ZARGEN ƘAYA

1

by @aishaangel

*ZARGEN ƘAYA*



     *NA*
*AYSHER ANGEL*

Page 1

WhatsApp ***

*The Fractured Bond: When Resentment Runs Deep And Innocent Pay The Price...*

*Shin har sai yaushe ne mutanen yau zasu daina hukunta wasu akan laifin wasu? Shin har sai yaushe ne mutanen yau zasu daina wasarairai da zumunci akan son zuciya ko kuma dalilin da bai taka ƙara ya karya ba? Komai girman laifin da mutum yake ganin anyi mashi ai sulhu alheri ne bugu da kari zumunci ba abu ne da ya kamata ayi wasarairai dashi ba*


Daga inda nike zaune shurum ina iya jiyo maganata da ake yi wacce ba magana bace mai ɗaɗi a kunnuwa da zuci musamman ga wanda aka jefa da su, kalamai ne masu wahalar mantawa ga wanda aka furtawasu. Dangin mijina mai rasuwa suna aibatani akan abun da ya faru tun kafin aurena da shi. Zaman gaisuwa da ya kamata su yi mashi addu'a ni kuma su nuna min tausayawa akan wannan iftila'i da ya faru amma sai suka zabi maido maganar da ta riga ta wuce a tsakanina da shi.

Na saka hannuwana akan karamin cikin da nike dauke da shi ina ayyanawa a raina koda abun da za su yi min zai fi haka bazan yarda wannan zumuncin nasu mai wahalar sha'ani ya ƙara lalace ta dalilina ba saidai kuma kamar yadda hausawa suka ce idan an ciza a hura.

Tun kafin a haifi mijina mai rasuwa madakalar wannan zumuncin take wacce har wani ba ya son a dangantashi da wani, har ta kai ga matakin da wasu suke shan wahala akan laifin da aka aikata tun kafin a haifesu.

Tunda har suka nuna kulafuci akan ɗan da yake cikina ni kuma zanyi amfani dashi in gyara wannan zumuncin nasu mai wahalar sha'ani tamkar TABARMAR ƘASHI.

Dama ina da tabbaci akan ba zasu barni da abun da na haifa ba, kuma ba zan hanasu ba, da hannuna zan ɗauki yaron in basu ina da tabbaci akan duk yadda za su yi ƙoƙarin cusa tsanata a ransa idan ya mallaki hankalinsa ya ji abun da ya faru zai gane cewa bani da laifi and the fact that nice wacce aka yi wa laifin.

Zumuncin dai da suke son lalata da kuma fitina da suke son ayi ni Rumana ba zan bari a samu tangarda daga wajena ba saidai idan abun ya fi karfina. Namiji ne ko mace idan na haifa suka amsa zan bar masu domin na san komai daren dadewa zai neme uwarsa mahaifiya wannan abu ne da basu isa su hana ba.

Zumunci abu ne mai girma don haka na yarona da dangin ubansa ko kuma dangina ba zan bari ya samu nakasu a saboda rashin hakurin dangin mahaifinsa ba, komai za'a yi min zan yi hakuri domin shi hakuri ba ya faduwa kasa banza, Allah yana sane da ni kuma zai kawo min mafita.

Lamarin mutanen yau yana bani matuƙar mamaki da tu'ajjibi da har wasu lokuttan nike jina kamar wacce ta kamu da ciwon MUTUWA A MAƘOSHI koda yake shi HAWAYE AKAN RUWA idanun da suke fitar da shi ne kawai suka san raɗaɗi da kuncin da ya ke fita da fitarsa, kamar ZANE AKAN RUWA ne mai wahalar gane kamanni.

Shin har sai yaushe ne mutanen yau zasu daina hukunta wasu akan laifin wasu? Shin har sai yaushe ne mutanen yau zasu daina wasarairai da zumunci akan son zuciya ko kuma dalilin da bai taka kara ya karya ba? Koda abu aka yi wa mutum zaman sulhu ya fi zama alkhairi akan lalata zumunci.

Ina ji Barira tana cewa, "Ni na rasa abun da ya gani akan wacce kodaddiyar wacce babu wani abu da take dashi sai farin shima na fitar hayyaci."

Anisah ta buga tsaki ta ce, "Kuma ta zo ta yi wa mutane zaune a gida."

Jasmine tayi dariya ta ce, "A dole ta zauna kada ta koma gida ta ɗora da cin tuwo da miyar kuka alhalin a nan ta saba da cin shinkafa da kaza, nifa na tsaneta."

