Babi na huɗu:Ki mini alfarma
by @dijensy
Hassan daga kan teburin katakon gefen gadon ya ɗora ledar akai ya waiwayo inda take yana ƙara maimaita mata sallama rai a haɗe ta shiga goge hawayenta da mayafin jikinta ta ɗago da rinannun idanunta "Amsawa aurena tamkar yin sallama ne cikin rayuwar uƙuba da baka taɓa ɗanɗanawa ba tun ba a je ko ina ba ka sawa zuciyarka salama ni ba tsararka bace balle har aure ya haɗa ni da kai a yanzu ka rubuta mani saki ka samar wa kanka lumana tun wuri".Jidda ta faɗa ba tare da tana nadamar kalmomin da ta furta masa ba ta shiga hura hanci mai nuni da a shirye take da koma mai zai faru Hassan ya yi ƙasa da kai ya gyara tsaiwarsa "Ki yi haƙuri Jidda aurenki na karɓesa ne sabida biyayya nasan tabbas an shiga huruminki sai dai ina so na tabbatar maki bazan taɓa cutarki ba ko musguna maki ba a yanzu dare yayi mai zai hana ki bari gobe da safe muyi magana".
Murmushin taƙaici tayi "Safiya ta yi min nisa duk wani abu da zamu yi shi yanzu yanzu ne".
Hassan rasa mai zai ce mata yayi kawai ya fita daga ɗakin ta bisa da harara tana miƙewa tsaye ta kalli tsukakken ɗakin tana nazarin ko ina ya je a yanzu ne ta fara tunani ko dai Baba zai kira ya kai ƙararta nan take tsoro ya kamata da faɗuwar gaba ta shiga safa da marwa.Hassan ko da ya fita shagon shi ya buɗe ya shiga shikaɗai yake shawarar ko ya zai da lamarin da ta bijiro dashi dukda daman malam Harisu ya faɗa masa yayi haƙuri da abinda zai iya biyo baya tunda ita kanta yarinyar auren titse ne ba saninsa tayi ba.Jidda ta gaji da jiransa ta buɗe ƙofar da take tunanin banɗaki ne ta tura tana haskawa da fitilar hannunta fasashe tayal ne a ƙasa a tsaftace yake ba wari sai ƙamshin freshener da yake tashi da aka manna a jikin bango masan ta kalla na tsuguno fari ƙal ne ba alamar ƙasanta ta ja tsaki ita yaushe rabonta da masan tsuguno tun tana ƙarama da Baba ya samu buɗi duk masan tangaran ce ta zama bokatai na fenti biyu idanunta ya sauka kai ta kalli fanfo tana gwada kunnawa ta ji ba ruwa hakan ya tabbatar mata a bokati suke ajje ruwa ta buɗe tana haskawa a tsaftace yake fari tass ta ɗago fitilar batir ya zazzago dunɗim duhu ya gauraye ko ina kamar ta tsala ihu ta zira hannunta tana lalubar batirin ta ɗauka da lalibe ta saka a fitilar ta ga tayi farfari ta kawo ta samu ta ɗiba ruwan da moɗar da ta gani kai ta zuba a buta sai da ta kwara rabin bokatin ta iya amfani da masan in banda fitsari ya matseta ba yadda zatayi ta shiga cikin bayinnan.Alwala ta ɗaura tana shinfiɗa ɗan kwalinta kan ledar ɗakin tayi salla maghrib da isha kafin ta juya tana kallon ledar da ya kawo ta yunƙura ta buɗe kaza ta gani ranta ya mugun biya tunani yazo mata ko ya zuba maganin bacci?ko fitar da yayi abinda ya shirya mata kenan?ƙullewa tayi ta mayar cikinta yayi ƙugi ruwan faro ma kallonsa tayi ta kauda ido yunwar da take ji bazata bari ta sha ruwa ba.Kan gadon ta koma zaman jiran dawowar Hassan ɗakin shiru har ta cira rai tana tunanin gujewa maganar saki da ta bijiro masa yayi,inda take zaune nan bacci ya ɗauketa sai tsakar dare ta tashi yunwa ta hanata bacci ganin ba sarki sai Allah Jidda ta jawo kazarta ta ci ta ƙoshi ta kora da ruwa ta rage abu uku cinya fifike sai wuya ta juya tana komawa baccinta.
