Page 46
💫MARYAMA💫
46.
_______A tare da dr, Umaimah ta dawo dakin,still yana nan yadda yake bai motsa ba,tun hawayen da ya sauka digo daya bisa filon da yake kwance kuma wani bai kara fitowa ba.
Stethoscope dake rataye wuyanshi likitan ya zare ya fara auna Jabeer gami da yin wasu yan dube dube irin na su na likitoci,bayan wani dan lokaci ya dago yana kallon su . "Bai farka bane dacta?" baffanmu ya tambaya cike da rashin kwarin guiwa ganin kamar Jabeer ya musu abin nan da ake cewa ta leko ta koma.
"Karku damu baba,jikin marar lafiyar yana kara yin sauki, sannan wannan hawayen da yayi shike nuna mana cewa zuciyarshi ta fara daidaita kuma ta na aiki yadda ya kamata,watakila da akwai wani abu da yaji a yanzu walau a zahiri ko a mafarki da ya taba mashi zuciyar har wannan hawayen ya samu nasarar zuba a likitance kuwa wannan ci gaba ne sosai,rawar da jikinsa yayi kuwa na nuni da irin sakon da ya kai zuciyar tashi ce ba mai dadi bane a gareshi,so ya kamata mu dinga kiyaye abin da zamu ke fada dan gujewa afkuwar matsala"dactan ya fada yana kara dudduba Jabeer.
Tun fara maganar Inna da baffa da abin da suka tattauna da kukan da Inna keyi yana jinsu dan a daidai lokacinne ya dawo cikin hayyacinsa,shigowar Umaimah da maganganun da ta sanar musu na yadda abubuwan suka afku shiya kara janyo tabarbarewar komai a lamarin jikinnashi,kwakwalwarshi ce ta bashi cewa da gaske ne kenan,Maryamar shi ce ta rike kwalar rigarshi tana ikirarin sai ya saketa, kenan ba mafarki yayi ba na cewa da bakinshi ya furtawa pretty kalmar saki, idan ya ji daidai kamar su Inna suna maganar Maryama bata gida ina ta tafi?.Shine tambayar da yai wa kansa,ina ta tafi a halin da ta ke ciki na mai juna biyu?wanne hali take ciki?Ya Ilahi mai yasa ban mutu ba, mai yasa ban mutu ba kafun wannan rana, rayuwata babu Maryama tamkar matacciyar shuka ce da bata samun ban ruwa.
Wadannan tunane tunane su suka hadu sukaiwa Jabeer rubdugu har suka haddasa masa rawar jiki da kuma digar hawayen da baisan da fitowarsu ba.A hankali yake bude idanunsa, da sauri ya mayar gami da rufe su ruff sakamakon wani haske da ya mamaye ganinsa.Zaro ido Inna tayi dan tsaf a idonta ya ware idanunshi.
"Dacta ya bude idanunshi wllh".Cewar Innarmu wani kuka yana taho mata.
"Ehh mama,amma bama bukatar hayaniya sai a hankali zai bude kinsan ya juma a rufe.
Kokarin bude idanun nashi ya kara dan jin kukan da Innarmu take yana taba shi....."plsss stop crying Innarmu" ya fada kasa kasa saidai babu wanda yaji abinda ya fada din,sun daiga alamar bakinshi ya motsa.Gaba dayansu kanshi suka yo " Sannu Hamma jay".Umaimah ta fada cikin tausayawa, tamke jajayen idanunshi yayi da sauri yana girgiza kai.Jin Muryarta da kuma irin sunan da take kiranshi da, yana tuna mashi wata hallitar da baison tuna wa da ita a duniyarshi ta yanzu,bai son tunawa da ita amma abin mamaki shine bai jin haushinta ko kadan...Duk sannu suke mashi amma bai tankawa kowa ba sai ma kara rufe idanunshi da yayi gam,duk sadda Umaima tayi magana kuwa sai yaga tamkar idan ya bude idanunshi maryama zai gani wajen,sosai su Innarmu suka yi murna da farfadowar Jabeer, magani da kulawar likitoci ya cigaba da karba har tsawon sati biyu kafun a ka sallamoshi duk da ba wai ya warke bane dan har lokacin Jabeer bai cewa komai, idan ana magana ma saidai yai ta bin mutane da ido,ganin hakan yasa baffa cewa a sallamosu gwara su hada da na gida,duk yadda likitan yaso fahimtar dasu cewa jinyar Jabeer baya bukatar gargajiya amma baffa yaki dole aka sallamosu din.
