HASASHEN SOYAYYA

Hs 32

by @legendspen

_Page 32_

Tun gama wayarta da Yaya Karima ta sami waje ta zauna ta rafka uban tagumi, me ke shirin faruwa da ita kuma? Duk tsoronta kar ace Senate ba wai son ta yake ba. "Me ya kawo wanan maganar?." Zuciyarta ta tambayeta, a fili ta ce. "Yau kwananmu nawa da aure, amma har ya canja komai." Sai kuma wani ɓari na zuciyarta ya ce. "Bhatool ki yi masa uziri ko wani abu ke damunsa." Haka ta yini fama tunani. Sai wajen ƙarfe biyar ya shigo gidan, lokacin Bhatool ta ci Kuka ta ƙoshi, ko wanka ba ta iya yi ba tun tana kiran Yaya Karima ta faɗa mata bai shigo ba, har ta gaji ta fawwalawa Allah komai. 

Da sallama ya shigo cikin falon,amma Bhatool ba ta iya ɗaga kai ta kalleshi ba. "Na dawo." Ya faɗa tare da shigewa ciki bai jira amsarta ba. "Wai ni zaman me nake a gidannan ne?, wanda ya ajiye ni ba ya ta ni; me zan zauna na yi." Ta yi wa kanta wanan tambayar a fili, tambayar da ta doki kunnen Senate, bai fargaba ya ji ta kun ta ta shige ɗaki. Yana tsaye ya ga ta fito sanye da mayafi hankalinta ya yi waje gaba ɗaya. "Bhatool." Ya kira sunanta, ba ta waigo ba bare ta ba shi amsa. "Ki tsaya karki fita." 

"Wallahi sai na tafi, tun da banda amfani a wajenka." Daga haka ta buɗe ƙofa ta fita, kasan bin bayanta ya yi sai tsayawa da ya yi yana kallon hanyar da tabi ta huce. Kusan mintuna goma sanan ya fara tunanin kiran Mom, ringi ɗaya ta ɗauka tare da faɗin. "Senate lafiya dai?." 

"Mom ta tafi." Ya faɗa kamar zai yi kuka. "Wace ta tafi?." 

"Bhatool." 

"Ta tafi ina?." 

"Gidansu wai tun da wanda ya ajiye ta baya ta ita." 

"Bangane ba ka ta ita ba, wai me ya faru a gidan naka ne?."

"Mom nima ban sani ba, kawai dai....." sai kuma ya yi shiru. "Kawai me?." Ta tambayeshi. "Kawai dai...." Ya sake yin shiru. "Okay yanzu ta ina?." 

"Ta fita, ta tafi gida wai." 

"Innullahi wa'inna illahir raji'un, Senate ashe baka gama hankali ba na ɗakko maka auren 'yar mutane, mun shiga uku." Ta faɗa tana kashe wayar, tare da faman tunanin "yanzu idan Bhatool taje gida ta ce me?, tabar wa kan ta abun magana, to amma me Senate ɗin ya yi, tabbas nima ina da laifi yazo tun safe ko karyawa bai yi ba kuma na barshi anan har yamma." Wayarta ta ɗauka ta fara kiran Bhatool amma wayarta ba ta tafiya, daga nan ta mayar da kiran ga Yaya Karima, bayan sun gaisa ne take faɗa mata abinda Senate ɗin ya ce da ita, sai da Yaya Karima ta sauke ajiyar zuciya sanan ta ce. "Kai Bhatool ba ta ji wallahi, tun ɗazu nake faɗamata wani aikin ne ta riƙeshi amma ta kasa haƙura, bata zo nan ba amma bara na kira Umma na ji." 

"A'a turumun lambar Umman naku kawai." Mom ta faɗa. "Okay bara na turu." Yaya karima ta faɗa tare da kashe wayar, ta hau mita da faɗin. "Na rasa yaushe ne yarinyar nan za ta yi hankali, gaba ɗaya ko sati baki rufa ba cikin gidanki amma kin fara ficewa kice zaki tafi gida, matsalal yi wa yarinya aure a ƙanana shekaru kenan." Tana faɗan ta turawa Mom lambar Umman, sanam ta ci gaba da kiran lambar Bhatool amma ba ta tafiya. 

Umma na zaune ɗaki, wayartav ta samo ringi alamun kira na shigowa, kallo lambar ta yi ta ga babu saving a jiki a fili ta furta. "Allah yasa alheri ne." Domin tun ɗazu take jin jikinta babu daɗi. "Hello, salamu alaikum." Ta faɗa bayan ta ɗaga wayar. "Amin wa'alaiku salam, Maman Bhatool ina wuni?." 

"Mun yi ni lafiya?." 

"Lafiya kalau Alhmdlh, Maman Usman ce."

"Aouho, ya gida ya gajiyarmu?." 

"Gajiya ta biki jiki, yanaku?." 

"Alhamdulillah wallahi." 

"Ma sha Allah, na ce su Bhatool ba su zo ba?." Mom ta tambaya. "A'a gaskiyya basu zo ba, lafiya dai ko?." 

"Ina fa lafiya, kin san yaran duk kansu sai addu'a, wai ya fita baisanar da ita ba, kuma bai dawo ba sai dare shine ta yi zuciya ta tawo gida."

"Na shiga uku na lalace, wai har yanzu Bhatool ba za ta yi hankali ba ne, du-du-du kwanan ta nawa da auren shine zata kwaso jiki ta tawo gida?." 

"Ki baro kawai, abune na rashin hankali, da rashin hankali." 

"Iskanci ne kawai wallahi, ba ta zo nan ba sai dai ko gidan Yayarta ta je." 

"Ai ita na fara kira ta ce ba ta zo ba." 

"To ina ga tana hanya, zan kuwa ci ubanta." 

"Ayi hakuri dai, Allah yakawo ta lafiya." 

"Amin-amin." Umma ta faɗa. "Idan ta ƙaraso ki taɓani dan Allah." 

"Babu damuwa ngde." 

Bhatool kam na fita waje ta sami waje ta tsugunna ta fara kuka, kuka sosai da sosai take yi ɗaɗinta ma anguwar nasu babu mutane sosai, ta kusa awa guda a wajem sanan ta fara tunanin inda xata nufa. "Yanzu idan naje gida xai xama abin magana a unguwa, idan naje gidan Yaya Karima faɗa xata mun, gashi ni ba maƙwafta ba bare naje gidansu." Ta kusa awa biyu tana zaune ta kasa tsayar da matsayar inda zata amma kam ba zata koma gidan Senate ba tun da abun na shi hakane. "Bhatool." ta ji ankira sunanta, ta gane muryarsa hakan yasa ta miƙe ta fara tafiya, shi kuma ganin ta fara tafiya ya sa ya biyo ta da gudu yana faɗin. "Ki tsaya Bhatool."

Legendspen
***

Sorry for the short page🥺