ZARGEN ƘAYA

2

by @aishaangel

*ZARGEN ƘAYA*



     *NA*
*AYSHER ANGEL*

Page 2

WhatsApp ***

*The Fractured Bond: When Resentment Runs Deep And Innocent Pay The Price...*


Abba ya dubi Umma da mamaki yace, "Amma abun nan akwai mamaki, nasan Mutallab, nasan halinshi, kai abun nan akwai ɗaure kai."

Har Umma za ta yi magana sai kuma ta fasa duba da idan lamarin ya juye furucin zai iya zama hujjar da za'a yi mata dabaibayi da shi, maganin kada a yi kada a fara, ta kama bakinta ta tsuke ta yi shiru kawai tana jinjina kai. Yadda dangin Abba suka tsaneta tana saka baki zasu ce itace take zugani.

Kuka ne ya kufce min, na durkushe a dakina tare da fashewa da kuka, na dauki lokaci mai tsayi ina kuka sannan na janyo wayata na duba balance naira hudu ne kadai suka rage min, babu maganar kira saidai sakon text message.

Na turawa Jalila text message kamar haka;

'Salaam Alaiki, gobe idan Allah ya kaimu ki shigo school da wuri, akwai maganar da nike so muyi.'

Message din yana shiga babu jimawa kiranta ya shigo saida na daidaita kaina sannan na amsa kiran.

Daga ɗaya bangaren tace, "Fatan maganar Mutallab ce don abun yana min yawo a rai kuma ya kira na kasa ɗagawa."

Nace, "Ehh a kanshi ne, aww yanzu da kunyar ta sakeshi shine har iya kiranki, ko a farko bai kiraki bane saboda yana min kunyar faɗa min abun da yayi min, anyway sai mun hadu goben."

Jalila ta ce, "Okay babu damuwa, tunda karfe goma muke da lecture sai mu haɗu kamar wurin tara haka."

Na ce, "Okay, to shikenan."

Daga haka mu ka yi sallama, na jima zaune ina sharbar kuka na takaicin abun da aka aikata min sannan na miƙe na fita na dauko buta a dakin Umma na yi alwalla na ƙara zuba ruwa ciki sannan na maidata a inda na dauka kafin na wuce dakina na zube akan yamutsatstsar katifar dake a ciki, na jima kwance lamo ina zubar da hawaye kafin na samu bacci ya yi awon da ni.

Makarantar da ban je ba washegari kenan a sanadin tashin hankali na abun da ya faru a gidanmu a tsakanin Abbana da Kawu Bala.

Da safiyar ranar Abbana ya samu sabani da kaninsa Kawu Bala akan lamarina, Kawu Bala ya tsaya kai da wuya akan ban isa in saka a mayar dasu mutanen banza ba, hujjar itace ƙanwata Nadiya ta yi aure har da yaro amma ni na tsaya karatu naki aure yanzu da na samu mijin shine nike kaucewa, Ummana bata tsira ba domin magana ɗaya biyu sai ya sakata yana fadi yana maimaitawa, 'Uwarta ce take hure mata kunne, kai sarkin son ƴaƴa daga ta kawo maka magana sai kabi ka haye a kai.'

Na shirya zan wuce makaranta Kawu Bala ya fusata ya biyoni da icce, a guje na shige dakina na maido kofa ina maida lumfashi, na tsorata da katon iccen da ya dauko wanda babu tantama idan ya buga min shi sai ɗan buzuna, maganin kada ayi kada a fara, makaranta ce na yafe zuwanta a yau, na hakura sai gobe naje tunda ba kwana zaiyi a gidan ba.

Ganin shiru-shiru Jalila ta kirani, ban faɗa mata abun da ya faru ba sai cewa na yi, "Kawai na tashi ne na ji ban iya zuwa shiyasa na yi zamana." Daga ɗaya bangaren tace, "Ko baki da lafiya ne?" Da wannan dan wannan, bazan fadi dalili ba domin abu ne namu na cikin gida hakazakila ba zan yi wa kaina ƙaryar ciwo ba haka kawai na gasken ya kamani in boni in lalace.

Na ce, "A'a lafiya qalau."

