MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 9

by @maimunabala209

MATAR GIDA 009



SHUUKRAN/022





P9




Ɗalha ne zaune cikin kantin ɗin kamfani daga gefin sa Muhsin ne kallo ɗaya za ka yi wa Ɗalha ka fahimci yana cikin damuwa sosai babban abinda ya fi damunsa shi ne maganar Ammi ko kaɗan baya son ɓacin ranta,a hankali Muhsin ya ajiye cokalin hannunsa bayan ya fahimci Ɗalha bai ko taɓa abincin gaban sa ba,lokacin karfe ɗaya ne na rana Muhsin ya mayar da dubansa ga Ɗalha ya ce ''ka daure ka ci abinci insha Allah za'a ganta,babu abinda zai same ta,ta yi fushi ne kawai amma with time zata baiyana kanta da yardar Allah,babu mamaki tana gidan wani dangi ko gefin mahaifinta ko mahaifiyarta'' Muhsin ya yi shiru yana ƙarewa Ɗalha kallo,ɓoyayyar ajiyar zuciya Ɗalha ya sauke kafin ya ce ''Allah yasa'' shiru ya yi kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce ''babban abinda ya fi damuna maganar da Ammi ta yi min ɗazu kasan fushin Ammi babu kyau akan Amirah zata iya daina min magana l know her vey well''Muhsin ya yi murmushi kafin ya ce ''ka yi kuskure,sanin kanka ne Ammi tana mutuƙar son Amirah,kawai saboda zaka ƙara aure sai ka sallame baiwar Allah wai kazantarta ya dameka''Muhsin ya kare magana tare da daukan cokalin gabansa ya cigaba da cin abincin sa bayan wasu ƴan sakkani ya sake kallon Ɗalha yaga har sannan bai fara cin abinci ba tea ɗin da ya sa a kawo masa ma bai ko taɓa ba,hakan yasa Muhsin faɗin ''ka daure ka ci abinci ko kaɗan ne because you need it'' jiki babu kwari Ɗalha ya dauki glass cup dake cike da ruwa ya sha ruwan cup ɗin kusan rabi kafin ya ajeyi kofin, murya can ƙasa ya ce ''ka ce ta dauki annual leave?" Muhsin ya ce ''eh haka abokiyar aikinta ta faɗa min'' Ɗalha ya ce ''annual leave is 31 working days kusan sati shidda kenan'' Muhsin ya ce ''eh haka ne'' Ɗalha ya ajeyi cokalin hannunsa kafin ya ce ''kana ganin zata iya dawowa kafin nan'' wayancewa Muhsin ya yi kafin ya ce ''l don't know but l hope da yardar Allah zata dawo kafin wannan lokacin'' murya can ƙasa Ɗalha ya ce ''Allah ya sa'' Muhsin ya masa masa da ameen,wayar Ɗalha ne ya fara ƙara alamar shigar kira,a hankali ya kai hannu ya dauki wayar ganin me kiran yasa ya ja tsaki ya aje wayar ba tare da ya amsa kiran ba,Muhsin da ke lura da shi ya jefa masa tambaya ya ce ''wa ke kira?" Ɗalha ya yi shiru kawai yana shan tea kamar bazai ce komai ba sai kuma ya ce ''Unaisa ce'' cike da mamaki Muhsin ya ce ''me yasa baka ɗaga ba tun safe fa take kiran ka'' Ɗalha ya aje kofin shayi da ke hannusa ba tare da kallon Muhsin ba ya ce ''ƙyaleta na lura yarinyar bata da hanklai'' kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce ''ta kirani ɗaxu bayan ka tafi office ɗinsu Amirah'' ya sake yin shiru kamar yana nazarin wani abu kafin ya ce ''na yima yarinyar bayanin halin da nake ciki kawai sai cewa ta yi ni na janyuwa kaina l should send her 100k ta ga wani food wormer tana son siya'' cikin yanayi na ɗan ɓacin rai Ɗalha ya ce ''can you imagine'' ya yi magana yana kafe Muhsin da ido Muhsin bai san sanda dariya ya kwabci masa ba sai da ya yi me isarsa kafin ya ce ''tun ba yau ba na fahimci masoyiyar taka akwai rawar kai na faɗa maka amma ka nuna min ƙuruciya ke damunta and with time zata dena'' Muhsin ya gyara zama tare da kankare murya,fuskarsa babu alamar wasa ya ce ''ina ganin with time zata dena'' sai kuma ya fashi da dariya tsabar ɓacin rai Ɗalha ya yi shiru kawai bai ce masa komai ba ya rinƙa tura shinkafa dafa duka a baki da yaji kayan haɗi ba dan yana jin daɗin abincin ba