Suka kwalkwale da dariya yayinda wata wacce ban tantance muryarta ta ce, "Please ku daina yi mamu maganar waccen ɗiyar talakawan wacce babu abun da ubanta yake dashi sai talaucinsa, yadda nike jin tsanarta, ko kallon inda take ba na son inyi saboda abun da ta yi wa yaya."

Suna jifana da maganganu marassa ɗaɗi akan abun da ya faru wanda ba laifina bane, shi mai laifin munyi maslaha da shi kuma na yafe amma su sai suka dauki riko da zafin zuciya suka saka a ransu wanda ya kai har yau da muke cikin zaman makokinsa basu ɗaga kafa ba, na rasa abun da ya saka gwoggo Maimuna tace in zauna a yi sati biyu kafin in koma gida, idan ta nice daga ranar da aka rufoshi zan nufi hanyar gidan ubana in zauna a can in amshi gaisuwa tunda koda na zauna a nan din ba zaman ɗaɗi za'ayi ba, saidai maganar gwoggo Maimuna yayar mahaifina tayi min togaciya kuma zan zauna dominta saboda yayar mahaifina ne kuma uwa take a gareni.

Hawaye suka zubo akan fuskata na saka hannuwa na share ina jin ciwon ta'addancin da aka aikata akan mijina, ya je kauyensu ƴan ta'adda suka shiga garin suna harbe-harbe, yana ɗaya daga cikin waɗanda su ka yi wa yankan rago bayan da su ka yi wa kanwarsa fyade a mafi munin yanayi, a take a wajen bakin ciki ya saka ta hadiyi zuciya tace ga garinku nan, na shiga tashin hankali da dimuwa, ikon Allah ne kaɗai ya hana cikin dake a jikina ɓarewa domin tashin hankali da firgici da na shiga a wannan lokacin ba ƙarami bane ba.

Mutum ukku muka rasa, mijina da aka yi wa yankan rago, ƙanwarsa da aka yi wa fyade da kuma mahaifiyarsu da ta hadiyi zuciya ta mutu na tashin hankalin da ta gani har zuciyarta ta gagara ɗauka.

A karo na biyu na saka hannuwa na ƙara goge hawayen da suka zubo akan fuskata ina mai tuna yadda komai ya faru tiryan-tiryan kamar a yau ne abun yake faruwa kuma duk yadda na juyashi amsa ɗaya ce nike samu, bani bace mai laifi, nice wacce aka yi wa laifi amma son zuciya da tsanar da danginsa su ke yi min ya saka sun gagara tsayawa su fahimce ni.

Ni Rumana Yusuf ba mai tara samari bace, infact samari biyu nayi a rayuwa Mutallab da Junaid kuma a wannan takin ne lamarin ya juye ya zame min tamkar KITSO DA KWARKWATA mai wuyar sha'ani. Shin miye ya faru? Shin ya aka yi aka kwana a ragaya? Shin waye na aura a tsakaninsu? Mutallab ko kuma Junaid? Ku biyoni a waiwayen baya na labarina domin jin yadda abun ya ke amma fa sai kun zama masu jumurin hakuri domin abubuwa da yawa sun faru masu taɓa zuciya wanda ni kaina idan na tuna nike jin kunci amma masu iya magana sun ce mai haƙuri ya kan dafa dutse yasha romonsa, ku biyo ni domin shan wannan romon.

*******

WAIWAYE

A durkushe nike ina rusar kuka kamar wacce tayi rashin iyayenta guda biyu saidai ni a durkushe a gabansu nike rusar wannan kukan, tambayar itace shin miye ya sakani wannan kukan? Amsar damuwa ce ta tarabbabin abun da zai biyo bayan buƙatar da ta sakani kukan, lamari ne mai wahalar sha'ani musamman yardar da sukayi da wanda zanyi magana a kansa, Mutallab maciji sari ka noke, suna mashi kallon mutum mai hankali amma ni da yayi wa aikin ganganci na san wannan duk show ne amma ainihin halinsa yana binne a kasan zuciyarsa.

A dukkanin lokacin zuciyata ta hasaso cewa ba za su yarda da maganar da nike tafe da ita ba sai inji sautin kukana ya ƙaru, ji nike idan basu yarda da muradina ba, rayuwata ta shiga garari, kuka nike babu ji babu gani ina mai tausayin kaina da kaina.

