JA DA BAYA...

ZAKI A HANNUN ALLAH😂

by @meelahbazata978

*JA DA BAYA...*  
*Book 1*  
*Page 16✍️*

***

Inarah kuwa ta tattara kayanta, ta saka notebook ɗinta cikin jaka. Zarah ta karaso ta ce, "Lily wannan tambayoyin haka masu zafi." 

Kai Besty, wai zafi? Ni fa na so ma sufi haka. Amma ki bari, akwai gaba ai,wannan mutumin Sam ban yadda dashi ba,Amma da alama ya iya takunsa. 
Kedai lily akwai daukar magana,mutumin na. Babban mutun ne,kawai zuciyarki ke gaya Miki haka,Amma ai naga ana yabonsa",Zara tafada 

Mikewa sukayi gaba ɗayansu suka fito daga ɗakin da aka gudanar da hirar. 

Fitarsu adakin da aka gudanarvda hirar hanyar fita suka nufa,Zarah ta kalli Inarah.  
"Lilly, mu tafi mu yi sallah kafin mu koma ofis."  
Inarah ta amsa tana jinjina kai.  
"To besty, mu tafi."

Tafiya sukayi suka nufi wajen da ake sallah.  
Bayan sun isa, suka shiga domin gabatar da sallarsu, yayin da sun tarar da wasu sauran ma'aikatan gidan jaridar suma a ciki suna sallah.

Bayan sun idar, Inarah ta zauna na ɗan lokaci tana gyara mayafin ta, kafin ta kalli Zarah.  
"Besty, tashi mu koma ofis."  
Zarah ta miƙe.  
"To, mu tafi gaskiya. Ai mun ɗan jima ma. Ni yunwa ma nake ji."

Tashi Inarah tayi suka fito tare da Zarah suna magana.  
Suna shiga ofis din nasu edita na aikowa Akira Inarah.
  
Bayan ta je yake tambayar, "Me yasa ki yi wadannan tambayoyin? Bayan Seda aka rubuta Miki tambayar da za ki yi, me yasa ki ka Kara wasu?"

Sir, "Na ga sune tambayoyin da mutane suke son jin amsar su, shiyasa na yi su."

"Fita ki bani wuri," shine kawai abinda editan ya iya fada. Dan ya san halinta da kafiyar masifa.  
Bayan ta fita a ranta ta fadi, "Ohoo dai, ni dai na yi abinda na ga dama,bawanda zan tsaya Yana sarrafani atoh,tafada hakan azuciyarta tana gunguni."

Tana komawa suka ci gaba da harkokinsu har zuwa lokacin tashinsu yayi.  
Bayan sun fito Zarah ta shiga mota ta tafi. Inarah kuwa Mahbub ne ya zo daukarta.

Suna tafiya suna hira a hanya cike da nishadi da barkwanci, kasantuwar Mahbub akwai wasa da dariya.  
Suna tafiya ya wai ga ya ce, "Ke Lily, gaskiya ba ki jin magana. Irin wadannan tambayoyin da ki ke yi wa Alhaji Gali,ai se ya rude gashi tambyoyin sun ɗauki hankalin jama'a. Kin san yadda media ta ɗauka kuwa? Na ga ana ta hayya hayya ai." Ya karasa maganar yana dariya.

"Kai Yaya, wai wannan tambayoyin ni ai ba su wadatar ba naso na kara wasuma,banso na  Tsaya haka ba. Amma na san komai tsarashi aka yi,dan har anamin fadan meyasa nayi wasu tambayoyin,Wai tambayoyin da zan yi masa ma rubuta min su za'ayi, shiyasa na Kara da nawa a kai." Ta fada tana turo baki gaba.

"Ba ki jin magana Lily? Yanzu wannan tambayar haka ma ba su wadatar da ke ba? Kin yi kokari gaskiya. Amma dai ki bi a sannu. Mutumin nan da alama makiri duba da yadda yake amsa tamboyin da ki ke masa.

Sannan kuma akwai yaron da aka kawo asibitinmu. Ina tsammanin a yadda na ji ana fada kamar shine yaron sa ya buge da mota. Wanda wasu suna cewa yana cikin maye a lokacin. Sannan abun ya faru ne bisa gangancinsa. Amma ban san me yasa ba yau da kwana daya suka yi suka dage akan se an sallamesu. Ita kanta mahaifiyar yaron tana jin jiki. Ai ina jin labarin yaron sam ba shi da tarbiya." Mahbub ya kasa maganar tasa da alamar takaici.

"Ai Yaya, kadan ma ka gani. Ni ma na samu labari a gurin wata abokiyar aiki na. Ta ce sam yaran abinda suke so shi suke yi. Amma a juri, zuwa rafi wata rana tulu zai fashe." Ta fada hakan bayan karasowarsu bakin gate din estate din na Mai Rabo.

Parking ya gyara bayan karasowarsu bangaren nasu. Inarah ta dauki briefcase din Mahbub hadi da jakarta ta nufi kofar babban falon.

Tana shiga da sallamarta cikin falon. Wanda ya ji kayan more rayuwa. Komai da ke cikinsa luxury ne. Ke da ki gani kin san na masu da shi ne, domin tsayawa fadin kyawunsa ba ta bakine.

