AMARYAR GADO

CHAPTER 3

by @xayyeesherthulhumaerath

AMARYAR GADO

NOBLE WRITERS ASSOCIATION

AISHA SANI ABDULLAHI

Xayyeesherthul-humaerath

©️2026

 

Jan hankali: Wannan littafi ƙirƙirarriyar riga ce da aka saka wa kowace ƙaddara da ke cikinsa suna. Kada wani labari ko sirri da aka bayyana a cikinsa ya sa a fassara shi da rayuwar wani na gaske. 

 

Gargaɗi: Haƙƙin wallafar littafin na marubuciya ce kaɗai. Ba a yarda a juye shi zuwa wani harshe, ko a canza shi zuwa sautin murya (audio) ba tare da rubutacciyar yarjejeniya ba.

 

SHAFI NA UKU

 

“Ku yi haƙuri… kar ku cutar da ni, don Allah.” Ta faɗa cikin rawar murya.

 

Sandar ta sake motsi, kamar ita ce ke magana. Sai ta ji an ce,

 

“Za mu bar ki. Amma sai kin hana auren Farida da Sufyan. Domin babu alheri a cikin auren nan sam. Mu ne aljanun da ke jikin Farida. Idan kika bari aka ɗaura auren, jikinki za mu koma.”

 

Inno ta kankame jikinta, ta tura kanta tsakanin cinyoyinta tana karkarwa.

 

“A’a… an fasa! Wallahi an fasa! Ba za a yi auren ba. Ni kam, ina ni ina kiran masifa.”

 

“Kin yi alƙawari?”

 

Inno ta girgiza kai da sauri.

 

“Eh… na yi. Na rantse da Allah zan hana a yi auren.”

 

“Za mu tafi. Amma idan baki hana ɗaurin auren nan ba, za mu dawo mu aiwatar da abin da muka faɗa.”

 

“Ina roƙonku… ban isa in ja da ku ba. Ku yafe mini.”

 

Nan take aka zare sandar.

 

Inno kuwa ta ci gaba da zama a wurin. Har lokacin ta kasa motsi, sai dai leɓunanta da suke rawa tana ta maimaitawa,

 

“Ku yafe mini… haɗa husuma ba daga gareni ba… ku yafe mini…”

 

Sai da ta ji komai ya yi tsit sannan ta ɗaga kanta a hankali. A hasken fitilar ɗakin ta ga babu alamar kowa.

 

Tun daga lokacin barci bai sake komawa idanunta ba.

 

Da ta ji ana kiran sallar Asuba, ta miƙe zumbur. Ta nufi ɓangaren Baba, zani da takalmanta duk tana riƙe da su a hannu.

 

A daidai lokacin Baba Haruna ya fito daga ɗakinsa zai tafi masallaci. Da ya hango Inno cikin wannan hali, ya tsaya cak.

 

“Subhanallah! Inno, lafiya?”

 

Inno tana share majina ta ce,

 

“Uhm… bari kawai, Haruna. Ku yafe mini. Haɗa husuma ba daga gareni ba. Yau na yi gamo… na yi gamo da fatalwa.”

 

Baba ya yi saurin ƙarasawa gareta.

 

Da sauri Baba Haruna ya riƙe Inno ya shigar da ita ciki. Ya kira Mama da Farida ya ce su zauna da ita.

 

Yana shirin fita, Inno ta kira shi.

 

“Haruna… idan kun idar da sallah, ku zo gaba ɗayanku. Ina da magana.”

 

Ta faɗa cikin murya mai cike da gajiya da firgici.

Baba Haruna ya girgiza kai.

 

“To Inno, In Sha Allah.”

 

Daga haka ya fita.

 

Kamar yadda Inno ta umarta, bayan sun dawo daga sallar Asuba, gaba ɗayansu suka hallara a gabanta.

 

Inno ta yi gyaran murya, ta kalli kowa ɗaya bayan ɗaya kafin ta ce,

 

“So nake a haƙura da auren yaran nan… Sufuyanu da Faridatu.”

 

Nan take kowa ya kalli ɗan’uwansa cikin mamaki.

 

Abba Shuaibu ne ya fara magana.

 

“Wane aure kenan, Inno?”

 

“Shi dai auren da jiya na ce a yi. Yau kuma na ce a fasa.”

 

Abba Shuaibu ya ɗan yi murmushi kaɗan kafin ya ce,

 

“Inno… ai an riga an ɗaura auren.”

