4
by @aishaangel
*ZARGEN ƘAYA*
*NA*
*AYSHER ANGEL*
Page 4
WhatsApp ***
*The Fractured Bond: When Resentment Runs Deep And Innocent Pay The Price...*
Junaid ya miƙa min Alƙur'anin saying, "Ki ja min dukkanin inda ranki yake so mu gani nima haddar tawa tana nan ko kuma ina buƙatar ƙara ƙoƙari akan wanda ni ke yi."
Tunda ya fara rera karatun nutsuwa ta sauka a wajen, ji nike kamar kada ya daina saboda yadda kira'arsa take min dadi a kunnuwa, the more yake rera karatun the more yake ƙara tafiya da ni, kira'arsa wata aba ce ta musamman a wajen ɗaɗin saurare, MashaAallah, a yau na ji a jikina cewa na samu mijin aure, fatana Allah ya sa mai amfani ne da ilimin da ya ke da shi ne.
Na lula a duniyar tunani na tsinkayi muryarsa yana tambayata, tambayar da matuƙar bani mamaki da ɗaure min kai, domin buɗar bakinsa cewa yayi, "Ina ƴar biyunki?"
Na dubeshi da mamaki, yace, "Ina nufin twins sister dinki."
Na girgiza kai na ce, "Ni ba ƴan biyu ba ce."
Junaid ya karkato min majigin wayarsa yadda zan iya ganin majiginta ya ce, "Ina nufin wannan ta kusa da ke."
Ashe Nadiya ya ke nufi, kanwata wacce shekaru biyu da watanni biyar ne a tsakaninmu amma da ya ke kusan tsayinmu ɗaya da kuma matuƙar kamanni da mu ke yi sai mutane suke mamu kallon tagwaye.
"Ƙanwata ce Nadiya," na sanar da shi.
Ya ware idanu da tsantsar mamaki ya ce, "A idanu kunfi kama da tagwaye, ki kirata mu gaisa."
"Tayi aure har da yaronta guda daya, sunansa Najib, ina ajin karshe a makarantar secondary na nuna karatu nike son in yi, Abbanmu ya siya min Jamb na zana naci na nemi admission na samu, ita kuma tana gama secondary ta ce aure take so, Abbana irin iyayen nan wadanda basu tauye yaransu duk da karatun yaso ta fara kafin auren amma tana nuna auren take so sai ya yi mata, da auranta ta fara diploma kuma Alhamdulillah ta kammala duk da haihuwa da tayi a tsakani amma ta jajirce har saida ta gama."
Na ja fasali na ce, "Mu shidda iyayenmu suka haifa, Yaya Ahmad yana aiki, Yaya Mustapha yana karantar likitanci a A.b.u Zaria, Yaya Ayan shi kuma a london yake karantar likitanci, daga shi sai ni sai Nadiya sai autanmu Affan ɗan shekara daya da watanni, shi kam ba ya san bakuwar fuska kun yi sa'a yana barci kuka shiga gidan da ya saka maku kuka, nifa sai nike jim kamar gani yake idan baki sun zo zasu tafi da shi ne shiyasa yake saka masu kuka."
A tare mukayi dariya, ya ce, "Afuwan, a wajen Jalila na samu hotunanki."
Koda bai faɗa ba, na san wannan aikinta ne tunda a wayarta nike ajiye hotunana kasancewar ba ni da babbar waya, ina ajiye hotunana a wayarta ne a zuwan idan na samu waya sai in turo.
Ya fuskanceni kafin yace, "Sunana Junaid Muhammad, mahaifina ɗan karamar hukumar Bindawa ne ta nan jihar Katsina, ita kuma mahaifiyata haifaffiyar unguwar liman ce ta nan jihar Katsina, mu ukku a wajen mahaifanmu, ni da ƙannena tagwaye Fatima da Zahra, mahaifinmu ya rasu shekarun baya da suka wuce, muna rayuwa tareda mahaifiyarmu da ƴan uwana twins, na yi degree dina na farko da na biyu a kasar london, na karanci architectural engineering... Uhm... I'm feeling thirsty, can I get water?" Ya faɗa yana mai tsareni da na mujiyarsa.
