SANADIN HIJIRA

Page 45/ 46

by @ummufadeela01

*SANADIN HIJIRA


     BY
Ummu Fadeela
Chapter.... 45/46


Tamkar kanshi zai fashe yake ji, ga tunaninshi da ya tsaya cakkk. Duk likitancinsa gudu ya yi ya barsa da empty brain, ga kukanta da yake ji tamkar saukar tafasashen ruwa a jikinsa. Badar tana takure a edge na gado sai kuka take kamar ranta zai fita. Tun bayan abun da ya faru komai ya kwance mata; tabbas ta fahimci wani abu ya gano, shi yasa ta zage tana kuka amma bai kulata ba. Wata dabarace ta fado mata, ta hantsilo daga gadon da hanzari, ko dar bata ji ba ta fadi gabanshi tana rike kafafunshi.


"I am sorry Sojana! Ka tashi ka dakeni idan har zaka huce. Beat me, Sojana! Ka dake ni don Allah, bana son ka yi shiru kuma. Ka min hukuncin da duk kake so matukar zaka yafemin, duk da cewa ba laifina bane. Ba laifina bane Soja, kaddarace ta fada min tun ina yar shekara goma a duniya. Ban yi zaton hakan zai janyo min matsala ba. Beat me, Sojana!" Ta fada tana janyo hannunshi da bugawa a kanta. "Kaway abun da na sani shi ne ina sonka. Ina sonka kuma zan iya zama da kai cikin kowanne hali ka samu kanka, ko da ace ka rasa sassan jikinka ne zan sadaukar da lokacina in zauna da kai. Ina sonkaaa Sojanaaaa! Kaddarace, kaddarace ta afka min!!!"
Take jikinshi ya yi wani irin sanyi, nauyin da zuciyarshi ta yi ta dan sassauta. Me yasa bai tuna hakan ba tun da farko? Amma al'amarinta bai kama da fyade ba tunda... Fadawa ta yi kanshi still tana fadin ka dakeni idan zaka huce, gaba daya ta rikice ta birkita mishi kwakwalwa ta hanashi space na yin tunani. Kafadunta ya kama, wani irin tausayinta yana maye gurbin haushinta da ya fara ji. Rinannun idanunshi ya sanya cikin nata, "Garin yaya hakan ta faru? Me ya faru? Me yasa baki taba sanar da ni ba, da sai in da karfina ya kare wajen kwatar maki 'yanci?"
"Sorry Sojana, ban san hakan zai janyo min matsala ba. Na dauka tun lokacin da abun ya faru shikenan ya wuce, ashe bai wuce ba, tabone na har abada. Abun ya faru ne lokacin ina gida farko-farkon rasuwar Mama kafin Anty ta daukeni, wata ranar asabar..." Wani irin karya Badar ta yanko ta mulmula ta jefawa Al'ameen. "Wannan shi ne abun da ya faru. Sun zalunceni kuma har yau ko mai kama da su ban kara gani ba." Ta fashe da kukan da ya fi na farko tana tuttura kanta cikin jikinshi. Kam-kam ya matseta yana jin zuciyarshi kamar zata tarwatse. Da ace zai ga wadannan mutanen, babu abun da zai hanashi sanya bakin bindiga ya dauke kansu har lahira. "Shhshhhshst! Kukan ya isa haka, bana son kuka, you know."
Da wannan Badar ta yi nasara a kan Soja; ya dauki yarda da amana ya damka mata. Ita kuma ta linka soyayya gareshi, wani lokaci tamkar zata tayashi numfashi haka take kula dashi. Dama zuciya tanason mai kyautata mata, dan haka Al'ameen ya sakankance ya zama ita, ta zama shi. Ta kowanne bangare kula take dashi; idan yana gida suna manne da juna, babu wanda bai shaida irin tarin kaunar da Badar take wa Aminu ba. Idan yana barrack kuwa, suna manne da Saudat da sunan zata tayata kwana, su ta taba-tabe juna abunsu. Cikin lokaci kadan Badar ta kara zama uwar mata kamar wata giwa, sai narka uban kiba take, hankalinta a kwance.
