Page 47
💫MARYAMA💫
47.
Laluɓe na fara yi cikin duhun karaff naji na damƙi wani abu, banyi aune ba naji wannan abun shima ya damƙe ni. It happen in a sudden.
Hakan kuwa yayi daidai da dawowar wutar da ta ɗauke. a take wajen ya ƙara ɗaukar hayaniya yayin da wutar ta kasance irin mai kala kala ɗinnan wal wal wal haka take haske fuskokinmu, a gefe ɗaya kuma kiɗar da ta ɗauke saboda ɗaukewar wuta ta fara bugawa,. Wani irin gingimemen abu naji ya sauka a kaina tamkar sauƙar aradu lokacin da na daga kaina sama ina hango shi tsabar tsahon sa, a lokacin shikuma yayo ƙasa da kai hakan yasa muka hada ido. Da hanzari na ɗauke nawa idon haɗi da fara kiciniyar kwatar kaina daga riƙon da ya yi mini lokacin da wutar ta ɗauke na zo fita shiko yana shigowa.
Sai dai duk ƙoƙarina na kasa kwatar kaina saboda ba riƙon wasa yai min ba, gashi ina hango ni wata yar ficika a gabanshi dan duk da tsayin da na ke dashi amma ko kirjin bawan Allahn ban kai ba.
Tamkar mai son gano wani abu a fuskata haka yake leƙo ni niko ina cigaba da kiciniyar fita daga jikinsa. Da sassarfa chioma dake tsakiyar fili tana ta kwasar rawa ta kariso wajenmu tana fari da idanu haɗi da rufe baki da hannunta cike da mamaki ta ce, "Ohh my God, wa nake gani kamar ABDALLAH!? Sauƙar yaushe babu notice? Sunan da ta faɗa shi ya janyo fiye da hankalin rabin jama'ar dake wajen dan da ɗan karfi tayi maganar, tana kara matsowa gami da mashi alama da hannu akan ya sakeni.
Bai musa ba ya cika ni yana lumshe ido da buɗewa a lokaci guda, da sauri ta yi ƙoƙarin faɗawa jikinsa amma ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu.
A take kuwa mutanen dake wajen suka zagaye mu suna ta chanting sai GUY sai GUY...Hayaniya sosai wajen ya ɗauka kowa burinshi ya kai ga wannan da ake kira guy, ba shakka kuwa ya amsa sunanshi, Dogo ne na gaske mai kakkarfan jiki kana skin nashi jajawur ne yana da kyau matuƙa sai lebenshi da ya kasance baka wuluk da basai an fada maka ba zaka fahimci yana zukar sigaari. idan ba don girman jiki da ya ke dashi ba kamar wanda ya haɗa zuriya da samudawa , zamu iya kwatantashi da mace dan kyau
Amma kirarshi irin ta majiya karfi ne.kallo ɗaya zaka mashi ka fahimci cewa shima ya fito ne daga ƙabilar IGBO dan yadda yake kama dasu. abin da ya ɗaure man kai kuma jin an ambace shi da ABDALLAH!.
Ganin mutane sun yanyameshi na yi ƙoƙarin fita daga wajen a rikice amma karaf na ji ya ƙara damƙe min hannu gam kamar zai ɓallani. Ido muka haɗa naga ya ɗaure fuska tamau babu alamar fara'a tattare dashi.
"Cika ni mana Malam me haɗina da kai da zaka min riƙo irin na waɗanda suka yi sata?" Na fad'a jikina yana rawa kadan kadan dan wani irin tsoro yake bani,ban dauka zaiji abin da na fada ba kasancewar da hausa na yi maganar shiko bai yi kama da wanda zaiji ko zo in kashe ka ba da hausa, amma bisa mamaki na sai naga ya zaro ido waje hade da sakin fuska a karon farko tun shigowarshi wajan.
Chioma dake ta kallonmu da sauran mutanen wajen ta ce, "Guy! wannan kawata ce kuma mutumiyarku ce itama daga arewa ta zo" da turanci tayi maganar. Ba tare da ya kalleta ba ya ce " I see" Daga haka ya fara tafiya still hannuna rike cikin nashi. da yawan mutane sunyi mamaki dan sun san he's not kind of womanizers, sam baya harkar mata iyakarshi da mace tayi rawa a gabanshi ya jefa mata kudi amma yau abin mamaki ya rike mace, macen ma mai hijabi, da yake abaya ta saka kuma tayi rolling da veil dinshi....
