CHAPTER 2
AMARYAR GADO
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
AISHA SANI ABDULLAHI
Xayyeesherthul-humaerath
©️2026
Jan hankali: Wannan littafi ƙirƙirarriyar riga ce da aka saka wa kowace ƙaddara da ke cikinsa suna. Kada wani labari ko sirri da aka bayyana a cikinsa ya sa a fassara shi da rayuwar wani na gaske.
Gargaɗi: Haƙƙin wallafar littafin na marubuciya ce kaɗai. Ba a yarda a juye shi zuwa wani harshe, ko a canza shi zuwa sautin murya (audio) ba tare da rubutacciyar yarjejeniya ba.
SHAFI NA BIYU
Zaune take a falo, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, hannunta riƙe da rimot tana kallon TV cikin isa da kasaita. Kwatsam, sai ta ji an fisge rimot ɗin daga hannunta.
Da sauri ta ɗago kai, sai ta ga Sufyan tsaye a gabanta. Har ya juya ya nufi kujerar da ke gaba, hankalinsa kwance yana canja tashar TV.
Cikin fushi Farida ta miƙe ta ƙarasa gabansa.
“Wannan wani irin iskanci ne? Ina zaune ina kallo, kawai ka zo ka fisge min rimot, har ma ka canja tashar?”
Ko kallonta bai yi ba, balle ya ba ta amsa. Hankalinsa na kan wasan ƙwallon ƙafa na World Cup da ake bugawa.
Ran Farida ya ƙara ɓaci. Ta miƙa hannu tana ƙoƙarin ƙwace rimot ɗin, amma cikin sauri ya hankade hannunta gefe.
A daidai lokacin ne Inno ta shigo.
“Subhanallah! Me zan gani haka? Faridatu, Sufuyanu… kun sake farawa kenan?”
Ta ƙarasa tana janyo Farida daga gabansa.
Farida ta nuna Sufyan da yatsa.
“Inno, wallahi yaron nan ya raina ni sosai. Ina zaune ina kallo, kawai ya zo ya fisge min rimot ya canja.”
Inno ta girgiza kai.
“Ke ma dai kamar ba ki san halinsa ba. Amma kai ma, Sufuyanu, wannan yayarka ce. Akwai tazarar shekara biyar tsakaninku. Sannan ko ba komai, matar da yayanka zai aura ce. Ya kamata ka riƙa ba ta girma.”
Sai a lokacin Sufyan ya ɗaga ido ya kalle su.
“Don Allah ku yi shiru mana. Kallo nake.”
Yana gama faɗin haka ya mayar da hankalinsa kan TV.
Inno ta ƙarasa gabansa ta tsaya gaban talabijin ɗin.
“To, idan haka ne, ka tashi ka ba ni ɗakina. Ai ba gidan ubanka ba ne.”
Ta fisge rimot ɗin daga hannunsa.
Sufyan ya buɗe baki zai yi magana kenan…
Sai aka ji ƙarar buɗe ƙofa.
Mama ce ta shigo a gigice, fuskarta cike da firgici.
Tare da Aunty da ke bin bayanta.
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!… Inno… Ahmad ya yi hatsari!”
Dukansu suka miƙe a razane.
“Suna ina?” Sufyan ya tambaya cikin sauri.
“Asibiti… ku zo, ka kai mu yanzu.”
Ba tare da ɓata lokaci ba suka fice.
suna isa asibitin, suka tarar da Abba, Baba da Uncle tsaye sun yi jingum-jingum, A tsakiyarsu kuwa Ahmad ne kwance, an rufe jikinsa da farin kyalle.
Farida ta taka a hankali kamar wadda aka zarewa laka a jiki,Ta durƙusa kusa da shi, hannunta na rawa yayin da ta ɗaga gefen kyallen.
Da ta hangi fuskarsa…
Numfashinta ya tsaya.