Karfe biyar da rabi Ɗalha ne da yaransa zaune cikin parlourn Husnah,tun sanda Husnah ta fara magana Ɗalha ke kallon ta kamar yau ya fara saninta magana take kan yadda ta yi ta kiran mutane daga dangin Ammi har zuwa ƴan uwan Amirah amma duk wanda ta kira bashi da labarin inda Amirah take har ƴan uwan Abba duk ta kira,shiru Husnah ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta ce ''ina ganin ta yi fushi ne'' Ɗalha dai bai ce komai kawai ya mayar da dubansa kan tv parlour ganin ba shi da niyya magana yasa Husnah ƙara ƙaryar da murya ta ce ''dazu bayan na idar da sallar la'asar Captain(mijinta) ya kirani ya ke sanar min da rasuwar ɗan uwansa Al-ameen ƙaninsa wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya a can ƙasar Niger,insha Allahu ni da yara zamu je Niger har ya siya mana ticket karfe goma jirgin mu zai tashi'' Ɗalha da hankalin sa ya gama tashi ya ce ''subhanallah Allah ya gafarta masa yasa ya huta'' Husnah ta ce ameen kafin ta daura da ''ka sami wani labari ne kan Amirha?" ɗage kafaɗu Ɗalha ya yi kafin ya ce ''har yanzu babu labari'' Husnah ta ce ''insha Allah za'a gano inda take'' Ɗalha ya yi shiru bai ce komai ba,Husnah ta fahimci ɗan uwa ta na cikin damuwa hakan yasa ta shiga basa hakuri tare da ƙara masa kwarin gwiwa cewar insha Allah za'a gano inda Amirah take shi dai jin ta kawai yake amma bayan damuwar rashin ganin Amirah maganar rasuwar ƙanin mijin Husnah ya ƙara sa shi cikin damuwa,saboda ya so ya zubawa Husnah yaran ne gaba ɗaya kafin Amirah ta dawo amma sai gashi itama ma Husnah zata yi tafiya barin ƙasar ma zata yi gaba ɗaya,haka jiki babu kwari ya wuce da yaran gida bayan tafiyar su gida zama ya yi cikin parlour yana maida numfashi,idanunsa rufe sosai ya gaji yau a office saboda tun dawowarsu daga cantin shi da Muhsin ogansu ya sa su aiki,ganin lokacin tashin yaran a makaranta ya yi ne yasa ya cewa Muhsin zai je daukan yara,gidan ko ina datti duk sun baxa kayan wasan su ta ko ina,ita dai Fauziyya tana kwance ƙafarsa jikinta da sauki sosai babu zafi amma har sannan bata da kuzari,Muryar Suhail ne yasa Ɗalha buɗe ido inda ya jefo masa tambaya ya ce ''Dady yau baza mu ci abinci bane?" Ɗalha ya yi masa banza kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce ''hutawa nake Suhail anjima zan tashi na dafa maku'' Suhail ya kafe babansa da ido can ya ce ''me yasa ka gaji? aikin me ka yi? yaushi Mumy zata dawo?"Ɗalha ya yi shiru bai ce masa komai ba Suhail ya daura da ''me zaka dafa mana?" nan ma Ɗalha bai amsa sa ba shi kuwa Suhail tsaye ya yi yana jiran amsar tambayoyinsa  can ya ce ''Dady kar ka sake dafa mana indomie ba ka iya ba,na fi son na Mumy,Mumy tana sa mana kifi da nama kai kuma kasa mana su carrot ni dai bana so kar ka sake sa mana?" a hankali Ɗalha ya gyara zaman sa tare da gyarawa Fauziyya kwanciya ya buɗe baki zai yi magana kenan Afef da Rayyan sun shigo parlour da gudu inda Rayyan ke bin Afef da gudun gaske Afef na kuka yana kiran Dady,da wani irin sauri Afef ya ɓoya bayan Ɗalha yana maida numfashi shi kuwa Rayyan tsaye ya yi yana wani huci a dole shi me karfi ya ce ''in na kama ka sai na maka dukan tsiya'' cike da mamaki Ɗalha ke kallon Rayyan duk cikin yaran babu marar tsoro kaman Rayyan har Ɗalha Rayyan bayan tsoron sa,Afef ya girme Rayyan amma haka Rayyan zai dage yama Afef dukan gaske sam baya barin ta kwana cikin ɗaga murya Ɗalha ya ce ''kai zo nan'' fuska haɗe Rayyan ya tako har inda Ɗalha ke zaune ya rusuna yana ɓata fuska Ɗalha ya ce ''me yasa baka da kunya ne Rayyan Afef fa ba sa'an ka bane'' Ɗalha ya mayar da dubansa ga Afef ya ce ''kai kuma ka cigaba da sake masa haka zai yi ta raina ka'' Afef ya sake kuka ya buɗe baki zai yi magana Ɗalha ya ce ''bani son jin komai,Rayyan maza ka bashi hakuri ka ce masa baza ka ƙara ba'' ba dan ransa ya so ba Rayyan ya ce ''ka yi hakuri bazan ƙaraba''









