Page 43/44
*SANADIN HIJIRA*
BY
Ummu Fadeela
Chapter.... 43/44
Hannu ya sanya ya dagoni, majestically yake taku har bakin kofar. Tunda Mummy ta harbo ni suka hada idanu, hakan yasa ta tsaya tana kare mishi kallo ita ma. Da kalar turancinsa yake magana da fada-fada, "Who the hell do you think you are? Me ta miki zaki aikata mata haka?"
Dan sassauta murya tayi, ta fara magana ita ma kusan minti biyu... "Money!" Ya fada yana yatsine fuska, gyada kai ta yi. Hannu Jack ya zura a aljihu ya kwaso kudin da bai san adadin su ba, ya watsawa Magajiya a fuska. Ya kamo hannuna da karfi, da sassarfa ya turani mota shi ma ya shiga. Ihu nake iya karfina, dan ai gwara min azabar Mummy sau dubu than komawa gidan wannan mutumin. Dashboard ya bude ya kwaso wasu kudaden masu yawa, daloli da kudin Spain dayawa, ya kuma watsawa Magajiya da ke tsaye tana kallon ikon Allah. Bata yi kasa a gwiwa ba kuwa, ta fito ta kwashe abunta tana fadin, "Can ga su gada, ni dai gaba ta kaini."
Gudu yake shararawa saman kwalta, ni kuma ina ihu kamar raina zai fita. Kiiii! Ya gangara gefen kwalta, yana kallona strictly ya ce, "Rufe bakin nan." Shiru kuwa na yi dan na ji shi sarai, sannan ina tsoron abun da zai iya aikata min. Yana kallon cikin idona ya ci gaba da cewa, "Yanzu ke baiwa ta ce, sai yadda na yi dake. Kudi na sanya na siyeki don haka ke din baiwa ce. Yes, you're my sex slave, so be ready! Ki shirya karbata a kowanne lokaci." Ba sosai na gane abin da yake fada ba, amma na fahimci dayawa daga ciki. Tabbas na shiga uku ni Fanne! Zuwa yanzu na kuma yarda bani da wata mafita, amma akwai Allah.
"Shin Ubangiji zai karbi addu'ata cikin wannan gida da ake bautan waninsa?"
Na fada daidai lokacin da ya iso gidan. Yana bude motar ya fita, ni ma na pita. "Fanne ki gudu kawai," zuciyata ta fada. To, ko na gudu ma ina zanje? Wa na sani?
Bayanshi nake bi a hankali har cikin falon. Mace ce zaune da yarinya saman keken guragu.
A dan rikice Mom ta ce, "Son, ina take?" Nuna ni ya yi da yatsa daidai sadda nake shigowa. Sake baki da hanci uwa da yar suka yi suna kallona. Mom ta karaso gareni har tana hadawa da dan gudu, ta rungumeni ba tare da ta dubi mummunan fuskata ba da kuma hijabin da ke jikina wanda na tabbata bata saba gani ba.
Tana shafa fuskata ta ce, hawaye na sauka saman kuncinta, "Thank you daughter, na gode da sadaukarwarki garemu. Na gode, na gode."
Bana fahimtarta, amma kalmar godiyar da na kasa fahimtar abun da na mata take gode min haka, shi ya fi tsaya min a rai. Hannuna ta janyo har tsakiyar palon ta ajiyeni kan kujera tana ci gaba da gode min, still hannunta na saman kuncina.
Da wani irin clouded expression Jack yake kallonmu, kafin ya sanya hannunshi duka biyu cikin aljihu ya fara tafiya. Bin shi na yi da kallo dan a gareshi na yi tunanin samun karin bayanin godiyar da matar take mi ba tare da na mata komai ba. Har ya yi nisa, sai kuma ya tsaya gami da juyowa. Karaff idanunshi suka shige cikin nawa; da sauri na rumtse nawa idon, kirjina na bugawa da karfi-karfi. Murmushi Jack ya yi yana sosa habarshi, ya wuce part nashi!
