ZARGEN ƘAYA

3

by @aishaangel

*ZARGEN ƘAYA*



     *NA*
*AYSHER ANGEL*

Page 3

WhatsApp ***

*The Fractured Bond: When Resentment Runs Deep And Innocent Pay The Price...*


Ashe bayan na shigo gida Mutallab zubewa yayi kasa ba ya lumfashi, aka kwasheshi aka wuce da shi asibiti, ban sani ba, kuma babu wanda ya sanar da ni.

Washegari da marece ina zaune daga dakina na jiyo Yaa Ahmad yana faɗawa Umma ta bashi abinci ya kai asibiti, bayan ya wuce, na fito na dubeta da mamaki na ce, "Umma wanene babu lafiya?"

Umma tayi shiru tana kallona saidai bata ce komai ba, nima kuma ban sake mata maganar ba saidai na yi matuƙar mamaki akan shirun da ta yi wa tambayata.

Washe gari tunda muka shiga lectures har muka fito kira yana shigowa a wayata babu kakkautawa sai kace wacce taci ta gudu daga gari, ga shi ina aji idan wayar ta yi ƙara fita waje ta tabbata a gareni, Allah ya taimakeni na sakata wayar a silent, ka'ida ne kafin kowace lecture ina saka wayata a silent domin gujewa irin wannan, abun da ya ƙara rikitar da ni shine ankara da na yi akan mahaifiyar Mutallab ce take kira lambar tawa, tunda muka fito daga lectures nike tarabbabi, course dinmu suna da hirar wata test mai zafi da mukayi kafin shiga lectures amma ni nawa hankalin ya tafi akan tarin miss calls da mahaifiyar Mutallab ta yi min, na shiga tsaka mai wuya na rasa mi zanyi, idan na amsa kiran ince mata mi?

Cikin hakan ne kiranta ya ƙara shigowa, na zubawa wayar idanu kawai ina tarabbabi, Jalila ta lura ta taboni na yi firgigit, ta ce, "Ki amsa kiran mana."

Kamar zan yi kuka na ce, "Ba wai amsa kiran ba, abun da zan faɗa idan na amsa kiram shine ban sani ba, uwa uwa ce, ban san mi zan ce mata ba."

Jalila da ba ta gane inda maganata ta dosa ba tace, "Ban gane ba, care to explain."

Fuskata dauke da tsantsar damuwar dake ragargazata a ciki na ce, "Mahaifiyar Mutallab ce take kira, mutuniyar kirki, mai mutunci da dattako, amma kin san a matsayin mi Mutallab ya gabatar min da ita, maƙaryacin ce min ya yi matar kawunsa ce wanda ya rasu, ta dauki cikinsa tsayin watanni tara ta haifeshi ta raineshi har ya girma ya kai yadda ya ke amma wai yake jin kunyar gabatar da ita a matsayin mahaifiyarsa, wannan lamari da mi ya yi kama, saidai a kirashi da abun turr da Allah wadai. Tausayi take ba ni, a gefe guda kuma ina jin kunyar na abun da zan sanar da ita."

Jalila ta ce, "Ki kashe wayar mana."

Na girgiza kai domin shima ba zaɓi ba ne ba, girman da take da shi a idanu da kuma mutuncin da nike ganinta da shi bazan iya kashe mata waya ba.

Na rubuta sakon kar ta kwana wato text message na tura mata shi kamar haka;

'Ammi kiyi hakuri, ina hujja na dalilin da ya saka na rabu da Mutallab, na rabu da shi saboda yayi min ƙarya akan komai ciki har dake uwarsa mahaifiya wacce ta yi dawainiya da shi tsayin shekaru, amma ya gagara gabatar dake a matsayin mahaifiyarsa sai ce min yayi ke matar kawunsa ce, Ammi ki gafarceni amma na yanke hukuncin ba zan iya rayuwa da shi ba, idan har zaiji kunyar alakanta kanshi dake da kika dauki cikinsa kika yi wahalar dawainiya da shi tsayin lokaci, kenan ni da na ganshi da girmansa ko sharar kasuwa sai ta fini mutunci a wajensa. Lokacin da girma ya fara cimmani shi kuma a lokacin yana jin ganiyarsa karamin aikinsa ne ya nuna ni yace yayarsa ce ko ma yace gyatumarsa ce.'

