RIKON KA'KA

Page 2

by @rukyelmuaz

RIKON KAKA 

✍️Written By Rukayyat

(Rukyelmuaz)
 ***

YOTA

page 2


Tafe suke gwanin sha'awa agurinsu, amma a idon sauran muta nan dake kallon yanda tafiyar tasu ke kasan cewa kuwa. Kallo ɗaya za ka yi musu indai kai mazaunin ƙauyen ne ka san, ce wa gaskiya wannan tafiyar ba ta daɗi ba ce. 

Domin yanda kaka ke riƙe da hannun Haisu da wannan safiyar da gani ka san ta ɗauko mata wani fitinar ne.

Yanda ita ma take biye da ita kamar raƙumi da akala kawai zai baka dariya.Domin kuwa tafiya ce suke irin tafiyar gurgu da ɗan jagora.


Duk wani abu da zasu gamu dashi a hanya saita tsaya ta ƙare mishi kallo, idan taji ya burgeta kuwa saita tsaya ta ɗauka tasa a hijabinta, sannan tayi tako na gaba.


Tafiyace suke yi wacce zamu iya kiranta da yin bayin ba barin ba, Barin ba barin ba.


Ganin tafiyar ba mai ƙarewa bace yasa kaka sakar mata hannuta, ta fara tafiya ita ɗaya murya irin ta sangarta Haisu ta buɗe bakinta tayi magana da wata murya irin sangarta da ita tayi magana ta ce.


"Kaka...me yasa kika sakar min hannu???? wallahi ni ki dawo baya mu tafi tare. Ta ƙare
 maganar cikin yanayin da kaji maganar kasan cewa wannan sangarta ce.

Ba tare da Kaka ta juyo ta kalli inda take ba ta bata amsa.....

"Kina tafiya kamar wacce ƙwai ya fashemawa a ciki baxan iya wannan tafiyar taki ta ƴa'ƴan kasa ba."

Ko maciji ya haɗiya ƙwai sai yafi mu sauri da wannan tafiyar taki shekara zanyi a ti'ti..

Kaka tana kai nan a ƙarshen maganar ta tayi gaba ba tare da, ta jira jin amsar da zata fito daga bakin Haisu ba.

Haisu kuwa ganin cewa kaka ta barta baisa ta damu ba domin kuwa itama tafiya takeyi ita ɗaya hankalinta kwance yanayin garin yana mata daɗi yanda iska ke kaɗawa ta ko ina ni'imar Allah ta sauka tsalle take rungume da tarkacen shirme da take tare dasu a hijabinta rungume da kayanta.


Daga nesa da ita ta hango Bishiyar dalbejiya.

Masu abinci sun taru kowa da abinda yake saidawa hange da waige' waige ta fara kamar wacce akaba umarnin in taje gurin ta ɗauki wani abu.

Murmushi ta saki tare da rugawa da gudu ganin hakan kaɗai zai tabbatar maka cewa taga abinda take nema.

A dai"dai bishiyar ta yada zango a hankali ta fara wuce muta,nan dake gurin suna sana'a. Duka yara ne sa'anninta sai kuma wanda suka fita da shekaru amma ba wata, ta zara mai tsayi suka bata ba.


Wasu daga cikin masu saida abinci suna ganinta kallo ɗaya suka mata suka kauda kai daga gareta sai dai yara sa'aninta ne wasu suka fara magana...

"Yar larabawa....... kowa da abinda yake faɗa amma ita fa batasu take ba.

Ƙara shigewa take dai'dai gurin masu saida Gyaɗa a karkashin bishiyar., 

Wata ƴar budurwa ta hango zaune a gaban farantin Gyadarta da tasha rufi da ƙatuwar farar leda.

Budurwa ce wacce bata wuce shekaru sha biyar ba zuwa sha shidda.

Yar budurwa ce irin black beauty dinnan wanda zakaga baƙin su irin mai kyau dinnan ne.
Kallo ɗaya zaka mata kasan tabbas wannan babu muni a tare da ita Masha Allah akwai kyau dai iya nata.Zaune take a gaban....


Gyadarta, tayi sharr, gwanin sha'awa, da gudu Haisu ta isa wajen tana fadin, “Mairo, aminiyar asali!”

Wacce aka kira da Mairo, ne tayi saurin juyawa domin koda a bacci ta, tashi taji an kira ta da wannan sunan zata bayar da amsar waye.

 Cikin murna da farin ciki ta mike tsaye daga inda take zaune, ta zo wajen da Haisu take cikin murna suka fara ƴar rawa suna gir'giza kai kamar wasu sabbin hauka. 

Ƙo ƙarin taɓa kayan da Haisu tazo dasu a jikin hijabinta take. Buge mata hannu Mairo Haisu tayi tare da tacewa ke matsala ta dake kwaɗayi ya miki yawa wallahi ta ƙare maganar tana murguda ƙaramin bakinta.

Ɗan harara Mairo ta jefawa Haisu ta ce, ke akwai wanda yafi ki kwaɗayi ne muje a zauna a raba koma meye wallahi.