Sannu a hankali kwanaki suka fara rikidewa zuwa satittika, sati ya koma wata har suka cika wata shiga da aure. Wani matsalan da Badar ta fara fuskanta shi ne na rashin sha'awar Al'ameen kwatakwata; sometimes sai ya yi ta mata magiya, watarana ma da karfi yake karban hakkinshi idan ta kureshi. Abun yana damunta; tana bukatar kasancewa dashi amma when it comes to mu'amalar aure sai ta ji baya kore mata kishin ruwarta ko kadan, amma idan suna tare da Saudat kamar mayunwaciyar zaki take komawa. *(Badariya abu biyu basa gamuwa waje guda kuma duka su biya bukata).*
Abun ya fara bata tsoro duk da sojan yana mata kawaici. Ta fara dagewa da bankawa cikinta magungunan mata; duk inda ta gani zata yi oda, both na gargajiya da na bature, amma a banza. Har China Badar tana odan organic herbals nasu amma shiru, abun ma kamar daduwa yake.
A gefen Abeey kuma ya gama dasa bomb nashi, lokacin tarwatsewa kawai yake jira. Umma ma ta gama hada makaman yakinta...
A fusace ya ce, "What do you mean ne Badar? Or you want me to look for wata macen a street ne, ehyeem? Ki zaki kawomin kanki sai kin kai ni bango, kuma ki matsa kina zarar ido, me hakan ke nufi ne?"
Sosai jikinya yake rawa tana cigaba da kuka kamar zata shide, "Ban sani ba Sojana, nima ban sani ba. Ina jin kamar ba ni da lafiya wani lokaci, kuma kamar ba ni da hankali, haka nake ji." Cike da muryar kuka ta kare maganar. Janyota ya yi kusa da shi, ya dauki rigar baccinta ya mayar jikinta. Yana kallon cikin idanunta, "Yaushe rabonki da ganin al'adarki?"
Dan jim ta yi kafin ta ce, "Kwana goma da ya wucene." Fuskarta ya kama, ya bude idanunta da hannu biyu yana kallon cikinsu, sai kuma ya sake ya kamo tafin hannunta yana kare musu kallo. A hankali ya dan zame rigar jikinta hadi da kama kan nipple nata, nan ma ya dade yana kallonsu sannan ya sake yana sauke ajiyar zuciya. He thinks ko ciki gareta, canjin hormones ya sa take gudunshi, amma ya ga babu komai...
"Sojana, ba ni da lafiya ko? Ko asibiti zamuje?"
"No, yi kwanciyarki. Da safe zamu duba yiwuwar zuwa asibitin."
"To sai mu ce masu me idan mun je?"
Lakace hancinta ya yi yana kakaro murmushin dole, "Sai mu ce masu matata tana guduna a shimfida." Zamewa ta yi tana kwanciya dan wani abu take ji yana tsungulinta; kamar ta fira ta ganta kusa da Saudat haka take ji, ko zata samu saukin tashin hankalin da ke taso mata. Sosai Badar take daurewa, shi ma a nashi bangaren jarumta kawai yake yi. Bayan shudewar lokaci ya ji kamar ta yi bacci; a hankali ya zame jikinshi daga nata ba tare da ya yi making wani sound ba ya fita a dakin. Saman doguwar kujera ya kwanta rigingine, ya yi folding hannunshi kan kirjinsa, bai dade ba bacci ya daukeshi.
Tun da ya fita a dakin ta bude idanunta, sai uban zufa take hadawa. Kamar wacce aka tsikara, ta mike ta fara zagaye dakin tana faman cizar lebe kamar mai nakuda. Daga karshe saman tayils ta kwanta, sanyi wajen yana ratsata, da kyar wani wahalallen bacci ya dauketa...
