5
by @aishaangel
*ZARGEN ƘAYA*
*NA*
*AYSHER ANGEL*
Page 5
WhatsApp ***
*The Fractured Bond: When Resentment Runs Deep And Innocent Pay The Price...*
Ashe jiya da dare bayan na sauka hirar maganar suka cigaba da yi a group, saboda kusan kawayenmu sun sanni da Mutallab kuma sun san anyi mamu baiko, nikam ban damu ba koda za'a ce saboda kudi na guji Mutallab na so Junaid, Allah yasan zuciyata kuma yasan dalilin da ya saka na rabu da Mutallab, I'm the victim here, ni aka cuta ba ni ba ce na cutar.
Jalila ce na ga ta yi magana na rufe data kawai na maida wayar a jikka, karfe takwas daidai a lecture hall tayi min, na samu Jalila har tayi min wajen zama, na cire jikkarta da ta saka akan kujerar na mayar mata akan teburi.
Bayan mun fito daga lectures, ni da Jalila muna zaune a bus, da ya ke macpolo ce muka tarar kuma mutane kaɗan ne a ciki sai munyi zaman jira tukunna, taso mubi kekenapep na ki saboda kudin dake a hannun bus kawai zan iya affording ban kuma son in zame mata dawainiya.
Ta zaro kwalin waya tare da tsohuwar wayata ta miƙo min, daman na san za'a runa, dama na san dubara ce kawai ya yi min ta yadda dolena in amsa, ta ce, "Ga shi, in ji Junaid."
Amsa na yi na saka a jikka ina faɗin, "Ta tabbata dubara ce kawai ya yi min."
Jalila ta fuskanceni ta ce, "Rumana, Junaid yana sonki sosai, Junaid abokin Jabir ne sosai, mutumin kirki ne, ba ya da damuwa ko kaɗan, Jabir ya sanshi ciki da bai domin a tare suka tashi don haka ka da ki ji komai. Idan lamarin Mutallab ya saka maki shakku akan maza ina mai tabbatar maki da cewa lamarin Junaid zai wanke waɗannan shakkun."
Na ɗan kalleta na ce, "Waye kuma Mutallab?" Ni kaina na yi mamakin yadda na yi maganar cike da serious.
A tare mu ka yi dariya, na ce, "Ke ni fa har na mance da wani Mutallab."
Ta katseni da faɗin, "Kuma kika kira sunanshi."
Na ɗan ware idanu na ce, "Aww shi ɗaya ya ke da sunan ne."
Ta ce, "Kuma fa haka ne."
A tare mukayi dariya, tace, "Kin san kuwa Junaid miskili ne, magana wahala ta ke mashi, da alama jiya zancen kurame ku ka yi."
Na cika da mamaki domin tabbas na lura da haka amma kuma idan yana tare da ni miskilancin raguwa ya ke sai ya koma min mai barkwanci da sakani dariya.
Na ce, "Nima na lura da haka amma ba haka ya ke ba, yana da barkwanci, farko murmushi da gyaɗa kai kawai nike amma saida ya saka na yi magana, yana da surutu a gabana."
Jalila ta cika da mamaki, "Oohhh... Unbelievable... Ta tabbata yana sonki sosai da sosai, koda yake dolensa ya cire miskilancin idan yana gabanki."
Nace, "Sosai fa ko kuma in rabu dashi da miskilancinsa."
Ni fa dukkanin namijin ba zai iya manta miskilancinsa a gabana ba to babu shakka bai cancanceni ba.
Na murmusa kafin daga bisani na ce, "Yeah, Junaid's love has brought happiness into my life, and I'm very greatful for that."
