She love him more than she love her self 💔
*JA DA BAYA...*
*Book 1*
*Page 17✍️*
***
Inarah ta shige dakinta tana goge hawayen fuskarta, amma murmushin da ke kan fuskarta ya kasa ɓoyuwa. Tun da Ayzaan ya ce ya ji sauƙi, sai ta ji kamar ita ma an sauke mata wani nauyi daga zuciya. Gaba daya se ta ji wani sabon farin ciki duk da ta san bai gama warwarewa ba. Amma tunda ya tashi ya zauna se ta ji dadin hakan.
A gaggauce ta yi wanka ta fito, ta sauya kaya. Zuwa kananan kaya wandon da kadan ya wuce gwiwarta se rigarsa mai fadi. Duk da rigar ta kai har cinya amma kayan sun yi matukar yi mata kyau. Hula ta dauka ta sanya a kanta sannan ta fito.
Da saukowarta falon, ta tarar da Ammie tana magana da Mahbub. Wanda fitowarsa daga wanka kenan ya sauya kayan jikinsa zuwa na shan iska.
Ayzaan kuwa yana kwance har yanzu. Kansa na jikin Ammie yana danna wayarsa.
Tun daga nesa ya shaida karasowarta, saboda kamshin turarenta mai matukar dadi. Tana matukar san turare shiyasa wani sa'in Ammie har fada take mata in za ta fita ta saka wannan uban turaren se ta ce mata ta koma ta sauya kaya ta sa kadan.
Karasowa tayi kusa da inda kafarsa take ta zauna.
"Yaya na dawo."
"Ki ci abinci to." Ya fada yana danna wayarsa.
Inarah ta kalle shi ta ce, "Yaya kai fa?"
"Dena kallo na haka. Ki je ki zuba abincin."
"Amma ai kai ɗin za ka ci ko Zakina? Ka ga ba ka da lafiya kila ma ba ka ci abinci ba. Allah Sarki." Ta fada cikin tausaya wa.
"Na ce na ji sauƙi."
"To shikenan. Amma yau anan za ka kwana ko Yaya?"
Ayzaan ya ɗan kalle ta, sannan ya yi murmushi.
"Dagaske Yaya? Ammie anan ze kwana ko? Yaya, ni a gurinka zan kwana yau. Kar ka kwanta kai kadai da dare. Karasa yadda za ka yi. Banso nake ka zo kana jin ciwo."
"Wa ya ba ki wannan ikon?" Ya fada yana kallonta.
"Ni da kaina na ba kaina." Ta fada tana tabe fuska.
Mahbub ya fashe da dariya.
"Wallahi wannan yarinyar ba ta da lafiya a kanta. Ke sam ban san sanda za ki yi wayau ba. A haka za a yi miki aure? Silly girl." Ya fada yana harararta.
Inarah ta juya ta kalle shi.
"Yaya, ka bari. Ai ba ruwana da kai. Kuma ko ummee ta ce ina da wayau ai."
Ammie ta girgiza kai tana murmushi.
"Ku dai kullum sai kun samu abin da za ku yi gardama a kai. Ba zan iya da shiririta ba. Mahbub sam ba ka girma. Ke kuma ba za ki tashi ki tafi gurin Hajja din ba?"
"Ammie zan je. Amma se Zaki ya ji sauki tukunna."
Mahbub ya ce, "Ai idan na yi shiru, Lily ba za ta samu wanda za su raba hali ba. Bare ta takura masa. Tunda wancan sangamemen ya shagwaba ta."
"Ni kuma?" Inarah ta nuna kanta.
"Eh fa."
Ta turo baki.
"To daga yau ba zan sake magana da kai ba."
"Allah ya taimaka. Da na huta nima da surutu."
Ayzaan da ke zaune yana kallonsu ya ɗan yi murmushi. Amma kafin ya yi magana, sai ya ji wayarsa ta yi ƙara.
Duba screen ɗin yayi. Fuskarsa a dan cushe.
Ya miƙe ya ɗan matsa gefe domin ya ɗaga wayar.
"Hello..."
Shiru ya biyo baya.
Sai ya ce, "Yanzu?"
Dan jim kadan ya ce, "To. Zan duba."