"Daughter, tashi muje in nuna maki inda zaki zauna kafin lokaci ya yi ko?" Tana jan hannuna muka haura sama, wani madaidaicin daki ta nuna min da sunan nawa. "Ki yi wanka ki huta, bari in kawo maki abinci." Daga haka ta fita. Kallona na mayar cikin dakin wanda ya kunshi ababen more rayuwa da jin dadi; a hankali na kai zaune bakin gadon ina share hawayen da suka ki daina kwaranya daga idanuna, daga ranar da na budi ido na ganni a matsayi yar adam har zuwa wannan lokaci da rayuwa take mini juyin waina.
Saman gadonshi ya fada ba tare da ko takalma ya cire ba. 'Na yi daidai dawar da ita cikin rayuwata da na yi? Na kyautawa tata rayuwar da hukuncin da na yanke ba tare da yarda ko amincewarta ba?' Zuciyar Jack ta motsa. 'But she's nothing, she's your slave. Bata da wani gata sai yadda ka yi da ita. Sayanta kayi and a yanzu lafiyar Elisha ya fi komai muhimmanci a gareka,' wata zuciyar ta kara tunatar da shi. Mikewa ya yi ya fara zagaye dakin; yadda ta rumtse idanu dazu da suka hada ido ya fado mishi. Murmushi ya yi, "Me yasa take haka idan na kalleta?"
Kuka sosai Badar take yi kamar wacce a kayi wa mutuwa, har da bubbuga kafa. Bude kofar dakin a kayi, Umma ta shigo, Saudat biye da ita a baya. Da gudu ta mike ta rungumeta tana sakin kuka mai tafe da shessheka, "Na shiga uku na lalace Anty! Ni tunda nake a duniya, ko a littafi ko a finai-finai, ban taba jin labarin amarya kamata ba."
"Rufa min asiri baki shiga uku ba. Me Aminun ya aikata? Kada dai a ce haka ya barki ko gasa ki bai yi ba ya sa kai ya fice? A'a to gaskiya ni ma ban taba jin kalar wannan abu ba. Daga daura aure jiya zuwa yau da safe kawai an samu matsaloli mara iyaka. To, shi haka ake, sai ka sha romo kuma ka kasa wanke kwanon?"
Wani hade rai Saudat ta yi, "Haba Ummah, me haka kuma? Shi ya ce maki ya yi wa small mom wani abu ne? Ai dai ya kamata idan yana da ta ido ya bari sai sun tashi daga gidan nan, amma tsakanin uwarshi da babanshi da ke yayar matarshi ne zai wani ce zai..."
"Wayyo Anty, ni dai na shiga uku! Gefe da gefe muka kwana ko hannuna bai rike ba, kuma asubar farko ya fita. Ko fa irin ya dan hura min iska a kunne ya ce, 'Sweetheart wake up, it's time for prayer' dinnan bai ba. Kawai ficewa ya yi ya bar min wata shegiyar takarda wai ya je sallamar abokanshi. To fisabilillahi Anty, haka ake? Kuma abokanshi sun fini ne?"
"Eh to, Aminu dai bai kyauta ba Badariya, amma ki mashi uzuri tunda asali kin san yadda yake, baudadden hali ke gareshi amma kika nace. Yanzu ga Saudatu ta tayaki ku gyara ko ina, kema ki tsala wanka kafin ya dawo. Ki mashi uzuri; kinga abokan nashi tafiya zasu yi, ke kuma kuna nan tare ai har abada." Gyada kai Badar ta yi kamar yar goye. "Yauwa, idan kun gama ga breakfast saman dining sai ki ci, idan zaki jirashi kuma to..."
"Anty, zan jirashi."