Na ja fasali na dora da faɗin, "Tabbas shigowar Junaid a rayuwata alheri ce, ya zama sanadin mantar da ni halin ni ƴasu da Mutallab ya sakani a ciki amma sai kuma nike ganin kamar akwai sauran runa a kaba, idan na tuna wanzuwar Safiyya a rayuwarsa da yadda yake matuƙar sonta sai in ji jikina ya yi sanyi, ina gujewa kaina in yi zurfi a sonsa ta bayyana ya gujeni tunda a rashinta ne yake kulani, sai gabana yake dukan ukku-ukku a dukkanin lokacin da na tuna da hakan, ina gujewa kaina ka da a zo lamari ya juye zuwa KITSO DA KWARKWATA mai wuyar sha'ani."
Jalila ta kama hannuna tace, "Rumana idan har kin yarda da ni to ina san ki yarda da abun da zan faɗa maki, Junaid mutumin kirki ne mai ilimi kuma mai amfani da ilimin, yana da zuciya mai kyau, yana da tausayi musamman akan mace mai rauni, don haka ni Jalila ina mai jaddada maki cewa hakan ba zai faru ba, ko da a yau Safiyya za ta bayyana ina mai tabbatar maki da Junaid ba zai rabu da ke ba, idan kinga ya rabu da ke saidai idan matsalar daga bangarenku ne, abun da bama fata."
Na ɗan yi jim ina nazarin maganganunta sai kuma na ce, "To shikenan."
Ta ce, "Ooohhh ai na gani, miƙo wayarki inyi mamu hoto, sabo hana barci."
Na murmusa na zaro wayar na miƙa mata, ta ba Kausar ta daukemu hoto, kuma ya yi kyau babu ƙarya, lallai wannan wayar da Junaid ya bani taci kudinta makurar haduwa ce ga camera mai ubansun clear.
Tana tura hoton zuwa wayarta kira ya shigo wayata, daga ni har ita aka rasa wanda zai yi min magana ganin Ammi ce take kira, ina nufin Ammi mahaifiyar Mutallab.
Ban samu zarafin ɗaga wayar ba koda na ɗauka ban san abun da zan faɗa mata ba, saida kiran ya yi yawa sannan na tura mata sakon text message.
_Ammi ki gafarceni amma koda na ɗaga kiran ban san abun da zan ce ba, Ammi kiyi hakuri ba laifina ba ne_
Lokaci guda wannan kiran ya rikidar da yanayina daga farin ciki zuwa akasin hakan, na rasa abun da ya ke min dadi yayinda hawaye suke zubowa daga idanuna.
Jiki a sanyaye na isa gida - saidai mi? Ina juyowa da nufin haurawa lungunmu na hangoshi, Junaid ne jingine da zukekiyar mota kirar Mercedes Benz ya zuba min idanu yana sakar min murmushin da ya saka na ji baki ɗaya damuwata ta yi ɓatan dabo, kai soyayya ta yi a rayuwa musamman idan ka yi dace da masoya na gaskiya mai ƙaunarka da gaskiya, mai son farin cikinka da gaskiya.
Alamu sun nuna daga wajen aiki yake, shigarsa ta sakani fahimtar hakan, yana sanye da suit, the more nike kallonshi the more yake ƙara min kyau a idanu, sumarshi baka wuluk tana kwance, yalwatacciya, ina ƙoƙarin ciro naira dari biyu in baiwa mai napep kudinsa, ya rigani a yayinda ya karaso ya zaro wallet ya zaro sabbin kudi ƴan dubu-dubu da ni kaina ban san adadinsu ba ya miƙa mashi, mai napep ya amsa ya yi godiya.
Kallonshi na yi ya yi min murmushi, na yi sama da niqab da ke fuskata tare da mayar mashi da martanin murmushi, muka jera zuwa inda motarsa take, na jingina da ita yayinda ya tsaya a gefena ya zuba min idanu yana min kallonsa da ke sakani jina a cikin nutsuwar samun wanda zai iya yaƙi a saboda ni, ya ce, "Kin san mey? I missed you."
Na rausayar da kaina ina murmushi ba tare da na ce uffan, yace, "Na zone in ganki kuma na ganki don haka bari inja motata in koma inda na fito."