 

Da sauri ta ɗago kai.

 

“Me ka ce?”

 

“An ɗaura auren yanzu da muka idar da sallah, Yayane ya ce a ɗaura shi kawai, tunda dama yanzu ba wani biki za a yi ba.”

 

Kalaman Abba Shuaibu suka ji sun sauka kamar tsawa.

 

Nan take Inno ta ji wani irin mummunan faɗuwar gaba.

 

Farida da Sufyan ma suka kalli juna cike da firgici.

 

Baba Haruna ya ce,

 

“Mun dai ga bai kamata a ƙara ɓata lokaci ba. Shi ya sa muka ga a ɗaura auren kawai. Sai sanar da ke. Da Sufyan ma ban gan shi a masallaci ba, da alama makara yau.

Kifi-kifi da ido Inno ta yi, ta rasa me ke yi mata daɗi. Ta ce,

 

“Shikenan, za ku sa su dawo jikina. A yafe mini, haɗa husuma ba daga gareni ba.”

 

Ta ƙarasa tana share hanci.

 

Baba Haruna ya ce,

 

“Me kike nufi kenan, Inno? Wai me ya faru da ke ne?”

 

“Fatalwa ce ta zo ta ba ni umarni. Amma Allah na gani, ba da hannuna ba aka haɗa husuma. Sai ta biyo ni ba ni ba, tunda ni dai ban san an yi ba.”

 

Baba Haruna ya gyara zamansa ya ce,

 

“Babu wata fatalwa fa, Inno. Da alama mafarki ne kika yi saboda kin sa abin a ranki. Amma ba fatalwa ba ce. Ki kwantar da hankalinki.”

 

Inno ta yi ajiyar zuciya. A ranta tana cewa,

 

“Yoo, ana mafarki da ido biyu ne? Ni dai haɗa husuma ba daga gareni ba, Allah na gani.”

 

“Yawwa, kuma gobe za ku tare. Ba abin da za mu jira, tunda dama an kammala gidan. Kawai shiga za ku yi.”

 

Baba Haruna ya faɗa yana kallon Farida da Sufyan. Dukansu sun kasa faɗin komai, domin kowa da abin da yake sakawa a ransa.

 

Tashi suka yi, kowa zai koma gidansa. Sufyan da Farida kuwa, ban da kallon ƙiyayya babu abin da suke yi wa junansu.

 

•••

 

Gidan Alhaji Audu Mai Tangaran babban gida ne a Jihar Filato, ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, in ji Turawa Jos North. Yana zaune ne a unguwar Rimi, wanda rabin unguwar gaba ɗaya ahalinsa ne suka cika ta, tamkar wani gari ne da yake mallakinsu.

 

A tsarin gadon gidan, ba a taɓa auren bare ba. Tun kaka da kakanninsu, auren zumunci ake haɗawa.

 

Inno ita ce matar Alhaji Audu tilo. Sai ‘ya’yanta biyu maza kacal, Baba Haruna da Baba Shuaibu.

 

Baba Haruna shi ne babba. Yana da yara maza biyar da mata huɗu.

 

Sai Abba Shuaibu, yana da yara maza uku da mata biyar.

 

Sai kuma Goggo, wadda take ƙanwar Audu, da kuma Kawu, ƙanin Inno, da suke mata da miji. Su ma suna da yara maza biyu da mata uku. Duk sun aurar da yaransu ga juna.

 

Marigayi Ahmad da Farida tare da Sufyan ne kaɗai suka rage a cikin jikokin Inno. Aka haɗa Farida da Ahmad, amma Allah Ya yi masa rasuwa, daga nan kuma aka koma ga Sufyan.

 

Farida irin matan nan ce masu jiki da diri, black beauty,

amma kuma kibar jikinta sai yake boyw mata kyawunta mussamman da ta kasance bakar fata.

 sannan irin ’yan matan nan ce da ba sa ɗaukar raini ko kaɗan. Hakan ya sa tun suna yara ba ta taɓa shiri da Sufyan ba, saboda tana son a ba ta girma, shi kuma akwai sa da isa da kasaita.

 

Sufyan yana 300 Level a University of Jos, yana karantar Computer Science. Haka zalika ya iya buga ƙwallon ƙafa sosai, wanda hakan ke ba shi damar fita ƙasashe. Yana samun kuɗi sosai, wanda ke ƙara sa masa izza da jin cewa ya isa.