(Anya bazamuje MARYAMA ta bamu sirrin farin jini ba kuwa? ko ya kuka gani?😀)
Tafiya mai dan tazara yayi a cikin hall din yana damke da hannuna har lokacin yayinda na ke binshi tamkar jela kamar zan kwala ihu a can gefe wajen wasu shiryayyun kujeru da ka gani kasan na musamman ne, zaunar dani yayi akan kujera daya sannan ya zauna a wacce ke gefenta yana daure fuska hadi da daura kafa daya kan daya.
Da sauri mai kula da wajen ya iso ya durkusa ya fara dibar gaisuwa kamar yaga sarkin garinsu, hannu kawai ya karkada masa da daga yatsu biyu, da gudu ya tashi a wajen ya bude wata fridge na glass ya dauko kwalaben giya manya guda biyu da babbar glass cup irin mai fadin nan ya dire a gabanshi, murmushi Abdallah yayi ya bude kwalbar ya zuba kadan can kasan cup din sannan ya matso dashi saitin bakina. Da hanzari na kawar da kaina gefe zuciyata tana bugawa da sauri sauri har kamar tana wuce ka'idar bugawarta.
"Allah ya sauwaqe insha giya, kai bakasan haramun bane shanta? gaka da suna irin na bayin Allah amma kake aikata abin da ya haramta maka".
A karon farko na ji muryarshi ta doki kunnena dan har na sadakar cewa kurma ne.
"Ke da kika kasance baiwar Allah ta gari me kike aikatawa a nan, ko kinzo wa'azin shekara ne malama?" ya fada yana kafe ni da idanu. Kamar in nutse a kasa naji tsabar kunya sai dai ba kunyarce ta fi damuna ba, irin yadda ya yi maganar da harshen hausa kamar jakin kano shiyafi bani mamaki.
"Hmmm,baki ce komai ba kin kafeni da wadannan idanun naki mas....."
Kid'ar da aka canza ne ya fara tashi a wajen kuma shiya hana Abdallah karisa abun da yai niyyar fada..Sosai mata suke rawa a tsakiyar wajen yayinda wasu ke zaune saman kujeru kamar yadda muke zaune da Abdallah, saidai sabanin namu yawanci a kujera daya suke zama mace da miji suna ta shafa da tsotsar juna, idan abin yai nisa ma sai su mike su wuce sama inda dakuna ke jere reras.
Daya daga cikin mutanen da suka shigo tare da Abdallah ne ya matso kusa gareshi yana mika mashi wani briefcase da bansan me ne a ciki ba. hannuna dake rike da nashi har lokacin ya sake ya fara kokarin bude jakar, da wannan damar nayi amfani wajen tashi tsaye zan bar wajen ya kara rikoni da sauri a fusace na juyo na ce, " Ka daina rikeni , niba yar iska bace,ban sanka ba baka sanni b....."
Sauran maganar tawa ce ta makale a saman labbana sakamakon arba da nayi da daloli sinki sinki kwance cikin wannan akwati da ke gaban Abdallah. Dum dum haka kirjina ya bada sautin amma sai nayi kokarin saisaita nutsuwata. Abdallah da bai kula da yanayin da na shiga ba ya yafito chioma dake tsaye gefe damu cike da mamakin Abdallah wanda ba iya ita kadai ba daukacin jama'ar dake wajen kuma suka sanshi ya basu mamaki a yau, da sassarfa ta kariso tana fari da idanu irin na tsoffin karuwai idan sunga maiko.
Magana ya mata kasa kasa yadda ni da nake kusa da su ma banji abin da yake fadin ba.Gyada kai kawai chioma take tana murmushi kamar kadangaruwa. Sannan ta dago tana kama hannuna, daurin dalolin nan guda daya ya dauka gami da zaro masu yawa a ciki ya bata a hannunta kana ya dau wasu dauri biyu yana mika min.
Ba karamar jarumta na yi ba wajen girgiza kaina alamar bazan karba ba ina banka mashi harara ganin wani kallon da yai min na baki da hankali. dai dai kunnena ya matso ya ce, "Abdallah baya kyauta a ki karba,so kar ki batawa kanki lokaci yan mataaa.