Da wannan don wannan bai yi kama da wadanda zasu sha ruwan tulu ba ni kuma ko ranyo bana da shi ballantana in siya mashi bottle kuma dai yadda Maman Dijeh take da aikin bin bashi bazan ci bashinta ballantana har ta tayar hankali da aike babu safe babu dare, maƙota sun ce har Allah ya isa takeyi idan mutum ya kwana bai aika mata da kuɗinta
Na ɗan murmusa sannan na ce, "Eh akwai amma na tulu ne, tulun dake dakin Umma, ruwan suna da sanyi, idan kana so sai in zubo maka."
Nifa ƴar gaskiya ce, diyar talaka nike shiyasa na fito na faɗa mashi gaskiya, idan bai so ya saka kuɗi ya sayi na gora sai yasha.
Nayi tunanin zaice ne a'a amma ga mamakina sai na ji ya ce, "Kawo min dama nayi kewar ruwan randa rabona dasu tun zuwanmu Bindawa na karshe."
Na yi murmushi sannan na ɓalle murfin motan na fito na taka a hankali na shige gidanmu, na tarar da Umma inda muka barta, ta kalleni da tuhuma ta ce, "Mi ya zaunar dake wajen?"
Nayi shiru sai kuma nayi sauri nace, "Ayyerh Ummana, Abokin Junaid ne yake jin kishirwa shine zan ɗebar mashi ruwa a tulunki." Na faɗa mata haka ne domin in kawar da waccen maganar.
Umma ta kalleni na tsayin wasu dakiku sai kuma tace, "Amma mi ya hana ki amso mashi pure water gidan Maman Dijeh?"
Na ce, "Umma mai kudi ne sosai bazai sha ba, ni kuma bani da kudin da zan siya mashi ruwan gora shiyasa na ce mashi akwai tulu a dakinki idan yana son ruwan telu yace torh."
Ta ɗan yi jim sai kuma tace, "To shikenan amma na yi maki tambaya baki amsa ba. Mi ya zaunar dake waje?" Ta maido min tambayar da na gocewa.
Nayi tsuru-tsuru da idanu na rasa abun da zance mata, ta ce, "Shikenan jeki ki dibar mashi ruwan."
Na sauke ajiyar zuciya, na kutsa kai dakinta na dauƙi sabon kofin silver na fito na wankeshi sannan na koma na cikashi da ruwan tulun Umma mai sanyin ɗaɗi, ruwan suna da ɗaɗin, saida na rufe kofin silver din sannan na fito na zura takalma na fice zuwa kofar gida, har na miƙa mashi kofin sai kuma na yi wani tunanin, da sauri na kawar da hannuna na ce, "Please idan har kunyata ya saka za ka sha ruwan nan ko kuma don kada inga kamar kana min fariya ne ya saka za ka sha, please ka da ka sha, ka da ya zo ya baka damuwa tunda ba saba shansa ka yi ba."
Ya ɗan waro idanu ya ce, "Ikon Allah na faɗa maki idan muka je Bindawa garinsu Alhajinmu ina sha."
Kamar mai tsoro na miƙa mashi kofin silver din, ga mamakina amsa ya yi ya sha har yana lumshe idanu tabbacin ruwan sun yi mashi ɗaɗi.
Ya ware idanu yace, "Kinga dadinsu ya saka na shanyesu, ji nike kamar cikina zai fashe," ya ƙarasa maganar yana shafa cikinsa, na murmusa kawai, na lura Junaid mutum ne mai barkwanci, saidai kuma akwai wasu alamu da suke nuna min kamar miskili ne watakila saboda yana sona ne ko kuma don na samu lokaci da shi shiyasa na lura da haka.
Ya miƙo min waya kirar samsung fold da ya saka Layina a ciki, na kalleshi na kalli wayar saidai ban amsa ba, ina dai zaune shurum ina neman karin bayani.
Ya ce, "Ya dai kin bar min hannu yana shawagi a iska, ara maki nayi kafin inje in koyi wayarki."
Labari kenan, koda dai ya fi ni shekaru amma ina jin maganar na san dubara ce ya ke son ya yi min kawai ganin ba zan amsa, har ila yau ban amsa ba, ya ce, "Ki amsa, aro na baki ba kyauta ba, don amsar abuna zan yi."
