Gaskiya daga bakin Mai ita✍️
*JA DA BAYA...*
*Book 1*
*Page 15* ✍️
***
Safiyar ranar Monday ce.
Yau Inarah da wuri da ta tashi ta shirya domin zuwanta wurin aiki.
Ayau Monday ne Kuma hirarsu da alhaji Gali.
Sakkowata tayi daga dakinta zuwa babban falon gidan. Abbie ne zaune shi da Ammie suna karyawa. Gefe guda ga mahbub cikin Shirin fita aiki.
Cikin sigar wasa Inarah ta karasa tare da fadin "the great doctor". Murmushi yayi tare da cewa "my stubborn sis".
Abbie Ina kwana ta fada tare da Dan tsugunnawa. Shafa kanta yayi tare da fadin "lafiya lau mamana, kin fito?"
"Eh Abbie" ta fada tana zuwa kusa da Ammie. Dan rumgumeta tayi tare da fadin "Ammie Ina kwana?"
"Lafiya lau Rabin Rai kinfito eh Ammie".
"Masha Allah kici abinci to se kifita, yau se sauri kike." Ammie tafada tana zaunar da inarah akan daya daga cikin kujerun dining din.
"Ayyah Ammie ni bayanzu zanci abinci ba zandai tafi dashi" Inarah tafada tana kallon Ammie.
"A'a mamanah kiyi hakuri kici kadan kinji, ko kisha tea ko Rabin Rai" Abbie yafada cikin rarrashi.
"To Abbie" ta furta tana amsar tea din da Ammie ta hada mata.
Bayan sungama break fast, Abbie da kansa yadau Inarah yakaita gurin aiki. Suna tafe ahanya suna tattaunawa haka yakara bata sharwarwarin yadda hirasu zata kasance da alhaji Gali.
Seda ya tabbatar da shigarta sannan ya wuce wurin aikinsa.
Tun ƙarfe tara na safe gidan Alhaji Gali Matawalle ya kasance cikin Kai kawo. Masu gadi na ta kai da kawo, yayin da motoci masu tsada suke jere a harabar gidan. Wasu daga cikin masu tsaronsa suna duba komai kafin fitarsa.
Seda suka tabbatar da komai lafiya sannan suka koma wajan zamansu, yarage alhaji Gali kawai suke jira.
A cikin babban falon gidan kuwa, Alhaji Gali na zaune cikin shigar farar shafa Hadi da babbar riga mai kyau da tsada. Yafito akamili babban mutun ga farin glass da yasanya a idonsa yana duba wasu takardu, yayin da p.a dinsa yake tsaye kusa da shi.
"Ranka ya Dade Yakamata mu fita yanzu tunda naga goma ta wuce gashi da karfe Sha daya kabasu lokaci, yanzu naga lokaci ya kusayi." Cewar p.a dinsa cikin girmamawa.
Jinjina kai Alhaji Gali ya yi, ya rufe file ɗin da ke hannunsa sannan ya miƙe.
"An shirya komai?"
"Eh Alhaji. Motoci sun shirya, jami'an tsaro ma suna waje suna jira."
"Madalla."
Yana fitowa daga cikin falon, Hajiya Kaltum ta biyo bayansa.
"Allah Ya tsare hanya. Excellency"
"Amin." Ya amsa cikin taƙaitaccen murmushi.
A harabar gidan kuwa, motoci biyar ne sukayi jerin gwano. A gaba akwai motar jami'an tsaro guda sai motar Alhaji Gali a tsakiya, sannan motoci biyu cike da masu tsaro da mataimakansa.
Yana shiga motar da aka ta nada don shi, direban ya tada motar a hankali. Nan take motocin da ke bayansa suka biyo bayansu suka fice daga katafaren gidan na alhaji Gali Matawalle.
A hanya mutane da dama na daga hannu suna gaishe shi. Wasu kuma na ɗaukar hotuna da wayoyinsu yayin da ayarin motocin ke wucewa.
Kasantuwar yanzu kowa wayarsa ta zama cemarar sa.
Bayan tafiyar kusan mintuna talatin, ayarin motocin suka iso gaban Haske Maganin Duhu Media House.