Wani irin yarrr na ji jikina ya yi,tun bance komai ba ya bude hannuna ya sanya kudin ya mayar ya rufe sannan ya kalli chioma da wani yare wanda na fi zaton igbonci ne ya mata magana dan haka banji abin da yace ba, ta dai kama hannuna sosai tana gyada mashi kai sannan muka nufi hanyar fita daga hall din, car keys Abdallah ya jefawa daya daga cikin boys nashi dake zagaye dashi, cike da kwarewa ya cafe keys din da idanu yai mashi magana cikin girmamawa ya ce, "Yes oga" sannan yabi bayan su Maryama da dan gudu gudu, tunga naja lokacin da muka fito ina kallon siyama idanuna kamar zasuyi aman wuta, da turanci kamar yadda muka saba hira da ita na ce, "Nayi nadaman biyoki wajen nan chioma, bansan haka yake ba da bazan zo ba."
Cikin dariya ta ce, "Da ba ki zoba da kinyi missing kuwa, dan ina tabbatar maki kinyi dacen da mata dubu basuyi ba cikin minti daya, haduwarki da Abdallah tamkar yankewar duk wani damuwa ne a tattare dake, ke din mai sa'a ce, dubban mata ke kawo mashi kansu a kyauta don kawai ace suna alaka dashi ma amma ko kallo basu isheshi ba sai gashi ke within two minute da alama kin tafi dashi gaba daya, kinsan nawa ne wannan kudin dake hannunki idan aka canza shi zuwa naira kuwa? To gwara ma ki kwantar da hankalinki kici arziqi ki yi rayuwa mai inganci atoh.
Isowar yaron Abdallah wajen ne yasata yin shiru da zancen da take yi tana cewa "muje zai kaimu gida a motar oganshi, dan yace daga yanzu bazaki kara hawa taxi ba.
A raina nace, "Ikon Allah, wayaga shiga da iyawa, shi baisan ina da mota ta kaina ba? yayinda nake ta juya kudin dake hannuna ina ta kidaya nawa suke idan an canza su kamar yadda chioma ta so fada min?...Koda muka iso gida ma kusan kwana chioma tayi tana bani labarin Abdallah da irin dukiyar da ya mallaka ta kuma sanar min a DUBAI yake da zama amma yakan zo nigeria time to time, ta sanar min shima musulmi ne kuma mahaifinshi dan arewa ne mahaifiyarshi ce yar nan kuma ta kasance kabilar igbo, musuluntar da ita baban Abdallah yayi ya aureta zuwa kano,yan uwanshi sun nuna adawa da hakan sosai amma Allah yace akwai rabo a tsakaninsu, don haka ta haifi Abdallah, yana da shekaru biyar a duniya uban ya rasu, tsananin kiyayyar da danginshi ke nuna mata yasa dole ta tattara danta cikin dare suka gudu wannan shine dalilin kasancewar Abdallah a nan.
Duk hirar da chioma take min bana fahimta, inda hankali da lissafi na yake daban. Shigowar kira cikin wayata ne yasa hirar tata tsayawa ta juya min baya tana kwanciya,Sadeeq ne akan wayar dan haka na dauka tare da yin Sallama ina lumshe idanuna gami da dafe goshina dake sarawa tsabar damuwar da na ke ciki. Daga daya bangaren ya amsa sallamata tare da fadin "how are you?".
"Ina lafiya, kaifa?" "Alhamdulillah just missing you".Cewar Sadeeq dake aiki a laptop dinshi waya kare kunnenshi.
"Hmmm,yaushe zaka dawo?"
"Kema kinyi kewata?" ya tambayeni ba tare da ya bani amsar tambayar da na mishi ba. Murmushi na yi har hakwarana suna bayyana na ce ina rufe idanuna, "Na yi kewarka mana sosai" Wani irin dadi ne ya mamaye zuciyar Sadeeq yace, "Then dole in dawo dan ki ganni, but the problem is, ai kema bakya nan, ba kince min gida kika koma dan yin hutu ba?".
Zaro ido nayi dan shaff na mance da nace mishi na koma Adamawa yin hutu a can, amma sai na wayance da fadin, "Ai idan ka dawo atleast nasan muna kasa daya da kai, ko tari na yi daga Adamawa zuwa patakwat ai zakaji amma kaifa kana har America". Na kare da shagwabar da yake halittata tin asali."Beside hutunma ya kusa karewa ai".
Ajiyar zuciya Sadeeq ya sauke kasa kasa yace, "Dole inyi wani abu kafun yarinyar nan ta halakani".
"Me kace?" na tambaya dan da gaske banji abin da ya fada din ba..."No bance komai ba dear,kawai ki kwanta ki huta sai zuwa safiya zamuyi magana yanzu wani aiki ya rike ni sosai. Ohk good night and sweet dream."
