JA DA BAYA...

The stubborn lady

by @meelahbazata978

*JA DA BAYA...*  
*Book 1*  
*Page 14* ✍️


***


Da sallama yashiga bangaren hajja tsohuwa Mai dattaku da nagarta.  
Da fara'a ta amsa tana "lale da Mai babban suna", zama yayi kasa kusa da kafarta Yana fadin hajja barka da yamma ya gidan?  
Alhmdlh" ta fada tare da da shafa kansa tana cewa alhmdlh Muhammadu.  

Muhibba ce ta tashi daga kwancen datake akan kujera ta gaida Abbah.  
Da kulawa ya amsa mata tare da tambayarta ya aiki.  
Shafa kafar hajja yayi Yana cewa "hajja yau naga kafar ma tadan tasa, kodai zaa koma Egypt dinne?  
Kasantuwar duk lokaci suna kaita adubata sabida matsalar kafarta.
A'a ta furta tare da fadin "Ina ni Ina yawon kasashen nan Muhammadu? haka ma ai da sauki ai ankwana biyu Kuma,"tafada da murmushi afuskarta"sannan jiya ma Mahbubu yakawomin Wani magani Kuma naji dadin kafar Dana shafa".  

To hajja Allah yakara lfy da Nisan kwana bari naje zan Dan leka innah kafin magriba.  
Addua taimasa sosai tare da Kara masa magana akan aikinsa don ita Kam bata son aikinnan nasa tun farko shiyasa duk sanda yashiga seta masa addua akan aikin, da Ameen ya amsa Yana fita a dakin.  

Sakko wa muhibba tayi daga kan kujerar tana dawowa kusa da hajja ta zauna, tare da fadin "hajja dagaske fa inasonshi dan Allah kigayawa Abbah nasan zai auramin shi.  

Kamar yadda kikaji uwarki tace ki hakura shine yafi Miki alkhairi, Mai sunan alhaji(Ayzaan ) Wani sanin bayida dadin shaani, tunda ba shiga sabgarku yake ba, Dan haka kiyi hakuri kinji." tafada cikin sigar rarrashi.  

Jinta kawai muhibba takeyi Amma aranta ta kudurce ko ta halin kaka se ta samu Ayzaan. Allah kadai yasan kaunar datake masa azuciyarta, shiyasa ta tsani Inarah Bada wasaba ganin irin yadda Ayzaan yadau komai nata da muhimmanci. Ko ganinsu tare tayi setaji kamar taje ta kasheta, gashi ita iyakar gaisuwa kawai itace a abinda ke hadasu se ta kwashe kwanaki ma bata ganshi ba indai ba tana bangaren inna ba hakan yasa yanzu Tama Fi zama agurin innah.  

Zaune yake gaban hajiya innah tsohuwar arziki sundade suna tattaunawa amatsayinta na mahaifiyarsa Kuma ta bashi shawarwari sosai ko game da aikinsa da rayuwarsa.  
Tabbas uwa babban jigo ce duk kuwa girmanka, da shekarunka.  
Acikin hirar ne take ce masa "wai nikuwa Yaya(haka take kiransa) Wani Hali ake ciki game da lalurar Mai sunan alhaji? Ana samun cigaba kuwa ?  
Hmmmm numfashi ya sauke tare da fadin "munadai ta addua akai innah, sannan yau inshallah zuwa anjima zan Kara bincikar mahbub nagani, sannan karshen watannan zaiyi tafiya inyaso Sena sa yakara zuwa abincika mugani".  

Allah yasa adace a wannan karon ubangiji ya dubi rayuwar wannan yaro" ta fada cikin damuwa.  

Abbah ne yace "innah Ina tinanin Ayzaan ma bazaije ba tun bayan bayanin likitoci dakyar ma yayarda aka daurasa akan wasu magunguna.  
Sannan Sau uku Ina matsa masa muka koma can Egypt aka dubasa Amma Babu sauyi shiyasa nikaina na sare Innah nadau wannan kaddara, Amma Ina tausayawa rayuwar sa sosai, babban damuwata innah shine abinda muke ta buya, dazu karkiga rigimar da ma mamana tayi akan wai wasu yanmata sunce suna sonshi, innah kinga ko Nan gaba akwai damuwa Inarah ta Isa aure, dole zasu rabu Amma na Lura rabuwarsu ba abune Mai sauki ba, gaba daya Ina tausaya musu".  

Kafin ya Kara Bude Baki suka tsinkayi sallamar Abbie yana karasowa falon.  
Aa Yaya barka kananan eh Ahmad karasowa yayi ya zauna kusa da kafar innah kamar yadda yayansa yake zaune kusa da kafarta, innah munsameku lafiya?  
Lafiya lau autana ta fada tare da Shafa kansa.  
Cigaba sukayi da tattaunawa game da matsalar ta Ayzaan da Kuma wasu sauran batutuwan.  

Lokacin sallah ne yasa suka Mike tare suna wa innah se anjima tare da fita daga dakin. Kallonau tayi cikin tsananin kauna da Kuma tausayawa, gwanin shaawa haka suka jero.  
Haduqa sukayi da Mahbub da Ayzaan Wanda Suma da alama masallacin zasu duk jallabiyace ajikinsu. Ayzaan milk Colo mahbub baka sunyi matukar kyau acikin rigar.  
Karasawa sukayi gaba daya suna tafiya gwanin sha'awa zuwa masallaci.  