Ƙarfe biyar ya fito masallaci bayan an idar da sallah ya komo gida yana fargabar komawa cikin gidan yana kuma tsoron kar Anty Ruƙayya ta ga ba gida ya kwana ba idan ta fito hakan yasa shi shiga banɗaki yayi wanka yana saka kaya gogaggu farin yadi ya ɗora hula yana buɗe gidan da makullin wajensa ya shiga ba tare da hayaniya ba kwance ya tarar da Jidda ta yi ruf da ciki tana sharar bacci ya ƙarasa bakin gadon tsahon minti biyu yana tsaye kafin ya samu ya yi gyaran murya "Jidda"Ya kira sunanta ba alamar ta ji sa ya ƙara sautin muryarsa sannan ta motsa "Lokacin sallah har ya wuce kada ki makara".Hassan ya faɗa kafin ta miƙe zaune tana haɗe rai ta sauke ƙafafunta ƙasan gadon ta tashi ta shige banɗakin ya taka zuwa sif ɗin ya buɗe murfi ɗaya ya ɗakko sallaya yana mai shinfiɗawa inda gabas yake ta fito ta na ganin abin sallah bata samesa ɗakin ba ta taɓe baki akwatinta ɗaya da aka haɗota dashi ta hanga daga kusurwar ɗakin ta ɗakko ta kwantar kan gadon tana dubawa ta ga hijab ɗinta da Anty baby ta saka mata cikin kayan ta ɗauka ta sa tana tada sallah gabas ɗin ma jiya ba dai dai ta kalla ba.
Anty Ruƙayya da sassafe ta fito ta shiga kitchen doya da 'kwai ta haɗa musu kazar jiyan da ya basu rabi ta ɗibar musu ita da yara ragowar ta yi sauce mai ɗankaran daɗi ta juye a sabbin warmers ɗinta ta shirya musu tana ɗora kayan tea a tray ɗin ta yi .Tana tunanin yadda zata kai musu breakfast ɗin bata son tura yara ta ga ya shigo gidan tana tsakar gida ya tsaya gisheta ta amsa da murmushi a fuskarta ta bashi kayan karin kumallon ya shiga musu da shi ɗaki bayan ya mata godiya ta zubawa su Amal a flask na makaranta don sunyi late ragowar biredi suka sha da shayi a tsaitsaye suna saka takalmansu Usman ya matso kusa da Mamanshi "Ba mu gaida anty amarya ba".Ya raɗa mata Anty Rukayya murmushi tayi "Idan kun dawo".Ta furta tana mika musu lunch box dinsu shafiha na musu bye bye "Kema kin kusa fara zuwa ai kina musu bye bye ko".Ta furta tana bakin ƙofar ɗakin kafin ta zauna ta yi nata breakfast ɗin.Hassan ko da ya shiga ɗakin ya sameta kan gado ba bacci take ba tana kwance abin duniya ya isheta ganinsa ya shigo yasa ta tashi zaune.
"Ina kwana?"Ya gaisheta yana ajje tray ɗin ya yi ƙoƙarin sauke idanunsa a kan fuskarta.Bata amsa shi ba sai haɗe rai take tana cin magani "Tun ɗazu ka fice baka dawo ba jiya ba cewa kayi zami magana ba?"Hassan ya sauke idonsa ganin tana sarƙesa da nata idon shikuwa baya iya sa mutum a cikin ido.
