MATAR GIDA PAGE 10
MATAR GIDA 010
SHUUKRAN /022
P10
Washegari karfe biyar na safiya Ɗalha ya farka daga barci,wani irin ciwo kansa ke masa sakamakon rashin barci me kyau sau uku Fauziyya ta tashi sa daren jiya,cike da juriya ya wuce kitchen saboda yadda kansa ke masa ciwo har baya iya buɗe idanunsa da kyau,taliya ya dafawa yaran sai dankalin turawa ya soya masu da kwai,duk aikin da yake Fauziyya na manne da shi,duk inda zai sa ƙafa tana tare da shi,binsa take kamar jela,karfe biyar da mintina hamsin ya samu ya gama dafa masu abinci,bayan ya yi sarving ɗinsu wanda za su ci a gida ya kuma zuba masu wanda zasu je da shi makaranta cikin lunch box ɗin su,ba tare da ɓata lokaci ba ya wuce ɗakinsa inda ya shiga bathroom ya haɗawa kansa ruwan wanka,bai bar bathroom ɗin ba sai da ya dauro alwala,bayan fitarsa daga bathroom ya tarar Fauziyya tsaye kofar bathroom ta kafe sa da ido cikin Hausar ta da bai fita ta ce ''Dady fiyaye'' da sauri Ɗalha ya shigar da ita bathroom ɗinsa ya cire mata wandon jikinta da kuma pampers ya daura ta kan site,bayan ta gama ya yi mata tsarki,wando da ya cire mata ya dauko ya maida mata kafin ya shirya kansa cikin wata farar jallabiya,nan cikin ɗaki ya gabatar da sallar asuba,bayan ya idar da sallah yana nan zaune kan darduma yana azkar Sudais ya shigo ɗakin bakin sa dauke da sallama Ɗalha bai amsa masa sallama ba kallon sa kawai yake yana jiran jin abinda zai faɗa cikin rawar murya Sudais ya ce ''Dady fanfon tiolet ɗinmu ya ƙi kashuwa'' Ɗalha bai san sanda ya katse azkar ɗinda yake ba ya ce ''ya ƙi kashuwa ko kun karye fanfon?" Sudais ya yi narai narai da ido alamar yana son yin kuka ya ce ''Dady ba karyawa na yi ba ya ƙi kashuwa ne,ina ta son na kashe amma yaƙi shine...shine...''wani irin tsawa Ɗalha ya yiwa Sudais ya ce ''shi ne me?" Sudais da ya gama tsorata da babansa cikin kuka ya ce ''Dady l'm sorry'' shiru Ɗalha ya yi bai sake cewa komai ba,shi kuwa ya gaji da tsayuwa daga karshe ya fita daga ɗakin yana share hawaye
Karfe shidda da mintina ashirin Ɗalha ya shafe addu'a,saif dake cikin ɗakin ya buɗe ya cire kayan da zai sa yau, ya shirya komai yadda da ya zo kawai daukawa zai yi ya sa,barin ɗakin ya yi bai tsaya ko ina ba sai ɗakin su Sudais bayan shigar sa ɗakin bathroom ɗin su Sudais ya shiga ya ga yadda Sudais ya karye fanfo,ruwa na ta zuba jiki babu kwari ya shiga tiolet ɗin ya tsaya yana ƙarewa fanfon kallo ya fara tunanin wata hikima zai yiwa fanfon ruwan ya tsayar,yaga babu wata hikimar da zai yi,mafita kwara ɗaya ce kawai ya kashe ruwan gidan gaba ɗaya daga control,fita ya yi zuwa can gate inda ya kashe control ɗin gaba ɗaya,yana shirin barin wajen ne idonsa ya sauka kan wata ƴar karamar sanda,da wani irin sauri ya dauki sandar,kitchen ya koma ya samo wata leda ya naɗe sandar da wannan ledar,daga nan ya wuce bathroom ɗinsu Sudais da wannan sandar ya yi amfani ya toshi fanfon,sake