Kama hannunta Mairo tayi suka nufi gurin Gyadarta.

 Suna tafiya ta ce ta kalli Haisu kafin su zauna tace,  

“Ƴar larabawa, tun ɗaxun nike jiranki, amma kinqi zuwa da wuri".

”Hannun mairo Haisu ta saki, suka idasa wajan zaman su, suka zauna.


Haisu, cikin halin ta na rashin ji, tace,.

“Tun ɗazu nikeson zuwa, amma Malam Bala mai zikiri ya tsareni a gona, ni da ƴan tawaga ta".  

Tana kai nan ta turo baki yanda kasan a gaban kaka take.


Cikin ma'maki Mairo ta zaro ido, ta ce, 

“mai ki'kayi mishi da har zai tsare ki a cikin gona keda ƴan tawaga?”

Taɓe baki tayi kafin ta ba Mairo, amsa, kwashe labarin abinda ya faru tayi kaff, ta fadawa mairo.

Mairo ta ce, 

“kai ! dama ina nan, ai da munyi mishi ruwan duwatsu.”

Cikin murna da farin cikin ƙwarin guiwar ɗaukar fansa tace ma mairo, “ai ko yanxu saiya gane ya taɓa haisu, "ƴar larabawa.” 

Tana kai nan a ƙarshen maganar ta, ta fara kici ,kicin kwance kayan dake kulle a hijabinta.

 Kwance kayan tayi baki ɗaya ta fara fiddo kayan wasan da duk ta tsinta a hanya Mairo tana ganin kayan tana ce wa..

 "Yar larabawa ki ban wannan ita ko ƙara wani tsare gida take nima inason su duka amma a raba biyu Mairo cikin son ɗaukar kayan duka ta ce..

Kefa kinga ko a gida kina da wasu kuma in daddyn ki na Abuja zai,zo yana kawo miki wasu da yawa.

Haisu banza tayi mata saima ɗauko mangoron da tazo dashi gurin tayi..

Mangoro ɗaya taba mairo, itama ta ɗauki ɗaya ta fara sha.

 Sannan tace ina, Gyadata?? Inno ta ƙullo min yau ko sai naje gidan.

Cikin dariya Mairo ta buɗe ledar Gyada ta ciro wani karamin kulli ta mikawa Haisu sannan ta ce.

Yarinyar ai Inno tsoron ki takeji bazata manta ba.

Dariya sukayi, irin ta ko a jikin su ɗinnan, suna cikin dariyar ne, ....


Tukur mai chajin Waya ya zo sayen Gyada matashin ne wanda bai wuce shekara ashirin ba, sanye yake da wani shohon wandon red da wata white t-shirt. shi a dole, manyan gayun Kauye ne ya kure adaka ya kai karshen gayu.

 Tafiya yake kanshi tsaya ya nufi gurin da Mairo, da Haisu ke shan mangoro suna dariya.

Kusada farantin ledar, Gyaɗa ya durkusa ya fara ɗauka yana ci, irin ɗan ɗano, ɗinan da aka saba.

, Haisu na kallon shi cike da rainin wayo a lamarin shi don wannan abinda yake ya wuce a ce ɗan ɗano sai dai ace sata kawai ko son banza.

 Tsugunuwar da yayi, ya sake gyarawa da kyau.

   Domin shi fa, yanda, Gyaɗar yau tayi daɗi, ji yake kamar bai taba cin, Gyadar da tayi mishi daɗi kamar wannan ba.

Mairo ta kalle shi cikin fuskar da babu annuri ko wasa a cikin ta duk da kasancewar ta yarinya me karamin shekaru akan nashi ta ce...

Kai Tukur, Gyaɗar nawa za'a baka ne ka tasamin, Gyada kanaci kaida baka faɗa ta nawa za'a baka ba.

Kallonta yayi cikin rainin wayo yace amma kinsan ko ta nawa naci zan iya biya koh??? Daga haka bai sake cewa komi ba sai dai ci gaba da cin, Gyadar da yayi.

Ido suka bishi dashi domin suga iya gudun ruwan shi.


Bayan ya gama ci ne ya kalli Mairo, yace, “zaki kawo caji ne, Mairo?”

Cikin ɓacin rai tace, “dama kaga ina kai chaji ne"?

 "Ka faɗa, Gyaɗar nawa za'a baka, kazo ka tasamin kayan sana'a, kana ci babu tambaya babu neman izinin" 

Ta faɗa tana ƙarewa Tukur kallon sama da ƙasa

Wata kodaddiyar naira ashirin ya ciro a tsohon wandon dake jikin shi, ya miƙawa Mairo, “ungo, zubamin ta ashirin, sauran canjina kenan.”

Cikin bacin rai, da ya gama kashe Haisu, ta tsaya da shan mangoron dake hannunta, ta ce..

“To ai ko wacce kaci tafi ƙarfin gwangwani biyu, zaka miko wata kodaddiyar naira ashirin, kace a baka Gyada."