Kamar yadda Ummah ta fada, haka Saudat ta zage suka gyara bangaren da ba wani datti ne da shi ba dama, ko ina ya dau haske. Ta kunna burner, tana kallon Badar ta ce, "Wuce ki yi wanka, zan karasa sauran." Ba musu ta wuce. Saudat ta bita da kallo tana murmushin jin dadi. Kwanukan da Aminu ya bata wajen girkin jiya ta tattara ta wanke, komai ya zama neat, sannan ta shige dakin Badar. A daidai lokacin ta fito wanka daure da towel da bai gama rufe mata ko mazaunai ba, and that changed everything. Kawai jinta ta yi jikin Saudat tana mata kalan wasu abubuwan da ya rudata.
"Stop it Saudat, stop it please kar ki bata min shiri! Ba haka mukayi da ke ba, dan Allah ki bari kar ki bata min komai. Innalillahi Saudat, stop it I said stop it!!!" Duk ta rude ta rikice, sai kyarma take yi. Saudat da ta fahimci ta rigada ta yi turning Badar on, ta ci gaba da abun da take. Badar kuma tuni ta gama saki dan tabbas jikinta yana bukatar abun da take mata din, amma zuciyarta baya so dan ba karamin gyara ta yi wa sojanta ba, gashi lokaci daya Saudat zata bata mata shiri.
Sai da komai ya kammala ta rushe da kuka, "Why Saudat? Me yasa zaki min haka, kinsan nawa na kashe kuwa?" Janyota ta yi tana lallashinta, daga haka suka kara komawa ruwa. *(Allah ka shiryamana zuriya alfarman Annabi S.A.W).*
Tun asuba da ya fita, ba shi ya dawo gidan ba sai karfe goma sha biyu na rana. Ya shigo a gajiye likiss. Tana zaune saman kujera as a bride she is, ta sha kwalliyarta na alfarma sai baza kamshi take ta ko ina. Kallo daya ya yi wa kumburarrun idanunyi ya fahimci ta sha kuka ta koshi. "Me ya samu amaryata?" Ya tambaya in a naughty way. Tura baki ta yi gaba, a ranta tana tsinewa Saudat ya fi sau cikin kwando. Sosai Al'ameen ya yi rarrashi, amma Badar ta kasa daina kuka; da ta tuna barnar da Saudat ta mata, sai ta kara rushewa da kuka. Tun abun yana bashi dariya har ya koma bashi mamaki.
Ajiye spoon da yake breakfast din ya yi, "Wait, tell me meke faruwa? Dan wannan kukan bana fitata bane kawai, there's something da kike boye min." Da sauri ta goge hawayenta, zuciyarta na tsinkewa; na shiga uku, kada dai ya gano abun da ya faru ne? Amma tunda bai taba ganowa ba sai yanzu yau kawai. Kara saisaita nutsuwarta ta yi, "Ko ba kai ne ba? Kawai ka yi tafiyarka ko tadani bakayi ba Sojana, kamar fa wanda aka yi wa auren dole," sai hawayen suka kuma balle mata.
Hade hannayenshi duka biyu ya yi saman table din gami da daura habarshi a kansu yana kallonta. Kukanta yana tuna mishi da yarinyar; a duniya bai taba ganin yarinyar da ke da saurin kuka kamarta ba. Lumshe idanu ya yi. *'Allah banacin mangwaro, ba na cin kifi ko a miya ban taba ci ba shaaaa'* sai hawaye kamar an bude famfo. Wani lallausan murmushi ya saki still idanunshi a lumshe, "Cry, moody girl!" Maganar ta subuce mishi. Badar da ke ganinshi cike da nishadi ta kuma sakin kuka, wani dadi yana mamayarta zatonta da ita yake. Da hanzari ya bude idonshi kasa-kasa ya ce, "Me kuma a kayi?"
"Kai ne ai baka bani amsa ba, kamar wadanda aka yi wa auren dole."
"Ohh Badar, ni na ce?"
"Baka ce ba amma haka kake behaving."