“Yah Ahmad… tafiya ka yi ka bar ni? Yah Ahmad, ka manta da alkawarin da ka yi min? Shikenan… na shiga uku… na lalace…”
Kukanta ya ƙara tsananta, jikinta ya yi sanyi kafin ta zame ƙasa.
Inno ta kalli waɗanda ke wurin cikin ruɗani.
“Ni ban gane ba… me ake nufi da an rufe shi da farin kyalle haka?”
Baba ya runtse ido na ɗan lokaci kafin ya fara magana cikin muryar alhini.
“Inno… ki yi haƙuri. Allah Ya yi wa Ahmad rasuwa.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!”
Jiri ya ɗebi Inno. Tana kokarin faɗuwa, Aunty ta yi saurin tare ta.
Farida kuwa tuni ta suma.
Sai bayan an yi wa Ahmad sutura, aka yi masa jana’iza, aka dawo daga maƙabarta ne Farida ta fara farfaɗowa.
Da ta buɗe ido, Goggo ta fara gani.
Cikin raunin murya ta ce,
“Goggo… ina Yah Ahmad? Bai mutu ba ko? Don Allah… kar ki ce min ya mutu.”
Goggo ta shafa kanta a hankali, idanuwanta cike da ƙwalla.
“Yana wajen Ubangijinsa, Farida. Ki yi haƙuri. Wannan ƙaddarar Allah ce, kuma babu mai guje mata.”
Farida ta girgiza kai.
“A’a… ba zai yiwu ba… Yah Ahmad ba zai bar ni ba… Ya yi min alƙawari…”
Ta fashe da wani irin kuka mai karya zuciya, yayin da Goggo ta rungume ta tana share mata hawaye, ita ma nata hawayen na zuba ba tare da ta iya hana su ba.
Kwanaki uku kenan da rasuwar Ahmad.
A wannan ranar Inno ta tara gaba ɗaya iyalan gidan a falonta. Daga ‘ya’ya, surukai har jikoki, kowa ya hallara cikin nutsuwa. Babu wanda ya san dalilin wannan taro.
Inno ta gyara zamanta kafin ta fara magana.
“Na san har yanzu alhini na rasuwar Ahmadu bai fita daga zukatanmu ba. Allah Ya jiƙansa da rahama.”
A tare suka amsa da, “Amin.”
Ta ɗan dakata kafin ta ci gaba.
“Amma rayuwa ba ta tsayawa saboda mutuwar mutum,Kuma akwai wasu al’adu da iyayenmu suka gada suka bar mana, waɗanda ba za mu bari su mutu ba.”
Falon ya yi tsit.
“Kowa a gidan nan ya san cewa tun kaka da kakanni, auren dangi ne muke yi. Ba don mun rasa mazaje ko mata a waje ba, sai don muna son zumunci ya ci gaba da ɗorewa a cikin gidanmu.”
Ta sauke numfashi.
“Ahmadu Allah Ya karɓi abinSa kafin aurensa da Faridatu. Amma wannan ba yana nufin an fasa kenan ba kila wata damace Ubangiji ya kara ba mu.”
Sai ta ɗaga kai ta kalli kowa.
“Na yanke hukunci… auren nan zai tabbata kamar yadda aka tsara. Sai dai wanda zai auri Faridatu shi ne Sufyan.”
Wani irin shirune ya mamaye falon.
Farida ta zaro ido tana kallon Inno, kamar ba ta ji daidai ba.
“Inno… me kika ce?”
“Ina nufin abin da kika ji.”
Farida ta fashe da kuka.
“Wallahi ba zan iya ba! Sufyan fa ƙanina ne. Ta yaya zan aure shi? Ai gwanda in mutu ba aure.”
Sufyan ma ya girgiza kai cikin rashin yarda.
“Ni ma ba zan iya ba, Inno. Wannan ba zai yiwu ba. In kaita ina? Wallahi ba zan aure ta ba.”