Tun kafin su ƙarasa tsayawa, jami'an tsaro suka fara sauka suna tabbatar da komai lafiya.
Bayan sun gama duba wajen, ɗaya daga cikinsu ya buɗe ƙofar motar cikin girmamawa.
Alhaji Gali ya sauko cikin natsuwa, ya gyara babbar rigarsa sannan ya nufi ƙofar babban ginin jaridar.
A ciki kuwa, Inarah da Editan jaridar tare da sauran ma'aikata sun riga sun shirya domin tarbar babban baƙonnasu.
A ƙofar Haske Maganin Duhu Media House, ma'aikata da dama sun fito domin tarbar Alhaji Gali Matawalle. Kowa na ƙoƙarin nuna masa girmamawa saboda matsayinsa na babban mutun a cikin al'umma.
Me gidan jaridar, Malam Sulaiman, ya ƙaraso da murmushi a fuskarsa.
"Assalamu alaikum, ranka ya dade. Barkan ku da zuwa."
"Wa alaikumus salam. Barkan ku." alhaji Gali yafada.
Suka yi musabaha cikin mutuntawa.
"Masha Allah. Muna matuƙar godiya da karbar gayyatarmu yallabai."
"Babu komai."
Da hannu me gida jaridar ya yi masa nuni da hanyar shiga.
"Mu ƙarasa ciki mana ranka yadade"
"To." alhaji Gali yafada tare da nufar babban ginin jaridar, yayin da masu tsaron Alhaji Gali biyu suka biyo bayansa, sauran kuma suka tsaya a harabar ginin.
Suna shiga ma'aikata da dama suka miƙe suna gaishe shi.
"Barka da zuwa, ranka ya dade."
Ya amsa da yalwataccen murmushi.
"Barkanku, ya ayyuka"
Inarah kuwa tana zaune a ofishin Edita, gabanta na ɗan bugawa kaɗan. Batasan dalili ba Amma gaban ta tunda akace zasuyi hirar Nan gaban ta yake faduwa.
Edita ne ya buɗe ƙofar.
"Inarah."
Da sauri ta miƙe tsaye.
"Na'am, Sir."
"Baƙonmu ya iso."
"To, Sir."
Ta gyara mayafin da ke jikinta, ta ɗauki notebook ɗinta, sannan ta bi bayan Editan zuwa ɗakin taro.
Suna shiga, Alhaji Gali yana zaune cikin natsuwa. A gefensa kuwa mataimakinsa, Malam Bashir ne.
"Inarah..." Editan ya kirata.
"Na'am."
"Wannan shi ne Alhaji Gali Matawalle bakonmu kenan" yafada yanata murmushi.
Ta yi murmushi cikin ladabi tare da kallon mutumin ta tasan tabbas zaiyi sa'an Abbien ta.
"Assalamu alaikum, Alhaji barka da zuwa"
"Wa alaikumus salam yanmata barkanki da wanna lokaci, ya kokari?."
"Alhmdlh" ta furta da fara'a.
"Madalla" ya fada Yana kallon Inarah sosai.
Editan ya ce,
"Yallabai Inarah na ɗaya daga cikin fitattun 'yan jaridunmu. Ita ce za ta gudanar da hirar ku"
Alhaji Gali ya kalli Inarah na ɗan lokaci, sannan ya ce,
"Ina fatan tambayoyin ba za su yi mini tsauri sosai ba yarinya" ta yafada da alamar wasa.
Kowa da ke ɗakin ya yi dariya.
Inarah ma ta yi Dan murmushi tace
"A'a yallabai, aikin ɗan jarida shi ne ya tambayi abin da jama'a suke son sani. Kuma nasan tambayar me sauki ce agareka."
Alhaji Gali ya ɗan gyara zamansa.
"Hakane... To, Allah Ya ba da sa'a."
Editan ya kalli Inarah.
"Kuna iya farawa."
Inarah gyara zama ta yi, da murmushi akan fuskarta tana kallon camera.
