SHI SO DABAN YAKE

Babi na biyu:’Ka’ka’kara- ‘ka’ka

by @dijensy


[Ƙaƙaƙara ƙaƙa]



2



  Yau ta ke jajibere azumi mai talatin ne aka kaishi Umma suna ta aikace aikace bayan shan ruwa Jidda na ɗaki ta sanƙame tun ɗazu wuni tayi a kasuwa da Anty baby ta matsa mata sai ta bita takalmi zata siyowa Umma ta bata sautu sai kayan cefane cake don ta iya duk kayan soye soye fulawa har aiki ake kawo mata Jiddan ta kafe sai ta bita ga azumi a bakinta tun a kasuwa ta gama laushi harda kuka ta sawa Anty baby ta ji tausayinta ta baro kasuwar ba ma ta gama siyayyar ba tunda ta sha ruwa ta baje a ɗaki Sallamar ya ibrahim suka tsinkayo Umma fuskarta ɗauke da murmushi ta fito daga kitchen tana ajje kwanan da ta yanka kabewa "Ibrahim kune haka da daddarennan ai mu har mun fidda rai na ce bazaku zo gida sallah ba ina Sadiq ɗin?" Mumurmushi yayi yace "Yana ƙofar gida".

  

   Ɗakinsu ya nufa da yake daga shigowa ya ajje akwatin kayansu ƙofar ɗakin kafin Anty baby ta ɗakko mukullin don ita ke ajje musu sabida gyara ɗakin idan Umma ta ajje zuwa jidda take ta ɗauki wannan ta ɗauki wancen.Durƙusawa yayi ya gaishe da Umma tana amsawa Anty ta ɗakko mukullin ta kawo mishi suna gaisawa Sadiq ya shigo a ido ma sai ka rantse shine babba ya fishi girma da komai muryoyinsu ya sa ta tashi tana jin muryarsu ta tashi tana leƙowa uffan bata ce musu ba kanta a sama gashinta buya buya don yau ta tsife bayan shan ruwa ta tuge hular zaka rantse wata aljana ce  Anty Baby ta bita da kallo suka ga ta hau dariya tana rufe baki duka suka bita da kallo suma ga fitilar ƙwan parlourn da ta hasketa ta murtuke fuska tana koma ɗakin ta turo baki "Baki iya gaisuwa ba ko jidda ?"


   "Ba dariya suke min ba?"Ta faɗa ta turo baki ta kalli kanta a mudubi tana ɗaukan ribbon ɗinta da ƙyar ta iya tufkeshi gashinta akwai yawa da cika yana da taushi kawai rashin gyara ne yasa Umma take korata kitso wataran kuma Anty baby tayi mata sai dai suna kwashewa duk sanda zata mata kitso sai ta ta sata magana bazata zauna waje ɗaya ba ko kuma ta sa kuka tace da zafi shiyasa sai ra ga dama take mata.Sai da ta ga sun fara soya kaza ta fito ƙwaɗayi ba tayin aiki sai dai a sammata."Anty baby zaki min wanke kai da daddaren?kin ga gobe masallaci zan bi Baba".


  "Ni in miki wankin kai kice na sa miki sabulu a hanci ki yi eidi da tsatstsaman gashinki".Jidda ta ƙwaɓe fuska kamar zatayi kuka tana zura hannu zata sake ɗaukan cinyar kaza Umma ta ƙwaɗe hannun ta kyalkyale da dariya "Umma kin gano wayona ,Anty baby zan aske kan kowa ya huta".


"Mai ruwan wani ni sauken hannunki daga kan cinya ba ga tayin aiki ba sai ƙara min nauyi son jiki kamar mage".Anty baby ta faɗa tana matsar da cinyarta da jidda ta ɗora mata hannaye ta turo baki tana tashi kai tsaye ɗakinsu Ya ibrahim ta leƙa ta hangi ya miƙar da shaddar shi da iron a jone da socket ta tsaya kallar sabuwar blue shaddar ta ji motsin sa a banɗaki hakan ya tabbatar mata yana ciki ta kunna socket ɗin tana ɗorawa kan hannun shaddar ta fara gogewa tana murmushi ganin tana miƙewa sosai wayarsa ta ga tayi haske daga gefe sai hankalinta ya koma kai tana duba notification saƙone na kafar sada zumunta ta whatapp  "Masoyi idan ka ga saƙona ka kira ni "Ta karanta ta ƙunshe dariyarta tana ajjewa ta juyo kan kayan ido ta waro ganin ysna hayaƙi ta ɗsuke iron ɗin ta ɗauke ta ga ya ƙwashe gabaɗaya wajen ta gwalalo ido tana saurin kashe socket ɗin ta tashi ta fice tana shigewa ɗaki ya ibrahim na fitowa ya tsaya da mamaki yana kallo shi dai ya san bai bar shi akai ba kuma bai kunna shi ba ya kashw sanda zai je banɗakin dole wani ya shigo ya masa taali fita yayi su Abdallah ya samu yana tuhumarsi suka rantse masa ba su bane "Jidda!"Ya ƙwala kiranta cikinta ya ɗuru ruwa ta ƙwanta baccin ƙarya "Taali tayi ko".Umma ta tambaya ya faɗa mata kaya ta ƙona masa.