Ya cigaba da faɗin, "Na tura maki hotunanki, na buɗe maki WhatsApp, har application na turaki da na tura daga wayar maki Zahra irin naku ne na mata."
Da neman magana na ce, "To na ji aro za'a ba ni amma fa wayar mai tsaɗa ce idan kuma na fasa screen fa?"
Junaid ya murmusa yace, "Sai mu sauya wani ai muna da kudi."
Yau ɗaya mutum ya yi ikirarin yana da kuɗi kuma maganar ba ta nuna tunkaho da nuna isa ba, ta tabbata Junaid ya san abun da ya ke yi.
Babu yadda na iya dolena na amshi wayar, ya miƙo min kofin yace, "Ki maida shi."
Amsa nayi na maidashi gida na dawo, gani nayi ya miƙo min wata wayar, na amsa yayinda naci karo da hotona a gaban wayar, Amma sai dai meyy? A lock screen ne hotona yake amma akan home screen hoton wata kyakykyawar budurwa ce wankan tarwaɗa, a tareda suka dauki hoton da murmushi akan fuskokinsu, sunyi kyau sosai, gabana ya tsananta faduwa ina tambayar kaina wacece domin da bakinsa yace min ƙannansa mata guda biyu ne ƴan biyu, kenan wacece wannan wacce har hotonta ya samu tagomashin zama akan majigin wayarsa, na dubeshi da alamar tambaya na neman ƙarin bayani akan wannan hoton, gani na yi baki daya yanayinsa ya sauya yayinda damuwa ta maye burgin farin cikin da ya ke yi a yanzu, ni dai na zuba mashi idanu ina jiran amsa domin abu ne da na cancanci a yi min karin bayani a kansa ko don in gujewa kaina shiga inda ba zan iya surviving ba.
Junaid ya ce, "Sunanta Safiyya, cousin dita ce, a gidanmu ta tashi, Safiyyya ita ce mace ta farko da na fara so a rayuwa, mun tashi cikin soyayya da kaunar juna saidai kash ƙaddara ta riga fata, ta ɓace har yau bamu san inda take ba, munyi nemanta har yau muna ci ga ba da nema amma babu labari, tana raye tana mace bamu sani ba, Rumana ina sonki, Rumana ina matuƙar kaunar Safiyya."
Ya sakani a kejin ruɗani ya furta cewa yana sona amma kuma sai ya ce yana matuƙar kaunarta, kenan ya fi sonta a kaina, anya kuwa ba zan gudu da kafafuna ba, ina gujewa kaina ta dawo rayuwarsa shi kuma ya gujeni a barni da ciwon so mai wahalar mantawa, a barni da ciwon yaudara mai wahalar mantawa, koda ya ke idan zanyi mashi adalci bayyana min gaskiyar da ya yi shine daidai sannan kuma abun da ya dace a mahangar hankali.
Na yi nisa a duniyar tunani na tsinkayi muryarsa yana faɗin, "Mu je in kaiki wajen Ummana in ce mata ga surukarta, in rama abun da Jalila ta yi mamu."
Na zaro idanu waje, ganin haka ya sa ka dariya har fararen hakoransa suka bayyana wanda ya ƙara mashi kyau, ya yi haka ne domin kawar da yanayin da na shiga kuma yayi nasarar kawar da shi, ya haɗe hannayensa waje guda alamar roko sannan ya ce, "Sorry wasa nike maki," Sai kuma ya sa ka dariya yana faɗin, "Amma fa yadda kika yi da fuska, nayi fatan akwai waya a kusa in daukeki hoto."
Kiran sallar zuhr aka fara da yake garin akwai lullumi shiyasa mutum bai fiye fahimtar lokaci ya ja ba, ya ware idanu yana maida dubansa akan agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa, ya ce, "Kai lokacin sallah ya yi."
Naja Jalila muka shiga ciki na cika butoci guda biyu na ba yara suka kai masu, Jalila ta hakime akan katifa tana danna waya, na ce, "Sallar fa?"
Ta ce, "Ina fashi."