Wace ni auren wanda ya barranta kansa da uwarsa mahaifiya wacce ta dauki cikinsa na tsayin watanni takwas, tasha wahalar nakuda, ta raineshi ya girma har ya kawo wannan munzalin da yake jin ya fi karfin ya alakanta kansa da ita saboda bata da arziki.

A dukkanin na tuna wannan lamari sai inji takaici ya tokare min makoshi.

A karo na farko mahaifina da muke kira da Abba ya dubeni yace, "Rumana ki nutsu ki faɗa mamu damuwarki."

Ban ce komai ba, kuma ba ni da nufin furta kalma ko ɗaya, ni dai ina zaune shurum ina luguden laɓɓa na abun da ya kamata in faɗa, na yi nazari na tuna na ƙara tunawa ina mai juya tunanin a masarrafar kaina amma na gagara yanke shawara akan da kalaman da ya kamata inyi amfani dasu domin sanar da su lamarin ta yadda za su fahimce ni, idan na tanka ince mi, lamari ne wanda zai yi wahala su fuskanceshi duba da yardar dake a tsakaninsu da wanda yayi abun, a dukkanin lokacin da na tuna turka-turka da baya da kurar da lamarin da zan kawo masu zai fuskanta sai inji gabana ya bada ras amma bani da wata mafitar da ta wuce in furta domin nemawa kaina mafitar da itace mafita mafi a'ala a gareni.

Mahaifiyarmu da muke kira da Umma wacce take zaune a kusa da Abba ta dubeni da tausayawa tace, "Ki daina kukan ki faɗa mamu damuwarki. Ki buɗe baki ki yi magana. Baby ba kya ji ne, Abbanku yana magana."

Maganarta ta saka min karfin gwuwa na ɗago a karon farko a yayinda hawaye suka zubo akan fuskata a yayinda nike ƙoƙarin furta kalaman da nike da tabbaci akan dole zasu tada zaune tsaye a gidan musamman duba da Mutallab ta bangaren Abba ya zo kuma ya yarda dashi ba kaɗan ba.

Da muryata da bata fita sosai saboda kukan da na sha na ce, "Abba ka gafarceni kayi min aikin gafara amma ba zan iya auran Mutallab ba, ba zan iya aurenshi ba, a baya na ce ina sonshi amma yanzu lamarin ya sauya, ba zan iya ba."

Daga haka ban ƙara cewa komai ba na miƙe na bar dakin da gudu ina gumjin kuka yayinda tausayin kaina ya cika min zuci, HAWAYE A KAN RUWA mai wahalar gane kamanni, ni kaɗai nasan kuna da raɗaɗin da ni ke ji a yayinda ƙaryar da Mutallab ya yi min take ragargazata a zuciya, jina nike tamkar wacce aka dauko katon mashi aka soka mata a tsakiyar zuciya.

Na yarda dashi na kyautata mashi zato amma shi sai ya zaɓi da ya munana min zaton.

Naki mai kuɗi nace sai talaka, gashi nan talakan ya sakani a damuwar da har take ƙoƙarin tarwatsa min zuciya.

Na shiga ƙaramin dakina wanda dake kusa da kofar da na fito na zube a kasa ina mai fashewa da kuka, na haɗa kaina da gwuwa ina sharar hawaye yayinda wasu sabbi suke zubowa, na gagara tsayar da hawayen dake zubowa daga idanuna suna sauka akan fuska, a duk sa'adda na tuna abun da Mutallab ya yi min sai inji hawayena sun kasa tsayawa, wannan wacce irin alaƙa ce, wannan wacce irin soyayya ce, wannan wacce irin dauka ce ya yi min, ina zaune da shi da zuciya ɗaya ashe shi fassarar da yake min daban. I'm not gold digger and I will not take what he did to me.

Abba yace, "Ta fada maki wani abu da ya faru tsakaninsu ne?"

Umma ta girgiza kai tace, "A'a sam babu abun da ta ce min."

Yayi jim na tsayin lokaci kafin yace, "Babu damuwa, zan kira Mutallab din inji ta bakinshi." Ya mike tsaye ya goya hannayensa a baya yana kaiwa da komawa yana mamakin furucin Rumana ya tabbata ba za ta kawo wannan maganar ba sai idan tana da kwakwkwarar hujja, abun da ya ƙara bashi mamaki shine sanin halayen Mutallab tunda shine ya kawoshi, ya tabbata zai yi wahala Mutallab ya aikata wani abun da zai saka ta yi haka.

Tunda na shiga daki ban fito ba ina kunshe kamar garar kunya, na yi kuka har na nemi hawayen na rasa saidai aikin ajiyar zuciya da nike saki lokaci zuwa lokaci.

