HASASHEN SOYAYYA

Hs 31

by @legendspen

_Page 31_


"Bawani nan." Amrah ta faɗa, tana zama. "Bhatool Amarya." Amrah ta sake faɗa. "Uhm wai kin san me?." Bhatool ta faɗa. "Faɗi ina jinki."

"Wai kinsan an fara zancen neman auren Jannah, amma matarnan ko ta faɗa mana." 

"Aurenta kuna da wa?." Amrah ta faɗa cike da mamaki, dan ita ko yau sun haɗu da Jannah a makarantar, kawai bata sam zuwa tare da ita ne. "Saurayin da ta yi a bikina, abokin Senate mana." Bhatool ta faɗa. "Kai, amma yarinyar nan ta cika muguwar munafuka, kinga yadda take mun yanzu a makaranta?." 

"Me take yi miki?." 

"Wani iskanci-iskanci, kin san yanzu ma Suhaima bata zuwa ta fara laulayi." 

"Eyh ta faɗamun ɗazu, amma Jannah ta cika butulu." Bhatool ta faɗa. "Ki bar shigiya in dai mune damu take zancen." 

"Wallahi Allah kam." Bhatool ta faɗa. "Me kike da shi?." Amrah ta tambaya. "Komai ma, muje babban kitchen." Bhatool ta faɗa, ta shi suka yi suka nufi kitchen ɗin Amarah na ta santin gidan, kaza kawai ta gasa da dankali ta ci sun ta hira daga haka suka shiga zaga gidan, ko ina sai da suka shiga kuma ko ina sai Amrah ta ƙare musu kallo, har sai Bhatool ta gaji da ganin wajen ta yi gaba ta bar ta tana faman santi. 

Haka suka gama zagaye gidan, sai yamma Amrah ta tafi ta bar Bhatool da kaɗaici. 

Sai bayan magariba Senate ya dawo cikin gidan, lokacin Bhatool na zaune da waya a kunneta. "Ai ni kallonki kawa nake, ace anzo maganar aurenki bazaki faɗamana ba sai dai muji a bakin mutane." Bhatool ta faɗa cikin wyaar. "Bawani nan, yanzu wane kinibibin ne yasaki faɗamun kuma?." Ta faɗa bayan an bata amsa a cikin wayar, kallon ta ya yi ya shige ɗaki ita kuma ta ci gaba da wayarta abunta. "Bawani fa, bawani wallahi." Ta sake faɗa, sai kuma can ta ce. "To Allah yasanya alheri, yaushe zaki shigo?." 

"Tom sai kinzo, sai anjima." Ta faɗa tare da kashe wayar ta bi bayan senate, kwance ta same shi kan gado ya yi rub da ciki, idanunshi a rufe. "Sannu da zuwa." Ta faɗa, amma shiru babu amsa, ƙarasawa ta yi sanan ta ce. "Kagaji ne, xaka yi wanka?." Buɗe idonsa ya yi ya kalleta sanan ya ce."kaina ke ciwo."

"Ya salam!, sannu bara na kawo ma magani." Ta faɗa tana ta shi ta nufi Frist aid box dake falon gidan. Maganin ta dakko mai ta haɗa masa da ruwa ya sha, bayan ya sha ta ba shi waje ta dawo falo, sai dai takasa yin komai sabida ba ta saba zama ita kaɗao gidan ba, kullum ko da yaushe tana tare da shi. Yau sai take jin ta kamar marainiya, har wajen tara da rabi bai fito ba haka yasa ta tsakuri abinci iya yanda zata iya ta shigo ɗakin, yana kwamce idonsa a rufe haka ta raɓa ta kwanta. Ta daɗe a kwance kafin bacci ya dauketa. 

Washe gari. 

A hankali ta buɗe idonta tare da kai su ga inda Senate ke kwamce sai dai babu shi a wajen baki ɗaya, a hnakali ta ta shi tana mamakin ina ya je, toilet ta shiga ta ɗaura alwala ta fito ta yi sallah, tana idarwa ta nufi kitchen ɗaura breakfast sabida takwas ta kawo kai. Ta yi mamaki sosai ganin senate a falo yana danna wayarsa, amma sai ta kauda mamaki ta hanyar cewa. "Ina kwana?." 

"Kintashi lfy?." Ya faɗa hankalinsa a kan wayarsa, kasa tanka masa ta yi sai hucewa da ta yi zuwa kitchen, sai dai ta kasa tsinana komai cikin kitchen ɗin sai faman tunani kala-kala. "Me kuma na yi wa senate, me ya faru da shi kuma haka?." Ta ce wancan ta ce wancan, daƙyar dai ta kammal tea ta soya ƙwai ta fito. Sai da taga jera kayan akan dinning sanan ta ce. "Ga Breakfast." 

"Yanzu zanje gidan Mom, zan yi acan." Ya faɗa yana miƙewa, wata ƙwalla ce ta gangaro da fuskar Bhatool ba ta sami damar yin magana ba ya fice. "Na shiga uku ni Bhatool." Ta faɗa tana shigewa ɗaki, wayarta ta ɗauka ta dannawa Yaya karima kira, ringi biyu ta yi ta ɗaga tare da faɗin. "Lafiya Bhatool zaki kirani da farar safiya haka?." Cikin muryar Kuka Bhatool ta ce. "Yaya ba lafiya wallahi, Senate ya daina sona?." 