Al'ameen ya dade zaune dafe da kai a kokarinshi na son fahimtar abun da mafarkin ke nufi. Karo na barkatai kenan da yake irin mafarkin. "Ina take? Wanne hali take ciki?" Ya yi wa kanshi tambayar da babu mai ba shi amsa. Komawa dakin ya yi daga karshe, nufar Badar da ke kwance rub da ciki ya yi, da kyar ya iya dagata tsabar weight dints ya mayar saman gado. Har asuba ya yi bacci bai kauracewa idanunshi ba; daga karshe ya mike, wanka ya yi gami da dauro alwala ya fara nafilfili har asuba ta yi ya wuce masallaci...
### SPAIN
Tun bayan da na rasa Maahh dita, ban kara rayuwa cikin dan karamin farin ciki kamar zamana gidansu ba. Babu tsangwama, babu kyara, babu yi, babu bari. Sai wani kula da tattali na musamman da Mom take bani. Jack ne kawai matsalata a gidan, shi ma wani lokaci ina dadewa ban ganshi ba; sai a bakin Lisha nake ji bai cika zama a kasar ba, suna yawan fita kwallo a kasashen waje. Idan akwai abun da suke bani tsoro, to idanunshi ne. Tunda ya fahimci hakan kuwa yake yawan bina da ido; da zarar mun hada ido zai zarosu, ni kuma in takure waje daya ina kyarma. Aiko ya dinga dariya kenan, wani lokaci har da hawaye. Bai kara attempting taba ni ba tunda ya dawar da ni gidan, amma duk inda na bi idanunshi a kaina, har na daina zaman palon na gwammaci in ta takurewa a daki ni kadai.
Sallah kuwa kintatar lokaci kawai nake ina yi hadi da na neman yafiyar Ubangiji. Sau uku suna kaini wani hadadden asibiti ba tare da na san dalili ba, likitocin su dinga sanyani cikin injuna kala-kala ana min gwaje-gwajen da ban san na menene ba. Ni dai bani da bakin tambaya, bani da gata sai na Allah, kuma na tabbata duk yadda ya yi dani shi ne daidai.
A zuwanmu na karshe asibitin, na ga Mom da likitocin suna ta taya juna murna bayan an fito da ni daga dakin gwajin, kuma an bani wata zungureriyar takardar da ban san na miye ba na sanya hannu a kai, bayan na ga Mom da Jack (da na kasa gane yanayinshi) duka sun sanya hannu a kai su ma. Sannan kasancewar zama ya yi zama, na dan fara iya fahimtar maganarsu har na ji likitan na fadin, "Congratulations Madam Mareyya! Tabbas wannan shi ne daidai da kashin Elisha. Muna saka ran nan da sati daya za a yi aikin dashen, kuma nan da wata biyu yarki Elisha zata fara takawa da kafafunta. Congratulations once again!" yana miko mata hannu. Hannun ta mika mishi ita ma suka gaisa, dukkansu suna dariyar jin dadi.
Faduwa kawai gaban Jack yake yi, bai jira sun gama maganar ba ya fita office din. "Idan an yi wa Elisha dashen ta fara takawa, ita kuma yarinyar fa?" Ya tambayi kanshi daidai lokacin da muka fito, Mom sai dadi take ji. Ba wai na gama fahimtar maganganun likitan bane, amma jikina ya fara ba ni akwai wani abu a kasa tabbas.
Mom ce ta zo wucewa hannunta dauke da wani karamin bowl da spoon a ciki. Kallona ta yi sadda ta ji landline dake saman table ya dauki kara, "Daughter, mikawa Jack wannan yana cikin garden." Bowl din ta ajiye da nufar wayar. A hankali na tsugunna hadi da dauka na fita, kamar kazar da kwai ya fashewa nake takawa. Yana zaune cikin garden din karkashin wata bishiya mai kyau da laptop a kafarshi. Tunda na nufoshi ya dakata da abun da yake yana kallona. Saura kwana hudu a yi wa Elisha aiki, hakan na nufin ita kuma saura kwana hudu ta daina tafiya ko ma a rasata gaba dashi. Take gabanshi ya yanke ya fadi; irin yanayin da yake yawan ji kenan a duk sanda ya tuna hakan.