Bayan dawowarsu daga masallaci kowa bangarensa ya nufa. Ayzaan da Mahbub dama bangaren inna sukayi gaba dayansu acan suka tadda kusan duk yan matan gidan muhibba, hibba, Inarah, najlah, khairat, zaune suke duk suna ta Hira a sun cika dakin.  
Amma muhibba ita jiran shigowar Ayzaan takeyi, haka itama najlah. Sam Babu jituwa tsakanin najlah da muhibba, sabida kowa Yana son Ayzaan, shiyasa a hirarsu ma hibbah ce se khairat da inarah suke hirar.  

Da sallama suka shiga falon innah datake zaune Saman sofa Tana Jan carbi, amsawa tayi tana fadin "maraba da zuwa mazan fama, wadannan yayan gasu duk sun cikamin falo da hayaniya barinma aku sarkin surutu", tafada tana kallon Inarah da ta tabe fuska Dan tasan da ita ake.  
Dariya suka tuntsire da ita, suna kallon Inarah wacce tafara matso kwalla.  

Fitinanniya sarkin rigima, aikinki kenan kuka yar kauye kawai mahbub yafada hakan Yana mata gwalo Dan yasa yanzu zasu raba Hali da Ayzaan.  
Aikuwa Wani kallo da Ayzaan yayi masa besan sanda dariya ta kubce masa ba, bayan ya tsagaita da dariyar ya Kalli Ayzaan Yana fadin "sedai kallo dai Amma bazan bugu ba ehheee".  

Ita kuwa gwanar rigimar bilhakki take kokarin fara kukan nata ma sabo.  
Dakyar yabude Baki yace "chuchu kibarshi zan rama Miki".  
To zakina agaban yacemin yar kauye yakarasa maganar da sa kuka.  
Eh nafada yar kauye inji mahbub Yana sake mata gwalo.  

Innace tace "wlh kafita idona mahbub inkasa yarinyar Nan kuka ranka zai Baci kyaleshi" takwara tafada da sigar rarrashi.  
Ba ruwana Dake bakece kika janyo yacemin yar kauye ba, bayan kince ma nacika surutu" tafada tana sake matso kwalla.  

Karasawa kusa da ita Ayzaan yayi ya dago ta tare da goge mata fuska da handky din din sa "ki kyaleshi kinji zamu rama, kidena Mai kuka".  
Jinjina Kai tayi tace "to ka ramamin mana".  
Kallon mahbub yayi yace "Dan kauye kazami".  

Dariya ta kyalkyale dashi cikin Jin dadi tana kama hannunsa ta buya tanama mahbub gwalo Wanda yayi kanta kamar zai bigeta.  
Rankwashi Ayzaan yakai masa ya kuwa sameshi tabe fuska yayi Yana kallon Inarah yace "Sena rama zamu hadu ai".  

Dariya Inarah takeyi sosai ganin yadda mahbub ya tabe fuska tace "Yaya kaga fuskarka kuka" tana Kara fashewa da dariya.  
To tunda kin hakura Kuma anarama Miki seki dakko abinci kuci, innah tafada tana kallon Inarah.  

Muhibba tace azuciyarta tacika da bakin ciki ganin har zuwa lokacin hannun inarah Yana cikin na Ayzaan.  
Dakyar ta iya Bude Baki tace "Yaya barka da dare" barka shine kadai a binda Ayzaan ya furta Yana Jan hannun inarah zuwa gun cin abinci.  

Mahbub kuwa cikin kulawa yawaiga Yana amsawa tare da kallon hibbah Yana fadin "ta kusa da ran rufe fuska tayi cikin Jin kunya tana murmushi tare da fadin "Yaya barka da zuwa .
zama yayi kusa da ita yace zo muje muma muci abinci, waccen fitinanniyar yar uwar taki tanason cajamin Kai kidinga mata fada ,tacika rikici".  

Yaya ni naci abinci na koshi, tafada cikin Jin kunya.  
Yanzu ni Zaki ciwa, oya tashi kizubo kizonan muci.
 tashi tayi ta nufi kitchen din innah.  

Inna yarage sauran muhibba da najlah azaune. Tashi najlah tayi batare da tace komaiba cikin fusata ta fita a bangaren na innah gaba daya.  
Innah na magana bata ma jiba kawai fita tayi cikin tsananin bakin ciki da alwashi kala kala aranta.  

Karshe itama muhibba haka taciga da azabtar da kanta ta hanyar kallon Inarah da Ayzaan Wanda suke cin abinci cikin kwanciyar hankali.  
Tana zaune batasan kwalla na zubo mata ba seda mahbub ya kalle ta yace "lafiyarki muhibba kike kuka?"  

"Bakomai ta furta tare da mikewa tana shigewa bedroom din innah".  
Inna ta furta "kagamin yara kwana biyu duk sunkoyi nukufarci, aita magna suyi shiru, duk zakizo kusameni ai"  

Haka dai ranar zaman bangaren inna baiyi wa wadannan mutun biyu dadi ba.  
Shigar muhibba dakin kuka ta fashe dashi sosai take kuka. Allah yasani tana kaunar Ayzaan ba kadan ba Amma shi ko kallonta batajin yataba Yi Sau biyu, tanajin inama itace tasamu kulawar da inarah ta ke samu agaresa, shiyasa har zuciyarta yanzu takejin bata kaunar Inarah, Kuma taci burin ko ta halin yayane seta raba Ayzaan da Inarah, dole ma ta auri Ayzaan.

Bayan gama cin abincinsu tashi sukayi tare da yiwa innah sallama suka nufi bangaren Ammie se da ya shiga yarakata ta kwanta ,sannan yawuce bangaren su.
Dama shi mahbub  yadade da fita Dan daga asibiti aka kirasa Kuma asibitin  ya wuce tunda direct tunda 
emagency ake nemansa.