Baiwar Allah sanin ni ba mai fashin makaranta bane ba hakanan ya saka jikinta yayi sanyi, ta kasa haƙuri har saida ta biyo daga school saidai kiranta na samu, ina ɗagawa tace, "Gani akan santar gidanku amma kiyi sauri tareda yaya Jabir nike kuma sauri yake."

Nayi hanzarin daidaita muryarta daga kukan da na gama sharba sannan nace, "To shikenan gani nan fitowa, a gaishe da min da yaya Jabir namu na gargajiya." Ta amsa da, "Gashi idan kin zo kin faɗa mashi da bakinki, ai kunfi kusa."

Wannan fitinar da muka wuni da ita ta saka na rikice na rasa inda na saka hijabina saidai katon mayafi na ɗaura akan atamfar da nike sanye da ita wacce ta kasance dinkin umbrella gown, na sanar da Umma zuwan Jalila sannan na fita.

Su ukku ne ita da yaya Jabir sai wani wanda ban san waye ba. "Rumana manyan kasashen yau kece da mayafi?" Jabir ya faɗa na tabbata ya yi maganar ne saboda mamakin ganina da mayafi, bana tunanin ya taɓa ganina da mayafi ba sai yau.

Na ɗan murmusa wanda na yi nasarar ɓoye damuwar dake ragargazata a zuci na ce, "Ina sauri na rasa inda na ajiye hijabin shine na fito da mayafi."

Jalila tace, "Ko na ce, nima na yi mamaki." Na leƙa bangaren mai zaman hakanan na ce, "Jabir shi abokin naka bai magana ne." Kafin Jabir ya yi magana wanda ya ke a motar ya taso min kamar wanda ya ke jira, "Ina da matsala dake ne? Ko kuma ance ne dole sai na yi maki magana?"

Saida ya yi magana sannan na gane ba wanda nike zaton ba ne, na yi tunanin Muslim ne ashema ba shi ba ne amma duk da ban yarda kaina ya kulle ba saida na mayar da raddi domin na ji haushin yadda ya yi min magana, a rayuwa na tsani raini, cikin ruwan sanyi na maida nawa raddin, "Ayyerh na yi tunanin muslim ne shiyasa na yi magana, akan tambayarka kuma, ehh ba ni da matsala da kai saidai tuni da zan yi maka murmushi sadaka ne, kalami mai kyau sadaka ne."

Tunda kuma na mayar da raddi shikenan magana ta wuce ya je ya ji da kansa.

Shi kanshi Jabir baiji ɗaɗin yadda abokin nasa ya yi min ba, ya kawar da maganar da faɗin, "Kin tadawa gimbiyata hankali saidai ta ganki garas sannan hankalinta ya kwanta." Kafin in samu zarafin maganar naji saukar mari a saman kumatuna; waye mai karfin halin da ya mareni a saman titi?

Na dafe kuncina na ɗago a cikin shirin zazzaga bala'i akan mai karfin halin da ya iya min wannan cin mutuncin a tsakiyar santa. Jikina yayi sanyi ganin Kawu Bala ne kanin mahaifina, ban iya cewa komai ba saidai hawaye da suke zubowa daga idanuna.

Abokin Jabir ne ya tambayar min ba'asin da ni na gagara tambaya, ya shiga tsakaninmu da zafinsa yana fadin, "Uban miye tayi maka da zaka mareta? Kana hauka ne!...." ya ƙarasa maganar da ƙaraji.

Kawu Bala ya taso mashi da fada, "Ehh haukan nike! Miye ruwanka dan iya?" Ban san yadda aka yi saidai jin sautin mari nayi, da farko nayi tunanin Kawu Bala ne ya mari abokin Jabir, saida na maida dubana inda suke sosai sannan na fahimci Abokin Jabir ne ya mari Kawu Bala.

Na waro idanu waje yayinda baki ɗaya jikina ya fara rawa na wannan gangancin da aka yi a saboda ni, dama ya lafiyar giwa ballantana kuma tayi ciwo, shikenan ni da Ummana mun boni a wajen Dangin Abbana.

Zai ƙara mashi Jabir ya rikeshi yana fadin, "Calm down Junaid."

Junaid yace, "Ka rabu da ni in koya mashi hankali, ban da wulakanci sai ya mari diyar mutane akan santa."

Ba Kawu Bala da aka mara har ni kaina da aka yi marin saboda ni saida na sha jinin jikina.

