JA DA BAYA...

Abunda ake jira

by @meelahbazata978

*JA DA BAYA...*  
*Book 1*  
*Page 19✍️*

***

Jay ya fita daga ɗakin ya rufe ƙofar a hankali. Amma kalaman babban yaya sun tsaya masa a rai. Lallai wannan karon akwai gwarama tunda har ya so yan jarida su sani. 

"A sanar da 'yan jarida game da abin da ya faru jiya." Shine a inda ya sake maimaitawa a zuciyarsa. Caiii, akwai rikici. Ya fada tare da wani irin makirin murmushi. 
Tsayawa na ɗan lokaci yana nazari. Tambayar kansa ya ke yi. 
Me yasa babban yaya yake son a sanar da 'yan jarida? 
Me yake shirin yi? 
Amma ya san ba shi da damar tambaya. Kuma bashi da amsar tambayar. Saboda haka aiwatarwa shine nasa kawai. 

Falon ya koma ya ɗauki wayarsa. Nan take ya fara aika saƙon zuwa ga wanda aka umarce shi. 
Bayan ya gama, ya zauna yana kallon ƙofar ɗakin Mayah. 
Mama tana lura da duk abinda ya ke yi. Tana matukar jinjina shakuwar da ke tsakanin Mayah da uncle din nata wato Jay.

"Jay, ka yi haƙuri. Kada ka bari abin nan ya karya maka zuciya. Na san kana da juriya. Amma damuwarki ita ke kara wa yayanku damuwa. Ku dena matsawa kanku sannan ku rage damuwa." 
Ya sauke numfashi. 
"Mama, ba zan iya mantawa da abin da aka yi wa Mayah ba. Ba zan taba manta yadda aka wulakanta rayuwarta ba. Mama ko rasa mahaifiyar Mayah da mu ka yi kawai ya isa." 

Hawayen fuskar ta ta share. A duk sanda ta kalli Mayah fuskar mahaifiyarta take gani. 
"Allah ne kaɗai zai iya saka mana. Amma tabbas sun cancanci hukunci. Se dai Allah yana son mai yafiya." 
Jay ya jinjina kai. 
"Amma mama dole mu nemi hakkin mu. Sannan dole mu nemi gaskiya." 

Yana cikin magana ya ji wayarsa ta yi ringing. Dauka yayi tare da dubawa. 
"An samu wanda zai iya bada bayani game da lamarin. Amma yana tsoron magana." 
Jay ya daɗe yana kallon saƙon. 
Da hanzari ya miƙe. 
"Mama, zan fita yanzu. Amma ba zan dade ba inshallah." 
"Ka kula da kanka. Ubangiji ya tsare ka. Kiyaye." 
"Ameen mama." Ya sa kai yana fita. 
Ya nufi ƙofa. Har ya kusa fita a falon ya waigo tare da kallon kofar dakin Mayah. A ransa yake fadin, "Ki yi haƙuri Mayah. Zan gano wanda ya yi miki wannan mummunan al'amari. Tabbas za mu gan su."

A ɗakin kuwa, babban yaya yana fitowa daga banɗaki. Ya tsaya gaban madubi na ɗan lokaci. 
Fuskarsa a daure take. Sam ba shi da fa'ara. Kuma kasantuwar yanayin ya kasance masa yana cikin damuwa ya sa gaba daya se fuskar tasa ba walwala. Ga wani kwarjini. Wanda har ya so ya masa yawa. Dan mawuyaci ne ka iya kallon idonsa ga da ga. Kamilalluyar fuskarsa kuwa wacce kallo daya za ka mata ka shaida haiba da nagartar ta. 