Direct gidan su Innarmu aka wuto dashi nan tsohon dakinshi aka gyara mashi gidansu kuwa iya kayan sawarshi da na bukatarshi aka debo kana aka garkame gidan da kwado, shikenan tamkar basu yi rayuwa a ciki ba.Sannu a hankali rayuwa ta fara juyawa yau lafiya gobe babu watarana zaki watarana madaci cikin ikon Allah Jabeer ya fara gane kanshi,idan ana mashi magana yana dan responding,haka kuma babu wanda ya kara dago zancen Maryama a gidan a zahiri, saidai Allah kadai yasan ruwan hawayen dake tsiyaya cikin dare da kuma irin sujjadar da wadannan ahali ke yi akan al'amarin.Wasa wasa Jabeer ya fara dawowa normal self nashi,thou dai yasan har abada ya zama rabin mutum amma yana iya kokarinshi na ganin ya ragewa iyayennasu tsanin tashin hankalin da yake karanta a idanunsu.ya koma makaranta inda yake karantar da dalibanshi haka kuma da yamma yakan leka wajen aikinshi koda bazaiyi komai ba dan yanzu bai cika kuzari ba.
**************
Kwanaki uku Maryama tayi a asibiti sannan ta dawo daidai,saidai duk lokacin da ta tuna abin da ya sami Siyama ba karamin rudani ta ke shiga ba, a gefe guda kuwa Sadeeq ya yi matukar kokari wajen ganin an yiwa pieces na jikin siyama da aka kwashe da tebur aka dura cikin buhu sallah kamar yadda addinin musulunci ya tanadar,shi ya sai wajen da aka binneta dan su acan sai ka sai waje kafun a binne naka.
Koda aka sallamota daga hispital din bai barta ta koma cikin makaranta ba gidanshi ya kaita duk da maganar mommy na yi mashi yawo a ka amma ya yi biriss da hakan da tunanin cewa wa gare ta a nan din? idan ya barta ma karshe tagyara kawai zatai....Tsananin kulawa Sadeeq ke ba Maryama, har yanzu bai sanar da ita baki da baki yana kaunarta ba amma yana nuna mata a aikace sannan yana da tabbacin bata manta abin da ya fadawa mommynshi wancan ranar ba.Cook ya dauko na mussaman take dafa musu abinci da kuma debe mata kewa,taji dadin hakan kuwa dan sosai matar take kula da ita dan duk zatonta matar gidance.
Irin girmamawar da matar keyiwa maryama da irin yadda Sadeeq ya sake bakin aljihunshi a kanta yana kaita wajajen shan iska daban daban da manyan boutique boutique da nufin ta manta abin da ya faru ta yi karatu kamar yadda yake bukata, su suka hadu suka tadawa Maryama asalin burinta na ainahi, suka mayar da ita asalin Maryamar ta mai dogon buri da son rayuwar kawa,son wadannan dogayen benayen da manyan motoci suka fara dawo mata sabo,tana daga zaune saidai ta ci tasha ta yi kallo, a take jikinta ya murje sirrin kyau fiye da na da wanda ya samu sanyin ac, da lafiyayyar abinci suka bayyana a jikinta,sau tari Sadeeq bai iya kallonta sau biyu dan yarinyar kashe masa idanu take, sai yaji tamkar ana ingiza shi zuwa gareta, haka zai kwana bankawa kanshi ruwan sanyi da matsar lemon tsami tsabar yadda mafarkanta suke hanashi nutsuwar gangar jiki,saboda haka ne yayi niyyar ta koma cikin makaranta a gobe kafun ayi abin kunya.amma ya naso yayi suprising dinta da wani abu kafun ta wuce,Hakan ko akayi....
Washe gari misalin karfe sha daya na safe Maryama na zaune a palo tashinta daga bacci kenan ta watsa ruwa gami da sanya wata doguwar riga mai gajeren hannu onion colour sai gashinta da ta dura cikin hula ko mai bata shafa ba ta fito amma idan ka ganta sai ka kara ganinta tsabar yadda tayi wani luwai luwai kamar a cikin kwalba take rayuwa, zama tayi tana canza tasha gami da daura kafarta bisa table na glass dake gabanta, yadda tayi din idan ka ganta zaka rantse irin matan nan ne da suka kame ko ina na gidajensu sukai kane kane.
Cook na su ce ta fito daga kitchen daure da apron na girki ta durkusa har kasa cikin harshen turanci ta ce, "Barka da fitowa madam, breakfast yana nan ready a shirya a table ne ko a kawo nan?".
Yamutsa fuska tayi saida ta ja wasu sakwanni kafun ta bude baki ba tare da ta kalli matar ba tace, "ki shirya a dining table".
"Yes ma'am" ta fada gami da juyawa,har ta kai kofar shiga kitchen Maryama ta kira ta,cike da bada Umarni tace, "Mikoman remote control", du tsakaninta da remote din baifi taku biyu ba amma haka cook din ta juya ta dauko mata sannan ta wuce dan shirya table din, yayinda Maryama kuwa ta canza tasha zuwa Zee Drama dan shine favourite site nata a yan kwanakin...Tsawon minti biyar kenan da cook din ta sanar mata cewa ta kammala shirya dining, amma ko alamar zata motsa Maryama ba tayi ba,kuri tayiwa tvn dake ta babatu shi kadai tamkar tana kallo ne amma zahiri hankalinta baya tarw da ita, tunanin g.....Tafin da ya mata saitin idanunta ne ya dawar da ita daga duniyar tunanin da ta tafi,.