Kawu Bala yana zare idanu yace, "To ina ruwanka? Mi ya shafeka damu? Diyar dan uwana ne, Diyata ce ta zumunci."

Jikin Jabir da Jalila yayi sanyi amma shi Junaid ko a jikinsa, yace, "Sai kuma aka ce ka mareta a tsakiyar titi." Kawu Bala da har lokacin yake dafe da kuncinsa yace, "Amma sai ka tsaya ka ji dalilin da ya saka na yi marin."

Ya jashi gefe ban san mi Kawu Bala ya faɗa mashi ba, naga dai ya zaro kudi ya ba shi, ji nayi na muzanta kenan cinikin marin sukayi ya biya shi, wannan wulakanci ne kuma ba zan dauka ba, duk abun da Kawu Bala zaiyi min bazai saka in daina ganin girmansa ba, kawuna ne matsayin uba yake a wajena.

Yana dawowa wajen na tsareshi da tuhuma, "Kaga malam bana son shiga sharo ba shanu, miye kake takama da shi da har zaka saka hannu ka mari kanin mahaifina koda kake ganinsa bai girmeka ba sosai amma ni uba yake a wajena." Ya kalleshi ya watsar yace, "Amsa kike bukata." Da tsawa nace, "Ehh kuma dole ka bani amsa a nan a yanzu ko kuma in tara maka jama'a."

Jalila tace, "Rumana." Na ɗaga mata hannu nace, "A'a babu ruwanki a wannan maganar ki barni na koya mashi hankali ka mareshi sannan ka dauki kudi ka bashi kenan biyansa marin kayi, lallai rashin mutuncinka ya shahara."

Rashin sani wanda yafi dare duhu da nasan amsar da zan samu da banyi tambayar a wajen dake da mutane ba. A karo na biyu yace, "Amsa kike bukata."

Nayi mashi kallon kaskanci nace, "Ehhh kuma dolenka ka bayar domin ba zan dauki rashin mutunci ba."

Ya ja hannu zuwa gefe, na fizge hannuna ina binsa da mugun kallo nace, "Ban san iskanci, koda wasa kada hannunka ya ƙara kaiwa jikina, sai kwasheka da marin da sai hular kanka ta dunguri ƙasa."

Yayi tsaye kawai yana kallona da mamaki, da nasan abun da ya saka ya bayar da kuɗin da banyi haka ba. "Kuɗin neman aurenki da aka bashi ya kashesu shiyasa yake ta tada jijiyoyin wuya akan dole sai anyi auren domin kada bashi ya biyo gyarte."

Ji nayi na muzanta jikina yayi sanyi, ban iya ɗaga idanu na kalleshi ba, na juya jikina a sanyaye na nufi hanyar gidanmu ba tareda nayi sallama da su Jalila ba, babu abun da nike ganewa, har wani jiri-jiri nike gani ina haɗa hanya, har mamakin kaina nayi da na iya kai kaina gida a wannan yanayi.

Ina mamakin Kawu Bala, Abbana mai fahimta ne na tabbata idan ya faɗa mashi babu kudin bazai yi magana ba. Tunda na shiga dakina ban fito ba sai lokacin da zanyi alwalla, na kudura a zuciyata cewa babu wanda zaiji maganar a bakina. Saidai zancen duniya ba ya ɓuya, maganar marina da ya yi da ramamin da aka yi tazo har gidanmu, daga baya har maganar kashe kudi da yayi ta fallasa wanda ban san ta inda maganar ta fita ba.

Rai babu dadi muka kwana na cece kuce da ake tsakanin Abbana da danginsa shi yana faɗa akan mi yasa Kawu Bala bai faɗa mashi gaskiya ba, su kuma suna ɗaura laifin komai a kansa a cewarsu ya wulakanta ɗan uwansa akan kuɗi, maganar babu adalci ko kaɗan a ciki, yaushe ne ya san da maganar da har za'a ce ya yi wulakanci a kai, shifa maganarsa itace 'Ai da ya faɗa min ya san bazan ɗaga maganar ba, zan bayar ne a wuce wajen, ɗan uwana ne abun da yafi haka zan iya kawar da kai a kai.'

Amma sai suka zabi su juya maganar suyi mata fassara daban.