Tawul ya dauka ya goge fuskarsa sannan ya koma bakin gadon ya zauna. 
Wayarsa ta yi ƙara. 
Ya ɗauka, ba tare da ya duba ba. Dan ya san mutun daya zai kira shi a wannan lokacin. 
"Hello." 
Muryar da ke ɗayan ɓangaren ta ce, "An fara motsi." 
Ya ɗan yi shiru, kafin ya bude baki da kyar ya ce. 
"Su waye?" 
"Mutanen da ka ke nema, sir. Yau an samu babban motsi." 
Idanunsa ya lumshe. Da alama hakan dabi'arsa ne. 
"Ka tabbata?" Shine abinda ya fada. Idanun nasa a lumshe kamar mai bacci. 
"Eh, ranka ya dade dari bisa dari." 
Ya miƙe ya zauna sosai, sannan ya ce, "Ku yi hankali. Bana son a san muna bibiyarsu. Ku tabbatar kun yi komai cikin taka tsantsan. Sannan kai da Lukman kaɗai na yarjewa yin wannan aiki." 
"Inshallah haka za a yi. Na fahimta." 
Kiran ya yanke. 
Yana sauke dogon numfashi. 
Shekaru sun wuce, amma abin da ya faru da Mayah har yanzu bai bar zuciyarsa ba. Mahaifiyarta kawai yake gani a idonsa. Taya ma zai iya barin wadannan mutanen? Dole su girbe abinda suka shuka. 

Wayarsa ya dauka yana kurama wani hoto ido. Sosai ya shagala a kallon hoton. 
Hoton Mayah ce tun kafin abin ya faru. Tana ta murmushi. Se dayan wanda shi da ita ne tana cin cake ta goga masa a fuska. Ya ba ta fuska. Abin ya ba ta dariya. Take ta dariya. Dayan hoton kuwa da ya bude. 
Murmushi take yi sosai da sosai. 
Ya kalli hoton na ɗan lokaci. 
"Zan dawo miki da rayuwarki, da ka rasa Mayah inshallah."

A bangaren Inarah kuwa, safiyar ranar da hada hadanta ta fara. Kamar kullum da hayaniya da cikakken walwala. Duk da a kwanakin nan gabanta na yawan faduwa. Sannan tana yawan mugayen mafarki. Amma da yake yarinya ce mai kazar kazar se ba ta cika nuna hakan ba. Shima abokin shawarar ta yana ta kokarin barin kasar. 

Daga dakinta ta fito tana gyara hulan da ke kanta. Ba shirin fita bane a jikin ta. Da alama yau ba za ta fita ba. Ko kuma ba za ta da wuri ba. 
Ammie tana zaune tana karin kumallo. Abbie shi ba ya garin. Domin duk mazan gidan ka fi iyaye sun tafi Mambila duba gwagwgwo. Karime ba ta da lafiya. 

"Kin tashi, rabin rai? Ammie ta fada tana kallon Inarah." 
"Eh Ammie." 
Ta karasa ta zauna kusa da ita. 
"Ammie Yaya Ayzaan?" 
Ammie ta yi murmushi. 
"Ya tashi lafiya. Yanzu ma ya fita. Kin san dole se ya fita motsa jikin nan na sa na ka'ida." 
Nan take Inarah ta sauke numfashi tare da fadin, "Alhamdulillah." 
Ammie ta kall ta kawai ta yi murmushi. 
"Ammie." Inarah ta kira ta a hankali. 
"Na'am." Ta amsa cikin kulawa. 
"Ammie kwana biyu gaba na yana ta faduwa. Ina jin wani abu na shirin faruwa da Zaki na. Ko kuma wani abu na shirin faruwa da ni." 
Gaban Ammie ne ya yanke ya fadi. Dago Inarah tayi daga jikin ta ce, "Me ya faru? Ba ki da lafiya ne? Ko kuwa ki na jin alamar ciwonki zai tashi?" 
"A'a Ammie. Ba ko daya. Kawai kwana biyu ne se gabana ya dinga yawan faduwa." 
"Ki dinga addua. Ba abinda zai faru inshallah. Kin ji ko!" 
"To Ammie inshallah zan dage." 

Karar wayar Inarah da ya karade falon shi ya katse musu maganar da su ke yi. Daukar wayar ta yi. 
Ta duba screen din. 
Zarah ce. 
Ta daga. 
"Hello besty?" 
Muryar Zarah cikin zakuwa da gaggawa take fadin. 
"Lilly, ki zo office da wuri. Akwai wani sabon bayani game da case din da ki ka yi min magana a kai. Yanzu kuma wani sabon al'amari ya bayyana. Kin san kwanaki mun fara magana a kai. To ki dai maza ki fito." 
Take murmushin da ke fuskar Inarah ya gushe. 
"Me ki ka gano?" 
"Ba zan fada miki ba ta waya Lily. Ke dai ki zo." 