Na dubi Jalila na ce, "Na tura mata text message."

Jalila ta amshi wayar ta duba sakon ta ce, "Har ta bani tausayi, ka haifi ɗa amma yana kunyar alakanta kanshi da kai saboda baka da ɗaudar duniya, wallahi haushin Mutallab ni ke ji sosai, ji ni ke kamar in ganshi a gabana in ci ga ba da dukansa, maƙaryacin banza kawai."

Na dubeta kawai saidai ban ce komai ba, har na koma gida Ammi bata sake kira ba, kamar in kirata sai kuma na fasa, bayan na fito daga wanka na zauna zanci abinci, wani yaro ɗan makotanmu ya shigo wai ana kirana, jim nayi sannan nace, "Waye? Ina nufin wanda ya aikoka ka sanshi."

Na tambaya ne saboda Mutallab yasha aikoshi kirana, kenan idan Mutallab ne zai ganeshi, ya girgiza kai wanda ya tabbatar min da ba Mutallab bane ba, na cika da mamaki ina mai tambayar kaina, to waye kuma? Nifa ban shirya shiga wata soyayyar ba musamman a yanzu da nike tsaka da jinyar raunikan da Mutallab ya yi min a zuciya ba.

Na ce, "Ka je ka ce mashi gani nan fitowa."

Na zura hijab tareda zura takalman soso na bi bayansa bayan da sanar da Umma sallamar da aka aiko ana yi da ni, ashe Ibrahim ne abokin Mutallab, muka gaisa a mutunce ya yi shiru nima na yi shiru, sai shine ya kawo karshen shirin ta hanyar cewa, "Baby kin san Mutallab ba shi da lafiya kuwa?"

Na kalleshi da mamaki sai kuma na girgiza kai ba tareda na ce uffan ba, ya ce, "To Mutallab dai ba shi da lafiya, yana can rai a hannun Allah. Ranar da ya zo nan na karshe bayan kin shiga gida ya zube kasa ba ya lumfashi aka kwasheshi aka wuce da shi asibiti."

Na yi jim sai kuma nace, "Allah ya bashi lafiya."

Ibrahim ya ce, "Baby, ina ganin ya kamata ku yi magana."

Da sauri na shiga girgiza kai ina mai faɗin, "A'a bai kamata mu yi magana da shi ba."

Da mamaki yake kallona, "Amma mi ya hadaku?" Ya tambaya.

Kenan bai faɗa masu dalilin rabuwarmu ba, koda yake abun ne da kunya, ba zai iya faɗa ba saidai ya yi ta marairacewa domin a tausayawa mashi ni kuma a zargeni, ni ce dai kaina tsaye zan fada, babu dalili da zai saka in yi shiru a tura min laifin da ba laifina ba.

Kaina tsaye na ce, "Ƙarya yayi min akan matsayinsa, ya nuna min shi dan masu kudi ne, ƙarya daban-daban har ummarsa ce min yayi matar kawunsa ce."

Da mamaki yake kallona, na lura da wani abu duk wanda ya san Mutallab idan na faɗa mashi yana mamaki amma wannan ba damuwata ba ce ba, mutum tara yake bai cika goma ba don haka su yarda ko kada su yarda shima yana da nashi nakasun.

"Na riga na yanke hukunci, magana ta ƙare, ni Rumana ba zan aureshi ba, ni Rumana ba mayyar kudi ba ce ba, tunda har ya mayar da ƙarya halinshi sai yaje ya nemi makaryaciyar mace irinsa suje suyi ta ƙaryarsu."

