SHAFI NA ARBA’IN DA SHIDA
by @zeeeyybawa
LIKITAN RUHI
BOOK 2
Na
ZAINAB BAWA
Arewabook @Zeeeyybawa
Marubuciyar BIBIYATA AKEYI
SHAFI NA ARBA'IN DA SHIDA
Sai wajen misalin ƙarfe tara Mami ta tashi daga bacci, domin ta raba dare tana yi wa Hammad addu'ar samun sauƙi, Bayan ta tashi, ta yi wanka ta shirya sannan ta fito falo, Masu aiki ne kawai suke ta zirga-zirga a lokacin, don haka ta fito zuwa waje.
A zuciyarta ta ji kamar ta je ta duba jikin Hammad, amma sai ta tuna cewa yana tare da matarsa a wannan lokacin, Kuma tunda ba a ji shiru, hakan yana nufin yana lafiya, domin Ameerah a tare da shi, kuma idan akaji shiru toh lafiya ce domin ita ke ɓuya.
Sai ta nufi sashen da aka sauƙi su Yaa Mu'azzam, domin ta duba jikin Fatima. A bakin ƙofar ta yi knocking, amma tana iya jiyo maganarsu a ciki, Yaa Madu ne ya tashi ya je ya buɗe ƙofar. Da ya ga Mami, sai ya saki murmushi yana faɗin.
"Shigo Mami." Mami ta shiga ciki, Bayan ta zauna, Yaa Mu'azzam ya ce:
"Ina kwana, Mami?" Mami ta amsa.
"Lafiya ƙalau. Mu'azzam, ya mai jiki da Jannah?"
"Da sauƙi. Tana ciki tana bacci."
"Ma sha Allah. Allah ya ƙara mata lafiya."
"Amin," suka amsa gaba ɗaya. Yaa Madu ma ya gaida Mami, ta amsa masa, Mami ta ɗan nisa kafin ta ce:
"Babu wani abu da ya faru jiya da daddare ko?"
Yaa Mu'azzam ya girgiza kai.
"Babu abunda ya faru, Tunda Ameerah ta ce mu kunna karatu, ko razanar da take yi cikin dare bata yi ba, Sannan nima kusan kwana nayi ina sallah. Alhamdulillah, har zuwa yanzu dai komai lafiya."
Mami ta jijjiga kai tace.
"Toh mungodewa Allah, Yanzu next step ɗin sai mu jira Ameerah ta tashi kafin mu san abun yi ko?"
Yaa Madu ne ya amsa da.
"Ai Mami, inaga Ameerah kam ta tashi, Ko ince bata yi bacci ma gabaki ɗaya, domin bata bacci, Mu kirata kawai sai ta faɗa mana abun yi." Mami ta kalleshi da ɗan mamaki tace.
"Bata bacci? Kuma me ya sa?" Yaa Mu'azzam ne ya bata amsa.
"Mu kanmu Mami ba mu sani ba. Amma bata iya yin bacci, Gara kwanaki da Madu ya shiga damuwa sosai bayan ya fahimci hakan, sannan ya matsa akan lallai sai likita ya dubata, domin ba lafiya ba ne, ace mutum ya kasance baya iya bacci. Sai tace idan ta je asibiti tana iya yi, sanin bata ƙarya yasa muka yarda cewa tana yi a can ɗin" Mami ta kalli Yaa Madu tace.
"Haka aka haifeta kenan, ko daga baya ta samu?"
"Gaskiya daga baya ne, amma ba za mu iya faɗin dai-dai lokacin ba, Saboda da zarar dare ya yi take kulle ƙofofin ɗakinta, bata buɗewa sai safiya, Babu wanda ya san abunda yake faruwa, bayan ta koma gidan Mama Hajiya ne aka gano cewa kwata-kwata bata bacci, An tambayeta tun yaushe, amma bata faɗa wa kowa ba, Inaga dai tsawon lokacin da aka san bata bacci zai iya kaiwa shekara bakwai."Mami ta zaro ido a ɗan tsorace, a ranta tana ji Lallai akwai wani abu mai girma da yake damun Ameerah a fili kuma tace.
"Ameerah bata iya bacci sai a asibiti?, sannan bata kuka?, ba ta murmushi ko dariya. Me ya sa haka?"
Ta tambaya tana kallonsu, Yaa Madu ya sauke ajiyar zuciya.
"Duk ba mu da amsar wannan tambayar. Domin ko an tambayeta, ba zata amsa ba." Mami ta sake tambaya:
"Ko mahaifiyarku ta tambayeta ba zata amsa mata ba?" Yaa Mu'azzam ya ce:
"Ameerah zata iya amsawa kowa, amma banda Mommy." Mami ta jijjiga kai, Gashi suma sun ambaci cewa Mommy ce mahaifiyar Ameerah, ta nisa kafin tace.
"Allah ya sauƙaƙa mata."
"Amin," suka amsa gaba ɗaya, Sai Mami ta sake cewa:
"Game da case ɗin Fatima fa, ba ku ganin ya kamata a sanar da iyayenta halin da take ciki?" Mami ta yi wannan tambayar ne domin Ameerah ta ce mata ta tambayi wacece Fatima, Amma kai tsaye ba zata fito ta yi musu wannan tambayar ba, shi ya sa ta ɓullo ta nan, Yaa Mu'azzam ya amsa da faɗin.
"Ai iyayenta duka sun rasu." mami tace.
"Babu ko wasu 'yan uwanta majiɓanta?" Yaa Mu'azzam ya ɗan yi shiru kafin ya ce.