"To share hawayen nan, bani son ganinsu kuma. Ci abincinki ko in baki?" Ya dago chips a spoon yana nufar bakinta. Wage baki kuwa tayi tana karba cike da jin dadi har ta koshi. Aminullahi ya dade da fahimtar Badar macece mai son soyayya, tana son taga ya birkice ya rude a kanta amma ya kasa hakan, duk kuwa da cewa yana jinta sosai a cikin ranshi. Sai da suka kammala ya shiga wanka, ita kuma ta tattara kwanukan ta wanke a kitchen, ta hadasu gefe guda a niyyarta anjuma zata fitar da su kitchen na kasa.
Tsaff ya fito cikin shirinshi na bakaken yadi wanda ya yi masifar haska farar fatarshi, sai baza kamshi yake. Hannunshi ta rike gam kamar zata mai dashi ciki, "Sojana ka yi kyau! Tunda nake a rayuwa, ban taba ganin kyakkyawar halitta kamar ka ba. Komai ka yi ko ka sanya, kyau yake maka; kana girma kana kara yin kyau." Lakace hancinta ya yi, "See you, ai kin fini kyau. Idan ina kusa dake, disashewa nake ki karbe komai."
"Da gaske Sojana! Na godewa Allah. Ina fatan duk wata mace da zata kalleka idanunta ya tsiyaye." Dariya ta bashi sosai amma ya danne, yana dage mata gira daya ya ce, "Really?"
Ita ma girar ta dage ta ce, "Of course."
Daga haka suka wuce bangaren Abeey da ke palonshi, kasancewar yau din weekend ne bai fita ba sai yamma. Nasiha sosai ya musu na hakuri da juna da hakuri da rayuwa, "Ku kasance tsintsiya madaurinki daya, kada ku yarda wani ya ji sirrinku. Ku kashe tare ku binne tare; sai idan abun ya fi karfi ne zaku sanya mu a ciki. Wannan shi ne sirrin zaman tare. Allah ya yi maku albarka." Cewar Abeey yana kallonsu.
"Amin," Ummah ta amsa, ta daura da nata nasihar ita ma. Daga karshe ta ce, "Allah ya baku zaman lafiya da zuriya masu albarka." Wani kallon kasan ido Abeey ya mata. Mikewa suka yi, Al'ameen ya rusuna ya ce, "Mun gode Abeey, Allah ya kara girma. Zamu shiga wajen Ummie." Ummah ma mikewa ta yi ta rufa musu baya, baka gane yanayin da ke fuskarta. Abeey kuwa mikewa ya yi hade da goya hannayenshi a baya, ya fara zagaye dakin. "Ina godiya Badariya, ban tsammaci zaki ratso ta cikin aikina ba, amma na ji dadin shigowarki dan zaki saukaka min abubuwa dayawa. Dan haka na fi kowa farin ciki da wannan aure a zahiri da badini." Wayarshi ce ta yi kara; ganin Hosni ke calling, ya yi azamar dauka ya wuce cikin dakinshi.
Da kallo kawai Ummie ke bin Al'ameen da Badar, ta nutsu shiru. Shi kuma yana tsugunne gabanta tsawon lokaci, idanunshi ya kada jajir. "Ki sa min albarka, ki sawa aurena albarka Ummie. Ko da dukana ne ki yi in san kina sane da ni, Aminullahinki. Ki yi wani abu Ummie, do something please," ya karashe yana daura hannayenshi a kan laps nata. Ummie dai shiru bata ce komai ba, sai ma komawa da tayi ta kwanta tana lumshe idanunta. Tun dawowarsu asibiti last time, Ummienshi ta zama haka; ta daina duka da fashe-fashe sai dai ka ganta shiru. Idan abun ya motsa mata kuma, ta dinga birgima a kasa kenan tana buga kanta akan duk abun da ta samu. Dr. Shettima ya sanar da Abeey hakan na nufin tana tilastawa kwakwalwarta recalling abubuwan da suka wuce ne shi yasa take hakan. Wannan ya daga hankalin Abeey sosai, ya kara kaimi wajen kawo magungunan da suke kara rikitata. Ummah ma ta dage tana canza magani da wanda ita ma take so da burin da ta daukarwa kanta; dukkansu kowa da nufinshi na daban a kan Safenatu, baiwar Allah.