Na ja fasali na ce, "Ba zan gajiya da fadin ba ni da laifi ba koda kuwa ba za ku fahimceni ba, wannan shine abun da zan ci ga ba da maimaitawa duk da mafi yawanku ba za su fahimceni ba, amma da in auri makaryaci da yake kunyar nuna uwarsa mahaifiya gwara ace saboda bashi da kudi na gujeshi, Allah ya san zuciyata, ya san ba haka bane."

Daga haka ban ƙara cewa uffan naja kafafuna na koma gidanmu, na barshi a tsaye, a bakinshi naji rashin lafiyar Mutallab sai a lokacin na fahimci Mutallab ne wanda Yaa Ahmad ya kaima abinci asibiti, jim na yi na ɗage kafaɗa na shige dakina koma miye shine ya janyowa kansa, alhakin Ammi ne yake bibiyarsa, ta haifeshi amma yana barranta kansa da ita simply saboda bata da kuɗi.

Ina dora kuguna akan yamutsatstsar katifata sakon text message ya shigo wayata, na duba naga bakuwar number ce da sakon kamar haka;

'Yadda aka yi aka kwana a ragaya shine sonki da kaunarki da sukayi min kane-kane a ƙoƙon zuciyata, ina matuƙar farin cikin kasancewarki a cikin rayuwarki, haɗuwa dake tabbacin addu'ata ta karbu ne, zan ci ga ba da sakaki a addu'a Allah ya kawo maki sassaucin wannan lamari. Hakazalika kada ki manta taken soyayyarmu shine ina da barkwanci ke kuma kina da daukar abu da wasa kuma a cikin hakan ne za ki yi nutso a soyayyata ba tareda kin farga ba saidai kin tsinci kanki ana kiranki da MATAR JUNAID.'

Wannan shine abun da aka turo, daga gani babu tambaya Junaid ne musamman MATAR JUNAID da ya rubuta a karshen sakon, message na hudu kenan yana turo min tun bayan rabuwarmu amma bai taɓa kira ba, abun da na sani shine na fara sonshi, wani message ya ƙara turowa ban san lokacin da saki dariya ba, ganin abun da ya turo;

'Ga kyauta daga gareni, murmushi sadaka ne, kada ki bari damuwar duniya ta hanaki samun ladar wannan sadakar bugu da ƙari murmushi yana wa kyakykyawar fuskarki kyawu, idan kin musa kuma to ki kalli fuskarki a sakona ki duba za ki tantance gaskiyar da ke cikin magana ta.'

Wata kyauta kuma, kai Junaid yana da abun dariya, kasance da sakoninsa da maimaita karantasu yana rage min kaso mai yawa na cikin damuwar da ƙaryar Mutallab ta sakani a ciki, da kuma tashin tashinar da ake yi a tsakanin Abbana da ahalin akan case din Kawu Bala wanda ya kada baki ya ce ni ce na saka Junaid ya mareshi su kuma sun dauki maganar sun zauna a kai suna ta tsegunaguni ba tare da sun yi bincike ba.

Umma ta kwala min kira, na fito ta nuna min yaron da ya ke tsaye ta ce, "Aikoshi aka yi wajenki."

Yaron ya miƙa min wani karamin kit da aka yi wrapping, ya ce, "Wani mai mota ne yace in kawo maki."

Saida na amsa sannan nace, "Ina wanda ya baka yake?" Yace, "Ya tafi."

Murmushi ne ya suɓuce min gane aikin Junaid ne, na dubi yaron nace, "Na gode, kace wa Naja'atu ina gaidata."

Yaron ya gyaɗa kai sannan ya juya ya fita, na yi tsaye ina murmushi, soyayya gaskiya ce kuma ni Rumana Yusuf na faɗa kogin son Junaid na rabu da dakon wahalar Mutallab, ina juyawa na hango Umma tana kallona saidai ba ta ce da ni komai ba, kunya ta kamani, da sauri na shige daki.