Autanmu ya shigo ya ɗane bayana yana faɗin, "Rumama. Rumama. Rumama." Haka yake kirana kasancewar gwaranci yake har lokacin magana ba ta zauna mashi akan harshe ba.

Na saka hannu na jawoshi gaba yadda yake kiran sunana ya sakani goge hawaye na saki murmushi, yana kiran sunana ina tayashi, ina kiran Umma, Abba, yana tayani amma ina fara kiran sunayen sauran yayyenmu guda biyu sai ya fara wangame baki yana dariya tabbacin ba zai iya furtawa ba, shekararshi biyu amma gudu yake sosai, ga baki, ga shi yana da zakin murya, yana gudu yana kiran 'Umma. Abba. Rumama. Ayan.' Sauran yayunmu guda biyu kiran sunayensu wahala yake mashi, saidai ya yi ta gwaranci, wanzuwarshi a wajen ya rage min wani kaso na damuwar dake ragargazata a zuci, na biye mashi yana gwaranci ina tayashi muna dariya na nishadin da lamarin ya ke ba ni, na lallaɓashi ya yi bacci.

Nayi jim ina tunani, ina juya tunanin abun da Mutallab ya yi min a masarrafar kaina, wasu mutanen ba su da adalci, wasu mutanen yadda ka daukesu ba haka suka daukeka ba, ko a mafarki ban taɓa tunanin Mutallab zai yi min haka ba amma sai gashi ya yi shiyasa abun ya tsaya min a rai.

Na dauki kallabi na rufe yalwataccen gashin kaina mai tsayi da cikowa, wani kodadden zanin atamfa rubber ne a jikina tareda rigar t-shirt, ina da kaya daidai kwarkwado adadin yadda yarinya wacce take a gidan mutane masu matsakaicin karfi take da su amma a halin da muke ciki na matsin tattalin arziki a gidan musamman yadda kaso mai yawa na samun mahaifinmu yake tafiya akan hidimar karatunmu idan na ce zan rinƙa sakasu tsakar gida sai su koɗe in rasa na sakawa in fita shiyasa na yanko zannuwa falle guda-guda na atamfa rubber ina haɗawa da t-shirt ina sakawa a tsakar gida.

Da sanyin jiki na miƙe ina ɗaura kafafuna ina saukewa kamar wacce take tsoron daura kafafunta akan doron kasa, na fito tsakar gida na tarar Umma tana tankaden garin masarar da za ta yi mamu tuwon dare da shi, ka'ida ne gidan duk dare tuwo ake yi kasancewar mahaifinmu ma'abocin son tuwo ne musamman da miyar kuli-kuli.

Da sanyina na ƙarasa inda take ina tarabbabin abun da mutanen yau suka mayar da kansu na yadda ƙarya ta zama tamkar wani abun ado, miye amfani mutum yace yana da abun da ba shi da shi, miye amfanin mutum ya yi ƙaryar arzikin da ba ya da shi, da a ce ni mai idon cin naira ce ba zan ji komai ba tunda dukkanin abun da ya biyo baya na wulakanci ni na janyowa kaina, dama aka ce wanda ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa amma lamarin da ya saka ƙaryar take cigaba da ragargata a zuciya shine ban taɓa cewa sai mai kudi ba, a yadda nike tare da Mutallab koda yafi kowa talauci a garin Katsina zan zauna da shi domin shi nike so ba kyale-kyalen duniya da ba ya da tabbas ba.

Saidai kash ni ina nan ina kyautata mashi zato ashe shi ta bangarensa munanan min zaton ya ke yana min kallon mai kwadayin arziki.

Na isa inda mahaifiyarmu take na rusuna nace, "Umma kawo in yi."

Umma ta girgiza kanta tace, "A'a ki je ki haɗa wuta."

Na juya na wuce madafa na haɗa kan itacen da aka siyo na karya wasu na saka sannan na banka masu wuta na ɗaura tukunya na tsaida ruwa, ina fitowa daga madafar naci karo da Yaa Ahmad ya dawo daga wurin aiki shine babban yayanmu kuma dashi nafi shakuwa a cikin yayuna maza, kallona ya yi saidai bai ce komai ba, tabbacin ya ji hukuncin da na yanke akan Mutallab kenan tunda ba haka mu ke yi ba, Mutallab kamar aboki yake a wajensa duk da sai bayan da na fara soyayya dashi sannan suka fara abotar kuma shakuwar dake tsakanina dashi ne ya janyo har aka kulla abotar, saidai kuma abun da ya ɗaure min kai da sakani a mamaki da tu'ajji shine magana da baiyi min ba, yaga laifina kenan ko mi, ko kuma so yake ya nuna min WATA KUSAR TAFI WATA, koda yake ya kamata inyi mashi uzuri in zama mai kyautata zato watakila Abba ne ya hana suyi min magana, tunda gashi itama Umma ba ta ce da ni komai ba wanda shima abun mamaki ne sosai da kuma ɗaure kai.