Na ce, "Ohhhh."
Na fito na tarar sun aiko yaro ya maido butocin, na dauki buta na shiga bayi na kama ruwa na fito na yi alwalla na koma daki na yi sallah.
Bayan sun dawo daga masallaci Jabir ya kira Jalila, mun fito tsakar gida Affan ya maƙale min dole na daukeshi muka fita, Jalila tana mashi wasa ko kallonta baiyi ba saima nema da ya ke yi ya saka min kuka.
Junaid yace, "Affan. Ko?" Na gyaɗa kai na ce, "Ehh shine."
Junaid ya miƙa hannu da nufin ya amshesa aikuwa Affan ya maƙale kafaɗa ya ki zuwa, daman nasan za'ayi haka, Affan kenan, da ƴan gidanmu kawai yake yarda, ba ya yarda da bakuwar fuska ko kaɗan.
Junaid ya ce, "Ya ki yarda da ni."
Nace, "Bai yarda da bakuwar fuska."
Ya ɗan ware idanu, Jalila tace, "Ka daina wahalar da kanka ba zai yarda ka daukeshi ba, nima da nike yawan zuwa gidan yana ganina amma har yau bai taɓa yarda na daukeshi ba..."
Na amshi zancen da faɗin, "Amma kinci sa'a tunda ya daina kuka idan ya ganki."
Jalila ta saka dariya tana faɗin, "Da wannan don wannan, lokacin ina shiga ya ganni zai hau kuka, watakila gani yake kamar zan tafi dashi namu gidan ne in rabashi da nasu."
A tare mukayi dariya, Affan ɗan dirama ne, muna sallama ya miƙa hannu yana taɓa Junaid amma yana juyowa sai ya yi sauri ya makalkaleni, wai kada ya daukeshi, Junaid ya miƙa hannu kamar zai daukeshi, ya ƙara maƙale min yana faɗin, "Ba-by... Abba... Umma..."
Mu ka yi dariya, Junaid yace, "Baby." Na rausayar da kai nace, "Sunana Rumana."
Ya ce, "MashaAallah. Rumana suna mai dadi amma dai nima sai na rinƙa ɗana kiranki Baby kamar yadda ake faɗi."
Na juya wajen Jalila nace, "Besty, wacece admin a group dinmu?"
Ta ce, "Bindawa admin ce."
Har na yi shiru sai kuma nace, "Kice mata na dawo WhatsApp ta sakani a group, muga za ta sakani din ko kuma har yanzu tana bin bayan ɗan unguwarsu mai buhu-buhun ƙarya da ƙarairayi."
Junaid har da cewa bai siyo chocolate ba ballantana ya ba Affan amma ga dubu daya, ya zaro bandir na ƴan dubu-dubu ya miƙa mashi, Affan ya ƙara maƙale min yaqi amsa.
Junaid ya miƙo min kudin, "Gashi ki siya mashi chocolate."
Na kalleshi na kalli damin kudin na ce, "A'a wannan yafi karfin sayen chocolate, sunyi yawa." Ya ɗan ɓata fuska yace, "Amma ba'a maida hannun kyauta baya, beside ba ke naba ba, Affan na ba kuma yana so don haka kada ki ari bakinsa ki ci mashi albasa."
Na ware idanu nace, "Ahhh haba, to shikenan ta kwana gidan sauki ka bashi ya amsa da hannunsa."
A daidai wannan lokacin ne Kawu Bala ya danno kai cikin unguwarmu, saidai gabana ya yanke ya faɗi ganin kallon da yake binmu da shi, wannan kallo ba kallon lafiya bane ba, kallon tsana ne da haushi.
Ya shiga gidan babu jimawa ya fito, gadan-gadan ya nufo inda muke yana zuwa baiyi wata-wata ya kwasheni da marin da saida na sunkuya, na dafe kuncina ina zubar da hawaye yayinda Affan ya tsanyare da kuka, Kawu Bala ya daka mashi tsawar da ba yaron da aka yi wa ba har ni saida aka razanani.
Kawu Bala ya dubi Junaid da idanunsa sukayi ja na ɓacin ran abun da aka aikata a gareni, yace, "Ko kana da magana ne? Ko zaka rama mata ne?"