"Saboda ka raina muta ne ko? Bata jira abinda zaice ba taci gaba da magana.

"Saboda a gonar baban mutum ake zuwa a ɗebo Gyadar ko?”

Maganar da Haisu tayi ne ya bata ma Tukur rai, sosai kamar wannan yarinyar zata gaya mishi wannan maganar, domin yasan a kalla ya bata shekara biyar abinda yayi sama.

Mairo tace, “Haisu, gyaleshi dani,.

 "Kai Tukur, wallahi Gyadar da kaci tafi ƙarfin ta dari, sannan zaka bani naira ashirin me zanyi da ita?? Bata tsaya haka ba taci gaba da magana.


"Wai in baka ta ashirin, kace fa, to ka fara biyan kudin wacce kaci, sai ayi maganar ta nawa za'a baka.”

Tunda aka fara wannan rikicin, sauran masu kayan sana'a agun suka zura musu ido, domin sun san yau dai Tukur mai chaji ya taɓo abinda yafi karfin shi gobarar da babu wanda zai iya kashe masa ita. 

Sai kuɗin shi, in ko babu kuɗi, wannan marasa kunyar guda biyu zasu ɗebe mishi karama.

“Kinga, in bazaki bani ta dai'dai kudina ba, wallahi zan tafi. ya faɗa yana kallon Mairo dake rike da kwan'kwaso

Ni Gyadar ma yau bata dahu yanda kuka Saba dafawaba.,”

 Ya faɗa, yana kokarin maida kudin shi a aljihun tsohon wandon shi.

Mairo tace, “rodi ko icce ne ba Gyada ba. 

To wallahi saika bani kudin wacce kaci, inba hakaba sainaje har gidanku na fadawa iya mai kosai.”

Tana kai nan a maganarta ta tsaya, tana binshi da kallon banza ta rike kugu tana girki.

“Tunda bazaki bani ba , sai wani lokacin in Allah yasa nazo da kudi masu yawa,” 

ya juya ya fara tafiya.

Bakin ciki ya hana Mairo ƙara magana face kallon shi da take ya fara tafiya.

Ƙallon mangoron dake hannunta ta tsaya da lashewa.

Haisu ta wurga mishi akayi sa'a, ta sauka a ƙeyar shi, dammmmm, saita zame a bayan rigar shi. Da yake jin babu kamarta da zafin shi, ya waigo domin ganin meye haka ya bugi ƙeyar shi mai santsi haka da abun ma'maki sai ganin......

Ƙwallon mangoro a kasa, ɗago kanshi yayi da sauri ya kalli daga inda yaji jifar yazo mishi.

Haisu ce tsaye tana kallon shi ido cikin ido, ta rike kugu, hakan ya bashi tabbacin itace tayi wannan aikin, domin duk rashin kunyar Mairo a kauyen nan, bata fitina da maza.

Da hanzari ya dawo gurin da suke tsaye, yace, “wace yar iskar ce a cikin ku ta jefeni?”

Mairo tayi banza dashi.

Haisu ta ce, 

“Gani nice nan mana, tsohon mugu kazo kaci abun sana'ar mutum, zaka gudu” ji kake tauuuuuuuuu

Wani mari ya ɗauketa dashi, wanda yasa saida tayi baya ta fara taga, taga zata take sauran mangoron dake zube a kasa.

Cikin fushi ya ce, “Nafiki rashin kunya donni tawa rashin kunyar ba irin taki bace sannan ni ba irin sauran muta nan kauye bane dake tsoron in kinyi musu rashin kunya su hukunta ki.,

 "Saboda kada wannan kakar taki taxo tanama mutane koke'koke a fadar mai gari” da gidajen muta ne Idon shi ya rufe, masifa kawai yakema Haisu.

Waige-waige ta fara domin ganin da mai zata ɗauki fansa.

 Idonta ya saka akan.....saurin barin gurin tayi domin daga ganin yanda ta, tafi kasan ta samu abinda take nema.


Tukur yaci gaba da masifa, yana kokarin cire rigar domin yaga yanda ta baci, ya ce, 

“Dukan ki zanyi, Kuma inga wanda zai rama miki shegiya mai zubin yan ruwa.”Tukur ya faɗa yana idasa cire mana ita 

Bai gama idasa maganar shi ba, yaji saukar wani abu mai dumi da zafi-zafi an watsa a fuskan shi ya sauko jikin shi, dai'dai ciro rigar daga jikin shi zai fara dubawa.

Kokarin buɗe ido yayi, amma wani zafi ya shige idanun ji yayi ana fadin, 

“ke Haisu, miyar shinkafar Atika ce fa kika ɗauka! kuma yanxu tazo, ko ciniki bata fara ba.”

ihun da Tukur ya fasa ne tare da fara burgima a ƙasa,


Ihun zafi ya ke , tare da faɗin, “ku bani ruwa! don Allah, kuban ruwa! wayyo, me kika watsamin a ido?”

Rukyelmuaz 
***
RIKON KAKA