Ya shiga dakinshi yayinda ni kuma na zauna bakin rijiya na zura guga na janyo ruwa na cika mashi bokiti sannan na tara ruwan da zanyi wanke-wanke da su, ina jin diramarshi da Affan da ya maƙale mashi, saida dubara ya samu ya liƙama Umma shi sannan ya zo ya dauki bokitin da na cika mashi ya wuce bayi, ina wanke-wanke ya fito, ganin har lokacin ba magana zaiyi min ba nayi karfin hali nace, "Yaa Ahmad, ya aiki? Nayi laifi ne naga tunda ka shigo baka kulani ba."

Ya juyo yana sakin murmushi ya ja kumatuna yana faɗin, "Babu komai, kamota-kamota."

Mukayi dariya yace, "Ɗazu Ayan ya kirani, yana gaidaki." Na saki murmushi ina tuna ɗaya yayana dake karatu a london, nace, "Allah sarki mutanen London."

Affan ya riƙe mashi hannu yana kiranshi, "Amad." Ina tayashi muna dariya, Yaa Ahmad yayi mashi wayo ya wuce dakinsa, na lura yanayin kowa ya sauya a gidan har sauran yayuna sunji komai amma babu yadda zanyi, tabbas an dauki lokaci da saka ranar aurena da Mutallab amma saidai lamarin ba mai yiyuwa bane, abun da ya aikata min ya zame min babbar togaciya.

Mutullab ya mijin da ya dace in aura bane, zaɓinsa da nayi a baya zaɓin zumun dare ne kuma zanyi iyakar ƙoƙarina gyarawa fatana shine yayuna da iyayena su fahimceni su kuma gane illar da na hango a tattare da abun da ya aikata a gareni.

Bayan na kammala sallar isha'i nayi shafa'i da wutiri na fito tsakar gida ina cin abincin dare wanda ya kasance tuwo da miyar kubewa, ina zuba lomar tuwo yayinda dadin miyar yake kai min har tsakiyar kai, wani yaro ɗan makotanmu ya shigo yana sanar dani sallama da ake yi dani a waje.

"Baby, wani ya ce ki zo," ya sanar da ni.

Na ɗan kalleshi ina nazari, daga ji babu tambaya Mutallab ne don haka ban yi yunkurin miƙewa ba, sai ma ƙara gyara zama da na kara yi ina mai aika lomar tuwo a bakina. Fita dai bazan fita ba, kuma yayi karya ya shigo gidan, ba ni da lokacin sauraren duk wasu zantukan da zasu fito daga bakinsa.

Na soshi saboda Allah, nayi nufin aurensa saboda Allah ashe shi kallon mayyar kudi ya ke min tunda har zai yi min karyar matsayinsa a wajen aiki sannan ya rinka zuwa da motoci yana min burga.

Ni Rumana ba mayyar kudi ba ce, ba haka nike ba, ba miji mai kudi nike nema ba, mai sona nike nema mai rikon addini da ibada mai tausayi da jin kai, ba irinsu Mutallab masu karyar arzikin da ba su da shi ba. Ina tuna abun yana min kuna a zuci, wanda na shirya rayuwa ta har abada dashi shine yayi min haka, kaico, lamarin tur da Allah wadai.

Saida yaron ya kara tambaya sannan na bude baki na ce, "Ka je ka ce mashi kawai ya je abunsa."

Yaa Ahmad da Umma suna tsakar gidan kuma ina da tabbacin sun ji abun da na ce amma babu wanda ya ce da ni kanzil, yaron dai tunda ya fita bai dawo ba, saidai Yaa Ahmad da ya amsa kira wanda ina kyautata zaton Mutallab ne na fahimci hakan ne ta hanyar mikewa da ya yi ya fita, ya jima sannan ya dawo, kiran ba ya wuce na rokonsa da zaiyi akan ya saka baki in fita, na yi tsammanin zai yi min magana amma sai baice da ni komai ba.

