THE MARK SHADOW 🫡
*JA DA BAYA...*
*Book 1*
*Page 18✍️*
***
Zaune yake a cikin wani kebantaccen wuri. Wurine da babu hayaniya sam. Tunanin wannan zobe yana kara dawo masa a cikin zuciyarsa.
Tabbas ya taba ganin irin wannan zoben a wani wuri. Amma har yanzu ya kasa tuna ina ya gansa. Ya yi nisa cikin tunaninsa ya ji wayarsa da ke gefensa ta fara ringing.
Hannunsa ya kai ya dauka yana kallon screen din kafin ya daga.
"Hello."
"Sir, mun tura maka bayanan da muka samu, gaba daya."
"Mun samu mutune tara daga cikin wadanda suke da wannan zoben. Kuma shi zoben, zobe ne da aka ba su dan girmamawa. Mun samu daya daga cikinsu. Mun tattauna. Yana nan cikin unguwa uku. Wasu daga cikinsu sun bar garin aiki ya kai su wani garin. Wasu kuma ba sa kasar ma.
Kun samu bayanan ko wannensu, shine abinda ya fada?"
"Mun samu bayanan mutane takwas ranka ya dade. Saidai amma mutane biyu daga ciki abin mamaki mun kasa samun cikakken bayani a kansu."
Shiru yayi na wani lokaci, kafin ya bude baki ya ce.
"Me yasa?"
"Sir an goge dukkan bayanansu. Abu daya kawai muka samu daga cikin bayanan, shine wani tsohon address."
"Ka turo min komai yanzu." Shine abinda ya furta.
"To sir."
Kashe wayar yayi tare da miƙewa. Daga inda yake zaune dole ya yi nazari a kai. Domin tabbas masu laifin, suna da wayau.
Lokaci ya duba kafin ya miƙi tsaye daga inda yake zaune.
Karfe hudu saura kadan na yamma.
Fitowa yayi daga wurin tare da yin hanyar fita. Amma zuciyarsa na ta kai kawo. Murmushi kawai yayi yana tambayar kansa.
"Me yasa aka goge bayanansu?"
Da wannan tunanin ya isa masallaci. Bayan ya idar da sallah motarsa ya nufa. Bude wayarsa yayi ya duba bayanan da aka tura masa.
Sunayen mutanen tara a jere da bayanansu. Fara bi yayi daki daki yana karantawa.
Ya fara karanta na farko.
Ya bude bayanansa.
Babu wani abu mai muhimmanci.
Shi ma babu wani abu da ya dauki hankalinsa.
A haka yayi ta bi yana karantawa. A kan na bakwai ya tsaya. Tabbas ya san sunan. Ba ya mantawa. Aiki ya taba hadasa da mai wannan sunan.
Idonsa tsaye kamar akan sunan kafin ya furta. "Shine." Ya numfasa. Tina inda ya san sunan. Tabbas haka yake ya tinasa.
Ya bude bayanan, amma babu komai face suna da wani tsohon adireshi.
Babu hotonsa.
Babu lambar waya.
Babu wani karin bayani.
Taya hakan za ta kasance?
Kara kallon hoton zoben yayi. Take ya tina kuwa. Da sauri ya yiwa motarsa key ya dauki hanya.
Yana tafiya wayarsa ta sirri ta yi kara. Yana dauka a dayan bangaren aka ce.
"Sir mun sake samun wani bayani."
Shiru yayi kawai yana sauraro.
"Sir akwai wata kungiya wanda daya daga cikin masu zoben yake bincike a kansu. Sunan mutumin Ahmad Ishaq. Amma mun kasa gano takamaiman kungiyar sosai."
"Menene sunan kungiyar?"
"BLACK MAFIAN."
"Are you sure?" Ya fada cikin matukar mamaki.
"Yes sir."
Ya katse wayar.
Gefen titi ya koma, ya yi parking.
Tabbas yanzu ya fara gano bakin zare. "Black Mafian." Ya sake maimaitawa a ransa. Murmushi yayi a ransa yana fadin, "Yanzu za ku ga ainayin wasan."
Inda zai nufa ma fasa zuwa yayi. Yana bukatar zuwa gida. Domin kwana biyu kenan rabonsa da gidan.
Yana zuwa ya yi hon. Da hanzari aka bude masa gate din. Wani matashi. Zai iya yuwuwa dan uwansane, domin kuwa bai yi kama da mai gadi ba. Hasali ma suna da yanayi.
"Barka da dawowa babban Yaya." Ya fada tare da risinawa alamar girmamawa.
Da kai ya amsa masa tare da nufar hanyar falon.
"Yaya ina ganin se mun koma asibiti yau. Kwana biyu Mayah ta ki sauraran kowa. Kuma ba ta cin abinci."
Shigarsu cikin falon shine ya dakatar da maganar da yake gaya masa.
Mama tana zaune a tsakiyar dakin kan wani lallausan carpet. Yarinya ce a gabanta wacce za ta kai kimanin shekara goma sha biyu. Fara ce har daukar ido ta ke yi. Se dai da alama ba ta da kafiyar kwakwalwa. Domin daga yanayin yadda ta ke yi kawai za ka tabbatar da hakan.