"Ohk byeeeee" Na fada ina sauke wayar. Tun bayan da suka gama wayar sai ya kasa cigaba da ayyukan da yake yi, yana jin son yarinyar yana bin jini da bargo na jikinsa yana zagayawa, dole ya tura laptop din gefe guda ya kishigida jikin kujerar da ya ke kai a cikin garden na hotel din da suka sauka kasancewar su a lokacin safiya ce ba dare ba. Tunani ya fara na maganganun Mommy akan Maryama wancan karon I have to do something, ya fada a zuciyarshi yana rufe idanu.
Wasa wasa alaka mai dan kauri ya shiga tsakanina ni Maryama da Abdallah cikin sati biyu kacal dan kullum sai yazo wajena, tun ina tsoronshi dan har ga Allah yanayin zubin suffarshi yana bani tsoro, har na fara sakewa dashi, duk abin da zai yi da Umarni yake magana, wannan na lura dabi'arshi ce, ma'ana yadda yake so haka za'ayi, yana yawan daukata mu fita gari wurare musamman joint joint da abokanshi ke zama ya ringa nuna masu ni cike da alfahari da dagawa, and he's a little bit touchy. Sai dai tun randa na cire tsoronshi na zazzaga mishi masifa bai kara rike min hannu ba, dama yawanci hannuna yake son tabawa bansan mai yake ji a jiki ba, daga ranar kuwa bai kara tabawa ba sai na lura ashe tsoron nashi da nake ji ma kwarjini ne kawai yake min ba wani abu ba.
Duk sanda mukayi irin wannan fitar kuwa ba kananan kudi nake dawowa dashi ba, dan dagashi har abokan nashi mahaukatan kudi suke bani da sunan wai insha chokulate, zuwa yanzu na mallaki kudin da bazasu gaza million biyar ba cikin sati biyun da muka hadu kawai. Saidai maganar soyayya bata taba shiga tsakanina dashi ba.
Shirye shiryen komawa makaranta muke yi babu kama hannun yaro dan sati mai zuwa zamu koma, duk wani abun bukata Abdallah ya sai mana ni da Chioma babban mall ya kaimu dama muka sai komai da muke so harda abinda bamu taba amfani dashi ba ma dan ganin arha...Ana saura two days mu koma Muna waya da Sadeeq yake tambayata yaushe zan dawo. Kamar munafuka na yi kasa da murya na ce, "Gobe Insha Allah zan tashi".
"To Allah ya kaimu ki kular min da kanki sosai plsss sannan zaki ga alart sai kiyi kudin flight ticket. nima Insha Allah in the next 5days ina hanya"
"Allah ubangiji ya kawo ka lafiya da aminci,na gode da dawainiyar da kake yi dani kullum babu gajiyawa."
"Wannan ba dawainiya bane pretty, ina yin abin da yake dole nane akan ki so ki daina gode min plsss"
"To na gode"
Haaan kin kuma kenan, dariya mukayi a tare dukkanmu, muka dan kara hira yawanci akan karatu nane, sai mutanen gida da yake tambayata, a cewarshi wai ina mashi rowar iyayena naki na hadasu su gaisa. Bayan yanke wayar da wasu yan mintina naga alert ya shigo min, naira dubu dari biyu kudin Nigeria Sadeeq ya turo min, amma abin mamaki sai na samu kaina da raina kudin da jin cewa ai nafi karfinsu yanzu tunawa da irin barin mahaukatan kudin da Abdallah yake min.
Da wannan muka koma makaranta muka daura karatu zango na biyu, farin jini kuma a wajena sai abun da ya karu kowa so yake yayi abota dani baga student yan uwana ba, baga malamai ba, Amma babu wadda nake kulawa harkokin gabana kawai nake yi.
Sadeeq ya dawo kwanaki hudu da suka gabata kuma yazo har cikin makaranta ya ganni, sosai yaji dadin yadda ya sameni din nan ya bani tsarabar da ya yomin akwati guda shake da dogayen abaya kala kala da perfumes shima different colours a cewarshi babu macen da abaya ke yiwa kyau a Duniya kamata.
Yau ma kamar yadda ya saba zuwa kusan kullum muna zaune gaban katuwar motarshi muna hira wanda rabi da kwata duk shi yake yi kuma akan kasuwanci ne, ni amsata bata wuce ehh ko ah'ah dan hankalina bai nan, kwannan nan ina kewar gida da duk jama'ar gida. Ina yawan tunanin Hamma Jay da tambayar kaina ko a wanne hali yake yanzu?.