"Mu fara karyawa tukun ko?".Ya furta a tausashe tayi shiru tana maida kallonta ga tray ɗin da ƙaramin flask na shayi sai faranti da cokula da warmers biyu da kayan shayi ,fita ta ga yayi ya dawo da wani carpet ƙarami da alama sabo ne a shagonsa ya ɗakko ya shinfiɗa musu ta ƙosa ta ga ko wace ƙwaɓar ce ciki don ba abinda take tsammani zai fito daga gidannan mai kyau zaunawa tayi ta buɗe ta ga doya ce ta ɗauka spoon ta ɗiba san ranta ta kwashe sauce din ta haɗa shayinta murtuk ta zuba sugar tana fara ɗibar abincin wani daɗi ta ji a bakinta sai da tayi mamaki nan ta cigaba da ci tas ta cinye ta ƙarasa shayinta ta ɗora komai kan tray ta hakimce gefe a sannan Hassan ya ci a cikin warmer ɗin don ragowa ce bata fi ƙwaya shida ba da ta rage ya haɗa ruwan bunu don baya shan madara yana zama ya ci ya gama ya haɗa kan komai ya fita dashi bakin rariya ya kai da kansa ya wanke kwanukan ya kai kitchen ya dawo ɗakin.Daga ƙasan ya zauna kan kafet ɗin tana kan gadon ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.Ya ɗaukesa sama da minti uku kafin ya tattaro karsashinsa ya fara magana "Ni Hassan ba ɗan kowa bane,na taso gidan da ba su da hali mu uku iyayenmu suka haifa mahaifiyata 'yar bauchi ce mahaifina bafulatani ne ɗan garin gombe shekarsa goma sha uku da rasuwa yayanmu ya cigaba da kula da nauyin komai kasuwanci yake yana iya ƙoƙarinsa bayan na gama sakandare shi ya ɗauki nauyin karatun jamia ɗina na karanci lissafi yayanmu yayi aure da matarsa Anty Ruƙayya hali na rayuwa a gidannan ya zauna da matarsa duk wata ɗawainiya tana wa mahaifiyarmu bayan gama jamiaata na samu aiki da wani kamfanin shinkafa ina shigar musu da bayanai nima ina tallafawa a gida tsahon lokuta yayana ya kwanta rashin lafiya yayi jiyya ta tsahon lokaci kafin Allah ya amshi abinsa ni na cigaba da ɗaukan nauyin gida daga baya mahaifiyarmu itama ta rasu ko shekara ɗaya bata yi ba Husna ƙanwata tayi aure yanzu bata tare damu tana Jos da zama ya rage sai iya matar yayana da yaranta uku da ya barta dasu a da gidansu zata koma yanayin rayuwa na sa ta cigaba da zama a gidan shagona a waje yake nake kwana zuwanki ne ya sa ta kawo shawarar gyara maki nan ɗin sabida yanayin da yadda aurenmu ya zo Jidda amma ina gini ba zamu jima anan ba zamu koma can kiyi haƙuri da zaman nan amma na taƙaitaccen lokaci ne nasan ba abune mai sauƙi ba amma abinda kike buƙata daga wajena abune mai girma ki taimaka ki duba ki ɗauki lokacinki bazan takuraki ba Jidda kuma nayi miki alƙawarin sauke haƙƙoƙin da ke kaina na aure in sha Allah ba zan gajiya ba”
Shiru jidda tayi kafin ta kallesa "Kamar baka fahimci inda na dosa ba an taɓa zaman aure ba so ne?ban taɓa ganinka ba bansan ka ba sabida haka kada kayi tunanin za a samu daidaito tsakanina da kai idan kuma kaƙi lokaci zai bayyana maka hakan don bazaka taɓa kasancewa zaɓina ba".Ta ƙarashe maganar tana kallon wani waje guda Hassan yayi shiru da ƙyar ya iya buɗe baki "Alfarma nake nema guda ɗaya a wajenki don Allah ki je wajen Anty Ruƙayya ku gaisa da safennan buƙatarki kuma zan duba in sha Allah ki bani lokaci".Jidda ta bisa da ido "Sirikata ce ita ko kuma kishiya?”
"Ba sirikarki bace kiyi haƙuri naga ta hidimta mana ko sau ɗaya ne alfarma nima na roƙa nasan kuma zaki min".Hassan ɗin ya faɗa a tausashe Jidda bata sake cewa komai ba tana turo baki "Sai nayi wanka tukun"Ta furta ya jinjina kai "Ba damuwa ki shirya a tsanake ruwan zai isheki na ciki?"Zai isa amma son ta bashi wahala yasa tace a a ya tashi nan da nan ya fita ya ɗebo mata ya kawo ya cika ɗayan botikin ta miƙe tana ɗaukan babban flask na ruwan zafin da Anty ta ajje mata tun jiya.