Na kutsa kai dakina na zauna a gefen katifa na warware wrapping din, "MashaAallah," Na furta ganin abun da ya ke a ciki, wani karamin kit ne, daidai rikewa a hannu, ina buɗewa na ga ashe madubi ne a ciki, murmushi ya subuce min, ranar wuni nayi ina kallon fuskata a madubin ina murmushi, tabbas gaskiya ya faɗa da ya ce murmushi yana min kyau, na gani kuma na shaida akan cewa kyau yana yi wa kyakykyawar fuskata kyawu na gaske-gasken.

Washe gari bamu da lectures, tunda safe nike a gida ban fita ba, da hantsi ina zaune a daki ina ƙara karanta message din Junaid da suka kasance min ababen debe kewa ina murmushi, Jalila ta shigo, na ɗago da sauri ina fadin, "Kai ƙawata har kin bani tsoro!..."

Jalila ta rike kugu tace, "Aaahhh lallai wato har kina da bakin magana, ina ta sallama kika yi min shiru, kin zubawa wannan gwaramar wayar taki idanu kina murmushi kamar wacce ta faɗa soyayya da wayar salula koda yake watakila hakan ne abu a duhu."

Na ɗan kalleta kallon lallai kin ci abinci, "Wayata kike kira da gwarama, to babu komai, muma Allah ya bamu kudi mu sayi shafa shafa mu raye gori."

A tare mu ka yi dariya, tace, "Ki dai rage mako ki sayi wayar zamani kawai."

Na ɗan harareta nace, "Ohhhh, to na ji, hausawa suka ce ɗan guntun gatarinka yafi sari ka bani."

Na murmusa na ce, "Ki zauna mana."

Jalila da neman magana ta harareni tace, "Nima gidanmu ne, idan zan zauna ai zama zanyi."

Nayi dariya kawai, tace, "Ke tare nike da sweet JB har da Junaid, kuma kin san Allah idan kika ɓata lokaci bomb zan haɗa maki kamar yadda nasu bomb din yake jiransu don haka ki yi sauri ki shirya ko kuma in yi maki halin."

Ina mata magana ta fice, ina ji tana cewa Umma su Jabir za su shigo gaidata, Umma tace, "Aaahh kice manyan baki gareni, to jeki dakina ki dauko tabarma ki shimfiɗa masu."

Cikin raina nace, "Tofa lamari ya girmama koda yake shigowar Junaid a rayuwata alheri ne, yana rage min kunci da damuwar Mutallab kuma ina ji a jikina idan na aureshi na yi dace miji na gari samfurin ta more miji."

Na laɓe a daki naki fitowa, Ina jin shigowarsu, Jalila ta shigo tana dariya kasa-kasa, na ce, "Besty kina da damuwa, bomb dinsu kenan kika sakasu shigowa babu shiri."

Saida ta zauna sannan tace, "Kinga kuwa yadda suka zaro idanu da na faɗa masu abun da na kitsa, haka suka shigo kamar wasu marassa gaskiya, suna can suna sunkuye-sunkuyen kai na gurfanar su a gaban sararkuwa."

Da ya ke ban dade da fitowa daga wanka ba, powder kawai na murza, na shafa kwalli, na janyo dogon hijab na aje a gefe.

Bayan sunyi sallama da Umma sun fita babu jimawa wayar Jalila kirar samsung ta fara tsuwwa, ta kwashe da dariya, "Sweety ne," ta sanar da ni.

Nima dariyar na yi na ce, "Ki ɗaga kawai ki amshi hukunci."

Ta ce, "Bari kiga." Sai kuma ta ɗaga kiran tareda kanga wayar a kunne ta maƙe murya tace, "Halo sweety na nawa ni kaɗai."