"Gaskiya babu, Mami, Mommy ce kawai 'yar uwarta, kuma Ameerah ta ce kar a sanar mata." Mami ta so ta tsaya da tambayar daga nan, amma bata samu cikakken bayanin da take nema ba. Ta tabbata akwai wani abu da Ameerah take son ta gano, shi ya sa ta saka ta wannan tambayar, Ta nisa sannan ta ce:
"Allah sarki. Allah ya jiƙan iyayenta, Amma ita Mommy yayar mahaifinta ce ko mahaifiyarta?" Ta yi tambayar ne domin tana son gano alaƙar da ke tsakaninsu, Yaa Mu'azzam ya ce:
"A'a, Fatima kanwar Mommy ce, uwa ɗaya uba ɗaya. Shi ya sa nake ganin ya kamata a sanar mata, saboda Fatima bata da wacce ta fita." Mami ta kalleshi da mamaki. Tana son fahimtar ko yayi kuskure ne akan abunda ya faɗa, amma ta ga a fili cewa haka yake nufi.
Toh, har idan Mommy yayar Fatima ce, Mommy ba ita ta haifi su Yaa Mu'azzam ba kenan? Ameerah kawai ta haifa, ko da Madu? Ko Yaya? tana ta jero waɗannan tambayoyin a cikin zuciyarta da bata da yanda zata samu amsar su sai wajan Ameerah. Kan Mami ya kulle, amma bata so ta cika yawan tambayoyi, Sai kawai ta yi shiru, Ta miƙe sannan ta ce.
"Bari a kawo muku abun karyawa, Amma tunda Ameerah ta ce kar a sanar wa Mommy tukunna, a ɗan dakata, duk da yayarta ce uwa ɗaya uba ɗaya, ku dakata tukunna." Yaa Mu'azzam ya amsa:
"Toh, shikenan, Ba zan sanar ba Mami, in sha Allah. Allah ya saka da alkhairi."
"Amin" Mami ta amsa sannan suka fita tare da Madu. shi Madu zai ɗauko wasu kaya daga cikin motarsu, Mami ta kasa haƙuri, domin maganar da suka yi da Yaa Mu'azzam tana ta yawo a cikin zuciyarta ta dubi Yaa Madu ya ɗanyi gyaran murya.
"Uhmm, Madu, nikam na tambaye ka mana." Ya kalleta.
"Toh Mami, ina sauraronki."
"Mommy ita ta haifi Ameerah?" Yaa Madu ya yi murmushi.
"Itace Mami, ita ta haifemu."
"Ku biyu kenan?" Yaa Madu ya jijjiga kai.
"A'a, dukanmu. Hadda da Yaa Mu'azzam."
Mami ta jijjiga kai a hankali, A yanzu ta fara fahimtar abunda Ameerah take so ta sani lokacin da ta ce ta tambayi wacece Fatima, Tabbas akwai wani abu da ba daidai ba, Domin babu yadda za a yi Mu'azzam ya auri ƙanwar mahaifiyarsa, uwa ɗaya uba ɗaya, Akwai wani abu da Ameerah ta sani wanda kowa bai sani ba, Ko da yake, daga maganganunsu ta fahimci kamar ba su da ikon sanin gaskiyar lamarin ne ko basa hayyacinsu, taga alamu daga lokacin da Suka furta cewa Mommy ce mahaifiyarsu, sannan kuma sun ce Mommy yayar Fatima ce, uwa ɗaya uba ɗaya, ba tare da sun lura da cewa akwai wani abu da bai yi daidai ba a maganar su ba. Yaa Madu ya kalleta.
"Mami, kada ki damu da irin alaƙar dake tsakanin Ameerah da Mommy, Na san dalilin da ya sa kika tambaya kenan, Kowa ya rasa dalilin da ya sa hakan take faruwa, An yi nasiha, an yi faɗa, amma Ameerah ta ƙi gyarawa." Mami ta yi murmushi.
"Babu komai, Ai Ameerah har yanzu yarinya ce. Idan aka cigaba da addu'a da nasiha, zata gyara, in sha Allah." Ya madu ya yi murmushi.
"Allah ya yarda. Ai naga zamanta a Zaria ta canja sosai, har tani iya yarda da mutane." Mami ta ce:
"Ta canja kam sosai. Domin ko ni, a ɗan sanin da na yi mata zuwa yanzu, na lura ta canja." Suka cigaba da hira, mafi yawancin hirar tasu kuwa akan Ameerah ce. Har suka isa inda hanyar zata raba su, sannan suka yi sallama suka rabu.
Mami ta shiga ciki, ta samu Hajiya ta tashi har ta fito falo. Mami ta zauna, suka gaisa, sannan ta ce a kai wa su Mu'azzam breakfast. Hajiya ta kalleta.
"Kin je kin duba Hammad da jikinsa? Yaya jikin dai?" Mami ta yi murmushi.
"Ban je ba, domin naga har yanzu kamar basu tashi ba."Hajiya ta yi 'yar dariya.
"A'a, toh kada a takura musu. A barsu su tashi da kansu." Sai kuma ta sake cewa:
"Ai karki so ki ji yadda nake jin daɗin wannan auran na Hammad a raina. Likitarsa kuma matarsa ce, zata kula da shi fiye da tunanin mutum. Gaskiya Hammad yayi sa'a." Mami tana murmushi ta ce:
"Sosai ma. Jiya nan, kar ki so ki ji yadda hankalina ya tashi da jikinsa ya motsa. Amma yarinyar nan, a cikin wasu 'yan mintuna, ta zare ciwon dake damunsa." Hajiya ta gyara zamanta.
"Dole hankalinki zai tashi. Nima jiya ai na damu. Baku sanar da ni ba sai bayan kun dawo. Amma na so na je naga jikinsa. Da na ji an ce yana tare da matarsa ne, ban fita ba, saboda bana son takura musu."