Inarah ta miƙe cikin gaggawa tana fadin, "Ammie ina zuwa." 
Ammie ta kall ta tare da tambayar, "Me ya faru?" 
"Ammie wani aiki ne kawai ya taso a office. Akwai bukatar in je yanzu." Ta fada tana kokarin haurawa sama inda dakinta yake. 
Mahbub ya kalle ta. Ganin yadda take komai cikin hanzari bude baki yayi ya ce, "Ki kula da kanki. Sannan ki yi taka tsantsan. Ki dena kuma binciken komai. Ki bi a sannu." 
Ta yi murmushi tare da fadin, "Inshallah Yaya. Zan kula." 
Ta nufi kofar fita a falon tana cewa, "Ammie na tafi. Sai na dawo." 

Ammie da ta kasa ko motsi itama a gurin. Haka kawai ta ji gabanta ya fadi. Da sauri ta kawar da tunanin hakan a ranta tare da yi wa Inarah fatan alkhairi da nasara a rayuwarta. 

Inarah da zuciya daya take son yin bincike akan wannan case din. Se dai ba ta sani ba cewa abin da take ta kokarin bincike zai hada case din da take bincike da wani mutum da ya dade yana binciken irin wannan sirrin.

Inarah na fitowa daga cikin falon da sauri. Tun daga lokacin da Zarah ta kira ta, hankalinta gaba daya ya koma akan ta tafi. Domin abinda suka dade suna nema ne.

Mahbub da hankalin sa ya kasa kwanciya akan ya bar Inarah ta tafi. Ya tashi da sauri ya ce, "Ammie bari na je na kai ta dakina kawai. Kasantuwar a asibiti ya kwana. Se da safe ya dawo shiyasa yau bai fita ba."  
"Yawwa Mahbub maza je kawo ta. Ni ma hankali na zaifi kwanciya."

Fita yayi yana fadin, "Lily tsaya na kaiki kawai. Wannan hanzari da ki ke yi tsaf na san gudu za ki yi da mota."

"To Yaya muje. Amma dai ka yi sauri. Allah kuwa Yaya."  
A haka suke tafiya a hanya. Wanda yau sam hirar da Inarah ta saba ba ta yi ba. Saboda hankalin ta gaba daya yana kan case din.  

Suna isa gidan jaridar na Haske Media House. Inda ake parking ya aje ta tare da fadin, "Lily ki dinga bin komai a sannu. In ki gama ki yi min waya zan dawo na daukeki."  
"Toh Yaya inshallah. Se anjima. Ina kaunarka bye." Ta fada tana wuce wa tare da daga masa hannu.  
Murmushi kawai yayi yana kallonta har ta shiga. Allah kadai ya san yadda yake kaunar kanwar tasa a rayuwarsa.  

Kai tsaye office dinsu ta nufa. Direct tayi gurin Zarah wacce ke jiran zuwan Inarah.  
"Yawwa Lily karaso ki gani." Ta fada yayin da take neman wuri kusa da ita ta zauna.  
"Ki ga labarin kuwa daya faru jiya na wata yarinya da aka yi wa fyade. Kuma yarinyar itama shekarar ta goma sha biyune. Case din ya yi iri daya da na jikar Babah Adama.  
Sannan kuma yanzu haka akwai case din a kalla sun kai guda biyar a kasa. Jiya na samu sako ta email din da muka bude. Har mun samu information akan dan uwan daya daga cikin wanda abun ya faru da su. Kuma ya ba mu cikakken goyon baya akan inda za mu hadu mu yi magana.  
Amma Lily abinda yake ba ni mamaki shine ka fin yaran da aka yi wa fyade shekara sha biyu suke. Sannan duk a makaranta daya ne suke. Ke abin akwai daure kai."  