Saida tayi dariya sannan ta ce, "To an gama ranka ya dade, gamu nan fitowa ni da Gimbiyar Junaid." Ta dubeni tace, "Muje."

Ta yi sororo tana kallona ganin na zumbula dogon hijab har kasa, na gane manufar kallon na ce, "Ke nifa da hijab zan fita."

Ta ɗan kalleni ta ce, "Amma dai da wasa kike ko?" Na girgiza kai, da tsagwauran gaskiya na ce, "Da ita zan fita, barshi ya fara sona saboda tarbiyyata, kamalata, ilimi da rikon addini idan ya so daga baya sai ya ga kyawun da nike ɓoyewa a shigar kamala da ni ke yi."

Babu zato babu tsammani Jalila ta kama hannuna tana mai faɗin, "Please Rumana kada ki watsa mamu kasa a idanu, Junaid ya ɗaɗe a cikin damuwa yayinda farin ciki yayi mashi ƙaura  na dogon zango, sai a yanzu shigowarki rayuwarshi ya dawo mashi da farin ciki da walwala."

Na jinjina kai ina mamakin miye ya rushe mashi farin ciki har haka, miye tushen damuwar da take faɗa min, hausawa suka ce rashin sani ya fi dare duhu, da na san shigowata rayuwarsa zai ƙara sakashi a wata damuwar ne da bazan kulashi ba.

Muka fito tsakar gida inda Ummana take zaune, ban san abun da zan ce mata ba sai kawai na jera da Rumana muka fice ba tareda na ce da ita komai ba. Itama ba ta nemi ba'asi ba.


*******

Na ɗan tsagaita daga tuna rayuwata ta baya ina mai sauke dogon lumfashi har ila yau dai gulmata mutanen gidan sukeyi, kaico rashin sani ya fi dare duhu, a lokacin da na san abubuwan da za su faru kenan da bazan kula Junaid ba amma saidai rashin sanin shine ya saka na kulashi daga baya abun ya juye ya zame min HAWAYE AKAN RUWA mai wahalar gane kamanni ko kuma in kirashi da KITSO DA KWARKWATA mai wuyar sha'ani.

Zumuncinmu a yau kamar TABARMAR ƘAYA ce wanda yake ciki shine kawai ya san rigingumu da suke a ciki, shiyasa duk yadda kake ganin ana zaman lafiya idan ka matsa kusa za ka ga akwai matsaltsalu, kawai dai akwai masu hakuri ne a ciki shiyasa wasu za ka ga kamar babu damuwar komai. Ke da ni da ku ya kamata su zama masu hakuri da kawar da kai ta hakane zamu zamo Jakadun zaman lafiya a cikin danginsu kamar dai yadda mahaifina ya kasance a cikin danginsa masu cike da tsegumi da son zuciya, yasu-yasu kiris suke jira su fara zuba bala'i barinma shi da suka mayar karkatacciyar kuka mai ɗaɗin hawa a tsinko reshe.

Ganin shiru-shiru ban fito ba, Nadiya ta shigo tana kallona da damuwa ta ce, "Ba dai zama kikayi kina karawa kanki damuwa ba, komai za su faɗa ki rabu da su, su suka sani, ni wallahi ban ga amfanin wannan zaman nasu ba, babu wacce takeyi wa mamatan nan addu'a saidai faman gulma suna zaginki."

Na share hawayen da suka zubo min na dafa Nadiya wacce ta kasance ƙanwata na ce, "Nadiya ki yi mamu alkalanci shin abun da ya faru, ni da shi waye yake da laifi?"

Tace, "Laifinshi ne..." na katseta da faɗin, "Kuma na ce na yafe amma sunki fahimtar hakan sun zo suna daura min laifin suna zagina suna ci min mutunci."

Nadiya ta ajiye abincin da ta shigo da shi tana faɗin, "Ki rabu da su rashin ilimin addini ne yake dawainiya da su, na zuba masu idanu ne kawai domin a rabu lafiya amma da sai na taka masu burki, lamarin mutanen yau sai su kinga dai sun san ina wajen amma basu fasa maganar da su ke yi a kanki ba."