Karfe goma daidai Ɗalha ya samu ya gama yiwa yaran wanka ya inda ya yi masu tuwo da miyar danyar kuɓewa,da fari ya so ya dafa masu jollof ɗin taliya ne amma duk suka ce masa tuwo za su ci saboda duk dare tuwo Mumy ke masu,hakan ya samu asali ne daga wajen Ɗalha shi ya sawa Amirah doka duk dare ta dafa tuwo shi haka yake so,Allah ya taimake shi har shara da wanke wanke duk ya yi,yanzu haka home work suke bayan ya rubutawa kowanne su a peper ya ce su kwashi cikin text book ɗinsu,nan ma saida sun sa shi magana wannan ya dauki pencil ɗin wannan,wannan ya ce wane ya kalla masa text book wannan ya ce wane ya zauna masa kan text book haka dai Ɗalha ya yi ta fama da su har Allah ya taimake shi sun gama,ya rage Sudais,da kanshi ya kaisu bathroom yasa su duk sun yi fitsari kafin suka kwanta,ya dawo parlour hannusa riƙe da Fauziyya,bayan ya samu waje ya zauna ne ya dauki wayarsa ya yi dailing number Unaisa yau ta yi ta kiransa bai ɗaga ba tun safe da suka yi magana ta ce ya tura mata 100k bai tura ba ta yi ta kiransa amma bai ɗaga kiran ba,ya kira layinta sau uku amma bata ɗaga ba hakan yasa ya fahimci ta yi fushi,mobile app ɗinsa ya shiga ya yi mata transfer ɗin 100k daga haka ya ajiye wayar,tunawa ya yi da miyar stew da ke wuta, mayar da dubansa ya yi ga Sudais da ke home work ya ce ''Sudais je kashe gas ɗin miya'' Sudais ya amsa da to daga haka ya tashi ya wuce kitchen,bayan shigarsa kitchen ya shiga dube dube gaba ɗaya ya manta abinda ya shigar da shi kitchen kawai ya dauki kofi ya tare ruwa a fanfon kitchen ya sha ya aje kofin inda ya dauka ya fita daga kitchen ɗin bayan komawarsa parlour bai ga Ɗalha ba sai Fauziyya dake kwance kan kujera tana barci hakan yasa ya dauki home work ɗinsa ya cigaba da yi,bai ɗauke lokaci sosai ba ya gama,bayan ya gama ya wuce ɗakinsu,bai kwanta ba saida ya yi fitsari kamar yadda Ɗalha ya faɗa masa,shi kuwa Ɗalha bayan Sudais ya shiga kitchen Unaisa ta kira sa,bai amsa kiran ba saida ya fita entrance sanin halin Unaisa yanzu sai ta yi ta masa rashin mutunci a gaban Sudais hakan yasa bai amsa kiran ba saida ya fita,kamar yadda Ɗalha ya yi tsammani hakan kuwa ya faru bayan ya amsa kiran Unaisa ta nuna masa rashin dadin ta da bai tura mata ƙudi lokacin da ta buƙata ba, duk yadda Ɗalha ya kai wajen jin haushin Unaisa da ya fara magana da ita sai yaji ya nime ɓacin ran ya rasa haka zata yi ta masa tijara amma bai iya amsa mata sai dai ya yi ta bata hakuri,yanzu ma kiran sa ta yi tana masa tijara da rashi tarbiyya maimakon ya nuna mata rashin jin daɗin sa sai kawai ya shiga bata hakuri,da kyar ya samu ya shawo kanta,nan ma sai da ya ƙara mata 50k kan 100k ɗin farko kafin ta sauko,bayan alart ɗin 50k ɗin ya shigo wayarta ne ta karya murya ta shiga yi masa shagwaɓa,ya ƙara birkice mata ya rinƙa gaya mata maganganu masu daɗi haka dai suka yi ta hirar su,sha biyu da rabi Ɗalha ya yi mata sallama ya shiga parlour,bayan shigarsa parlour ne hayaƙi ya cika parlour ga kuma kaurin miya da ya cika parlour da wani irin gudu Ɗalha ya wuce kitchen hayaƙi ya cika ko ina a kitchen ɗin idon Ɗalha ya sauka kan miyar dake kan gas da sauri ya kashe gas ɗin tare da buɗe murfin pot ɗin miyar da sauri ya sake murfin pot ɗin a ƙasa dalilin zafin da ya ziyarci hannusa,sosai miyar ya ƙone ya yi baƙi kamar ba miyar tumatir ba,ya yi baƙi kirin kamar gawayi hayaƙi haɗe da kaurin miyar da Ɗalha  ya shaƙa ya haifar masa da tari nan ya shiga tari babu kakkautawa,tagar kitchen ɗin ya buɗe daga nan ya fita daga kitchen ya buɗe gaba ɗaya tagogin parlour dan bawa iska damar shiga parlour,bayan ga buɗe tagogin ne ya dauki Fauziyya dake kwance parlour ya wuce da ita ɗakin sa ya yi mata shimfiɗa,jiki babu kwari Ɗalha ya samu waje ya zauna bakin gado ya yi tagumi yana tunanin abinda zai dafawa yaran gobe na tafiya makaranta,ya daure ya yi wannan miyar ne dan ya samu sauƙin aiki gobe amma sai gashi Sudais ya bar miyar ya ƙone,doguwar ajiyar zuciya ya sauke kafin a hankali ya tashi jiki babu kwari ya wuce bathroom ya yi wanka,karfe ɗaya daidai ya kashe wutar ɗakin ya rige dim ligth,kwanciya ya yi kan bed yana karanto addu'ar barci










SHUUKRAN