 "Fito dan gidanku!ka mammareta wallahi"Cewar Umma dai dai lokacin  Baba ya shigo"Wa za a mara?"Ya tambaya yana kallon ya Ibrahim da ya haɗe rai yana komawa ɗaki "Kai idan ance ka mareta sai ka maretan yar ƙaramar yarinya?sakarci kawai toh wallahi bazan lamincewa cin zali ba bakina alaikum daga dawowarku zaku fara cin zalin yarinya ƙarama".Baba ya hau faɗa tana ɗaki tana hamdala ta na ƙunshe dariyarta ba wanda ya sake cewa komai.Ibrahim kuwa sai haƙura yayi yana ji yana gani da tsohon kaya yaje eidi don bai karɓo ɗaya ɗinkin ba ,kala ɗai ɗai har biyar ta ci sallah dashi su Abdallah yan maza uku na ukun ma Umma ta musu.


              

                    ****


  Dare ,rana ,ƙwanaki  shekaru sun sake shuɗewa Jidda ta kammala graduation ɗin matakin sakandare a yanzu hali ba abinda ya sauya gashi ta sake girma ta zama ƙatuwar budurwa wani irin girman jiki tsaho da kauri duk ta haɗa ga kyawun sura tabarakallah ,Ya ibrahim tuni ya juya masters yana China a yayinda ya Sadiq ya samu aiki a Lagos maaikatar ɗangote ,baba ya sake samun cigaba a kasuwancinsa ya buɗe katafaran store sosai sun wadata cigaba ya zo musu ya gyara musu gidansu komai sabo haka aka sake shi Jidda ɗakinta ya ƙawata mata da gadonta da wardrobe ta fi kowa morewa wani ji da kanta take na yan matanci shekara sha baƙwai ɗinta a aka take jinta kama daga shigarta zuwa kayan anfani bata sa na banza Umma har ta gaji da magana ta bi rayuwa a sannu taƙi ji ranar graduation Baba ya fello mata sabuwar iphone 13 haka zata ƙule ɗaki ta yi ta danne danne ba aikin fari balle na baƙi.Yau ma tana ɗaki jin tsaiwar motar Baba yasa ta fitowa ta iskesa a filin kewayen gidan tana mishi sannu da zuwa ya amsa "Baba ina tuni".Ta faɗa ya kalleta "Mai fa?"


   "Birthday ɗina saura kwana biyar na faɗa ma Anty baby zata min cake".


  "Ohh haka uwar masu gida gwara da kika sake tuna min tohm duka nawane ko bazaki gayyato ƙawayen naki ba?"Ya tambaya tayi dariya "Ai an daina irin wannan yanzu dai baba kuɗin cake ɗin ma yayi".Ta furta ya jinjina kai ya tambaya nawane tace "Dubu dari har na small chops".


  Anty ta girgiza kai tana tsinkayo muryarta duka duka dubu arbain ta mata lissafi shine zata chajesa wannan kuɗin yace "Tohm ba damuwa zan sa maki ɗari da hamsin a teens account naki har da na gift ko Allah wa rayuwa albarka".Ta jinjina kai "Ameen babana nagode"Ta yi gudu ta shiga ɗaki tana ɗaukan wayarta ta na shiga chat da suke da ƙawarta Malika itace aminiyarta a aji tare sukai makarantar boko tasu ta zo ɗaya har ma ta fi Jidda buɗewar ido da son gayu da abinda ya shafi kyalkyalin duniya.Kiranta Malikan tayi tana tambayarta nawa ya bata ta faɗa mata dariya malika tayi "Ke har yanzu duhun kai na damunki me 150k zatayi keda zaki karɓi 250k na faɗa maki abinda zaki kin ƙi ki zauna wata ɗari da hamsin ɗinki bazata kama miki ko ina ba ki sa kb show a harkarnan in ma kunya kike ji ni sai na faɗa masa wallahi komai sai ya miki yana mugun sonki kinki sakin jiki dashi ko kiransa ba amsawa kike ba".Shiru tayi Jidda kamar mai nazari ita kb show sam ba kwanta mata yayi ba.


 "Na kirashi?"Malika ta tambaya Jidda tace"Nidai tsoro nake ji".