Kamar daga sama naji saukar kakkauran muryarshi ya na fadin, "Da zaki amince sai ki bini mu tafi Dubai din tare idan kina so ma sai ki cigaba da karatunki a can "
"What?" na tambayeshi a dan firgice.
"Yess ki bini mu tafi tare zaki na taimaka min wajen harkokin kasuwanci na, idan kinason cigaba da karatunki ma sai ki samu wani university acan"
"Amma wasa kake min ko Abdallah?" na tambayeshi bakina a bude cike da mamaki...
Babu irin wannan wasar a tsakaninmu baby girl, kije kiyi shawara idan kin amince fine" Kwakwalwata ta kasa amincewa wai ni Maryama ake yiwa tayin tafiya Dubai, dubai shine dream city dina yanzu ga dama ya samu
Washe gari kuwa banyi kasa a guiwa ba na kira Sadeeq aka yi sa'a weekends ne yana gida na sanar mishi ina son muyi magana cike da damuwa yace, "wani abu ya faru ne pretty? ko dai ni inzo school din naku?".
Nace "ah ah basai kazo ba nima ina kan hanya yanzu, bayan kamar one hour kuwa na iso bayan nayi wanka na shirya cikin daya daga abayas din da ya kawo min light brown nayi kyau sosai tamkar dan ni akayishi dama.Yana zaune palo sanye da kayan sport da alama daga wajen exercise yake, damuwar dake zuciyarshi ta kasa boyuwa a fuskarshi, tun ban gama zama ba yace, "what happen pretty? duk kin kwaba min lissafi na kin daga min hankali, sai na ga ke kuma hankalinki a kwance kinsan irin damuwan da na shiga kuwa? na dauka something bad ya faru dake ne fa"ya fada fuskarshi dauke da madaukakiyar kulawa.
A take sai na ji jikina yayi sanyi, anya zan iya fada mishi abin da nazo dashi kuwa?
"Shikenan idan baki sanar dashi ba kinga sai ku zauna zuwa dubai ya wuceki, dubai fa Maryama," zuciyata ta tunatar dani.
Kinyi shiru pretty say something mana, cike da rashin kuzari na yi kundunbalar fadin, "Ina son zan je Dubai!"
"Doing what a Dubai Maryama?" ya tambayeni yana mai tsare ni da idanu. Rawa harshe na ya fara cikin kidima sakamakon yadda idanunshi ke yawo a kaina nace, "Zan fara kawo kayane na siyarwa irin na mata haka"
"A ina kika samu kudin zuwa dubai saro kaya? ya kuma mulmulo tambayar ya jeho min.
Still stammering na ce, "Am ehh ina dashi ne dama."
Calmly yace, "Ya karatun naki kuma?"
Wannan karon with full confidence na ce, "Zan cigaba da yin karatun a can"
Da hanzari Sadeeq ya mike yana kallona hakan yasa nima na mike da hanzari ganin kamar zai kai mini duka ne, "This is madness, actually madness. how dare you Maryama, wani irin banzan magana kike fadamin haka, are you on your right senses?"
A zafafe yayi maganar, dan haka nima da zafin nace, "ba wai shawara nazo nema a wajenka ba fa, nazo fadamaka abin da zan aikata ne dan kasancewarka wanda nake karkashin sa a nan, karatu kuma bani da interest akai yanzu, business zanyi kuma Dubai zan tafi, na fada cikin daga murya nima.
"Ah'ah no Maryama, kar ki mini haka dan Allah, Kar ki gujeni. Idan ma karatun ne bakya so shi ke nan na bari amma plsss kar ki bar kasar nan ki zauna muyi aure duk duniyar da kike son zuwa zan kaiki plsss don't go na rokeki, I love you with all my heart, a can't live without you, and i choose you over my parents, na kijin maganar mommy na saboda ke, plsss don't let go.
Da karfi karfi kirjina ke duka, idan na cigaba da sauraran maganganun Sadeeq tabbas zai yin nasara a kaina dan sosai ya bani tausayi, amma kuma inaji a jikina babu abunda zai hanani tafiya Dubai din nan da na samu a sama, dan haka batare da nakara kallonshi ba na dauki jakata na nufi hanyar fita.
"Plsss MARYAMA," Shine abin da Sadeeq ya furta kafun a hankali ya fara ganin palon yana juya mishi ya rinka kallon wasu stars suna haske da walkiya, a hankali ya kai bisa kujerar dake bayanshi ya zube yaraff kamar kayan wanki...
Hooooo MARYAMA, wai MAZA nawa kike son kaiwa kasa ne?.