Hawaye suna zuba akan idanuna na juya inda Junaid yake na ce, "Sabr, Sabr, Sabr dear, wata rana sai labari." Ban rufe baki ba ya ƙara kwasheni da wani marin da saida na saki ihun wahala saura kaɗan in saki Affan dake a hannuna Jalila ta yi saurin karɓarsa.
Junaid ya fusata ni dai ban san yadda aka yi ba amma dai naga gilmawar hannunsa wanda ban da gocewa da Kawu Bala ya yi da kuwa ba da babu shakka sai ya ci kasa a wannan naushin.
Kawu Bala yana ta zuba tujara yana zagina, "Ke da uwarki uwayen son abun duniya kunga mai kuɗi kun makale mashi, to bari ki ji da kyau koda kina mutuwa kina dawowa sai kin auri Mutallab, Ni Bala ba zan ba wannan marar kunyar aurenki ba, yaron da ya iya saka hannu a mareni a matsayina na ƙanin babanki."
Junaid ya ce, "Ka da ka ƙara zagin mahaifiyarta."
Kawu Bala ya ce, "An zageta," ya lailayo zagi ya ɗurawa Ummana wacce bata son hawa ba bata son sauka ba.
Hawaye suka wanke fuskata.
Dakyar Jabir ya shawo kan Junaid suka wuce tare da Jalila yayinda suka barni tsaye dafe da kuncina ina zubar da hawaye, tuni Jalila taba yarinyar makotanmu Affan ta mayar da shi gida.
A fusace Kawu Bala ya koma gidan, na ɗaga kafafuna a sanyaye na bi bayanshi, tun daga soro nike juyo yadda yake ball da dukkanin abun da ya tari gabansa a yayinda yake zubawa Ummana bala'i kamar diyarsa, a shekaru Yaa Ahmad yaba Kawu Bala shekara ɗaya amma ko kaɗan ba ya jin kunyar ya zauna yana zazzagawa ummarmu bala'i da jaraba wani lokacin har zagi da cin mutunci yana biyo baya kuma babu dama mu saka baki sai a ce mun yi rashin kunya, na maganar da za'a shekara a shekare ana maimaita.
Lamarin mutanen yau yana da matuƙar bani mamaki da tu'ajjibi, son zuciya ya yi yawa, shi idan ya yi wa ummarmu rashin kunya babu mai cewa uffan amma mu idan muka mayar da raddi sai cibi ya zama kari lamari ya lalace azo ana wallahi tallahin bamu da kunya.
Faɗi yake yana maimaita, "Yayana ya auroki domin ki yi wa yara tarbiyya amma kin kasa, har ita wannan ta isa ta tsaya da wani a waje, waninma wanda ya wulakantani, to bata isa ba, ba dai tace bata son Mutallab ba to ai shikenan a kauyen ƙarau zan nemo mijin in ɗaura mata aure in gani idan akwai wanda ya isa a cikinku ya ce ban isa ba."
Dukkanin abun da Kawu Bala ya ke a gaban Yaya Ahmad ya ke yi kuma da ya ke idonsa babu kwalli bai ji nauyi ba, haba inaga Yaya Ahmad ya cancanci Kawu Bala ya yi mashi kawaici amma inaa babu wannan a jadawanin yarensa, sai ma ƙara furzo maganganu da ya ke ba tareda ya taunasu.
Ya buga tsaki yana wa Umma kallon raini da kaskanci yace, "Aikin banza aikin wofi." Ya juya ya fice.
Mukayi cirko-cirko aka rasa wanda zai yi magana, Umma ta fashe da kuka tana mai jin zafin maganganun da yaro kanin bayan ɗanta ya faɗa a kanta kuma ya ci bulus domin ko rantsuwa ta yi babu kaffara babu wanda zaibi ta kan maganar, anya kuwa akwai adalci a wannan lamari.
Abba yana dawowa Yaya Ahmad ya sameshi da magana akan rashin kunya da Kawu Bala ya yi wa ummarmu amma buɗar bakin Babanmu sai cewa ya yi, "Ku yi hakuri, ku bata hakuri wata rana sai labari, yanzu idan na yi magana sai cibi ya zama ƙari, azo ana cewa na goyi bayan matata na wulakanta ɗan uwana, maganar da za'a yi tayi kenan rayuka suzo suna ɓaci don haka ku yi hakuri abar maganar a nan."