 

Ita kuma Farida ta kammala har Master’s dinta, sannan a halin yanzu tana lecturing.

•••

 

Dangi ya kaure da gutsiri-tsoma, ana ta surutai. Ita dai Farida, ƙara barin gidan ta yi ta koma gidan yayarta, Aunty Hadiza.

 

Shi ma Sufyan, figar motarsa ya yi kawai ya fice daga gidan.

 

A ranar aka je aka gyara musu gidan da ke unguwar, aka sanya komai.

 

Washegari da yamma, aka shirya Farida. Baba Haruna ne da kansa ya haɗa Sufyan da ita, ya kai su har cikin gidan. Ya yi musu nasiha, sannan ya jaddada musu cewa a danginsu ba a saki. Ya ce ya rage nasu su zauna lafiya, su ƙaunaci juna, domin babu rabuwa.

 

Daga nan ya bar gidan.

 

Yana tafiya, Farida ta tashi tana sakin tsaki, sannan ta galla wa Sufyan harara.

 

 

Za ta nufi ɗaki kenan, Sufyan ya dakatar da ita da faɗin,

 

“Dan dakata mana. Ke fa sarai kin san abubuwan da ke kaina sun zarce naki. Kuma ina miki albishir da cewa, sai kin gwammace wa mutuwarki a kira da sunan gawa fiye da zamanki a matsayin matar aure. Wai ma tawa? Ina zan kai ki? Gwanda ki fara kulla dammara da baƙin ciki, domin akwai alamun cewa ciwon zuciya ne zai yi ajalinki. Kar ki ga don kin cika kin batse da ƙirji kamar fanke, wallahi ko kaɗan ba ki min ba. A idanuna ma, ba ki da maraba da ɗan’uwana namiji, tsohuwa kawai.”

 

Farida ta kare masa kallo daga sama har ƙasa.

 

“Dan halak, ka fasa. In ni ciwon zuciya bai kashe ni ba, kai ya kashe ka. Yadda nake kallonka a matsayin wani ɗan taye gabana, ai ko a mafarki ban taɓa danganta ka da kalmar miji ba. Don ban jin cewa kaciyarka ma ta gama warkewa.”

 

Tana ƙarasa faɗin hakan ta wuce ɗaki, ta bar Sufyan tsaye cak, ya rasa abin cewa.

Kwafa ya yi yana maimaita abun da ta fada aransa. 

Girgiza kai ya yi kawai ya wuce daki.

 

Danna wayarsa ya fara, ya kira abokinsa Habib. Habib ya amsa cikin sigar tsokana,

 

“Ya ne, ango? Kai da na zata a yanzu ana ta harka, shi ne zan ga kiranka kuma?”

 

Tsaki Sufyan ya yi kafin ya ce,

 

“Dawa? Tir! Ai ko da wasa bana fatan wannan ranar ta zo, domin ko kaɗan ba ta cikin irin matan da nake jin daɗin mu’amala da su. Don haka ba za ta samu wannan damar ba. Amma babu shakka sai na nuna mata cewa ni ba tsaranta ba ne, sai na maidata tamkar baiwa a gareni.”

 

Habib ya ce,

 

“Kai, matsalarka kenan. Da ni ne, wallahi kwantar da kai zan yi in kwashi ragwada.”

 

Gajeren tsaki Sufyan ya yi ya ce,

 

“Na lura kana ƙoƙarin bata min rai.”

 

Kafin Habib ya ba shi amsa, har ya katse kiran.

 

Ya tashi ya shiga toilet ya yi wanka, sannan ya ɗauro alwala.

 

A ɓangaren Farida ma, tana kan sallaya ɗauke da waya a hannunta tana karatun Alƙur’ani.

 

Washegari da safe, Farida ta shirya za ta fita. Ta tarar da Sufyan zaune a falo yana aiki da laptop.

 

Ko daga kai ya kalle ta bai yi ba, ya ce,

 

“Ke, ina za ki je?”

 

Cikin kasaita.

 

Ko kallonsa ba ta yi ba, balle ta ba shi amsa. Ta buɗe ƙofa.

 

Ya ci gaba da magana,

 

“Kin manta cewa a ƙarƙashin ikona kike yanzu? Ko da yake Abba yana nan yana jiran duk wani rashin hankali da za ki yi dama.”

 

Har ya gama maganar idanunsa na kan laptop.