Takaicin abun da Mutallab ya yi min ya tokare min makoshi yayinda naji baki ɗaya abincin ya fita daga raina, na tsame hannuna daga cikin akushin da nike cin tuwon a cikinsa na daukeshi na wuce rijiya na wanke kwanukan da muka ɓata, Ummana macece mai tsafta bata son ƙazanta ko kaɗan, tunda na tashi da ita na fahimci kwanukan da aka ɓata da dare basu kwana da kazanta, sai ta wankesu tas, a wajenta na koyi tsafta kuma ina alfahari da hakan, shifa lamarin ƙazanta ba ya dadi ko kadan, ina amfanin doyi da hamami.

Bayan na gama wanke-wanke na yi masu saida safe na dora da fadin, "Umma karfe goma zan wuce school, lecture ɗaya gareni, ba zan jima ba idan na dawo sai mu yi wankin a tare."

Ta amsa da, "To, Allah ya kaimu, Allah ya yi albarka." Na amsa da, "Amin."

Na juya na kutsa kai cikin dakina wanda yake dauke da katifa, a gefe akwatu ne wanda nike saka kayana na fitar kunya a ciki sai kuma tsohon zanin gado dake gefe wanda na kulle kayan da nike sakawa tsakar gida.

Nayi lamo akan katifa saidai na kasa rumtsawa yayinda na nemi barci na rasa, abun da Mutallab yayi min yana min kai kawo a cikin kwanya, yana ragargazarta a zuci a gefe kuma waya ta isheni da tsuwwa, tatsuniyar gizo bata wuce ta koki, Mutallab ne da wannan danyen aikin, kuma bazan ɗaga ba, na yarda Abbana ba mai kudi bane, amma ba zan dauki wannan cin kashin da yayi min, bazan dauka ba domin ba haka nike ba, na fizgo wayar na maidata silent na turata a handbag.

Sai wajajen karfe ɗaya na dare sannan ɓarawon bacci ya yi nasarar awon gada da ni, da asuba a daddafe nayi sallar asuba na koma bacci, a lokacin na samu na rama baccin da ban yi da daren ba har na makara, ban farka ba sai wuraren karfe tara na safe, wata zabura nayi na miƙe a sukwane, a gaggauce na wanke bakina naci dumamen tuwon jiya nayi wanka, na shafa mai, na murzawa fuskata powder, na shafa kwalli shikenan ban daɗa ba ban ƙara ba domin iyakar kwalliyar tawa kenan.

Na shirya cikin atamfa dinkin riga da skirt, ina da dogon gashi sosai wannan yasa nike ɓata lokaci sosai wurin tufkeshi, dakyar na samu nayi mashi gammo na zura dogon hijab har kasa na rufe fuskata da niqab, haka shigata take kasancewata ma'abociyar saka dogon hijab, na saka naira dari duba ɗaya a jikkata na fita na leka dakin Umma nayi mata sallama, a koda yaushe Umma tana bina da addu'a, yauma bata fasa ba, cikin ikon Allah ina fita daga santarmu na samu kekenapep, naira dari biyu ya kaini national, na samu saura kaɗan bus ta cika na samu seat, babu jimawa motar ta cika kasancewar coaster ce bata da wahalar cika, shiru nayi yayinda muka dauki hanya amma shurin na baki ne kawai amma a zuciyata ba haka lamarin yake ba, domin tunani da sakeken zuci.

Akwai ƴan course dinmu a motar saidai tunda muka gaisa ban ƙara furta komai ba, na dauko littafi ina yi kamar ina karatu, na yi zuru ina tunani, ji na yi an taɓani nayi firgigit na ɗago sai a lokacin na lura da motar tana tsaye ne a bus-stop dake gefen faculty dinmu ne.

Jiki a sanyaye na miƙe na fita, muka jera da Zaynerb Abdul'aziz wacce ta ankara da rashin tashina ta taɓoni, duk da bamu magana irin sosai din nan amma mun san juna tunda course ɗaya muke karanta biochemistry, muna a ajin karshe wato 400 Level, ta ɗan dubeni tace, "Rumana baki da lafiya ne? Na ganki suku-suku."

Na girgiza kai nace, "A'a, lafiyata lau, babu komai, watakila kurar exam da muke tunkara ne ya saka kike ganin kamar nayi suku-suku kin san aka ce wanda aka yi wa hankali yafi wanda aka haifa da shi."

