RIKON KA'KAFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

RIKON KA'KA

  • 1views
  • 8chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

Sunana Rukayya Ismail, amma an fi sanina da Rukyelmuaz. Ina sha’awar rubutu domin nishaɗi da kuma bayyana abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma. Ina son rubutan labarai da za su nishaɗantar da mai karatu, su taɓa zuciya, sannan su kasance da darussa da zaka iya koya na rayuwa. Ru...

More from @rukyelmuaz

Sample · Book 1

RIKON KAKA ✍️ Written by Rukayyat (Rukyelmuaz)***Facebook, Tiktok, Instagram, Twitter, Snapchat, @Rukyelmuaz CHAPTER 1 YOUNG TALENTED WRITER ASSOCIATION (YOTA) BATSARI LOCAL GOVERNMENT Da sanyin safiyar ranar asabar gari yayi shiru iska mai daɗi tana kaɗawa haɗe da sanyi mai shiga jiki a hankali. Daga yanayin garin kaɗai ya isa ya tabbatar maka da cewa wannan lokacin damuna ne duk da kasancewar goma na safe yayi amma ka ɗauka karfe takwas din safiya ne.Gida ne irin ginin kauye jar ƙasa daga waje amma daga ciki kallo ɗaya zaka masa kasan cewa ko a ƙauyen wannan gidan bana ya ku bayi ba ne. Don daga tsarin cikin gidan ka san cewa, Alhamdulillah masu rayuwa a cikin shi tabbas ra'ayin zaman ƙauyen su ka yi.Dattijuwa ce da, ba ta wuce shekara saba'in ba a duniya ke kai kawo da gani kasan irin jikinsu na mutan da ne. Ga kuma hutu daya samu a jikinta. Kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin kwanciyar hankali da wadatar rayuwa domin kai komo take ba tare da gazawa ko nauyin jiki irin na mutan zamanin nan namu ba.Ƙarar gudu da hayaniyar yara ta karaɗe gidan tun daga soro kafin su iso inda take tsaye yanda kasan sunayi ne a gabanta alhali ko cikin gidan ba su kai ga shigowa ba.Muryoyin su ta karaɗe ko ina a cikin gidan da hayaniya.Fitowar ta kitchen yayi daidai da isowar su gabanta, ta kalle su cikin mamaki kafin ta ce,“Lafiya dai"? "Me ya faru kuke wannan ihu haka kuna kirana tun daga soro ba za ku bari ku ƙaraso ba lafiya?” Suka tsaya suna maida numfashi suna kallon ta. Haki kawai suke saboda tsananin gudun da sukayi, bayan ɗan lokaci ɗaya daga cikinsu ya ce cikin firgici.“Kaka Malam Bala mai zikiri ya kama Haisu. ya hana ta dawowa gida tana can a cikin gona yaki bari ta taho gida".Fuskar kaka Hasatu ta canza cikin rashin jin dadin abinda suka faɗa ta ce."Me haisu ta yi masa"?.Kallon juna sukayi kafin wani ya amsa ma ta abinda takeson ji."Wai saboda Haisu ta hau bishiya ta katso mana mangoro shine ya shigo gonar yasa aka tsareta ya rike ta yaki bari ta taho gida .”Ya karasa faɗar maganar yana kallon sauran yaran dake bayan shi suma kai suka ɗaga a tare alamar gaskiya ya faɗa.Girgiza kai tayi cikin damuwa da tashin hankali domin tunanin ta ɗaya kar a sabauta mata yar tsoka ɗaya amiya yar gudaliyarta.“To, ku dakata. Bari in saka mayafi, mu je mu ji abin da ya faru".Kaka ta faɗa tareda faɗawa cikin ɗakin ta da yayi tsaf dashi komi zaune yake a inda ya dace kamar ba ɗakin dattijuwa ba.Ɗauko mayafinta, tayi ta yafa a kanta sannan ta fito ganin ta fito sanye da mayafi ne yasa yaran duka suka juya da gudu suma bayan su tabi domin zuwa ta ganema idon ta abinda ke faruwa.Ba daɗewa suka isa gonar inda korayen, ciyawu da sauran anfanin gona sukayi gore sharr alamar damuna tayi albarka kunya suka fara t...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters8
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play