Da wasa na ce, "Awww ni kuma ko Oho, to ban gaji da kallon kyakykyawar fuskarka ba." Ya ɗan kalleni, "Kyakykyawar fuskata kuma, banda zagi dai, kyau ai yana wajenki, ke da kanki kyawu ce amma nikam saidai ki yi min kara, haka ranar kika ce muryarta mai dadi bayan ni kuma na san marabar muryarta da injin markade kaɗan ne."
Na ɗan ware idanu ina kallonsa, na ɓata fuska kamar da gaske na ce, "Nifa a daina kushe min saurayi ko kuma a gamu da fushina."
Ya haɗe hannayensa a waje guda ya ce, "Tuba nike, kaina a kasa, wane ni in kushe Junaid din Rumana, ƙaryana yasha ƙarya."
Yadda ya ƙarasa maganar dole saida na dara, ya saitani da waya yana min bidiyo saying, "Kina dariya kina ƙara kyau."
Har da daukarmu hoto. Na juya na shige gida ina dariyar maganar da ya yi, ina ƙoƙarin shiga daki na samu kiransa akan yayi mantuwa na juya ja koma, na jingina da motar na ce, "Gani tara ko bashi."
Ya ɗan waro idanu, "Rumana tawa ta kaina, komai kyawu yake maki kyakykyawata."
Ya amshi jikkata ya zaro abu daga mota ya saka min a ciki yayi zipping, ashe wani karamin kit ne mai kyau ya saka min a ciki, Yaa Ahmad ne ya shigo santar a mashin dinsa, ya ba Junaid hannu suka gaisa a mutunce.
Junaid ya ce, "Kuna kama sosai".
Nayi murmushi tareda gyada kai, ya ɗaga min hannu ya ce, "Na wuce sai munyi waya, ki saka sakona zai yi maki kyau."
Ina tsaye saida motar ta ɓace min daga gani sannan na juya na shige ciki.
Tuna rigingumun da suke shiga a tsakani ya saka hawaye suka zubo min na saka hannu na share a yayinda na furta, "MUGUN JAKADA kawai, ka tarwatsa min farin ciki sannan bai yi maka ba ka dawo kana ƙoƙarin tarwatsa tsakanin Abbana da danginsa da kullum zumuncinsu cikin tangal-tangal."
Wannan lamari ya gusar da farin cikin da na samu a tare da Junaid, rayuwa kenan, karfi da ya ji lamarin Mutallab ya hanani farin ciki.
Haka na ƙarasa wunin ranar babu walwala, washegari zan ɗauki handout a jikkata naci karo da karamin kit mai kyau, na ciroshi na buɗe ina mai sakin murmushi, zoben diamond ne mai kyawun gaskw, saidai ban saka a yatsana ba, na turashi a kasan kayana na maida akwatin na rufe.
Washe gari bayan na dawo daga school, ina saukowa daga napep na ci karo da wata katuwar Jeep parker a gefen gidanmu, wata farar yarinya da ba zata wuce sa'ata ba ta fito tana sanye da leshe dinkin half gown, ta ɗaura mayafi akan kafaɗa, tana tako cike da gadara da son nuna ita wata ce.
Kallo ɗaya na yi mata na doshi kofar gidanmu, saidai ga mamakina na yi ta nufo inda nike, fitowar Safeena ƙanwar Mutallab daga motar ya saka na fahimci kwanan zancen, abun haushi ranar da muka fara haduwa da ita cemin ya yi ɗiyar ƙanin babansa ce mai rasuwa.
Na rasa mi mutanen nan suke so da ni, kowa lamarin Mutallab yake dubawa an rasa samun wanda zai duba ni nawa lamarin, wai har sau dubu nawa zan maimaita cewa ba zan iya aurensa ba sannan a fahimceni, mutumin da zai iya farraƙa kansa da mahaifiyarsa wacce ta ɗauki cikinsa tsayin wata tara ni miye ba zaiyi min ba, tunda har na samu wani su rabu dani mana su barni inyi farin ciki da walwala.