Ta saki wani malalacin murmushi na ce, "Da gayya suke faɗa domin ki ji idan muka tayar da faɗa sai mu buge da guzuma su harbi karsana, kina ji cikin da ban haifa ba amma faɗa suke suna maimaitawa akan ba zasu bari jininsu ya tashi a cikin talauci gidanmu ba, ki ji cin mutunci koda nasan mahaifina ba shi da shi amma nasan cewa ya fi karfin abun da gidanshi zasu ci da sauran hidindimunsu na yau da kullum, amma saboda ba ya da babban gida da katuwar mota shine suke kiranshi da talaka, sun manta cewa a dare Allah kan yi Bature, arziki da talauci na Allah ne."

Nadiya ta ce, "Mu yi haƙuri, haƙuri ba ya faɗuwa ƙasa banza."

Ta fara zuba min abincin, na yatsine fuska na ce, "Ki barshi ba na jin yunwa." Ta murtuke fuska ta ce, "Baki so zaman lafiya ba kenan, zakici abincin ne ko sai an jimu, idan kika zauna da yunwa ta illataki mu da ke ne muke da damuwa, su babu abun da ya shafesu dama ba kaunarki su ke yi ba."

Ta tusani a gaba saida ta tabbatar na koshi sannan ta kwashe sauran abubuwan ta fita da su ta barni zaune ina tunanin rayuwa. Shin waye na aura? Junaid ko kuma Mutallab? Ku biyoni domin jin waye na aure da kuma yadda aka yi lamarin ya juye ya zame min tamkar HAWAYE AKAN RUWA mai wahalar gane kamanni ko kuma in kirashi da KITSO DA KWARKWATA mai wuyar sha'ani ta yadda wasu lokuttan nike jina kamar wacce ta kamu da ciwon MUTUWA A MAƘOSHI.

********

A gefen gidanmu sukayi parking dalleliyar motar kirar Mercedes Benz, suna zaune samanta daga baya, na jingina da motar yayinda Jalila ta wuce bayan motar ta zauna kusa da Jabir.

Yau ɗaya sai na ji Junaid ya yi min kwarjini na kasa haɗa idanu da shi, tunda ya doso inda nike na soma shakar kamshinsa mai sanyi wanda kamshinsa kansa na musamman ne, na maida kaina gefe ina mai cigaba da shakar kamshinsa yayinda bugun zuciyata yake karuwa, abun da ya fara furtawa ne ya saka na ɗago na kalleshi da sauri, cewa ya yi, "Ina sonki."

Cikin raina nace, "Ikon Allah, wannan magananne ne."

Ya ɗan ware idanu ganin yadda nike kallonsa yace, "Ehh ina sonki, gaskiyar kenan. Kin san mey? Lokacin da muka shiga ciki kunya naji kamar in nutse kasa, Allah ya soni manyan kaya ne a jikina, ai da Umma ta ce ba za ta ba ni ke ba."

Na yi gefe da kaina ina dariya mara sauti, yace, "Kin san meyy? You look lovely."

Na murmusa, ya miƙa hannu ya ce, "Ara min wayarki."

Ta ɗan yi jim, ba kunyar yaga yadda wayar take ni ke yi ba domin dukkanin wanda ya sanni ya san cewa ba na raina abuna ko ya yake kuwa. Ina mamaki ne na buƙatar amsar wayar da ya yi, Shin miye zaiyi da ita? Shine tambayar dake kai kawo a masarrafar tunanina. Na manta da akan message dinsa nike na miƙa masa aikuwa ya gani, ya murmusa yana faɗin, "Ta tabbata na fara shiga zuciyar RUMANA."