  "Ba wani fa abin tsoro kawai kice a gidanku hoto zamuje".Malika ta cigaba da tsara mata tuni ta amince  Malika na gama waya da ita ta kira Kb tana faɗa masa Kb yayan ƙawarta ne ta islamiyya kuma maƙobtansu ne tun sanda Jidda ta taɓa zuwa gidansu wajen Malika ranar tana gidansu kb ɗin shikenan ya kafe yana son Jidda har ta bashi number ta sanda aka saya mata waya amma Jidda ta ƙi bashi dama.Kb kuwa yana ji yayi amanna tuni ya turawa wata event planner kuɗi akan ta shirya komai na party Malika ta sa ta kira ta mashi godiya ya nuna mata ba komai hasali ma bai so aka faɗa mata ba ya fi so ya zama a bazata.Jidda tana ta ƙirga ranaku a kuɗin Baba ta haɗa da ragowar kuɗin hannunta ta siyo gown mai kyau ranar da takalmi ranar kawai ta ke jira kamar yadda suka shirya tayi ƙarya tace hoto zasu je Umma ta faɗa mata su dawo da wuri kayan sawar ma bata saka daga gida ba ta tafi dasu titi ta fita a fakaice ta shige motar kb da ya zo ɗaukanta gabanta faɗuwa yake amma tana son cika burinta daga shi sai ita a motar yana kallonta wani irin mayataccen kallo yake binta dashi wayarsa ya ciro ya ɗora mata a cinyarta har hannunsa na taɓata ta ɗan kallesa ta basar "Ki min hoton kyakyawar fuskarki".Ya faɗa cikin wata sigar magana ta kallesa banbarakwai "Ai bansan password ɗin ba".


  "Your birthday".Ta kallesa irin da mamaki y jinjina mata kai yana tuƙin motar hankali kwance 'kayataccen gini ya kawo ta bata da masaniyar ko ina ne ta ga sun shiga ciki tana kallo sai a lokacin ta ga a jikin ginin sunan hotel ɗin ta kallesa ya saurin buɗe ƙofar yana fitowa ya zagaya ya buɗe mata giwoyinta a sanyaye ta ks kallonsa ta miƙa masa wayarsa da iya uku ta ɗauka  wayarta ta ciro a purse ɗinta "Malika tana ciki kada ki wani damu".Ya furta yana rufo ƙofar ta bi sa a baya suka shiga ciki baba da ya ke cikin tashi motar ya girgiza kai sao dai mai kama da Jiddansa ce ya faɗa amma kuma kayan jikinta sunyi kama da nata.Fitowarsa kenan daga wajen receptionist ya sauki wani abokinsa daga sokoto yazo halartar wani taro  Baban ya raka shi hotel ɗin yayi booking.Umma ya kira yana tambayarta Jidda dukda ma zuciyarsa ta karkata ba ita bace "Ta fita hoto zasi wai da kawarta a gidan hoto ta dawo".Umman ta faɗa Baba ya sauke wayar a kunnensa "Baka ji?"


 "Ina zuwa"Ya faɗa yana katse kiran ya bude murfin motar tuni sun shiga ciki receptionist ya tsaya ta ga ya karɓi wani kati yana kiranta ta bi sa a sanyaye ba laka a dai dai ƙofar wani ɗaki ya tsaya yana kara kara katin ya buɗe ƙofar yana matsawa baya ya ce mata ta shuga duhu ta gani ɗakin ta kallesa "Its surprise".Takawa tayi tana shiga ya biyota a baya yana fara mata video ta ga ya haske ya karaɗe ɗakin wani baloons jajaye da kayan kyalkyali an rubuta "Happy birthday Jidda ta ɗayan gefen cake ne ƙarami Jidda na kallon ɗakin "Malikan fa"Ta faɗa ya murmusa "Ni kamar baki sanni ba zata zo a yanzu ina so muyi celebrating mu kaɗai.Jidda fuskarta bata nuna amincewa ba ta ɓata rai tana laluba wayarta ta shiga duba number Malika ta ji ya karɓe wayar"Don dai rana ɗaya ki tsaya muyi magana mana an tama faɗa maki ke me kyau ce kina ganin irin kyan da Alla ya miki?komai ya ji a jikinki Jidda"Kb ya faɗa yana matsowa daf da ita tana ja baya a tsorace ta ji ta ƙure bayanta gado ne hannu ɗaya ya sa a ƙirjinta ta faɗa kai Jidda hankalinta ya dawo jikinta ta fara fahimtar ko me yake nufi da ita ta mirgina da sauri tana yunkurin tashi ya yi kanta har rawa jikinsa yake "Ko da romance ne don girman Allah jidda".A rikice yake maganar tana kallon gaban wandonsa ya tasa ta kurma ihu tana kurari tana ja baya ya shiga rike mata hannu zai toshe mata baki yana lalubar jikinta tana kurma ihu haɗi da turesa da iya ƙarfinta tana kiran baba da Umma aka turo ƙofar suka kallo ƙofar a firgice take kallon baba da waitress da ya tursasa su zo su buɗe masa da rikici don sun tsaya faɗa masa hakan ba mai yiwuwa bane sai da ya fara zagesu ya nuna musu da gaske yake kuma 'yar sa ko sha takwas batayi ba hasalima ca yayi sato ta akai sannan suka haƙura suka buɗe kb yayi tsurutsuru kan gadon Jidda idanunta sun kasa gasgatawa baba take gani....