Ita dayar sai faman yatsine fuska take ni kuma ban bi ta kanta ba, yadda na rike talaucina hakanan babu wani da ya isa yace zai nuna min izza don yana da dukiya, ban ce ina son kudinka ba ballantana wulakanci ya shiga a tsakani.
Na wuce gida abuna, suka boyoni har daki, yunwa nikeji kuma na gaji don haka bani da lokacin maimaita magana ɗaya, idan ma kuma zan maimaita sai bayan cikina ya dauka sannan domin ban shirya wallahi tallahi da wannan yunwar dake ragargazata a ciki.
Na fita tsakar gida na debo ruwa na ajiye masu na dauki zani da riga na fita, na janyo ruwa daga rijiya na cika bokiti tare da daukar kwandon wanka na wuce bayi nayi wanka na sauya kayan dake jikina zuwa zani da rigar da na dauko, na shiga daki na samesu zaune kamar yadda na barsu, mai kawai na shafa na goge fuskata na shafa kwalli, yunwa nike ji sosai don haka saidai su jira idan yaso idan na ci na koshi sai in maimaita masu abun da suka gagara fahimta, na saka hannu na tattara dogon gashin kaina na yi mashi gammo na rufeshi da kallabi.
Na kutsa kai kitchen na zubo dumamen tuwo na koma daki tareda masu bismillah suka girgiza kai ina lura da ɗayar yarinyar har wani yatsine fuska take alamar wacce takejin amai, cikin raina na ce, "Oho a banza a je a dawo akwai dumamen tuwo a jikin mutum domin idan shi bai ci ba uwayensa sun ci idan suma ba su ci akwai kakanni."
Ganin ba da arziki suka zo na saka a raina saidai ran kowa ya ɓaci amma suna faɗa min banza zan maida masu martani da wofi.
Saida na ci tuwona na koshi na yi nak na kora da ruwa sannan na dawo a hayyacina daga yunwar dake ragargazata a ciki, na dubesu na ce, "Ina jinku da mi kuke tafe?"
Ɗaya budurwar ta dubeni a fusace tace, "Ke wai da uwar mi kike takama da za ki shanyamu."
Na ɗan kalleta na ce, "Ooohhh.. Ahh, haba, shine kuma har da tada jijiyoyin wuya amma bari in fara tambayarki tukunna; shin na aika maku goron gayyata ne ko kuma na yi shela a gari akan ina nemanku da har kike da bakin faɗin kun zo na shanyaku ko kuwa salon in burgeku sai in zauna yunwa tana ragargazata a ciki."
Na nuna kaina na ce, "Ni Rumana ban shanya kowa ba, yadda mutum ya kwaso kafafu ya zo ba gayyata hakanan ya kwashi kugunsa ya zauna ba tareda izini ba ballantana kuce na kiraku kun zo na yi maku wulakanci, ku tashi ku tafi mana ai ban tsayar da ku ba, na dawo daga makaranta da gajiya da yunwa ai bazan tsaya in wahalar da kaina akan maganar da an riga an gamata ba, wai don Allah mey kuke so inyi maku, sau dubu nawa kuke so in cigaba da ce maku ba laifina bane ba, laifinsa ne, ku je ku tambayeshi abun da ya yi min, ya yi min ƙarya akan mahaifinshi, mahaifiyarshi, kanwarshi, a hakan kuke tunanin in yarda in aureshi."
Na girgiza kaina na ce, "A'a babu wannan maganar, babu dalili in saka kaina shiga million wai takabar suruki."
Ta kalleni na kalleta na murtuƙe fuska, ganin hakan ta sassauta murya tace, "Ɗazu na ɓata maki rai, na yi maki ihu amma kiyi hakuri, Mutallab means a lot to me, damuwa da halin da ya ke a ciki ne ya saka hakan ya faru amma ina mai baki hakuri akan hakan, please kiyi hakuri ki koma gareshi, tabbas ya yi kuskure amma ina mai tabbatar maki wannan ba halinshi bane akasi aka samu."
Haƙuri sai in basu domin nidai na riga na samu miji na gari wanda zan iya bugun kirji in kirashi da ta more miji.