Abun da ya faru ya saka baki daya zaman gidan ya fita kaina ko kalaci ban yi ba na fice daga gidan na wuce makaranta, na samu empty class na zauna ina karatun Alk'ur'ani mai girma a cikin suratul Kahf yayinda nutsuwa da kwanciyar hankali yake saukar min, tabbas Alk'ur'ani waraka ne.

Aka yi sa'a Jalila ta shigo domin tayi karatu tana neman empty class da za ta yi karatu ta ci karo da ni ta yi mamaki sosai domin sai karfe sha biyu muke da lectures. Ta zauna a gefena tana faɗin, "Kawata kece da shigowa makaranta da safiya."

Nace, "Ke dai bari abubuwa ne sukayi min yawa." Ta dan kalleni tace, "Ban gane ba, mi yake faruwa?" Da mamaki nace, "Junaid bai fada maku bane?" Domin a tunanina ya faɗa.

Ta girgiza kai tace, "Junaid bawan Allah ina yaga lokacin fada mamu, shi ko magana bata dameshi."

Na kwashe abun da ya faru tsakanina da Mutallab na sanar da ita saidai ban faɗa mata ainihin yadda aka yi jiya ba hakazalika ban faɗa mata ainihin dalilin zuwana makaranta da wuri ba.

Abun yana min ciwo ba kaɗan ba, na jefa mata tambaya, "Jalila shin kin taɓa jin nace sai mai kudi zan aura?"

Da mamaki Rumana ta dubeni wanda alamu suka nuna tayi mamakin tambayar, jim tayi sannan tace, "A'a. Wannan abu ne da kowa ya sani, baki damu da abun duniya ba, mun sha magana akan haka, kin sha faɗa min ke miji na gari kike so koda bashi da ko sisi. Kin sha faɗa min cewa baki son auren masu kudi gwara ki auri talaka daidai ke."

Na dubi gefe kamar zanyi kuka sannan na juyo na dubeta na ce, "Amma duk da haka ban tsira daga kaidin maƙaryatan samarin zamani ba, Mutallab yayi min ƙarya, wannan abun yayi min ciwo matuƙa gaya, na yi kuka kamar zan mutu yayinda takaici da kunci suke ragargazata a zuci, wai ashe Mutallab mahaifinshi ya rasu amma yayi min ƙarya yace Alhaji Mahmoud ne mahaifinshi, ya ce mahaifiyarshi itace uwar gida, a lokacin ban kawo komai a raina ba saida aka sanar da ni cewa mahaifinshi ya rasu shekarun baya da suka wuce kuma Alhaji Mahmoud kanin mahaifinshi ne kuma mai kudi ne sosai sannan na fahimci wasan da ya buga min, da motocin da yake zuwa dasu wajena yana burga, a nan ne na gane yadda aka yi aka kwana a raya, zuciyata tana min zunga jina nike tamkar wacce aka yi wa KITSO DA KWARKWATA mai wuyar sha'ani."

Ta rike baki tana tu'ajjibi, lallai kaidai kaga mutum kawai sannan shi kuma mugu ba ya da kama, dariya tayi tace, "Kai... Woah... Amma wannan gayen ya raina maki wayo, shiyasa tun asalin farko na ce maki kinfi karfinsa gashi kuma tun ba'aje ko'ina ba ya nuna rashin dacewarsa dake, babu komai, Allah ya haɗa kowa da rabonsa na alheri." Na amsa da, "Amin."

Ina hasaso takaddamar da ake can ana yi a tsakanin Abbana da danginsa duk kuma ƙaryar da Mutallab ya yi min ce ta janyo amma mugun nunawa yake shi abun tausayi ne.

He is playing the victim while I'm the victim here.

Na kalleta kawai ba tareda nace komai ba, ta dafani tace, "Sabr, Sabr, Sabr dear. Maganar gaskiya Mutallab bai kyauta ba, ita gaskiya ɗaɗi gareta komai ɗacinta kuwa, saɓanin ƙarya wacce fure take bata ƴaƴa, ƙarya bata ɗaɗi ko kadan musamman ga wanda kake tunanin rayuwa da shi na har abada."

Da damuwa nace, "Jalila, mey yasa zaiyi min ƙarya? Gaskiya tayi a rayuwa, ya faɗa min gaskiya mana koda kasheni za ta yi, tunda na soshi tun bansan matsayinshi ba ai ƙaryar ba zata saka in ƙara sonshi ba, Mutallab ba mijin aure bane."