"Assalamu alaikum masu kallon tashar Haske TV. Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirin Gaskiya Daga Bakin Mai ita. A yau muna tare da babban baƙonmu, fitaccen ɗan kasuwa kuma ɗan takar gwamnan jihar nan, wato Alhaji Gali Matawalle. Barka da zuwa, ranka ya dade"
Alhaji Gali ya yi ɗan murmushi.
"Na gode ƙwarai. Barkanmu da wannan lokaci."
"Yallabai kafin mu shiga batun siyasa, muna son sanin mutumin dake bayan wannan suna, wato masu kallo da saurare sunaso su San wanene alhaji Gali, da Kuma yadda Kazama Dan kasuwa."
Alhaji Gali yadan Yi murmushi kafin ya amsa.
"An haifeni acikin wannan garin haka nayi makaranta acikin wannan garin tundaga primary har zuwa secondary. Kasuwanci ni wannan burinane na fara kasuwancine tun da kananun shekaru sannan ba da jari Mai yawa ba. Da taimakon ubangiji sannan da Kuma jajir cewa muka Kai wannan matakin."
Masha Allah "Inarah tafada tare da murmushi tace"fatan masu kallo da masu saurare zasuyi koyi da yallabai.
Inarah ta numfasa tace "yallabai shekaru dama kana cikin harkar kasuwanci, Wanda duniya ma tasan da hakan Ta shaida,ayanzu Mene ne ya ja ra'ayinka ga ya dace ka shiga siyasa?"
Alhaji Gali yace "Na yi shekaru ina hidimtawa al'umma ta fuskar kasuwanci. Yanzu kuma ina ganin lokaci ya yi da zan ba da gudummawata ta hanyar shugabanci, domin akwai abubuwa da dama da nake son sauyawa"
Masha Allah Inarah ta fada,sannan ta kalleshi tace " ranka ya Dade,Idan Allah Ya ba ka nasara, wane abu ne zai zama na farko da za ka fara aiwatarwa?"
Alhaji Gali yace "Tsaro, ilimi da kuma samar wa matasa ayyukan yi. Na yi imani waɗannan su ne ginshiƙan ci gaban kowace al'umma."
Jinjina kai Inarah tayi, tana murmushi tace Allah yasa yallabai ya cika duk wadannan magana tasa bayan yasamu kujerar gwamna,ta buɗe wani shafi a notebook ɗinta.
Ta ɗaga kanta ta ce,
"ranka ya dada game da siyasarka, ashekarun baya ka nemi takarar gwanma Amma baka samuba, shin me ya ja hankalinka kaga ya kamata kasake fitowa a wannan lokacin?"
"Rashin nasara ba yana nufin mutum ya ajiye burinsa ba ne. Na koyi abubuwa da dama daga abubuwan da suka faru a baya, kuma yanzu na dawo ne da sabon shri,Wanda burina shine kawo sauyi acikin al'umma ta yadda talauci zaiyi Nisa damu,matasa su samu aikin Yi,sannan dole al'umma na bukatar tsaro"
Masha Allah Inarah tace
"Ranka ya Dade yanzu zan koma kan wani batu da ya daɗe yana jan hankalin jama'a"
Alhaji Gali ya ɗan gyara zamansa.
Inarah tace "A wasu watannin baya, an samu wani mummunan hatsarin mota da ya yi sanadin rasuwar wata mata da ƙaramin ɗanta. Rahotanni sun riƙa yawo cewa ɗanka, Haisam Gali Matawalle, shi ne Wanda ke tukin motar a lokacin. Wasu kuma sun ce an rufe maganar ba tare da an hukunta Wanda ake zargi ba. A matsayinka na uba kuma ɗan takar gwamna, mene ne za ka ce wa jama'a game da wannan batu?"
Dan Jim Alhaji Gali bai ce komai ba. Fuskarsa ta sauya kaɗan.
Ya ɗan sha ruwa kafin ya ɗaga idonsa ya kalli Inarah.
"Wannan maganar ba gaskiya bace kawai farfaganda ce irin ta abokan hamayya. Amma abin da zan ce shi ne, wannan al'amari kawai labarin kanzon kurege ne."