"Saidai ku yi hakuri domin tuni na fitar da shi daga zuciyata na maye burginsa da wanda na duba na kara dubawa na tabbatar da shine ya fi dacewa da ni. Zamanin Mutallab ya riga da ya wuce, na warke daga ciwon da ya dasa min a zuci, yanzu Junaid a birnin zuciyar RUMANA."
Sai a lokacin Safeena kanwar Mutallab ta saka baki bayan da ta fashe da kuka, "Don Allah kiyi hakuri ki tausaya mamu shi ɗaya muke da shi, Ammi kwana ta ke yi tana kuka, watakila baki sani bane amma maganar da mu ke yi yanzu haka yana can kwance akan gadon asibiti a halin rayuwa ko mutuwa. Kin sani na sani kowa ya sani yana sonki."
Na dubeta na ce, "Ke yanzu matsalar shine ban san matsayinki a wajensa ba, da bakinsa ya faɗa min ke ɗiyar kawunsa ne yana tausaya maki da Ummarki ne shiyasa yake yawan zuwan gidanku."
Safeena ta marairace murya ta ce, "Please ki tausaya."
Nayi murmushi mai ciwo nace, "Hakika Mutallab yana sona amma wani amfani son ya yi min tunda har ta tabbata ba mijin aure bane, na yarda yana sona kamar hakane kuma ni Rumana ban ce sai mai kuɗi ba, to miye dalilin ƙaryar, ban san ba ya da lafiya ba, yanzun ma da na sani abun da zan yi shine mashi fatan samun lafiya, Allah ya ba shi lafiya, Allah ya tsareshi daga kamuwa da ciwon zuciya. Amma fa zan faɗa in maimaita dukkanin abun da ya faru shine ya janyowa kansa gashi nan har abun ya shafeni ya shafi zumunci Abbana da danginsa, fitina a kwance take Allah ya la'anci mai tayar da ita, wannan fitinar kuwa Mutallab ne ya tayar da ita gashi nan har tana nema ta lalata zumunci."
Babu zato babu tsammani ɗayar budurwar ce ta daka min tsawa ta miƙe tareda zaro bundle na naira dubu-dubu ta jefeni da su a fuska tana faɗin, "Ƙarya kike maitarki kika fito fili shiyasa ya yi maki ƙaryar kuɗin, kawai ki fito fili ki ce mai kuɗi kike so shiyasa kika rabu da shi da kika gane ba ya da su, don kina da farar fata shine kike tunanin sai mai kuɗi za ki aura, kodaddiya kawai, sai yanzu na gane ainihin abun ya ke faruwa, wato kin tashi kina cin wannan gwamacalar abun da ki ka yi mamu tayi ɗazu shine kika son samun sauyi, to ya kika iya tunda tsohuwa ta auri talaka dolenki ki ci tuwo dare da rana, safiya da marece har ma idan ya tashi aiki a ƙara dafawa a ƙara ci, aikin banza aikin wofi, dubi wannan gugurarran dakin babu komai a cikinsa sai talauci da tsiya a hakan kike tunanin ke wata gwaska ce bayan baki wuce bolar tsakiyar kasuwa ba. Har kike nema ki wulakantamu, Mutallab ya fi karfin wulakanci, kuma bari kiji dole sai kin aureshi koda kina mutuwa kina dawowa, idan har kuɗi suna amfani ni kuma zan yi amfani da su domin in tabbatar da kin aureshi, mayyar kudi kawai, mai idon cin naira, kudi kike so ko, to gasu nan dauka, kina banzar cima a gida shine kike burin idan kinje gidan miji ki sauya cima, kina so ki daina cin tuwo miyar kuka ki koma cin shayi da burodi da wainar kwai, fried rice da farfesun kaji, wato kin gaji da bulbular ruwan tulu kina kwadayin ki fara shan ruwan gora da drinks masu sanyi, watakam kin gaji da wahala da icce kina so saidai kina kwance a yi maki komai, mayyar kudi kawai, wato