Baba ya daka tsawa.
Nan take falon ya yi tsit.
“Tun yaushe yara suka fara mayar da martani kafin manya su gama magana? Ku shiga taitayinku”
Inno ta tabe baki, hawaye suka cika mata ido.
“To Haruna, ka ƙyale su. Su faɗa abin da suke so. Amma ni ba zan bari al’adar gidan nan ta mutu a hannuna ba. Na raini wannan gida, na ga yadda iyayenmu suka tafiyar da shi, kuma ba zan zama sanadin rushewarsa ba.”
Ta karasa maganar tana face hanci da gefen zani.
Baba Haruna ya gyara zamansa, sannan ya ce,
“Wannan gaskiya ne, Inno. Mu ma muna bayanki dari bisa dari. Babu mai ja da ke a gidan nan. Kuma batun girma ko shekaru ai ba shi da wani tasiri a batun aure. Manzon Allah (SAW) ma ya auri Nana Khadija (RA), wadda ta girme shi da shekaru. Hakan ma ya shiga cikin Sunnah. Don haka, kar in ji kar in gani, wannan auren babu fashi, sai an yi shi.”
Sufyan ya ɗaga kai cikin nutsuwa ya ce,
“Baba, ni fa ban isa aure ba tukuna. Kuma a yanzu ban da ra’ayin yin aure.”
Baba Haruna ya daka masa tsawa.
“In kai ba ka da ra’ayin yi, mu iyayenka muna da shi. Kuma ya zama wajibi ka bi abin da muka yanke.”
Yana kaiwa nan ya yi yunƙurin kai masa mari.
Abba Shuaibu ne ya tare hannunsa, ya ce,
“Amma dai, Yaya, idan aka duba maganar nan, shekarunsa ashirin ne kacal, ita kuma tana da shekara ashirin da biyar. Kamar za a kwaresa ne fa.”
Baba Haruna ya bi shi da wani mugun kallo.
“Da ba a gabana ka faɗi wannan ba, da na ce an ƙirƙiro mini ƙarya. Auren nan babu fashi. Kamar yadda Inno ta buƙata, haka za a yi.”
Kawu Hamza ya yi gyaran murya kafin ya ce,
“Amma dai ya kamata a tsaya a duba lamarin yaran nan. Tun da dukkansu ba su son auren, bai kamata a tilasta musu ba.”
Nan take Inno ta kakalo hawaye, tana gogewa da gefen mayafinta.
“Ai dama na sani. Haruna kaɗai ne yake ƙaunata a gidan nan. Ku kam, gara ma ku ce na faɗi na mutu na lura taron dangi ma kuke so yi mini.”
Haɗa baki dukkansu suka yi suna ba ta haƙuri tare da lallashinta.
Baba Haruna ya ce,
“Inno, kina nufin ranar da aka tsara auren wancan ne kike so a ɗaura wannan ma?”
Inno ta gyaɗa kai.
“Eh ƙwarai kuwa. A ranar nake so a yi komai.”
Baba Haruna ya ce,
“To shikenan. Ba matsala. In Sha Allah, daga yau za a ci gaba da shirye-shiryen komai.”
Gajeren murmushi Inno ta yi, sannan ta ce,
“Yawwa. Allah Ya yi muku albarka. Na tabbatar Alhajina da ke kwance a ƙasa yana cikin jin daɗi da alfahari da ku.”
Da haka taron ya watse.
Matan gidan kuwa ba su ce uffan ba. Sun san halin Inno sarai; duk wanda ya yi yunƙurin ja da ra’ayinta, to ya jawo wa kansa masifa. Saboda haka suka haɗiye abin da ke zukatansu, kowacce ta tashi da damuwarta, tana addu’ar Allah Ya kawo mafita cikin lamarin.
Farida ta kasa samun sukuni. Tun bayan zaman da aka yi a falon Inno, kuka ya zama abokin zamanta. Idan ta tuna abin da aka yanke, zuciyarta sai ta cika da baƙin ciki da takaici.