Yaya Ahmad da ransa ya gama ɓaci ganin wulakanci da aka yi wa mahaifiyarmu zaibi iska yace, "Amma Abba ya kamata a tsawatar mashi a nuna mashi kuskurensa."
Abba ya ja fasali yace, "Ahmad na sani abun akwai ciwo, na sani ba'a kyauta maku ba amma ina mai rokonku akan ku yi hakuri mu taru mu lallaba wannan zumuncin nawa da dangina da a kullum suke neman hanyar gurguntar da shi, ko ba yau ba, ko ba gobe ba, da raina ko bayan mutuwata zakuga amfanin wannan abun da ni ke yi, ku yi hakuri ku ba ta hakuri, wata rana sai ya labari."
Wuni Yaya Ahmad yayi yana mitar abun ni kuwa dama ban saka baki ba, tabbas abun da ya faru babu ɗaɗi kuma ba'a kyauta ba amma maganar Abba tana akan hanya, tunda su a kullum neman hanyar da za'a samu damuwa suke yi gwara mu zama jakadun zaman lafiya ta hanyar yin hakurin sai a zauna lafiya, mu kuma sai Allah ya bamu ladar haƙurin da mu ka yi da kuma ƙoƙari da mu ka yi matuƙa gaya domin a zauna lafiya.
Tun daga wannan ranar da Kawu Bala ya yi wa Ummarmu rashin kunyar da kaskancin nan ba tayi lafiya ba, maganganun suna ta ragargazarta a zuci, har ciwonta ya tashi, jikinta ya tsananta kamar ba zata rayu ba, na dawo makaranta na sameta yashe a tsakar gida na fasa ihu ina mai neman agaji, "Jama'a ku taimaka mamu, ku kawo mamu agaji, Ummarmu."
A daidai lokacin da wayata ta yi ƙara, Junaid ne na ɗaga da sauri ina faɗin, "Kana ina?" Daga ɗaya bangaren yace, "Ina akan titin gidanku." Na sauke ajiyar zuciya ina mai fashewa da kuka mai tsuma zuciya "Please ka zo ka taimaka min mu kai Ummana asibiti na dawo na tarar da ita yashe a tsakar gida."
Babu jimawa ya zo makociyarmu ta taimaka min suka saka Ummana a motarsa ina zaune a bayan motar ina tallafe da ita ya nufi asibiti da mu.
Babban asibiti ne na kudi, shine tsaye akan komai yayinda nike durkushe babu abun da ni ke yi sai kuka. A wannan buguren da rayuwata take zagaye da ƴan uwan Abbana da ba kaunarmu su ke yi idan na rasa Ummana rasuwata za ta shiga tasko.
Na kasa taɓuka komai sai shine ya amshi wayata ya ɗauki numbar yaya Mustapha ya sanar dashi halin da ake ciki, a lokacin yaya Ahmad ba ya a gari, Yaya Mustapha ya kira Abba, babu jimawa saiga Abba, Junaid ya gaishe da shi, ya amsa yana mashi godiya.
Junaid shine tsaye akan komai har aka sallami Ummana daga asibiti, kullum sai yazo sau ukku ya kawo mamu abinci safe, rana da dare, wannan ya saka ya ƙara kima da daraja a idanuna yayinda sonsa yake ƙara linkuwa a zuciyata.
Muna zaune a ward da aka kwantar da Ummana, ni, Yaya Ahmad da Yaya Mustapha, Junaid ya yi sallama ya shigo ya basu hannu suka gaisa, ya ƙara wajen Umma ya gaishe da ita da girmama, "Umma ya jikin?"
"Da sauki."
"Allah ya ƙara sauki."
Ta amsa da, "Amin." Ta ɗora da faɗin, "Na gode, na gode, Allah ya saka maka sa alheri, Jazakallahul khair."
Junaid ya girgiza kai ya ce, "Umma ke uwa ce, albarkarku muke nema domin ganin daidai a wannan rayuwa."