Sallamar sa ta sa mama ta ce, "Alhmdlh ga uban naki nan ya dawo. Kila ki sauraresa tunda mu duk ki ki ya."
Aikuwa da sauri ta miƙe tana kokarin karasawa garesa. Karasowa yayi ya riƙe ta. Ta na so ta yi magana amma ta kasa. Shafa kanta yayi tare da murmushi.
"Daddy." Shine abinda ta furta tana rikesh sa sosai.
"Daddy tsoro nake ji. Ka boyeni daddy. Ba na so. Ku dena. Wayyo, mommyyyy." Ta fada cikin gigicewa.
Luuu ta yi a jikinsa tare da sumewa.
Kuka mama ta ke yi sosai da sosai. Hakika duk sanda ciwon na yarinyar zai tashi yana tuna musu abinda ya faru da rayuwarsu ne.
Yayin da wannan matashin da suka shigo tare ya furta, "Ya subhanallah." Tare da goge hawayen da yake zubo masa. Yana goge wa. Wani na korar wani.
Yana matukar tausaya wa Mayah. Yarinya ce karama amma tana shan azabar rayuwa. Haka yana tausayawa babban Yaya bisa kaddar da ta samesu.
Shafa kanta ya ke yi a hankali tare da yi mata addua. Amma Allah kadai ya san yadda zuciyarsa take kunnai. Tafin hannunta yake murzawa a hankali a hankali.
Ta ja wani dogon numfashi tare da kiran, "Daddyyyy."
"Na'am." Ya furta yana gyara mata zama a jikinsa.
"Daddy ka boyeni. Daddy ina jin tsoro. Ka ce su bar ni daddy. Kar ku min komai. A'aaaa, wayyo daddyy, mommy ku zo, yayahhhh."
Haka take ta fada cikin sambatu.
Addua yake mata a hankali. Bacci ya fara daukarta. Gaba dayansu sun yi jugum jugum. Allah kadai ya san yadda suke jin zuciyoyinsu a duk sanda ciwon Mayah ya tashi.
Miƙewa yayi da ita a jikinsa ya nufi hanyar dakinta. Kwantar da ita yayi ya gyara mata kwanciyar tare da sumbatar goshin ta. Sannan ya juya ya fita a dakin. Tare da kuduri akan wadanda suka aikata. Tabbas ba zai ba su ba. Duk wadanda su ka yi sanadin shigar Mayah cikin wannan hali to tabbas ba zai ba su ba. Ko mutun daya a ciki ba zai bari ba. Wannan alkawari ne ya dauka.
Yana fita bai kalli kowa ba a falon. Ya nufi bangarensa.
Bilal ne ya tashi ya hada masa abinci tare da binsa bangarensa. Ya shiga ya aje masa. Wanda ko da ya shiga ya same shi kwance akan gadonsa. Kafafunsa suna kasa. Idanuwansa a lumshe.
Dawowa falon yayi. Wanda har izuwa lokacin shi wannan matashin yana zaune yayi tagumi. Da alama yana cikin dogon tinani.
"Yaya Jay ka dena tsananta tunani. Hakan zai maka illa. Inshallah za mu cinye wannan jarabawar. Mu ci gaba da tayi babban Yaya da addua. Sannan Mayah ita ma za ta samu lafiya inshallah. Se mu ga bayan azzalumai."
Jinjina kai kawai wanda aka kira da Jay din yayi.
Mama ta kara kallonsa cikin tausayawa irin ta uwa ta ce, "Ku dena damuwa. Inshallah za mu cinye wannan jarabawar. Amma yanzu akwai bukatar likitan nan ya dawo ya sake duba Mayah. Kwanaki kamar ta ji sauki. Kwanan nan abun ya ke so ya dawo mata. Na fi zaton har da rashin ganin ubanta. Amma za ta samu sauki da yardar Allah."
Miƙewa Jay yayi ya nufi bangaren da babban Yaya ya bi. Jay dan uwan babban yayane. Sannan yana matukar kaunar Mayah. Ya saba da ita sosai. Shiyasa yake ganin ya fi kowa jin ciwon nan nata. Sannan shi kanshi ya sha alwashin bin cikin duk wanda yake da hannu a rugujewar rayuwar yarinyar da ba ta ji ba ta gani ba. In ya tino mahaifiyarta se ya ji hawaye ya sake zubo masa. Yana matukar jinjina wa karfin hali irin na babban Yaya daya ke iya boye wannan bakin cikin.
Da sallama ya shiga dakin. Inda ya tadda babban Yaya kwance a kan gado. Idanunsa a lumshe. Da alama yana cikin tunani mai zurfi.
Karasowa gurinsa yayi ya zauna a bakin gadon. Hannu ya kai ya cire masa takalman kafarsa. Ya cire safar itama. Fararene kafafuwan nasa suka bayyana. Kuma har zuwa lokacin bai bude ido ba.
"Ka tura wannan bayanan ta email din wannan yarinyar. Sannan a sanar da yan jarida game da abinda ya faru jiya."
Iyakar abinda ya fada kenan. Ya tashi ya shige ban dakin.
Babbar magana kenan. Shine abinda Jay ya furta a zuciyarsa. Tare da miƙewa ya fita a dakin dan zuwa ya aiwatar da abinda Yayan nasa ya sa shi.
🔥