Sai lokacin na fahimci mantuwar da na yi, na kalli gefe kawai ina murmushi, hasken wayar ne ya dauke, ya yi jim yana juyata da alama gani yake kamar idan ya latsata zata samu damuwa na fahimci hakan ne ta hanyar yadda yake ta takatsantsan da ita, kuma iya gaskiyarsa kenan, ba wai izgili ba, kuma banga laifinsa ba domin nima kaina da na jima ina amfani da ita lallaɓawa nikeyi da ita ballanta kuma shi wanda yake riƙe manyan wayoyi masu tsada, ya dubeni ya ce, "Tsoro nike kada in latsa ta samu damuwa, amma ina zuwa."

Ya koma wajensu Jabir, ina ganin lokacin da ya mikawa Jabir wayar ya zaro sim card ya amsa, ya dawo ya buɗe bangaren mai zaman hakanan yace, "Shiga, zamuyi magana."

Na dubeshi na dubi murfin motar na yi jim sai kuma na shiga saidai ban rufe kofar ba, ya zagaya ɗaya bangaren wato bangaren direba, ya zaro kwalin kirar samsung fold, ya saka layina a ciki sannan ya kunnata yayi ƴan danne-danne, ya zaro wayarshi ya hadasu da alama abu yake turawa.

Yanayinsa yafi min kama da na ƴan boko gashi a gefe guda ina tsoron maimaita zaɓen tumun daren da na yi a bugiren amincewa soyayyar Mutallab, na tabbata har da rashin ilimin addini ya saka Mutallab ya aikata ƙaryar da ya yi, duk mai ilimi wanda ya san darajar uwa ba zaiyi haka ba, na yanke shawarar inyi wa tufkar hanci a wannan lokacin da abun baiyi nisa ba, idan yaso idan ba ya da ilimin sai ya fara nema ko kuma mu rabu kowa ya kama gabansa, tunda dai babu dole, an shani na warke ina ganin redflag zan gudu da kafafuna tun ba'a datse min su ba, na ɗan dubeshi na ce, "Bari in dauko Alƙur'ani a gida ka duba min, hardata ce nike jin kamar ta samu damuwa."

Ya dakatar da ni ya zaro Alƙur'ani ya miƙa min, na amsa na buɗe daidai inda ya saka alama a cikin Suratul Nisa'i, a rayuwata ina son SURATUL NISA'I da kuma SURATUL RAHMAN, na buɗe daidai inda nike da damuwa, na miƙa mashi nayi A'uziya tareda Bismillah, kafin na fara rero karatu a cikin SURATUL A'ARAF a cikin kira'ata mai sanyi, ko lokacin da mukayi hadda ƴan ajinmu suna yawan cewa nice ta biyu a dadin kira'a yayinda wata Shamsiyya ƴar rafukka na zama ta ɗaya wacce babu tamkarta a cikinmu, nasha mamaki sosai a lokacin da ya fara cina gyara yana gyara min inda na yi kuskure, maza masu ilimin addini kuma suke amfani da shi suna da dadin zama, ji na yi ya burgeni, saida na kai inda nike hari sannan nasa aya, a nan yake faɗa min shima Mahardacin Alƙur'ani ne.

Ya ɗora da faɗin, "Ina da shekaru sha biyar na haddace Alƙur'ani mai girma, kannena Hassana da Hussaina yanzu haka makarantar sekondire suke amma kowacensu tana sittin a kanta, muna godiya ga iyayenmu fatan shine Allah ya saka masu da alheri na yadda suka jajirce su ka yi tsayuwar daka domin ganin mun yi ilimi." Na amsa da, "Amin."

Ya ja fasali yace, "Ki rinƙa kula da haddarki, mafi yawan dalibai suna sakaci akan bibiyar haddarsu ne shiyasa take zubewa, saboda bibiyar yafi masu wahala akan hardar."

Na jinjina kai abun da yake faɗa min shine kwatankwacin abun da Ustaz Sulaiman Malamin mu yake yawan faɗa mamu.

Taku Har Kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)