"Bangane ya daina sonki ba?."

"Yau tun da ya ta shi bai kulani ba." 

"To Bhatool ko dai kin masa laifi ne?." 

"A'a Yaya Babu abinda na masa wallahi, yanzu ma yaƙi breakfast anan wai gidan Mom za shi." 

"Ki nutsu Bhatool kin ji, idan ya dawo ki zauna ki yi magana da shi cikin ladabi da biyayya, bawai da harigido ba kin ji." 

"Tom Yaya, Allah yasa ya kulani." 

"Zai kulaki ma kin ji. Sanan ki dinga yi masa uzuri ba ko yaushe yake da son hayaniya ba." 

"Shikenan Yaya na gode." Daga haka su ka ƙare wayr, Bhatool ta zauna ta rafka uban tagumi. 


~~~~~Red bricks 

Mom da Dad na zaune kan dinning suna breakfast, Dad dai ya rasa nutsuwarsa tun ganin Umma da ya yi a cikin hidimar biki wanda yasan ita ba ta gan shi ba, a kullum Justice ne yake ƙara lallaɓashi da basho haƙuri a kan kar yaje ya same ta. Da mamaki sosai suke kallon Senate bayan sun amsa sallmar da ya yi, ba gausuwa kawai ya huce part ɗinsa ya kulle kansa, Mom ce ta kalli Dad ta ce. "Lafiyan yaronnan kuwa?." 

"Gashinan dai kamar ba lafiya." Dad ya bata amsa, ta shi ta yi zata bi bayanshi ya riƙe ta sanan ya ce. "A'a, bar shi zuwa Anjima." Ba dan ranta ya so ba ta dawo ta zauna. Tana cin abincin amma hankalinta gaba ɗaya yana kan Senate. "Ina faɗamiki magana fa." Dad ya faɗa dan ya jawo hankalinta. "Sorry mema kake cewa?." Dad ya ɗan ji ba daɗi, amma sai ya ce. "Ina faɗamiki cewa na haɗo da tsohuwar buduruwata." 

"Wace tsohuwar buduruwar kuma kake da ita ba labari?." 

"Habiba mana." Ya bata amsa, yana faɗan sunan Habiba komai ya dawo kan Mom iri yadda ya dinga fama da soyayyar Habiba har bayan aurensu, yasu Allah ya bashi 'ya mace ya sanya mata sunan Habiba. "Amma da idan na tambayeka cewa kake ta mutu, shi yasa kake son sanyawa 'yar ka sunanta?." 

"Ƙwarai ada ta mutu a duniya ta amma yanzu ta sake rayuwa." Wani abu ne ya tokare ma Mom maƙoshi, hakan yasa ta ce. "Zaifi kyau mu ajiye wanan maganar anan, mu mayar da hankali akan ɗan mu muji mene damuwarsa." 

"Okay ni tawa damuwar ba damuwa ba ce?." 

"Bance ba, amma ina ganin kamar kai kaɗai ta dama." Murmushi mai cike da takaici Dad ya yi, sanan ya miƙe zuwa sashensa, ita kuma Mom miƙe zuwa sashen Senate. Yana kwance yana kallon sillin ta shigo ta zauna gefen gadon. "Senate are you okay?." 

"Yes Mom, just a little headche." 

"So why don't you even stay at your own house?, duk ka tsorata ni." Juyowa ya yi ya kalleta sanan ya ce. "Gidan gaba daya babu daɗi, yanayin iskarshi wani kala." 

"Kai dan ka saba da nan ne amma can ai yafi nan, ya Bhatool ɗin?." Mikeww ya yi zaune sanan ya ce. "Na barta ma tana haɗa breakfast, kawai ni banason zaman cikim gidan ne." 

"To ka kuma ofis mana, ya zancen tafiyanku?." 

"Zamuje Mom, but not recently." 

"Okay na kawo ma breakfast ne?."

"Yes Mom." Miƙewa ta yi ta fita zuwa falon. 

Dad, tun da ya shiga cikin ɗaki yake mamakin yadda Mom ta nuna rashin damuwa da al'amuransa ba, duk da cewa magana ya yi mata akan wata but atleast ya kamata ta saurareshi ko yane,yanzu kuma da zarar ya ce zai ƙara aure ta ce bai kyauta mata ba, amma ta tsaya ya bata labari su tattauna taƙi. Wayarsa ya ɗauka ya shiga nemawa kansa flight, dole zai bar ƙasar ko na wata guda ne ya samu nutsuwar zuci. 



~~~~~~New bra bra. 


Tun gama wayarta da Yaya Karima ta sami waje ta zauna ta rafka uban tagumi, me ke shirin faruwa da ita kuma? Duk tsoronta kar ace Senate ba wai son ta yake ba. "Me ya kawo wanan maganar?." Zuciyarta ta tambayeta, a fili ta ce. "Yau kwananmu nawa da aure, amma har ya canja komai." 

Legendspen
***