Haryanzu murmushin dake kan fuskar Inarah Bai sauyaba tace "Sai dai ranka ya Dade acikin satinnan ma Ankara samun irin wannan maganar. Wanda wasu da yawa sun shaida cewa danka haisam ya Kara bige wasu mutane da mota. Wanda wasu suke fadin lallai gangancine yakawo hakan, sannan danka Kuma Bai dauki Wani mataki ba. Shima, Wanda mutane ke ganin cewa anyi amfani da kudine Dan rufe maganar, ayanzu me zakace?."
Nan take fuskar mataimakin Alhaji Gali ta canza.
Ya yi yunƙurin yin magana...
"Haba Malama, wannan..."
Alhaji Gali ya ɗaga hannu cikin natsuwa, ya dakatar da shi.
"Ka ƙyale ta. Aikinta take yi."
Inarah ta ci gaba da kallonsa ba tare da ta janye idanunta ba.
"Wannan maganar itama fadine kawai na mutane wanna. Karon bazan Musa Miki ba, tabbas tsautsayi ya gitta, inda Dana haisam yabige Wani yaro cikin rashin sani. Wanda cikin gaggawa Kuma yadauki yaron zuwa asibiti. Wanda yanzu haka yaron Yana karkashin kulawar likitoci. Bayan haka duk Wani abu da ake Fadi kawai, zance ne na mutane. Inkuma Kuna shakka akan maganata zaku iya bincikawa ku tabbatar" yakara maganarsa tare da kallon Inarah cikin Ido.
"Sannan abinda nakeso kisani shine mutane suna da 'yancin faɗin ra'ayinsu. Amma ba zan yarda a ce na yi amfani da kuɗina ko matsayina wajen hana adalci ba. Idan akwai wanda yake da hujja a kan hakan, ya gabatar da ita."
"To ranka ya Dade, idan ka zama gwamna, shin za ka bari doka ta yi aiki a kan kowa, ko da kuwa ɗanka ne?" Inarah ta fada tare da kallon alhaji Gali.
Murmushi yayi wannan karon Yana kallon camera tare da fadin "ba akan Dana ba ko akaina hukuma zatayi aikinta. Sam ni ba mutun bane Mai ja da doka, duk abinda akace dokane Ina biyayya akansa dari bisa dari."
To ranka ya Dade, wannan shi ne ƙarshen hirarmu. Muna godiya da ka ba mu lokacinka, kuma mun gode da amsoshin da ka ba mu,fatan tambayoyin basuyi tsauri agareka ba.tafada da murmushi sosai akan fuskarta"
Alhaji Gali ya yi murmushi.
"Nima na gode da kuka ba ni wannan dama. Sam wadannan tambayoyin naki masu saukine yarinya ta,Ina fatan masu kallonmu sun gamsu da duk amsoshina, sannan zasu bamu goyon baya dari bisa dari Dan kawo sauyi Mai kyau ga rayuwar mu."
Tabbas. Muna yi maka fatan alheri a tafiyar ka ta siyasa. "Allah yabada nasara" Inarah ta fada ganin irin kallon da edita yake ta wurga mata.
"Nagode" ya furta tare da kokarin mikewa.
Bayan an kashe duk camera, edita ya karaso gurin alhaji gali Yana fadin "yallabai mungode sosai da hadin Kai da kabamu fatan nasara".
Amsawa alhaji Gali yayi sunayin munsaba tare da Mai gidan jaridar. Wanda suka nufi hanyar fita tare da Masu tsarinsa.
Inarah kuwa tana gurin har lokacin ba ta tashi ba ta rasa zaman me take awurin. Seda zarah ta karaso tana rumgumeta tace "Kai Lily irin wadannan zafan tambayoyin haka?"
"Kedai bari besty Allah bangama Mai tambayoyin ba. Kawai naga edita nata jefomin kallon gargadi shiyasa na takaita. Amma akwai zargi Kashi Kashi kan yaron mutumin Nan. Amma akwai next inshallah da kansa zaiyi bayani, domin yaron Yana zuba iskancinsa San Rai"
Tashi sukayi suka fito adakin Taron, suka fita domin yin alwala. Inda zuwa lokacin ayarin motocin alhaji Gali matawalle, sun Riga da sun fita agidan jaridar.