Jalila ta jinjina kai tace, "Hakane, Mutallab bai kyauta ba, ban taɓa zaton wannan abun daga gareshi ba, koda yake ai maganinki kenan, kince ba zaki auri mai kudi ba saboda kada ya ɗauka saboda kudinshi kika aureshi, ai gashi abun da talakan ya yi maki, ashe daukar mayyar kudi yake maki all along, ki ganshi dai sumi-sumi a idanu dai kamar mutumin kirki ashe bakin halin nashi yana a zuciya, mugu ba ya da kama."

Saida naja lumfashi sannan nace, "Jalila ki bani shawarar yadda zan yi mashi ya daina bibiyata, ya dameni sa kira, text message, shekaran jiya har gidanmu ya je."

Jalila ta ɗan yi jim sai kuma tace, "Kece zaki yanke hukunci da kanki domin kece aka yiwa laifin ni saidai inyi maki addu'a akan Allah ya kawo maki mafita." Daga nan bata sake magana ba.

Wayarta tayi tsuwwa ta zarota daga handbag ta amsa kiran ta ce, "Hello... Ehh na shigo... A'a ina medicine classes tareda Rumana... Okay kun baro hostel kenan, to shikenan babu damuwa."

Ta tsinke kiran ta dubeni tace, "Bindawa ce, wai tana son ganinki." Takaici ya kamani sanin zancen ba zai wuce Mutallab ya turota wajena ba. Na ja tsaki na ce, "Zancen ba zai wuce na Mutallab ba."

Ta miko min gorar ruwa na sha kadan sannan na rufe murfin na miƙa mata, tace, "Meyyy haka? Ai kina da jikka, ko kina nufin ni zanyi maki dakon ruwan."

Mu ka yi dariya, ta ciro gorar ruwa tasha ta rufe murfin ta maida a jikka ta miƙe muka sauko kasa, kai tsaye muka wuce venue din da muke da darasi, muka zauna a waje ɗaya, muna zama na ɗage niqab dake fuskata na maida hankalina baki daya akan darasin kasancewar course ne da nike tsoro sosai saboda wahalarsa, karfe sha biyu daidai muka fito daga lecture din, bindawa tace, "Rumana ina son magana dake akan..."

Na katseta da fadin, "Kinga ka da ki ɓata lokacinki akan maganar Mutallab, ki koma ki faɗa mashi soyayya ce na fasa, aure ne na fasa, wannan alakar ta riga ta wargaje ya je ya nemi wata."

Daga haka ban ƙara ba ban daɗa ba na janyo Jalila mu ka yi gaba, Bindawa ta riko hannuna ta ce, "Rumana don laifi Mutallab ya yi maki laifi amma ina son ki nuna da cewa sonki ne sanadi, ya sanar da ni ya yi hakan ne saboda yana ganin a matakin da kike zaki iya gudunshi saboda ba ya dashi, ki bashi wata damar mana."

Na fizge hannuna nace, "Tashin hankalin da Mutallab ya sakani ciki da ruɗani da saɓanin da ya janyo a tsakani, ina bakin cikin faɗa maki ko maza sun ƙare bazan auri wanda yayi sanadin saka iyayena a tashin hankali da damuwa. Ki je ki faɗa mashi ban soshi saboda abun duniya hakazakila karyar da yayi ta lalata komai don haka yayi ta kansa."

Na wuce, ina ji tana cewa, "Ai shima talaka mutum ne kuma arziki na Allah."

Maganar ta dokeni ba kaɗan ba, meyy mutanen yau suke son mayar da kansu ne, ga gaskiya kiri-kiri ana gani amma a juyar da ita saboda son zuciya.

Na fusata matuƙa gaya, ganin haka Jalila ta tausheni, "Sabr. Sabr. Sabr dear." Ban bi takan maganarta ba na juya a fusace na ce, "Eh hakane maganarki ita kuma karyar da ya yi miye mazauninta a wannan jawabin da kikayi, muna wa kanmu adalci, karfi da yaji nema kike ki nuna min wata kusan tafi wata, to koma miye kiji da shi, soyayya ce bana yi, yaje ya nemi ƴan mata ƴan karya masu cewa sai mai kudi, idan kuma abun ya yi maki haushi ai kema macece ki nuna mashi soyayyar."