"Kin yi kewata ko baby?".Sadeeq daya tsare ta da idanu ya tambaya yana dage gira guda daya hannayenshi boye a bayanshi.Kafun ta ce wani abu ya cigaba da fadin, "Nima nayi kewarki da kyar na iya kaiwa yanzu daga inda nake."
Hannu nasa duka biyu ina rufe fuskata dashi, dan sosai yadda ya yi din ya bani kunya, "yaushe ka shigo ban sani ba" na fada still idanu na a rufe.
"Ina zaki san da shigowata kina can duniyar kallon su shahrukhan da kajol suna soyayya".
Kara damke fuskata nayi ina dariya, yayin da ya shagala da kallo na.
"SUPRISE".... Ya fada da dan karfi, hakan ya sa ni dago kaina ina cire hannuna da na rufe fuskar dashi, ido na zaro da sauri ina mikew Ganin abin da yake karkadawa saitina....Ban samu damar furta komai ba sakamakon shock da na shiga har Sadeeq ya yi nasarar jan hannuna muka fita compound na gidan, daga bakin kofa ya walkiyar shi ya fara kashe man idanu,kar dai ace tawa ce wannan?.Har muka iso dab da motar kirar corolla baka wuluk mai daukar ido tsabar sheki ban samu damar rufe bakina ba.
Hannuna ya kama ya damka car keys din a ciki hadi da kara furta "Suprise".
Wani wawan tsalle na yi bansan ya akai ba sai tsintar kaina na yi makale a jikin Sadeeq ina ta kyakyata dariyar da yaki tsayawa, juyi ya fara yi dani a nan tsakar gidan muna dariya tare har saida yaji hajijiyar yana neman kadamu sannan ya dire ni kasa duk muka hau sauke numfashi,Sadeeq ya sai min mota,ni Maryama da mota, abin tamkar a mafarki.A washe garin ranar na koma makaranta inda na samu bayan chioma wasu mata biyu sun karu a dakin namu saidai dukkansu sun girme ni har ma da chioma dan haka namu da ita yafi zuwa dai dai,sai akayi dace ma department namu daya da ita dan haka tare muke tafiya mu kuma dawo tare, karatu nake yi ba kama hannun yaro a gefe guda kuma Sadeeq ya samu mai koya min mota wanda yawanci da yamma muke yi, cikin lokaci kadan na iya mota dan haka na dauko motata na dawar cikin makaranta, ko da yake an haramta zaman mota a cikin hostel amma da shike ina da daurin gindi sai ban samu tangarda ba.
Wannan shine dalilin da ni maryama na fara yin suna a cikin jami'ar patakwat.Cikin lokaci kadan sunana ya zagaye illahirin makarantar dan ni kadai ke da mota kuma a hostel, ga kyau ga ilimi, wannan yasa kowa burinshi yayi abota dani daga maza har mata yayinda lecturori kowa ke sona.A haka muka fara jarabawar zangon karatu na farko, cikin aminci muka gama cike da fatan samun nasarori mussaman ni da kawata da muka shaku sosai CHIOMA.
Anyi mana hutu cike dauki saidai na rasa inda zan nufa yayinda kowa yake haramar tafiya gidan iyayenshi amma banda ni Maryama,Sadeeq dana dogara dashi kwana biyu kenan da yayi tafiya America, dan haka gidan babu kowa ,lura da hakan da chioma ta yi ne yasa ta rokata da mu tafi gidansu mu zauna kafin ua dawo,ba tare da musu ba na bi chioma gidansu dake cikin gari, a dakinta muka zauna cike da rashin tsari babu laifi masu kudi ne amma nakan rasa yadda zanyi sallah, ni da kaina nasan ina yi ne kawai ba don ubangiji zai karba ba.
A kullum chioma tana fita da dare misalin bakwai bata tashi dawowa gida wataran sai karfe dayan dare, tun ina mamaki har na daina, lokacin da muka cika kwana goma da hutu ne chioma ta yi nasarar jana club din da take zuwa rage dare a cewarta,tun ban yarda ba har ta yi nasara a kaina na shirya cikin doguwar riga kamar yadda gaba daya kayana suke a yanzu, nayi rolling mayafin rigar banyi kwalliya ba sai perfumes dana shafa a jikina muka tafi,sosai jikina ya dauki rawa lokacinda muka shiga wajen, abubuwa ne ke faruwa a wajen anorganize,ba karamar rudewa na yi ba dan ban taba ganin inda ake hakan a zahiri ba tsawon rayuwata da sassarfa na juya zan fice daga wajen dan tabbas bazan iya gani ba, diffff wutar wajen ta dauke lalube na fara ina addu'a a raina karaff naj......