fita ya yi zuwa control ɗin ruwan ya kunna,karfe shidda da mintina hamsin Ɗalha ne zaune cikin bathroom yana yiwa yaran wanka,duk ya haɗa zufa kamar wanda aka bawa babban aiki,tun da ya tashe su daga barci suke ta sashi magana haka Ɗalha ya zama kamar wani zararre kalmomi uku zuwa huɗu ya rinƙa maimaitawa kamar karatu ''kai bari,ke tashi a wajen,kai bani,ke zo nan'' haka ya yi ta fama, karfe bakwai daidai Ɗalha ya gama yiwa yaran wanka ya shiga shirya su,shafar mai da sanyawa yaran uniform saida Ɗalha ya dauki a ƙalla mintina talatin,duk yaran sun gama sa uniform ya rage Rayyan kaɗai da ke ta faman dube dube Ɗalha ya haɗa kan yaran gaba ɗaya ya ce duk su fita su yi breakfast duk suka amsa da to sai a sannan ne Rayyan ya ce ''Dady na manta wando na a makaranta jiya'' Ɗalha ya ji kamar ya wanka wa Rayyan mari tsabar yadda ranshi ya ɓaci,amma sai ya dauri ya ce ''da wani wando ka dawo gida jiya?" cikin halin ko kola Rayyan ya ce ''ban dawo da wando ba,aiy haka na dawo gida babu wando'' ya karashi magana yana sa suck ɗinsa ɗan jimm Ɗalha ya yi yana tunani, kenan jiya babu wando jikin Rayyan da ya je dauko su,muryar Sudais ne ya katse masa tunani inda ya ce ''shi yasa kullum in Mumy ta je daukan mu sai ta duba komai nasa har tambaya anty su take ko Rayyan ya bar wani abu a school'' Ɗalha da ya gama gajiya da lamarin yaran ya mayar da dubansa ga Rayyan ya ce ''ka dauki ɗayar wandon uniform ɗinka ka sa'' Rayyan da ya dauki school sandal ɗin sa zai sa ya ce ''to aiy duk sun ɓata uniform ɗina ɗaya ne'' ya faɗa tare da sa sandal ɗinsa Ɗalha bai san sanda ya kaiwa Rayyan bugu ba ya mare mashi baki yana faɗin ''ka ƙara ɓatar da kayanka sai na maka dukan tsiya'' Rayyan ya buɗe baki zai yi kuka Ɗalha ya yi masa tsawa da yasa dole ya haɗe kukan,wani wandon jeans Ɗalhya ya dauko cikin kayan Rayyan ya bashi ya ce ya sa,daga nan duk sun fita daga ɗakin,karfe takwas da mintina goma duk sun gama breakfast har Ɗalha ya rage sai Fauziyya itama ɗin ta koshi kawai da wasa take da abincin,ganin haka yasa Ɗalha komawa ɗakinsa dan karass shiri bayan tashin sa Fauziyya ta dauki plate ɗin taliya ta bi bayansa,shi kuwa Ɗalha bai san Fauziyya ta biyo sa ba,bayan shigarsa ɗaki bai tsaya ɓata lokaci ba ya cire jallabiyar jikinsa ya rage iya boxers a jikinsa,farar zariyya da wadonsa wanda ya fidda ɗazu ya dauko ya sa ba tare da ɓata lokaci ba ya fice jikinsa da turare,hula da agogo dake kan bed site drower ya dauko ya sa daga haka ya dauki jakar kanfutar shi dake gefin site drower,mayar da dubansa ya yi kan agogon dake daure a tsintsiyar hannusa yaga karfe karfe takwas da mintina ashirin hakan yasa ya waigo da sauri da niyyar barin ɗakin ji ya yi yayi karo da wani abu,bai gama tantanci abinda ke faruwa ba sai ganin sa ya yi ƙasa ya faɗi nan take ciwon kai da ya ɗan lafa masa ya ji ya dawo sabo,muryar Fauziyya ya ji ta ƙarkashin ƙafarsa tana