Karasawa Inarah tayi kusa da Ammie wacce ke zaune saman sofa. Ayzaan kwance a jikinta ya daura kansa a kan cinyarta. Gashin kansa take gyara masa a hankali cikin kulawa. Shi kuwa idanunsa suna lumshe kamar mai bacci. Amma sam ba baccin yake yiba. Kansane yake ciwo. Ya fita motsa jiki kamar yadda ya saba kullum, ya dawo kenan da niyar ya huta Ya fita kuma se kanshi ya matsa masa, shiyasa ya tawo gurin Ammie. Bayan ta lallabe shi ya ci abinci kadan dan in bai da lafiya akwai rakin ciwo. Ammie ta fi kowa iya kula da shi in bai da lafiya, kasantuwar ita ce wacce kusan duk rainonsa ita tayi,inbaida lafiya komawa yake kamar jariri.

Bayan ya ci abincin ne ya shiga dakinsa yayi bacci. Bayan ya sha maganin ciwon kan shine fa yana fitowa. Ammie tana zaune a falon. Ya zo kusa da ita ya zauna. Bayan tambayar sa jikin masa tare da hada masa tea ya sha. Shine ya dan kwanta a jikinta tana gyara masa kanshi, kasantuwar kan da kito guda biyar da yayi, shiyasa ta warware masa tana gyara masa.

Mahbub da karasowarsa kenan yake fadin, "Ammie gaskiya kina shagwaba yarannan da yawa. Shi wannan me kama da samudawan ya zo ya yi ki kwance a jikinki. Ai kafarki ta karye. Ita kuma waccen parrot din an jima itama ta zo ta kwanta. Ammie kina shagwaba su da yawa. Allah ya fada." Yana harara Ayzaan cikin wasa tare da kai hannu zai mintsinesa. Ammie ce ta bige hannun tana fadin, "Ka da wo kenan? Ai ina ruwanka? Kai indai kananan ba za ka bar min yaro ya huta ba. Ai kai ne parrot din ba itaba." Ammie ta fada tana ture hannun Mahbub da yake so ya taba kan Ayzaan.

"Yau an bude file din mazaje. Da alama ba lafiya yau. Irin wannan sheme sheme da ka yi." Mahbub ya fada yana kallon Ayzaan. Dan ya fi kowa sanin halin sa in ba shi da lafiya.

"Yawwa Ammie, Yaya shine parrot. Amma yake ce min parrot? Kuma ai jikin mamanmu muka kwanta. Shima ba haka ummee take shagwaba shi ba." Inarah ta fada tana ma Mahbub gwalo.

Zabura ya yi kamar zai kamata. Ta yi kan Ammie da sauri tana kankame ta. "Ammie kin gan shi ko? Zaki na ka gan shi ko?" Ta fada tana kallon Ayzaan da ya dan bude idonsa.  
Da sauri kuma ta ce, "wayyo Zaki na, ba ka da lafiya? Na ji jikinka ya yi zafi. Sannan idon ka ya yi ja. Me yake damun ka? Kan ka yake ciwo ko? Ka je asibiti? An yi maka allura? Ka sha magani? Na san dama ba ki jin dadi. Amma ka ce min lafiya. Tun jiya kan ka ke ciwon ko?" Duk ta jero wadannan tambayoyin a tare. 
Gyara kwanciya yayi a jikin Ammie yana Kara lumshe ido da marairaice fuska. Dama shi kuma akwai raki in ba shi da lafiya. Se dai ba kowa ya san hakan ba.

"Bansan surutu." Shine abinda ya fada yana Kara lumshe ido.

Ammie ta ce, "Wai ke yaushe za ki yi hankali? Wadannan tambayoyin haka? Maza tashi ki je ki yi wanka ki ci abinci. Hajja tana nemanki tun dazu ta aiko." Ammie ta karasa maganar ba alamar wasa. Dan ta san halin Inarah. Yanzu ta saka wata rigimar. Dan abin fitina bai mata wuya. Bare yadda Ayzaan be da lafiya, tana iya zama ta dasa kuka kamar wani ne ya daura mata ba Allah ba.

Ba daɗewa ta miƙe tana fadin, "Zaki na ka ji sauki ko?" Ta fada cikin matukar tausayawa. Duk se ta ji ba ta jin dadin komai. Ita har ga Allah ko kadan ba ta son ta ga wani abu ya same shi ma ko kadan. Itafa gara kowa yayi ciwo a gidan akan ya zamana shine ba shi da lafiya. A jikinta take jin ciwon nasa. Haka a jikinta take jin duk wata damuwarsa. Har ta yi nisa ta sake dawowa ta ce, "Ammie ni ba zan iya wankan ba. Dan Allah ki bar ni a wurin shi." Ta fada tana kuka wiwi.

A ransa yake fadin, "Ahaf, na san hali ai. Ita sam kuka ba ya mata wahala ne?"  
"Ki yi shiru a wurin nan. Ki tashi ki je ki yi wanka ki sakko ki ci abinci. Karki bari na sake maimaitawa." 

Mikewa tayi tana kuka ta tafi tana waigensa.  
"Chuchu." Ya Fada cikin low voice dinsa mai matukar dadi wacce ta Kara haduwa da rashin jin dadin jikinsa Dayake se muryar ta Kara sanyi.

Da sauri ta waigo, "Yaya ka ji sauki ko? Kan ya daina ciwon? Har yanzu yana maka ciwo ko?"  
"Na ji sauki. Ki dena kuka. Ki yi wanka ki zo mu ci abinci." Ya fada a hankali dan ya san in ba yi magana ba za ta tafi ba.

"Kai ma za ka ci abincin Yaya?"  
"Eh." Ya fada yana nuna mata hannu alamar ta je. Aikam da sauri ta yi hanyar dakinta tana fadin, "Bari na yi sauri. To Ammie me aka dafa yau?"  
"Kirki tafi. Ki yi abinda ya dace. Ki tsaya tambaya." Ammie ta fada tana harararta.