Daga haka na ja Jalila muka bar wajen, komin banza na mayar mata da wacce za ta yi mata ciwo kamar yadda wacce ta faɗa min ta yi min ciwo.

Muna haka Jabir ya kira Jalila akan suna makarantar sun zo daukarmu, na yi mamaki da ta ce tare da Junaid suke, abun da ya faru jiya ya saka bana son ƙara haduwa da shi, kunyar abun ni ke ji, ina jin na muzanta.

Babu yadda banyi da ita ba akan ta tafi zan bi Bus amma tayi kememe ta nuna bata san zancen ba, har ƙaryar zan wuce library inyi karatu nayi mata amma tayi kunnen uwar shegu da ni, gashi babu dama in faɗa mata dalilin da ya saka bana son binsu, haka nan ina ji ina gani dolena na bita muka doshi inda motar take ina ji kamar kasa ta buɗe in nutse saboda kunya, kaina a ƙasa ina tafe sukuku kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.

Suna jingine da wata zukekiyar mota ruwan toka, tunda muka doshi wajen Junaid yake kallona sai a lokacin na ƙara gane kamanninsa, fari sol irin farin nan mai ɗaukar hankali kyakykyawa ajin karshe.

Lokacin da na hada idanu dashi saida naji gabana ya yanke ya fadi sai na nemi waccen kunyar na rasa kuma na rasa dalili, duk da gidanmu akwai maza masu kyau asalin kyau amma wannan kyanshi na daban ne, fararen gidanmu har yellow fatarmu takeyi saboda haske amma shi wannan haskensa na daban ne.

Maganar Jabir ce ta katse min hanzari, "Yan mata yane?" Ya faɗa da murmushi akan fuskarsa.

Nayi karfin halin amsawa da, "Lafiya lau yaya Jabir."

A bazata na jiyo muryar Junaid yana min magana, da muryarsa wacce take fita da sanyi yace, "Rumana babu magana."

Na ɗan kalleshi na tsayin dakiku ina juya maganarsa a masarrafar kaina shin miye nufinsa, shin yana sone ya raina min wayo? Izgilanci yake son yayi min ko kuma iyakata yake son nuna min akan abun da Kawu Baba ya yi, koma miye daidai nike da shi domin bazan bar magana a ciki ta kasheni sai na mayar da raddi saidai a mutu, itama masifa tana da ranar ta.

Ni Rumana guguwa ce daidai da kugun dukkanin wanda ya so cin zarafina, duk da abun da Kawu Bala ya yi abun kunya ce a matsayina na ƙanin babana amma ai ba a kanshi aka fara, bamu kaɗai muke da abun faɗa ba ballantana ya nemi yi min fariya a kai.

Kaina tsaye na mayar mashi da amsa da kalaman da ya yi min jiya, "Ina da matsala da kaine? Ko kuma ance ne dole sai na yi maka magana?"

Ya murmusa yace, "Ta tabbata abun da na yi maki jiya ne kike san ki rama, to yi hakuri, huce, kaina a kasa ina bada hakuri."

Dariya maganarsa ta bani har saida na dara, ya murmusa yace, "Kin san meyy kin tafi da ni?"

Mamaki nike anya kuwa shine? Har Jalila da Jabir sun yi mamakinsa saidai ban san miye dalilinsu na mamakin ba domin dai ya sha banban da ni nawa dalilin.

Na murmusa nace, "Kana da barkwanci." Shima ya murmusa ya ce, "Ke kuma kina da daukar abu da wasa, kince mashi yaya Jabir, nima ba yaya bane saidai ace min sweet Junaid."

Cikin raina na ce, "Wannan magananne ne, ba ya rasa abun faɗa."

A take na tattara tunaninsa na watsar bayan abun da Mutallab ya yi min yanzu mazan tsoro suke bani domin ba gane gabansu kake yi ba.

Da kanshi ya buɗe min mota yana mai furta, "Ranki ya dade."

Na yi turus ina tu'ajjibi, saida ya ƙara magana sannan na shiga, Jalila ta zauna a ɗaya bangaren yayinda shi da Jabir suke a gaba, Jalila tace, "Rumana ƙara min bayani ban fahimci nan ba." Tana nuna min handout dake a hannunta.

