Babi na uku :Tariya
by @dijensy
3
Kai kawai Jidda ta shiga girgizawa tana saukowa daga kan gadon kan gwiwoyinta "Baba wallahi ba abinda na bari yayi bai komai ba wallahi bansan nan zamu zo ba".
"Abinda zaki saka min dashi kenan Jidda?"Ya faɗa tana girgiza kai wannan baban da ta sani take neman gani a fuskarsa ta nema ta rasa baba ɗinta mai sauƙin kai mai ji da ita "Baba ...."
Kamar da ƙiftawar ido ta ga yayo kanta ya kama hannunta suna ficewa daga hotel ɗin a fusace har sai da suka ƙarasa mota ya daka mata tsawa "Shiga ciki!" jikinta na rawa ta faɗa motar gidan baya ta shiga kuka kawai take.Umma da ke ɗaki suna kallo a parlour suka ji shigowarsu "Baba dan girman Allah kayi haƙuri"Suka fara ji sama sama Anty baby ta tashi tsaye tana kallon Umma "Jidda ce?"
"Ki shigo da ƙafarki mai kike tsoro?"Ya tsawata da sauri Umma ta tashi ta na fita daga parlourn suka ga Jidda na turjewa Baba ya cikata sandar goge -goge ya ɗauka yana jinta shafal ya kai mata duka da ita ta karye tana riƙe hannu ya cakumota wani irin duka yake kai mata da marika lafiyayyu "Ni zaki ja ma abin kunya?duk irin gatan da na miki na tabbatar baki rasa komai ba kike fita da maza ?Jidda hotel fa har kinsan ki bi namiji ya kama maki ɗaki?"Baba yake faɗa yana kai mata ƙafa ya shiga takata Umma ta rike baki tana "Innalillahi wainna ilaihi rajiun"
"Gata nan bata da amfani ina ma anyi ɓarinki wallahi nayi danasani yara na maza sun isheni ashe na ɗora maki son duniya da abinda zaki saka mani 'yar iska mara mutunci"Anty baby ta fashe da kuka tana faɗowa wajen ta shiga roƙon baba kar ya tsinewa Jidda "Ki faɗawa uwarki mai kika yi ,ɗauka yarinyarnan Amina ku je asibiti ayi gwaji ko ta kwaso ƙanjamau ko ciki yanzu yanzu ku tafi idan tana da juna biyu kada ta sake shigo min gida".Hawaye ya silalowa Umma tana kallon Jidda baki ya fashe fiska tayi himm ta nufeta "Ni kika ci amana jidda daga fita hoto karya kikai?"Umma ta faɗa ta na kallonta hawaye na zuba daga idanunta "Zanyi bayani Umma wlh bai taɓani ba ba a taɓa min komai ba tsautsayi ne kuma nayi nadama wayyo Ummana baba dan girman Allah kayi haƙuri".
Tana tsugune ta ci kukanta anty baby ma ta tashi ta shige ɗaki Umma ta ɗakko hijabi tana cilla mata don mayafinta ya fita a hayyacinsa daman siriri ne "Tashi mu tafi asibiti".Tana gunjin kuka ta miƙe Umma ta ɗakko jaka ta tasa ƙeyarta sai asibiti wata likita ta samu ta mata bayani a dubata ta fahimci ko me Umma take nufi suka shiga ciki da ita tana sawa ta ƙwanta hawaye na ƙwaranya daga idanunta likitan ta sa safa a hannu tana dubata ta ce ta sauke ƙafafunta Jidda jikinta na rawa suka fito ta kira Umma.
"Ba abinda ya sameta ƙalau yarinyarki take bata san namiji ba".Likitar ta faɗa.
"Ayi mata gwajin juna biyu likita har da na HIV".Umman ta faɗa dr ta girgiza kai "Baki yarda ba ?ki ɗau abin da sauƙi koma mene Allah ya taƙaita janta zaki a jiki ta miki bayani da kyau amma ba abin da ya sameta budurcinta na nan idan ma akwai ɗinki da yara ake musu na zamani muna ganewa ba abinda ya sameta".
Shiru Umma tayi tana ɗaga hannu ta godewa Allah "Sabida mahaifinta dan Allah ayi mata gwajin ya tabbatar ta jinjina kai tana tashi ta kira Jidda ɗakin gwaji bayan wasu mintina aka basu sakamako ta tasa ƙeyarta suka koma gida.Baba ta shiga ɗaki ta samu ta bashi hannu da hannu ta koma gefe yana buɗewa ya karanta Umma ta faɗa masa abin da likitar ta faɗa yana ganin sakamakon gwajin ya nuna ba komai.Miƙa mata yayi ya tashi ya fice ta bisa da kallo ɗakin Jidda ta shiga tana kallonta tana duba ciwukan daya ji mata a baya da kafaɗata ta ɗago ta kalli Umman hawaye ya silalo mata ta shagwaɓe fuska "Umma kiyi haƙuri kada ki fushi dani kar Allah yayi fushi dani".Tausayi ya kamata ko rankwashi bai taɓa haɗata da baban nata ba sai yau "Sai kin faɗan gaskiya tukun".Umma ta zauna Jidda ta jinjina kai da sauri tana fara bata labarin duk yadda akai Umman ta gamsu amma ta san baba ba lallai ya saurareta ba daɗinta ɗaya shine Jidda wani abu bai sameta ba.Wunin ranar kamar anyi mutuwa gidan shiru su Abdallah ma da suka dawo daga islamiya basu ga ɗuriyarta ba.Bayan ƙwana biyu da faruwar abun ibrahim ya kira Umma yake tambayarta ko lafiya Baba ya kirasa yana bashi haƙuri yana nuna musu banbanci akan Jidda su yafe masa.Umma ta faɗa masa duk abinda ya faru ya girgiza sosai yace a haɗasu da ita a waya da Umma taje ta ƙi yarda ta karɓa don duk kunyar kowa take ji ibrahim yace a rabu da ita.Sati guda da faruwar hakan Malika har sannan bata zo ba ta janye jiki kamar ruwa ya ɗauke Umma ta ƙwace wayar Jiddan da daddare dawowar baba ya kira Umma ɗaki.