A tare mu ka yi dariya, daga nan hirar ta koma ta karatu wacce bata yi tsayi ba tsuwwar wayata ya tsinketa, na zaro wayar wadda ta kasance keypad, taci duniya har rubberly na saka na nannadeta, Jalila ce, ƙawata ta amana.

Daga ɗaya bangaren tace, "Ina kika shiga ƙawata?" Nace, "Na shigo yanzu, gani nan a tsallaken bus stop."

Na nufi hanyar department ina tunanin ko tana can sai ji nayi ta ce, "Ina medicine classes."

Na ɗan ware idanu na ce, "Kai kai kai, serious student, an sha boko kenan... Alright then, ki fito gani nan tafowa..."

Saida na mayar da wayar a Jikka sannan na fara tafiya cike da nutsuwa ina daga kafafuna ina saukewa a hankali, ina gab da library na lura da shi yana tafowa daga bayana, kamar wanda aka jefo, ba ya tare da nutsuwa ko kaɗan, daga nesa na kalleshi ya kalleni, Mutallab ne.


Har zan wuce sai kuma naga wannan ba shine mafita ba, bani bace ya kamata in ganshi in gudu shine ya kamata ya ganni ya gudu tunda shins marar gaskiya.

"Rumana ki tsaya saureni," ya faɗa kamar zai yi kuka.

Na gyara tsayuwa na ce, "A tsaye nike ka faɗi ta cikinka domin ina da abun yi."

"Rumana ki yi haƙuri," ya faɗa da muryar tausayi.

"Mutallab young millionaire, ina motar taka, naga kullum da sabuwar mota kake zuwa wajena."

"Rumana ki yi haƙuri na yi nadamar abun da nayi maki."

Na murtuƙe fuska na ce, "Mutallab zan tambayeka, shin tunda muke da kai na taɓa ce maka sai mai kudi zan aura?" Ya ce, "A'a." Na ce, "To mi ya sa kayi min ƙaryar arziki?" Ya ce, "Saboda ina tsoron ka da mai kudi yazo ki gujeni."

Takaici ya zo kin wuya, a zafafe na ce, "Mutallab kenan, da na ina da ra'ayin auren mai kudi da yanzu ina gidan mijina har da yara."

Ya ce, "Ki yi haƙuri."

Na ce, "Okay zan haƙura amma sai ka faɗa min uzurin da ya saka ka barranta kanka da mahaifiyarka har ka iya ce min matar kawunka ce, koda yake amsar daya ce saboda ita talaka ce bata dashi kai kuma kana son ka yi ƙaryar arziki."

Bai iya tanka ba, yana tsaye kamar wanda aka dasa a wajen, yayi kasa da kansa, na ce, "Ina jira ka yi min bayanin da zai saka in fahimceka."

Na saki siririn tsaki na juya heading to library, yana kwala min kira nayi mashi banza, Rumana zata fara min surutu na janyo hannunta muka ƙara sauri, nayi wuf muka shige library, muka haura saman benen dakin karatun.

Rumana ta fizge hannunta tace, "Baby, Mutallab fa na hango ina maki magana kika janyoni."

Na zauna akan kujera dake a kusa da ni yayinda nike hangoshi ta waje ta gilashi, na ce, "Ganinsa shine dalilin da ya saka na janyoki."

Na ƙara sakata a duhu, ta dubeni da mamaki tace, "Mutallab nike nufi, Mutallab wanda zaki aura."

Ita a tunaninta ban gane wanda take nufi bane ba, kaina tsaye na ce, "Na gane mana." Ta ƙara shiga mamaki da tu'ajjibi ta ce, "Kunyi fada ne?"

B ana a cikin yanayin da zan iya amsa mata wannan tambayar, a takaice nace, "Ki bari kawai idan na shirya za mu yi maganar."

Kamar zatayi magana sai kuma ta fasa tace, "To shikenan amma abun da mamaki da ɗaure."

Na ce, "Believe me I learn that the hard way."

Daga sama muna hangoshi ya durkushe kasa tareda dafe kansa, tuni na dauki littafi ina dubawa yayinda Jalila ta kasa karatun tana ta kallonsa da alama tausayinsa ta ke ji.

Bayan wani lokaci na leka naga wurin wayam, ashe wani abokinsa dake masters ne ya zo wucewa ya ganshi shine ya jashi suka wuce, na duba wayata tareda dafe kai nace, "Gosh, lokacin lectures ya yi."