Junaid ya yi karaf ya ce, "Jalila ya da haka hira muke fa?" Ta ɗan murmusa tace, "To babu damuwa."

Jabir ya yi karaf ya ce, "Ban da mugunta ki faɗa mashi da maganar auren wani a kanta tun bai zurma da yawa ba."

Junaid ya ɗan kalleshi, har zan yi magana sai kuma na fasa, ta tabbata Junaid bai faɗa mashi komai ba.

Jalila ce ta katse shurun da ya wanzu a motar ta hanyar furta, "Sun rabu da Mutallab."

Da mamaki ya ce, "Ban gane ba, sunyi faɗa ko kuma kun rabu?"

Jalila ta ce, "Sun rabu, ko ni ce ba zan yarda in auri maƙaryaci ba."

Junaid idanunsa akan titi yace, "Jalila za mu yi magana." Ta amsa da faɗin, "To, babu damuwa."

Muna dosar hanyar unguwarmu na daina gane komai, zuciyata ta cika da tsoron abun da zan tarar a gidanmu na tashin hankali da ɓacin da na baro, ina tsoron abun da zan je na tarar, gabana ya fara faduwa, duk da faɗana amma ni nawa faɗan na fatar baki ne, lamari idan har ya shafi zumunci ba na wasa da shi musamman zumuncin Abbana da danginsa wanda a kullum neman dalilin da zasu ce ba'a kyauta masu ba suke yi, su fa idan za ka shekara kana kyautata masu to ba za su gode ba amma kuma duk wannan suka nema ya ce babu to kuwa sai su ɗauki  bakin hali su yafa su kirashi da mai hannun jarirai, sun mayar da kudinsa na gwammati su kuma nasu na ajiye, babu abun da suke tsinana mashi saidai shi su isheshi da bani-bani.

Ni suka fara saukewa, ina dosar kofar gidanmu na hango nacaccen tsaye a kofar gidanmu ya yi wuru-wuru da shi kamar mutanen kirki, ji na yi raina ɓaci dukkanin fitintunu da suke faruwa a tsakanin Abbana da danginsa shine sanadi amma saboda idanunsa babu toka shine yazo yana nuna shi abun tausayi ne a tausaya masa, tunda safiyar yau har zuwa wannan lokacin babu abun da na saka a cikina sai ruwan da Jalila ta ba ni, tashin hankali ya saka na gagara saka komai a cikina, saboda tsabar yunwa da gajiya dake dawainiya da ni har wani jiri-jiri nike gani.

Tun daga nesa na hangoshi, Mutallab ne tsaye ya rame ya fita hayyacinsa ya koma wani iri, yana tsaye yana kallona, na dauke kai na yi gaba ina jin haushinsa na abubuwan da suke faruwa a gidanmu.

Da saurinsa ya sha gabana kamar zai yi kuka ya ce, "Please Rumana ki ce wani abu."

Ji na yi raina ya ɓaci bayan duk abun da ya faru amma shine ya zo gabana yana min wannan maganar, saida na yi mashi mugun kallo sannan nace, "Aww so kake inyi magana to babu damuwa indai magana ce ka tara ka samu, dama na yi shiru ne domin shirun ya fi maganar zama alheri amma tunda har ka roka da kanka zan zazzage maka ta cikina. Mutallab tun wuri ka daina ɓatawa kanka lokaci kaje ka nemo mai irin halinka ku daidaita, ni Rumana bazan aureka ba, ni Rumana ba zan auri makaryaci ba, Ni Rumana bazan auri wanda yake barranta kansa da mahaifiyarsa ba, Ni Rumana na ce bazan aureka ba don haka sai kaje ka nemi wata tunda bani ɗaya bace mace a garin Katsina, akwai sauran mata birjik a garin Katsina da kewaye, farare, bakake, dogaye, sirara, ƴan mata da zawara, sai wadda ranka yake so."

"Ke ce a zuciyata," Mutallab ya faɗa.

Ya dafe saitin zuciyarshi yana tari a yayinda na tsallakeshi na wuce gida. Yunwa da na sha ta tado min ulcer, ba karamar wahala nasha ba a wannan ranar, wahala na sha sosai kamar zan mutu, saida na fidda tsammani daga rayuwa.


Har Kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)