"Nayi mata miji jibi za a ɗaura mata aure".Umma ta kallesa "Aure fa kace shekarar jidda nawa?"
"Idan kin ga ba ai auren ba tohm bana raye shine kaɗai gata na ƙarshe da zanyi mata a rayuwa ragowar ruwanta ne ta zauna ruwanta ne ta ƙi nidai na gama nawa".
Nisawa tayi Umma tace "Ɗan gidan waye?"
"Ba ɗan kowa bane Limamin masallacinmu nayi wa magana ina nemawa 'yata miji ya faɗa min yasan wani ɗalibinsa zai masa magana dayaka ɗan albarka ne shi bai musa ba ya amince da aurenta sadaki kaɗai zan karɓa bana son komai nasa ba kuma da abinda zan kaita daga ita sai kayan jikinta."Shiru Umma tayi ta rasa ta cewa tashi tayi tana fita daga ɗakin ,bata iya faɗawa kowa ba har ana e gobe tukun kannensa mata suka kira suna faɗin sun ji labarin ɗaurin auren da zaayi na Jidda Umma ta faɗawa Anty baby kowa mamaki yake har Jidda ma ta samu labari ranar ɗaurin auren ne suka zo iya su biyu ƙannen Baban Anty Mairo da Anty Zaliha suka mata faɗan da zasu mata kuma a ranar ya ce za a kaita Anty Baby dai ta haɗa mata kayan sawarta da abubuwan da zata iya buƙata auren da yazo a gaggauce ko shiryata ba ai ba ta siyo mata yan kayayyakin gyara a ranar ta sa mata a akwati shine ake ta daru da ita baba ya sake zaneta kafin a tattara a kaita gidan mijinta.......
_Cigaba_
'Karfe goma da 'yan mintina ya shigo gidan yafi minti talatin a 'kofar gidan rashin sanin ta ina zai fara ya saka ya tsaya a waje,abu ne da bai taɓa tsammani ba rana ɗaya kuma a lokaci guda ace aure ya zo masa haka ba tare da shiri ba?bai taɓa sanyata a idanunsa ba bai san wace iri bace mafi abin tsoro garesa shin zata karɓesa hannu biyu?shi ba ɗan kowa bane bai tara komai ba .Sallama yayi bayan ya shigo tsakar gida ɗakin farko da ke da veranda ne inda take nan Anty Rukayya tace zata gyara mata a maganar da sukai da ita jiyan.Wucewa yayi ya nufi parlourn Antyn tsakar gidan ba haske dinɗim ɗakin ne da fitilar sola 'kwaya ɗaya yake kunne ya sake yin sallama anty rukayya ta amsa da fara'a a fuskarta "Ango kasha kamshi"Ta tsokanesa bai san me zai ce mata ba yayi kokarin 'kalo murmushi dukda dama shi mai fara'ne amma yanzu yana cikin wani hali ya zauna daga wajen farkon ɗakin tana miƙa masa abin sallah dukda ba kalle ya shinfida ba "Tun ɗazu nake sa ranka".Anty Ruƙayya ta faɗa.
"Na tsaya na karɓi abu a hanya".
"Allah sarki ga can amarya a ɗakinta tun d'azu suka kawota har sun tafi".
Shiru yayi bai ce komai ba kansa sunkuye "Su shafiha sun yi bacci?"Ya tambaya ya rasa me zai ce ta amsa da eh ya jinjina kai "Mungode Anty Allah ya biyaki"Ya furta .
"Godiyar me kuma Hassan ka jika da wani abu,idan tana buƙatar wani abu ka min magana dan Allah kada ka dinga shiru ɗinnan da ka saba sannan abu ɗaya ne daman zan faɗa maka gameda shawara kuma nasan daman ka gaji hakan haƙuri kana dashi ka 'kara a Kai Allah ya albarkaci rayuwar aurenku ameen".
"Ameen nagode".Ya faɗa yana tashi leda baƙa guda biyu da ya 'boye daga gefe ya ɗauki daya yana ajje mata daga gefenta yace ta bawa yara sannan ya fita da ɗayar a hannunsa ya mata sai da safe "Baka gajiya da ɗawainiya mungode"Ta furta ya fice tuni tsaye yayi a bakin ƙofar ɗakin nasu yana 'kwankwasawa a hankula ya jira tsahon minti ɗaya ba a buɗe ba ya murɗa marƙin ƙofar yana turawa ya shiga da sallama a saman laɓɓansa fitilar da anty ruƙayya ta ajje mata a ɗakin ya kalla daga gefen gadon 'karamin gadon da ya kasance na anty Rukayyan ko ina an gyara shi tsaf komin rashin kyawun kayan ciki hakan bai hana fito da kimtsa ɗakin ba kama daga labile da wardrobe din me kofa biyu jingine a bangon ta kuma kunna musu turaren wuta a ɗakin yana bada daddaɗan 'kamshi.Inda Jidda take ya kalla tana zaune kan gadon ta haɗe gwiwa ta kifa fuska kan gwiwoyinta window ɗin dakin a buɗe take iskar kewayen gidan na ɗan shigowa ya maida ƙofar ya rufeta ya saka sakata sai a sannan Jidda ta ɗago da kanta.
Dijensy