Chapter 14
by @smauta
Follow this link to join my WhatsApp group: ***
Hanyar komawar manar gida ta haɗu da iftila'i ke ba magana nake maki dan Allah kuyi hakuri karku cutar dani bansan ba'a bi ta nan ba bakuwa ce ni a garin dan girman Allah kuyi,ki zube kasa dan uban babarki nace duk wanda ya taka gona ta ni uban fada saina taka tashi,ubanwaye ya turo ki nan????
Na rantse da girman Allah ba turoni akayi ba hanya ce ta biyo dani,wani daga gefe ne daya gaji da shaye shaye yace hanya ta biyo dake tanan,kai kwalwa na'am oga banso in bude idona baka ballaman yarinyar nan biyu ba,angama wanda aka kira da kwalwa ne yayo kan manar a sukwane wani halbin bibbiyu yayi mata akan allon kirjin ta dayasa taga wata bakar wuta ta gifta mata jikkar hannunta ta watse kasa kudin dake ciki da sauran kayan ne suka tarwatse a wurin kwalwa ne yace kai oga kan yarinyar nan fa akwai tsaba…..…
Kudin ya dauko ya mikama ogan yawan kuɗin da yagani ne yace kwalwa sai mai gida,cajeta agogon ka dauko min shi in kaima shalele tsomakaran kabar mata kayan ta haka akai kuwa cikin sumar datake a ciki ne taji ana lalubar ta da sauri ta farka ta zabga wani uban ihu nashiga ukku karka ketaman haddi indai kudi ne gasu,kwalwa yace keeee kudin ne zamu tsaya ki bamu da kanki ai fizga zamuyi da babbar bara'uba ma,daga bayan kwalwa taji wani yace kyaleta muma ya kamata mu ɓace a wurin nan fa……….
Tashi ki sata ko in karyaki rarrafawa tayi ta mike sai gata ta kara komawa kasa dabas a karo na biyu ne data yunkura ta kalli gefen kafar ta ta fada kan dutse jini ke fita kadan kadan amma duk ya bata kafar bata tsaya bin takan komai ba tunda ta tsira da rayuwarta alhamdulillah tafe take tana jan kafa kunci yayi kane kane a zuciyarta ga hadari na haduwa gangan gangan garin damuna…………..
Tafiya kawai take batasan inda take jefa kafar ta tayi kusan minti ashirin kafin ta fara hango hasken motoci alamar tazo titi kenan kafarta na mata wani irin zugi aka balle da ruwa kamar da bakin kwarya tana gaf da isa titi kafar ta tace bata iyaba ana ta zube ƙasa tana kuka batada tudun dafawa tana kallon titin highway bawani mai tsaya ga ruwa mai karfi kowa kawai tada gudu yake baji ba gani………..
Kusan hour ta daya cur a nan ruwa mai karfin gaske na dukanta ga kafarta da tayi tsami numfashinta ne ke kai kawo makoshin ta zuwa cikinta hannu ta fara dagawa tana neman taimako ba mai tsayawa,yawancin ma duk masu wucewar manyan motoci ne tun daga nesa dasu yake hango kamar mutum Idris na'am oga gaban mu kadan naga ana waving hannu ko eh oga amma dai sbd security karmu tsaya,kasan hanyar nan sun baci da barayi yanzu mata suke turawa su tsaya bakin titi kamar suna neman taimako daka tsaya wlh saidai wani lbrn bakai ba…………
Bai kara cewa komai ba haka sukazo suka wuce shaaaaaa sunyi nisa sosai zuciyar sa ya kasa nutsuwa Idris kada motar nan mu koma inda mu koma wurin nan oga shut up shuru yayi ya shiga u turn dazai maidashi baya kara gudun motar tasu yayi suka iso har lokacin yarinyar na wurin tana neman taimako kasan kafar shi ya jawo wani waje ya fiddo bindiga Idris najinshi yayi kit kit alamar ya haɗa ta saukeman glass daya Ka fita ka dauko matar can,jiki na kyarma Idris yabi umarnin boss………….
Gaban manar yazo jikinshi na rawa baiwar Allah lafiya bakin manar a bude tace tai tai tai kawai ta sheke a wurin subhanallah,daga cikin motar ne yake cemashi hurry up jikin idris kyarma yake ya kasa taba manar a zafafe ya fito bindigar hannun shi ya soke ga ruwa mai karfi na dukan shi atishawa ya fara sosai ɗaukar manar yayi tsam bayan mota ya shimfidar da ita yashiga gaba rigar shi ta sama ya cire saboda ta jike da ruwa sosai………
Har lokacin jikin Idris kyarma yake ba wanda ya kara cewa komai daga shi har Idris din saida suka shigo cikin birnin abuja sannan ya kalli Idris yace muje gwarinpa okay sir,tafiya suka karayi mai tsawo kafin su shigo jerin gidanje dake gwarinpa,hannunshi yasa ya laluba ba wayar shi tunawa yayi da tana back seat tsaki yaja kawai gaban wani katafaren gida Idris yayi horn da gudu mai gadin gidan ya bude gate……….