kin gaji da wanka da ruwan rijiya wadanda sai kin janyo kin zuba a bokiti kin cika sannan ki dauka kije bayi kiyi wanka shine kike mafarkin wanka a bahon wanka da shower wanda kina juya makunni ruwa zasu zubo maki shaaa. Kin tashi a wannan gurrurarran gidan kin gaji kina so ki koma katon gida na alfarma mai lambu, swimming, ac, da manya-manyan dakuna, da parlour na alfarma wadanda ɗaya kawai yafi girman wannan kufen da kuke kira da gida. Idan ba wannan ba, miye abun ƙyama a auren Mutallab. Yaa Mutallab ya fi karfin ya yi maki ƙarya, ba zai maki ƙarya ba, ai mai kudi kike so ko? Ahhh tou kin samu, Mutallab cousin dina ne, Abbana kuma attajiri ne, mai kudi na gasken-gaske, waccen motar da muka zo a kanta, zan iya siyen guda goma irinta ba tareda na girgiza ba. Mutallab yana da gatanshi, kuma kinji na rantse idan sunana Hafsat sai na saka kin aureshi ta dole, idan har a danginku akwai mayyun kudi to kuwa sai kin auri Mutallab domin ko nawa ce zan kashe sai na kashe na siyesu sun tilasta maki aurensa. Ba'a raba tsaki da tsaɓa ni kuma ina da ita kinga kuwa ina jefe masu zasuyi chaaa suna tsuwwa..."
Wannan wulakanci da mi ya yi kama, a tarar da ni har gidan ubana a yi min wannan cin mutunci, tozarci da muzanci.
Na juyar da kaina gefe tareda maida kwollar dake neman zubowa akan fuskata, bana son in zubar da hawaye a gabansu ballantana har suga wallena.
Yadda take maganar ya saka gaba faduwa musamman yadda take faɗin zata yi amfani da kuɗi ta sayi waɗanda suka isa dani, ni shaida ce akan yadda wannan lamarin zai tayar da kura musamman idan aka biyo ta wajen Dangin Abbana, dama ba kaunar Ummarmu sukeyi ba, wannan tsanar itace ta shafemu, hujjarsu itace Abbanmu ba ya taimakonsu sun manta da cewa idan dambu yayi yawa ba ya jin mai, mu kanmu lallaɓawa mukeyi domin kaso mai yawa na samun Abba akan karatun yake tafiya.
Yarinyar tana ta cika tana batsewa. Tana ƙoƙarin ta ƙara jifata da wata maganar ta miƙe a fusace na nuna mata kofa na ce, "Get out. Ki fice min daga daki, Mutallab ne ba zan aureshi ba. Kuma ni Rumana ba mayyar kuɗi bace ba ballantana suyi tasiri a kaina."
Ta fashe da dariya tace, "Idan ke kudin basu gabanki ai kina da kawunai da gwaggonni, sai na sayesu da kudi sun sakaki auren Mutallab ta dole."
Ta bangajeni ta fice fuu.
Safeena ta ɗurkusa ta ɗauki kuɗin tana mai bani haƙuri, "Baby ki yi hakuri."
Da sauri na katseta tareda nuna mata kofa na ce,
"Babu abun da za ki ce min, dukkanin wulakanci da tozarci da ta yi min kece kika janyo min, da kika kawota har inda nike ta ci min mutunci, tou dai Mutallab ne ba zan aura ba, nice Rumana kuma na ce ba nayi sai kubi wani sarkin. Ai bani ɗaya bace mace a garin Katsina ballantana a zo a tayar min da hankali akan auren wanda bana ra'ayi. Aikin banza aikin wofi. Marassa zuciya kawai, ance ba'ayi daku amma kun nace kun manne kunki kuyi zuciya ku tafi."
Safeena tabi bayanta jikinta a sanyaye, na rumtse idanu hawaye suna zubo akan kumatuna, duk da ba na so amma saida suka sakani na furzar da bakaken maganganu.
Taku Har Kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)