Ta ce, "Allah ya sa albarka." Ya amsa da, "Amin." Ya jima sannan ya yi mata sallama ya fita na miƙe nabi bayansa na jingina da motarsa na ce, "Ina wuni?" Ya amsa da, "Lafiya lau. Ya mai jiki?"
"Da sauki."
"Allah ya ƙara sauki."
"Amin."
Ya zaro kuɗi bai san adadinsu ba ya miƙo min, "Gashi koda zaku bukaci wani abun."
Na noke hannuna na ce, "A'a muna da kuɗi." She was like, "Baby haba mana, ina son inyi hidima wa ummata amma kina yi kamar baki san in samu albarkarta."
Ya daureni da jijiyoyin wuyana a wannan magana da ya yi, na saka hannu na amshi kuɗin na yi mashi godiya na juya ina tafiya a hankali yayinda nike jin sonsa yana ƙara linkuwa a cikin zuciyata na kulawa da yake nunawa akan mahaifiyata saɓanin Mutallab wanda uwarsa ma barranta kansa yake da ita ballantana tawa uwar wacce daga uwar wacce zai aura ba ta kau ba.
Ina shiga na ajiyewa Umma kuɗin na dubeni ta ce, "Mey yasa kika amsa?"
Na labarta mata yadda mukayi, na jinjina kai ta ce, "To shikenan babu komai, ki baiwa yayanku kuɗin."
Na miƙawa Yaya Ahmad, ya amsa yana faɗin, "To shikenan Umma za'a mayar masa." Umma ta girgiza kai ta ce, "Ba haka nike nufi ba." Daga haka bata ƙara furta komai ba.
A ranar da aka sallamemu da kansa ya saka direba ya mayar damu gida kasancewar ba'a ƙasar a lokacin.
Sai a lokacin na samu kwanciyar hankali na bi takan wayar da ya ba ni, Samsung fold mai tsadar da na tabbata kudinta suna da yawa sosai, rayuwa kenan, kuɗi suna inda suke, fatanmu shine Allah ya bamu masu alheri ta hanyar halal.
Ashe har VTU ya yi min na saka min data ta shekara guda, na duba kudin da ya saka min dubu arba'in, kai nifa da ace a hannu ya bani kudin da ya fiye min, sai in shiga kasuwa in siyo leshe in dinka in samu na fitar kunya.
Da daddare ina buɗe data na samu tuni bindawa ta sakani group dinmu har da wani rubuta.
_Welcome back Mrs Junaid to be_
Dama maganganu suna ta yawo a tsakaninsu musamman wadanda suka je ganin Umma suka samu Junaid bayan kuma sun san akwai baikona da Mutallab.
Hafsat Lawal ta rubuta, _Mutallab dai ko, ko kin manta sunan wanda za ta aura ne._
Bindawa tace ai sun rabu, ita yanzu tana bangaren Junaid ne, da alama akwai abun da ya faru ko kuma ta gane gaskiya na dalilin da ya sakani yanke hukucin rabuwa da shi.
Daga nan abun ya zama abun sharhi, bamu voice suna yi, masu typing suna yi, bani da lokacin bin wadannan dogayen voice note din, idan ta nice voice note ba ya da amfani domin ban cika yi ba bugu da ƙari sauraronsa yana ba ni wahala saidai aka ce abincin wani gubar wani, dama kowa da ra'ayinsa, shiyasa a rayuwa don mutum ya nuna bana burgeshi bana jin komai, ni da ba kudi ba aikuwa babu dalili in sakawa kaina damuwar sai na burge kowa, ina ce kudi ne kawai suke burge kowa.
Na duba wadanda suka yi min sallama na mayar masu da amsa, na duba dp naga hotonsa ne, yana sanye da wasu tsadaddun suit limited edition, a birnin London aka yi mashi hoton kuma alamu sun nuna bai shiryawa daukar ba amma sai hoton ya yi matukar kyau, tabbas Junaid mai kyau ne, idan na ce kyau ina nufin kyau mai suna kyawu.
Na murmusa ganin da sunan da ya adana numbarsa dashi wato HEARTBEAT na shiga ciki na mayar dashi da yaren hausa a inda na rubuta BUGUN ZUCIYATA.