Ya katse kiran.
Ya dawo yana zama a inda ya tashi.
Inarah wacce take zaune bayan ta zuba abincin ta kalleshi. "Yaya ga abincin."
.Ya ɗebi cokali daya ya kai bakinsa, sannan ya ce mata, "Oya maza ki zauna kici, Kuma karki sake na ji bakinki."
Haka ta zauna tana cin abincin tana kallonsa. Ta gama cin abincinta, ta ɗauki plate din ta kai kitchen ta wanke bakinta.
Ayzaan yana zaune tare da Ammie. Mahbub kuma yana danna wayarsa har zuwa wannan lokacin kuwa.
Suna zaune suna ta hira. Wanda yawan firar rikicinta ne da Mahbub.
Kofar falon aka bude tare da sallama.
Abbie ne ya shigo, cikin kamala da natsuwa.
Da sauri Inarah ta miƙe, ta nufeshi da gudu tana fadin, "Abbieeee!"
Ta nufi wajensa tana murmushi, tare da rungumeshi. Ya bude hannayensa ya tarbe ta, yana jin wani farin ciki a zuciyarsa.
"Uwar masu gida." Ya fada yana shafa kanta tare da tambayar ya take?
"Abbie na, ina lafiya. Se dai gajiyar aiki. Gashi kuma Zakina ba shi da lafiya."
Ya yi murmushi yana shafa kanta.
"To yau ba kan ta Zakimu guda ba lafiya?"
Ta riƙe hannunsa.
"Ehmana Abbie. Kuma bai kamata ya yi rashin lafiya ba ko?"
Murmushi kawai yayi yana jinjina shirme irin na Inarah.
"Abbie, ka san yau an yi min faɗa a office?"
"An yi miki faɗa? Maman nawa guda? Me ki ka yi?"
Ta turo baki.
"Ni fa ban yi komai ba, Abbie. Kawai na tambayi abin da nake ganin ya kamata na tambaya ne."
Mahbub ya yi dariya.
"Sannu parrot. Ke sam ba ki da man kai. Yanzu ya dawo amma ba za ki bar shi ko hutawa ya yi ba. Abbie barka da dawowa. Ya kokari." Ya fada yana kallon Abbie da ke karasowa cikin falon. Idonsa a kan Ayzaan.
Inarah ta juya ta kalle shi.
"Yaya wai ba munyi fada da kaiba ne? Shine ka ke min magana?"
Inarah ta sake kama hannun Abbie.
"Abbie, kar ka saurare shi. Shi kullum sai ya sa maka ni kuka."
Abbie ya yi murmushi.
"To zo ki zauna. Ki ba ni labarin abin da ya faru."
Nan take ta zauna kusa da shi, ta fara ba shi labarin hirar tun daga farko har ƙarshe. Yayin da take magana, tana kara shagwabe fuska tana nuna masa yadda Editan ya yi mata faɗa.
Bayan ta gama ba sa labarin, da kallonta kawai yake yana jinjina. Surutu irin na yar tasa. Murmushi yake kamar bai ga komai ba. Bayan ya riga ya ga labaran.
"Abbie, ka ji fa? Har yana ce min 'fita ki bani wuri'."
Ta yi maganar tana kwaikwayon muryar Editan. Ammie dai murmushi kawai tayi. Mahbub kuwa se da ya fashe da dariya.
Abbie ma ya yi dariya.
"Ya waiga ya ce, Zaki na yau ba ka jin dadi? Ka sha magani Amma? Mahbub me yake damunsa ne?"
"Abbie ni ma ban saniba. Na dawo daga asibitin na same shi anan kwance. Amma ya ji sauki ai. Dama raki ne kawai." Ya fada yana harar Ayzaan.
"Abbie stress ne kawai. Kuma na ji sauki. Barka da dawowa. Su o'oh ba za su bari ma ka gan mu ba." Ya fada yana kallon Inarah.
"Abbie ka gani ko? Na san da ni yake Allah."
"Ni dai ba ruwana. Kunfi kusa. Kuma ki dena abinda zai yi miki faɗa a gurin aiki. Kin ji ko mamana? Ban so."
