu lafiya* Arewapen *** Youtube channel domin samun audio ku shiga link na ƙasa 500 kacal a biya ta Opay *** Khadija Ado Ahmad Free page *Wasu mutane suna shiga rayuwarka su zama mafarki, amma ƙaddara ta rubuta su a matsayin darasi. Soyayya ba ta tambayar matsayin mutum zuciya ce kawai take zaɓa* [Mafari] 1 Madaidaciyar parlour ce an ƙawata ta da kujeru da labulaye ratsin ruwan madara da ruwan ƙasa mai turuwa masu kyawun gaske sai plasma TV manne a bango gefen kusurwa fanka ce a tsaye ke busawa ba sautin da yake tashi sai shesheka kukan matashiyar da ke zaune dunƙule waje guda cikin mayafinta ruwan toka baka ganin fuskarta daga kan kujera mahaifiyarta ce zaune ɗaya gefen ƙanwar mahaifiyarta daga daya 'bangaren 'yan uwan Babanta mata suke zazzaune muryarsa suka tsinkayo daga tsakar gidan "Toh mene ake jira da bazata fito ba?! Cikin ɗaga murya yayi maganar mai kama da yana cikin ɓacin rai. Rushewa ta sake yi da kuka tana fara birgima a tsakar parlourn ɗaya daga cikinsu ta tashi tana riƙota "Jidda mene haka?" "Ni bazan je ba ,dan Allah dan annabi ku roƙi baba a fasa aurennan wlh mutuwa zanyi idan naje gidan bazan iya ba Ummana ku sa baki "Ta ɗago fuskarta da ta damile da hawaye da majina baba da ke jiyo kurma ihunta ya shiga ɗaki yana ɗakko doguwar wayar charger ya fito yana shigowa parlourn kamar daga sama suka ganshi ya shigo yayi kanta ya fara shauɗa mata a baya ta shiga birgima tana ihu tana riƙe bayanta sai da bulalar ta tsinke a jikinta cikeda takaici ya fara dukanta da hannunsa yana kai mata gula da 'kafa yana fatali da ita ɗaya daga cikin kannensa ta durƙusa har 'kasa tana riƙo kafafunsa "Yaya don girman Allah kayi haƙuri wallahi zata tashi yanzu a aikata karka ji mata rauni". "Tohm ai gwara in ji mata rauni ni idan mutuwa tayi ma ai hutawa kawai zanyi ko akwai wani abu da yayi saura?da nasan haka zata yi a duniya ba gwara ban haifeta ba ma".Rufe baki sukai maganar tashi na girgiza su ta cure jikin kujera tana gunjin kuka. Haƙuri suka cigaba da bashi Ummanta bata ce komai ba ta tashi tana barin parlourn 'kanwar mahaifiyar tata hawaye na gangarowa daga idanunta ta taso tana kamo hannuta ta gyara mata mayafinta "Tashi mu fita Jidda ki yi shiru ki dena gardama ba abinda zai canja karki bari ya faɗi wani abu mara kyau akanki mahaifinki ne shi ki guji sake 'bata masa rai". Tana shesshekar ku...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.