Har suka koma bangarensu, Al'ameen bai dawo daidai ba; lamarin Umminshi yana damunshi yana hanashi bacci. Kwakwalwarta ta fara tuhumar Abeey: 'Me yasa bayason a fitar da ita kasar waje? Dan kudi ya san ba matsala bane akwaisu harda na banza, amma me yasa?'
Kamar daga sama Thaufeeq ya fado falon da irin shigashi da ya saba na samari 'yan bana bakwai masu ji da kansu. Kare mishi kallo Al'ameen yake kamar ya ga sabon mutum; shi yaushe rabonshi da ganin yaron nan? "Tun baka tafi Borno ba," zuciyarshi ta bashi amsa.
Gyara zama ya yi yana amsa gaisuwar da Taufeeq din ke mashi. "Yaya, kawai sai naji labarin Anty Badar dai ta zama mallakinka! Hoo, mun huta fa a gidan nan, ko ba komai zamu huta motsi kadan 'Sojana Sojana'. Kai jama'a, ashe za'ai wannan biki!" Ya karashe yana kwaikwayon muryar Badar. "Kaga Yaya, saukana kenan daga Luxembourg kawai ina fada maka. Ba sai Abeey ya maidani can ba tunda ya mallaki share a wani kamfanin sarrafa tumatiri, kawai ya wakiltani wai in rage sharholiya."
Zaro ido ya yi yana maimaita, "Luxembourg?"
"Can fa Yaya! Kada dai a ce Abeey bai samar da kai ba. Ai ko ya ce zai sanar da kai, ko auren nan ya ce ba sai na zo ba, in maida hankali kan arzikinmu kawai. Amma nace ina, ai bazai yiwu auren babban yaya kuma bani ba..." Haka Taufeeq ya yi ta mashi surutu. Tun yana fahimta har ya daina gaba dayansa; hankalishi ya karkata kan abun da yaron yake fada mishi. Abeey yana wasu abubuwan da bai fahimta kwanannan ba, amma meke faruwa? Suna tare da shi har dare, Badar ma ta fito suka daura daga inda suka tsaya.
Bayan ya kammala duk abubuwan da ya saba kafin ya kwanta, ya harde hannu a kirji yana kallon ceiling. Maganganun da suka yi da Taufeeq dazu yake kokarin digesting amma ya kasa ajiyewa a kowanne matsaya. Bai ji shigowarta ba sai kwanciyar da ta yi a gefenshi hadi da daura hannunta saman kirjinshi tana shafawa a hankali-hankali... Lumshe idanu ya yi, ya bude murya kasa-kasa ya ce, "Badar!"
Kaway tsintar bakinta ya yi cikin nashi, salon da ya dauki hankalinshi duka. Yayin da reshe ke kokarin juyawa da mujiya, nan fa Badar ta raina kanta; ta fahimci lallai wasan yara suke da Saudat ashe! Lallai ko a cikin maza ma akwai maza, akwai kuma matamaza. Ba shakka Sojannata ya amsa sunan maza gaba daya. Kishin ruwanshi na shekaru talatin da biyu da kuma alluran sojan nashi yake kokarin sauke mata. Lokacin da komai ya nisa ne al'amura suka rincabe, domin ya samu abun da bai taba tsammani ba!
Rinannun idanunshi ya bude, kana ya zuro kafafunshi kasa a hankali. Ya daidaita zamanshi bakin gadon, kanshi da yake sarawa da karfi ya kama da duka hannayenshi. Wani irin bacin rai da azababben kishi ke taso mishi, a gefe daya kuma yana jin kukan da take rerawa kamar zubar ruwan zafi a kan fatarshi.