Na amsa sallama da ya yi min a WhatsApp, mun jima muna hira a online, Junaid yana cikin jerin maza masu murya mai dadin da idan ya yi magana sai an kalleshi, amma kamar yana min rowar muryar coz bai cika kirana ba saidai musayar sakon text message, ko a yanzu typing yake ba ya voice note, ni da na tsani a yi min voice note sai ya kasance ina fatan ya yi min koda zai kai tsayin mintina ukku ne zan tsaya in saurara in ƙara saurara, wajen karfe goma na dare mu ka yi sallama na kwanta saboda ina da aji karfe takwas na safe kenan dolena in tashi in shirya da wuri muddin bana son in makara.
Tunda na tashi da asuba ban koma ba, bayan na yi sallar asuba na yi karatun Alƙur'ani mai girma wanda mu ke yi tare da Junaid a video call, na shirya na yi kalaci a gaggauce, shadda ce blue a jikina a lokacin da zan dinkata na so in yi mata surfani saidai ba ni da hali kuɗin a lokacin, saidai aka dinka min ita hakanan aka ratsa dark blue net a gaban shaddar sai dinkin ya yi kyau sosai fiye da idan aka yi mata surfanin, saidai har yanzu ina dako ina da burin idan har na samu wata shaddar zanyi ƙoƙarin tara kudade inyi mata irin waccen dinkin.
Na zura dogon hijab har kasa na rufe fuskata da niqab na dauƙi sabuwar jikkar da nike zuwa da ita makaranta a yanzu, wacce Junaid yayi min kyauta, mai kyau ce da tsaɗa sosai, limited edition.
Na leka kofar Ummana nayi mata sallama, na fita na taka har bakin titi na tsayar da adaidaita sahu, karfe bakwai da mintina ashirin ta yi min a bus, a karo na farko na ji ina sha'awar in shiga gallery na wayar, ta fiddota daga jikka, wow, ashe har da hotunansa ya tura min aikuwa gasu nan birjik, kowane yayi kyau Masha Allah, har da hoton ƙannanshi ƴan biyu masu kama da shi, tare da hoton wata kamilalliyar mata wacce kallo ɗaya na yi mata na gane mahaifiyarshi ce saboda kamanni da su ke yi.
Har asibiti ta zo ganin Ummana tare da ƴan biyu saidai a lokacin na koma gida ɗauko kaya shiyasa bamu hadu ba amma a yadda naji Ummana tana yabonsu na tabbatar da ta nuna mata halin dattako ne.
Babu zato babu tsammani naci karo da hoton wata budurwa wankan tarwaɗa, na shiga al'ajabi da tu'ajjibin abun da wannan hoton yake yi a wayar da kuma dalilin da ya saka ya tura min shi, tunda na amshi wayar ban tura komai a ciki, kenan ta tabbata daga wajenshi hoton yake.
Saida nayi wa hoton kallon nutsuwa wannan na gane Safiyya ce, saida gabana ya yanke ya faɗi kwatankwacin abun da ya faru da ni kenan a lokacin da na fara ganin hotonta, da sauri na mayar zuwa wani hoton gujewa dadewa a wannan yanayin wanda zan ina kiranshi da fargaba da kuma kishi, saidai ban fita daga rami ba na faɗa rijiya, masu iya magana suka ce wai ba'a rabu da Bukar ba an haifi abu, na faɗi haka ne domin ina sauya hotonta ne na ƙara cin karo da wani hotonta tare dashi, shi kuwa miye dalilinsa na tura min hotunanta har haka, gashi babu dama in gogesu.
Kaina a likafa na fita daga gallery ahtoh tunda hanya babu kyau gwara in nemawa kaina mafita, na buɗe data na kutsa kai a manhajar YouTube ina sauraron Littafin HAWAYE AKAN RUWA na marubuciya AYSHER ANGEL.
Da yake karshen littafin nike babu jimawa na gama da shi, na kutsa kai channel na PINKISH LADY ina sauraren wani littafin marubuciyar da take karantawa mai dauke da dumbin darussan rayuwa.
Taku Har Kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)