kuka da wani irin ya ɗaga kafa yana dube dube,ganin Fauziyya ya yi tana shirin tashi tsaye fuskarta duk majina haɗe da hawaye tana kuka,kallon rigar jikinsa ya yi yaga duk ya ɓaci da manja,in ran Ɗalha ya kai dubu to duk ya ɓaci a wannan lokaci ji ya yi kamar ya kurma ihu ko zai samu sassauci ɓacin ran dake cikin zuciyarsa,cikin ɗan ɗaga murya ya ce ''shirt ohh my God wani irin abu ne haka yaran nan ke yi?" shiru ya yi yana ƙarewa Fauziyya kallo da ke kuka,haka ya tashi ya canza kayan jikinsa itama Fauziyya ya gyara mata jiki,daga haka ya fita daga ɗakin ba tare da gyara inda Fauziyya ta zubar da taliya ba gani yake in ya tsaya gyara wajen zai yi lattin zuwa aiki,hannusa riƙe da Fauziyya ya fita daga ɗakin,bayan fitarsa daga ɗakin ganin yaran ya yi sun gama shiri shi kawai suke jira hakan yasa ya nufi hanyar barin parlour yana faɗin ''oya les't go hurry'' bayan fitar sune hankalin Ɗalha ya kai kan Sumayya dake riƙe da hijab a hannunta bayan wanda yake jikinta,wani kallo ya yi mata kafin ya ce ''me za ki yi da hijab ɗinda ki ka dauka? ina za ki kai hijab ɗin?" Sumayya ta gyara tsayuwa ta ce ''makaranta zan je da hijab ɗin,in na yi zufa zan cire na jikina in sa wannan''ta kare magana tare da nuna masa daya hijab da take riƙe da shi Ɗalha na shirin magana Sudais ya taɓe baki tare da faɗin ''ba Mumy ta hana ki zuwa school da hijab biyu ba'' Sumayya ta yi shiru kamar ba da ita Sudais ke magana ba sai kokarin buɗe kofar mota take Ɗalha ya ce ''kee je ki aji hijab ɗin kafin na dake ki''ya kare magana fuska babu alamar wasa Sumayya kamar jira take ta sa kuka tana buga kafa a ƙasa Ɗalha ya nufi inda take tsaye da niyya karɓar hijab ɗin Sudais ya ce ''a'a Dady kar ka karɓar in ka kaɓar zata yi kashi a wando'' baki buɗe Ɗalha ke kallon Sudais ya ce ''za ta yi kashi?" Sudais ya amsa da ''eh'' cike da ɓaciwar rai Ɗalha ya mayar da dubansa ga Sumayya ya ce ''come on give me kafin na zane ki'' babu musu Sumayya ta miƙawa Ɗalha hijab lokaci guda kuma ta saki kashi cikin wandon dake jikinta baki buɗe Ɗalha ke kallon Sumayya ɓacin rai haɗe da mamaki suka haɗo masa lokaci guda,ji ya yi ba zai iya jurar halin yaran nasa ba,nan take Ɗalha ya shiga zane Sumayya saida ya zane ta da kyau kafin ya wanke mata jiki,karfe tara daidai Ɗalha ya kai yaran makaranta,ya yi iya bakin kokarin sa ɗan ganin basu yi latti ba amma hakan ya gagara yau ma sai da ya je wajen head mistress ya faɗa mata dalilin da ya sa suka yi latti ta ce babu damuwa,ya kuma yi mata bayanin cewar Rayyan ya baro wandonsa a school jiya, head mistress ta ce babu damuwa za'a duba wandon kuma za'a gani,bayan fitar su daga office ɗin head mistress ne Sudais ya kalle Ɗalha ya ce ''Dady na manta home work ɗina a gida'' Ɗalha ya yi kamar bai ji abinda Sudais ya faɗa ba Sudais ya daura da ''na daura kan daining bayan mun gama breakfast sai kuma na manta ban dauka ba''
SHUUKRAN