Inarah kawai ta ke yi saboda yadda take ganin komai ya fara zuwa musu cikin sauki. Saboda sun dade suna bincike kusan watanni biyar kenan amma ba su samu komai a kai ba. Kuma babu wani wanda ya taba shigar da kara irin case din. Se mutun daya kuma suma daga baya suka nema su suka rasa duk wasu bayanai a kansu. Sun yi bincike. Sun yi ta neman abanza.  
Sun yi ta neman duk wata hanya da za ta kai su ga wanda ke bayan lamarin. Amma shiru.  
Babu wata malama ko kuma hujja da za ta kai su ga mutum guda. Cikin ikon Allah se a wannan karon suka samu information a kai.  

"Inarah ta bude baki ta ce, wai besty kin manta wata yarinya da hakan ya faru da ita kuwa? A lokacin mun so samun bayani amma komai ya cabe. Inda za mu samesu yanzu to komai zai zo da sauki."  

"Sannan ina yarinyar yanzu wacce ki ka ce yayanta ya yarda mu yi magana?"  

"Yanzu tana tare da yayan nata. Se dai shi yayan nata yana aiki a wani kamfani. Sannan bai fi wata uku da fara wa ba. Kuma abin mamaki makarantar ba ta kananun mutane ba ce. 
Se dai shi din karamin ma'aikacine wanda albashinsa ba zai iya daukan dawainiyar makarantar ba."  

Inarah ta dago kai ta kalli Zarah sannan ta ce, "To me ya sa wannan bayanin yake da muhimmanci?"

Inarah ta matsa kusa da ita sosai sannan ta ce, "Kawai mu tashi mu tafi yanzu besty gurin sa. Ba ta lokaci sam ba. Nawa ne. Tunda har ya ba mu damar hakan."  
"A'a Lily da mu bari sai gobe." Zarah ta fada tana kallon Inarah.  
"Me yasa?"  
"Bakoma. Kawai se na ga kamar zaifi."  

"Kuma sannan in mu ka je yanzu ta yaya za mu same shi? Tunda mun yi da shi se gobe za mu hadu?"  

"Mu kira shi yanzu mu ce muna hanya mana." Ta fada tana kokarin miƙewa ta dauki jakarta.  

Zarah ta kall ta ta ce, "Amma Lily, mu fara sanar da edita mana."  

Inarah ta girgiza kai.  
"Za mu sanar da shi, amma ba yanzu ba. Bana son mu bata lokaci. Sannan akwai bukatar mu yi komai a sirrince."  

Ta dauki jakarta, tana kara yi wa Zarah magana.  
"Mun kwashe kwanaki muna neman hanyar da za ta kai mu ga gaskiya. Yanzu da muka samu wata alama, bai kamata mu yi sakaci ba."  

Zarah ma ta miƙe tana fadin, "Shikenan tunda haka ki ke so. To mu tafi."

Suna shirin fita, wayar Inarah ta yi kara.  
Dauka tayi tana duba screen din. A zatonta Yaya Mahbub ne.  
Ba lambar sa ba ce. Asali ma lambar private ce.  

Dagawa tayi tare da fadin, "Hello?"  
Shiru babu amsa.  
"Hello?" Ta sake fada. Still dai shiru ba amsa.  
Tana shirin aje wayar ne ta ji wata murya wacce ba za ta iya tantancewa ba tana fadin,  
"Kar ki jefa rayuwarki cikin matsala. Sannan kar ki fara wasan da ba za ki iya ba. Ki fuskanci kalubalenki kafin ki fuskanci na wani."  

Iyakar abinda aka fada kenan aka katse wayar.  
Zarah wacce ta ji duk abinda aka fada ne ta ri ke hannun Inarah gama cikin tsoro ta ce,  
"Lily mu dakata please. Ni ina ganin mu bar wannan maganar kawai. Ina jin tsoro. Ba na so wani abu ya same ki."

Wani tunani Inarah tayi. Kawai se ta yi murmushi ta koma kan kujerar ta zauna.  
Wani ne wanda ban samu damar ganin fuskarsa ba. Yana danna waya. Da alama sako ya tura. Kuma duk bayanan da su Inarah su ka yi ya saurara. Wanda su kansu ba su san dashi ba,Amma kaf abinda suka tattauna yaji.

To jama'a ko waye wannan mutumin? Kuma ohho