"Ni kuma? Abbie ai ban yi laifi ba. Kawai tambayoyin da na yi ne wai sun yi tsauri."
"Na sani. Amma ki yi a hankali. Kin ji mamana."
Ta ɗan yi shiru. "To Abbie zan kara kiyayewa."
Dan jim kadan ta yi ta kara kallonsa ta ce, "Abbie..."
"Na'am?"
"Ka san ban yi laifi ba amma ko?"
Abbie ya shafa kanta.
"Ban ce ki yi laifi ba. Amma ina son ki riƙa kula da kanki ne. Ke yarinya ce. Ba ki san illar mutanen nan ba ne."
Ta yi murmushi.
"To shikenan. Inshallah zan kiyaye sosai Abbie."
Ammie ta ce, "Abbie wai ko ni ba ka gani ba? Tun dazu ta Inarah kawai ka ke. Ta barka ma huta ma ta ki. Kai kawai ka bi wa shirmenta."
"Ba wani shirme. Inda zuwa ta agurin ai makancewa na ke yi ko mamana?" Dariya tayi sosai cikin farin ciki.
Abbie ya miƙe. Ya karasa kusa da Ayzaan ya taba jikinsa sannan ya ce, "Na ji temperature dinka normal. Mahbub ka sake dubashi da kyau. Sannu ka ji bobo na." Ya fada yana shafa kansa.
"Abbie na ji sauki fa na ce."
"Ammie ai na ji sauki ko?"
"Ka ji sauki Ayzaan. Fatan mu Allah ya kawo babban sauki rayuwarka." Ta karasa maganar a cikin tausayawa.
Abbie ne ya yi hanyar dakinsa. Ammie tana bin bayansa. Cike da walwala suke. Ba tare da sanin cewa wata sabuwar matsala tana gab da tunkaro rayuwar su wacce za ta sauya kaddararsu ba.
Alhaji Gali yana zaune a cikin wani ɗaki na musamman a gidansa. Gefensa kuwa P.A dinsa ne wanda ya kasance ɗaya daga cikin mutanen da ya fi yarda da su.
Fayil ne a gabansa, yana dubawa.
Alhaji Gali ya ɗaga idonsa ya kalle shi ya ce, "Yaya maganar? Fatan an ji da kowacce matsala."
P.A din ya sauke numfashi ya ce, "Har yanzu komai yana ƙarƙashin kulawarmu. Komai zai tafi yadda aka tsara Alhaji."
Alhaji Gali ya ce, "Na gaya maka bana son a sake samun wani kuskure a wannan karon. Ku yi komai cikin taka tsantsan."
"Ba za a samu ba inshallah."
Alhaji Gali ya jingina da kujerarsa yana lumshe ido. Jim yayi ya numfasa ya ce, "Ka san wannan yarinyar?"
"Ranka ya dade. Abinda na san iyar jarida ce. Amma sunanta da na ji tabbas na girgiza."
"Ba wai sunanta nake tambaya ba. Wacece ita?"
Ya ɗan yi shiru, kafin ya ce, "INARAH AHMAD MAI RABO. Yar gidan Barrister Ahmad Mai Rabo ce."
"Whattt, yar gidan Mai Rabo?"
P.A ya jinjina kai.
Alhaji Gali ya ɗauki wayarsa cikin hanzari tare da fadin, "Jeka ka waizannemeka."
Malam Bashir ya miƙe ya fita.
Alhaji Gali ya rage shi kadai. Jikinsa har rawa ya ke yi. Ya ɗan a wata number ya kira.
Kalaman Inarah suna sake dawo masa a rai kamar yanzu take masa su. A ransa kuwa fada yake, "No wonder barewa ba ta gudu da nta ya yi rarrafe."
"Idan ka zama gwamna, shin za ka bari doka ta yi aiki a kan kowa, ko da kuwa ɗanka ne?"
Ya rufe idanunsa na ɗan lokaci. Wannan tambaya ba karamin dukansa tayi ba.
Kiran ya yanke. Kara kallon wayarsa yayi wacce take kara alamar shigowar kira.
Yana dauka. Abinda aka fada shine ya sa shi miƙewa ba shiri tare da fadin, "Mark Shadow again." Cikin tsananin tashin hankali da gigicewa.