Da sauri muka sauko muna fito daga library muna sauri domin cimma venue da za mu yi darasin yayinda Jalila take korafin nice na janyo mamu, kai tsaye lecture threater muka nufa muna tarabbabi kasancewar kulle class yake idan ya shiga, munyi sa'a muna zama ya shigo.

Karfe biyu saura muka fito saida muka tsaya central mosque mu ka yi sallar zuhr na rakata hostel ta amso handout sannan muka kamo hanyar gida, napep ya fara saukeni a unguwarmu sannan ya wuce da ita, tun daga nesa na hangoshi, Mutallab ne zaune a dakalin dake kallon kofar gidanmu.

Nayi turus kawai, wai mi wannan ɗan tahalikin yake nufi da ni, yayi min ƙaryar da ta saka na fasa aurensa shine kuma zai isheni da na ci, ya san yana sona miye na karyar, ina jin sai na koyi jaraba da tujara sannan zai shafa min lafiya.

Yasha gabana yana min magiya, na murtuke fuska ina mashi wani mugun kallo nace, "Malam tara ko bashi, ko ka matsa ka bani waje ko kuma in yi maka ihu."

Yace, "Please Rumana." Na kara murtuke fuska nace, "Aww ka gwammace inyi maka ihun kenan."

Ganin da gaske ihun zanyi mashi ya matsa min na wuce gida fuuu ina buga tsaki, cikin raina nace, "Makaryaci baiyi ba, rayuwar ƙarya ba tayi ba, komai talaucin ubana zan nunashi ince shine ya haifeni, hakazakila komai lalacewar gidanmu zan nuna ince shine gidanmu, domin da uba ake ado riga ko a kasuwa a daura."

Ban san yadda Mutallab ya ƙare ba, naga dai bai aiko kirana ba, kuma koda ya aiko ba zanje ba.

Da daddare ina zaune a dakina na samu kiran Abba, na sameshi a dakinshi na zame a ƙasa na rusuna a gabanshi, yana zaune akan kujera yayinda Umma tana zaune a gefenshi.

"Rumana," ya kira sunana.

Na dago na dubeshi jin ya kira ainihin sunana na yanka.

Ya ja fasali yace, "Miye dalilinki na cewa kin fasa auran Mutallab?"

Tuna abun kawai yana sakani jin kuna a zuci, na fashe da kuka sannan na ce, "Ƙarya yayi min, ni bance sai mai kudi ba, kowa yasan halina, na soshi tun ban san waye shi ba amma shine yayi min ƙarya akan mahaifinshi, ya ce da ni Alhaji Mahmoud shine mahaifinshi bayan kuma mahaifinshi ya rasu hakazakila ya rinka zuwa da motoci yana min ƙarya wanda duk ba haka bane ba."

Abba ya ɗan dubeni sai kuma ya murmusa ya ce, "Baby kin cika wauta dama wannan ne dalilin." Kallonsa nike cike da mamaki da tu'ajjibi yadda ya ɗauki maganar a matsayin wauta.

Ya ɗora da faɗin, "Idan ban dake da abunki, Uncle dinsa ai matsayin uba yake a wajensa."

Ta tabbata dai Abba bai fahimci inda maganata ta dosa ba ashe dole kuwa in ɓeɗe mashi daga biri har wutsiya domin ya fahimci yadda lamarin ya juye ya zama tamkar KITSO DA KWARKWATA mai wuyar sha'ani.

Na ce, "A'a ba'a haka yayi min bayani ba, shi ya nuna min ne Alhaji Mahmoud shine mahaifinsa, akwai ranar da na ganshi a unguwarsu har na shiga na gaishe da mamarsa amma sai ya ce min Matar Kawunsa da ya rasu ce."

Daga Abba har Umma babu wanda baiyi mamaki ba, suna dai zaune shurum suna tu'ajjibin wannan lamari mai kama da almara, kamar Abba zaiyi magana sai kuma ya fasa ya ɗaga min hannu yace, "Shikenan tashi ki tafi, ba zanyi maki dole ba."

Na sauke ajiyar zuciya, na ji sanyi a raina, abu ne da banyi zato ba, na share hawayen da suke akan fuskata na miƙe na fita zuwa dakina yayinda abun ya koma min sabo, na so Mutallab na shirya rayuwar aure ta har abada da shi amma ƙaryar da yayi min ta rushe komai. Abu ya tarar min goma da ashirin ga sauran ɓurɓushin sonsa da ya maƙale min a zuciya, ga kuma ciwon abun da ya yi min da yake cigaba da ragargata a zuci. Damuwa ta yi min yawa har na fara ramewa.

Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)