Daddadar muryarta mai kama da busar algaita ce ta ratso kunnenshi cikin sallamarta da bai san me take fada ba. Hannu ya sa ya amshi bowl din dake dauke da fruit salad, ya ajiye gefe yana min nuni da kujerar da ke daura da shi. Samun kaina na yi da kasa musa mishi, na kai zaune ina tattare jikina waje daya, kaina a kasa, ko da wasa ban yarda mun hada idanu ba...


"Tell me about yourself, I mean anything about you!" Muryarshi ta ratsa dodon kunnena. Wani irin motsawa zuciyata ta yi; a karon farko wani ya tambayeni tarihi rayuwata. Ta ina zan fara? Dagowa na yi caraf muka hada idanu, na yi saurin maida kaina kasa. Murmushi Jack ya yi yana shafa kanshi, "Uhmm, I am all ears." Ya kuma fada idanunshi a kaina. Ina jin yadda idonshi ke yawo a jikina, hakan ya kuma haddasa min rashin nutsuwa...


"Sunana FANNAH MODU BULAMA!"
"FANNAH!" Ya ambata, hakan ya tilasta min dagowa aiko muka hada idanu. Da sauri na kawar da nawa ina cigaba da magana. Tsangwama da cin zarafin da muka fuskanta wajen uwa, zaman ukubar da muka yi, tsaftatacciyar soyayyata da ya Almuhajir, kashe min su da akayi gaba dayansu, azabar gudun hijirar da muka sha gami da yadda Maahh ta rasu; babu abun da na mance ban sanar da shi ba a cikin rayuwata daga farko har karshe. Ina kuka mai tada hankalin mai sauraro tuna labarin rayuwata, tuna mutane masu muhimmancin da na rasa a cikina; Maahh, Baba, Yaya Almuhajir...


Tunanina ne ya katse sakamakon shock da ya bani. Da hanzari na fara kiciniyar kwatar kaina ina zaro ido, amma na kasa dan ba karamar runguma ya min ba. "Baki cancanci haka daga garemu ba Fannah, baki cancanci haka ba! You deserve the most happiest life ever, ba wannan da muka dauraki a kai ba." Haka yake ta maimatawa. Da kyar ya sake ni, without looking at me ya nufi main house da gudu-gudu kamar zai kifa. Bin shi na yi nima da sauri, jikina yana rawa.
"Mom! Mom!!!"


Mom da ke tsaye kasake rike da kan waya a hannunta, with shock on her face ta juyo a sanyaye tana kallonshi. "Mom, ba za a yi transplant dinnan ba! Na fasa Mom. Zan iya kashe duk abun da na mallaka domin nemarwa Elisha lafiya, auctioning everything I own, amma this girl..." Ya fada yana dafe kai. "Mom, yarinyar nan bata cancanci haka ba! Zan tafi ko ina ne in..."


Saukar wani wawan mari da ya gama gigita kwanyarshi ya sa shi ganin taurari suna gilmawa ta saman idanunshi ya ji. Without letting him to recover, ta kuma kifa mashi wani marin tana huci kamar zakanya. "Wato ta baka abun da ke in between her legs ka dandana ko? Dama kai abun da ke tsakanin kafar mata ya fiye maka komai a rayuwarka, ciki harda ni da Lisha!"
Tunda yake a duniya, babu wanda ya taba sanya hannu ya dakeshi sai yau, shiyasa abun ya zo mishi bambarakwai har ya kasa motsawa a wajen. "Mom, try to understand me. Ba haka nake nufi ba, the girl..."


Fuuu! Mom ta wuceshi fuskarta na yamutsewa, ta tunkaroni dake tsaye bakin kofa. Saura kadan in saki fitsarin da nake dannewa ganin abun da ke faruwa. Damko gashin kaina ta yi, ta fara jana har tsakiyar palon kafin ta tsaidani saman kafafuna, tana kallona strictly ta ce, "Za a kwashe bone marrow dinki in four days' time. Za a dasawa yata Elisha da na haifa da matsalar bargo. Mun zaga duniya sosai amma bamu samu wanda bargonsu ya zo daya da ita ba. Luckily, my son ya sanya kudinshi ya sayoki dan ance mana dama you Africans kuna da bargo mai kyau. So ki shirya nan da kwana hudu ne aikin, and karki manta you are nothing but our slave, kudi muka saka muka sayoki!"


Wani irin gingirigim na ji kaina ya dauka, take abubuwan da suka faru na zuwanmu asibiti suka fara dawowa cikin kaina daki-daki, salasala. Wani irin sauti cikina ya bada kafin in ji kafata suna motsi, kwakwalwata na bani umarnin in gudu. Ban bata lokaci ba kuwa na yanka a dari da sittin zan na nufi kofar barin gidan. Ko taku uku ban yi ba Mom ta yi nasarar cafkoni, fuskarta yana rikidewa ta ce, "Zan iya yin komai a kan lafiya da farin cikin yata!"
Hannayena duka biyu ta murde, wani azababben kara na saki; fitsarin da nake ta rikewa yana sulalomin. Ga mamakina, hawaye ko digo daya babu a fuskata; tabbas wani tashin hankalin ya fi gaban kuka. "Ya Allah ka dauki raina kar in witnessing wannan bakar mutuwar, ka dauki raina irin yarda kake karban ran salihan bayinka," na fada ina lumshe idanu da jin yadda take daure jikina da igiyar da ta dauka.