Tun tana yarinya har ta girma, babu abin da ta fi tsana irin namiji ya ce yana sonta, ko da kuwa sa’anta ne. Bare kuma ace wanda ta san sarai ta girmi shekaru shi za a ce ya zama mijinta.
Ta daɗe tana mafarkin irin mutumin da take son aura—namiji mai kamala, natsuwa, mutunci da kulawa. Mutum mai cike da hikima da dattako. Halayen da marigayi Ahmad ya tattara gaba ɗaya.
Amma Sufyan kuwa, ko kaɗan bai taɓa shiga cikin jerin mutanen da take iya kallon su da wannan idon ba. Miskilancinsa, yawan yin shiru, nuna isa da ɗaga kai sun sa tun fil’azal ba sa shan inuwa ɗaya. Ko gaisuwa idan suka yi, sai dai saboda dole.
Kwance take, kanta shimfiɗe a cinyar Aunty, tana sharɓar kuka kamar ƙaramin yaro.
Aunty ta riƙa shafa sumar kanta cikin lallashi.
“Farida, ki yi haƙuri. Ki daina wannan kukan. Mu bayin Allah ne, ba mu san inda alherinmu yake ba. Wataƙila wannan ne Allah Ya zaɓa miki saboda alheri.”
Farida ta ɗago jajayen idanunta da suka kumbura saboda kuka.
“Aunty, ina alheri a cikin wannan? A kan yaron nan da na girmi shekaru? Wanda ko kallonsa bana iya yi saboda halinsa? A ce ni ce matarsa? Wallahi wannan ba alheri ba ne… sai dai sha…”
Tun kafin ta ƙarasa, Aunty ta sa hannu ta danne bakinta.
“A’a! Kar ki sake faɗar irin wannan. Kada ki yi sako. Komai yana hannun Allah. Ki yi haƙuri, ki ci gaba da addu’a. Allah Mai juyar da zukata ne.”
Farida ta sake fashewa da kuka, yayin da Aunty ta rungume ta tana lallashinta.
⸻
Dare ya tsala. Misalin ƙarfe biyu na dare.
Shiru ya mamaye gidan gaba ɗaya. Ba a jin komai sai kaɗawar iska da ƙarar agogon bango.
Cikin wannan shirun ne Inno ta ji an taɓa kafaɗarta a hankali.
Gabanta ya faɗi.
Ta buɗe idanu a firgice, zuciyarta na bugawa da ƙarfi kamar za ta faso daga ƙirjin.
Da ta ɗaga kanta, sai idanunta suka sauka kan wani dogon baƙin kyalle da ya miƙe tsaye a gabanta. Tsawonsa ya kai har ta kasa ganin inda ya ƙare. Tamkar babu farkonsa, babu ƙarshensa.
Wani irin sanyi ya ratsa ƙasusuwanta.
Ta soma ja da baya tana rawar jiki.
“Wa… wa… wa ne?… Astaghfirullah… Astaghfirullah…”
Muryarta ta kasa fitowa yadda ya kamata.
“Ina neman tsarin Allah… Kada ku kashe ni…”
Duk inda ta matsa, sai ta ga baƙin kyallen yana matsowa kusa da ita, tamkar yana shawagi ba tare da ƙafafu ba.
Ba zato ba tsammani, wata murya mai firgitarwa ta kaɗa ɗakin.
“In kika kuskura kika yi ihu…”
Muryar ta ɗan yi shiru na wasu daƙiƙu, kafin ta ci gaba cikin wata irin amo mai razanarwa.
“…za mu kashe ki…”
“…mu cinye namanki…”
“…mu kwakule miki idanu…”
Jikin Inno ya yi sanyi ƙalau. Ta rasa ko numfashi take yi, yayin da zufa ke gangaro mata duk da sanyin daren.