"Mom!!!" Ya fada da azabar karfi. Saurin daga mishi hannu ta yi tana hankadani cikin dakin hadi da banko kofar, ta datse da makulli. "A kan Elisha, ko raina zan iya bayarwa, lusari kawai!" Ta fada tana juyawa ta yi wucewarta. Dafe goshi Jack ya yi yana studying na kofar da tunanin yadda zai tseratar da ita kafin lokacin.
Kallon takardar kawai Abeey yake cike da tashin hankali, kafin Umma ta karba tana mikewa ita ma. "A'a, dan albarka, Sifen kuma? To kaje Sifen ka yi me a can kuma? Su basu da hankali ne da zasu turaka Sifen, ko can dinma yakin ake ne duk bamusani ba?"
"Ummah ba yaki bane, wannan wani kwas ne mai muhimmanci za a turamu. Ba kowanne likitan soja ke samun wannan damar ba. Yanzu ma mu uku ne kawai mukayi nasara bayan mun yi wani jarabawa, so har na fitar da rai ma ganin abun ya dade; a zatona ban yi nasara ba, kaway jiya na samu mail, yau kuma GM ya kira ya bani wannan. Kuma tafiyar jibi ce, idan mun je da kwana biyu kuma zamu fara halartar kwas din."


"Ah to alhamdulillah! To ai wannan abu ne mai kyau. Da ita Badariyar zaku wuce kenan?"
"A'a Ummah, zan duba yiwuwar zuwanta daga baya dai, amma yanzu mu kadai zamu tafi."
"To to, to ai shikenan hakan ya yi amma..." Wani tsawan da Abeey ya katsa mata ne ya sata yin shiru, duka suka hau zarar ido dan basu taba ganin hakan a gareshi ba.
A fusace ya ce, "Aminullahi! Yaushe ka fara rufeni a baibai? Yaushe ka fara yankewa kanka hukunci ba tare da ka nemeni ka ji shawarata ba?"


Sosai abun ya bawa Al'ameen mamaki amma ya danne, "Abeey, amin afuwa sharrin mantuwa ne. Kuma a zatona sai ka fi kowa murna da farin cikin wannan abu."
A fusace ya ce, "Aminullahi, hakan na nufin cigaba da karin girman mukami zaka samu a wajen aiki, kuma bazan taba lamun..." Da sauri ya yi shiru jin katobarar da yake kokarin yi, with surprise duka suka vai kallonshi. Daidaita kanshi ya yi yana sauke murya, "Aminullahi, kafi kowa sanin bana son wannan aikin naka mai cike da hatsari. So nake ka dawo ka tayani rike companies dinnan dan sun fara rinjayata, ga girma sai kara kamani yake. Shi kuma dan uwanka, sam ko kadan zuciyarku ba iri daya ba; banda sharholiya babu abun da ya sanya a gaba."
Ajiyar zuciya Al'ameen da Ummah suka sauke, ya ce, "Abeey, amin afuwa. Wannan din yana da matukar amfani a gareni."
Ba don Abeey ya so ba, yana ji yana gani Al'ameen ya sa kafa ya bar Nigeria bayan kwana biyu. Sosai ya sha artabu da Badar sai da ya tabbatar mata nan da sati daya zai samar mata biza ta taho ita ma, sannan ta hakura suka rabu cike da kewar juna.


A babban filin tashi da saukar jiragen kasar Sifen jirginsu ya sauka. A hankali yake saukowa yana karewa yanayin sanyi mai tafe da dusar kankara da ke sauka a garin kallo. Tafe yake yana karewa ko ina kallo cike da sha'awa, ba karamin burgeshi kasar ya yi ba. Ji yayi ya yi karo da mutum; a lokaci daya takardun da ke hannun mutum suka watse a kasa. Da sauri Al'ameen ya durkusa yana kwaso takardun, lokaci daya ya mike yana bawa fari sol din dattijon da furta, "Sorry."
Karba ya yi yana murmushi, Aminu ya wuce. Mutumin ya juya yana kallonshi; Aminu ma samun kanshi ya yi da waigowa, caraf suka hada idanu da shi yana tsaye a wajen still...
*SANADIN HIJIRA*