Mai rabo family
*JA DA BAYA...*
*Book 1*
*Page 20✍️*
*MAI RABO ESTATE*
***
A bangaren Daddy Sulaiman kuwa, Khalid ne zaune da matar sa da 'ya'yansu guda biyu, Ameera da Ameer. Shi a Lagos yake zaune. Yanzu ma ya zo garin ne kasantuwar ƙarshen wata ya kusa. Domin duk ƙarshen wata ake gudanar da meeting na family din na Mai Rabo. Kuma duk waɗanda ba sa garin ko ƙasar sukan dawo gida.
Yanzu ma ya ɗauki hutune a wajen aiki, shi yasa suka dawo gida.
Zaune yake gefen mahaifiyar tasa suna Hira kasantuwar ba su dade da zuwa ba. Bayan gama gaisawa suka shige part dinsu don huta gajiya.
Da yamma kuwa yana zaune a falon bangarensa tare da matarsa Husnah. Yayin da Ameera da Ameer suke can suna ta wasanninsu.
Matarsa ce ta kalle shi ta ce,
"Beb tunda na zo ba na ga Inarah ba. Ko dazu su Hibba kawai na gani."
Khalid ya cigaba da duba laptop dinsa ya ce,
"Ban sani ba. Ina ganin ta tafi aiki bata dawo ba. Inarah sarkin daru da rikici." Ya fada yana murmushi. Tuna fitina irin ta Inarah kadai dariya yake ba su.
Ta jinjina kai itama da murmushi. Tana tuna yadda suka kwashe da ita wancan karon.
"Za mu ga dai auren Lily. Ni kasan Allah beb, har zuci na ke so Ayzaan ya auri Inarah. Domin kaunar da suke wa juna ba kadan ba ce. Da dukkan zuciya da jini suke son junansu. Amma ba na ji ko da wasa wani ya taba furta hakan ba. Na ga sam ba ku da niyar hakan ma gaba dayanku."
Murmushi Khalid yayi tare da fadin, "Wannan baudadden yaron wa ya ke gane inda ya dosa. Ni ina ganin shakuwa ce kawai. Ai tun haihuwarta yake kaunar ta. Ba wanda ya isa ya tabata. Duk kuwa irin rashin jinta. Dan ma kuma se ciwo ya sa ta a gaba, se duk ta yi sanyi. Amma idan ta tashi fitina ka fin estate din nan babu mai bacci. Wannan rigimar ta ita tasa wataran na zane ta aikam. A ranar dai se da fasashshen kai ma kwana. Dan kuwa tsaf Ayzaan ya rotsemin kai da dutse." Ya fada yana dariya. Tuna irin rigimar da Ayzaan yayi a lokacin.
Dariya sosai Husnah ta ke yi. Ta kall sa tana fadin, "Wa ya ga ma rotsi. Ai da se ka hada da shi kawai ka zane."
"Ki raba kanki da fitina. Ba zan iya da Zaki ba atoh. Dan fadan Ayzaan baya mutuwa." Ya fada yana dariya.
Suna cikin wannan hirar Ameera ta karaso gurin tare da fadin,
"Daddy."
"Na'am."
"Aunty Inarah fa, tunda muka zo ba mu gan ta ba?"
Khalid ya kalle ta ya ce,
"Ta tafi office. Yau kin san Aunty Inarah ba ta son wasa da aiki."
"Yau ma daddy gaskiya to ka kai ni gurinta." Ta fada tana turo baki.
"Tohhh a yi hakuri daughter. Yanzu za ki gan ta ta dawo. Maza je ki gurin Ameer ku tafi gurin Aunty Najlah ku kai ku gurin Hajja."
Ameera ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ce, "To daddy."
Ta juya zata koma. Khalid ya kira ta.
"Ameera."
Ta waigo.
"Na'am Daddy?"
"Ki tafi a hankali. Ba da gudu kin ji princess."
"To Daddy."
Ta fada sannan ta juya ta tafi.
Khalid ya waigo ya kalli matarsa.
"Ni fa halayyar Inarah Ameera ta biyo na ke gani. Dan itama akwai daru."
Murmushi tayi ta ce,
"Ameerah rigima aini na. Na dade da sanin hakan. Shiyasa shakuwarsu daban take. Ina ganin ba ranar da ba ta maganar Aunty Inarah."
Ya jinjina kai yana niyar yin magana ya ji wayarsa ta yi ƙara.
Duba screen din yayi tare da yalwataccen murmushi yana daga wayar.
"Hello, mutanen Germany."
Muryar Haidar ta fito daga ɗayan ɓangaren. Yana gaida yayan nasa.
"Yaya k. Na san kun karaso gida ko? Mu ma muna hanya inshallah. Zuwa gobe jirginmu zai sauka. Da alama wannan meeting mai zafi ne. Yadda daddy yake ta fadin kowa ya hallara yau."
"Aikam mun karaso dazu. Sannan Ammar ma ya zo. Da yawa dai sun samu karasowa. Amma daddy suna Mambila. Se dai yau za su dawo suma. Ka san gwagwgwo Karime ba ta jin dadi. Ni ma kafin mu koma ina so in je na dubata. Dan na kwana biyu ba na jeba."
"Aikam ya kamata Yaya k. Inshallah ni ma in na zo zan je na dubata. Ina my babies suke ne?"
"Aikam yanzu suka tafi bangaren Hajja." Khalid ya fada.
"Okay ba damuwa Yaya. Se mu n karaso."
"Allah ya kawo ku lafiya." Ya fada yana yanke wayar.
Khalid ya ajiye wayar.
Wata magana ta zo masa a rai. Ya na jin lallai akwai maganar da daddy ya ke so ya yi a wannan meeting. Kuma da alama tana da muhimmanci.
Kuma babu wanda ya san mene.
Sai dai kowa ya san abu ɗaya...
Idan Daddy ya ce akwai magana mai muhimmanci to tabbas akwai. Domin kuwa sam ba mutun bane mai hayaniya. Yana da hakuri sosai.
Da wannan tunani ya miƙe ya kalli matarsa, "Honey bari na dan fita na dawo."
"Okay beb. Kar ka dade ka ji?"
"Inshallah." Ya ce tare da sa kai ya fice.
Gidan gaba daya yau cikin baki su ke yi. Bangaren Hajja cike da jikoki. Haka kuma bangaren Innah.
Shi kaɗaine zaune a garden din. Kasantuwar gidan akwai jama'a. Shi kuma sam ba ya son hayaniya. Dan kansa hallau bai dena ciwo ba.
Wuri ne kebantaccen mai matukar kyau da daukar hankali.
Yanayin furannin da ke wurin kadai ya isa ya ba ka sha'awa. Ga wata iska mai dadi da ke kadawa. Gefe guda kuwa ruwa ne mai matukar daukar hankali. Furannin ne kala sun zubo cikin ruwan. Hakan se ya bada wani yanayi mai kyau.
Kwance yake saman wata tattausar kujera. Ya daura kafafunsa a saman tebur din da yake wurin.
Pajamas ne a jikin sa masu taushi. Rigar armless ce se wandon iya karsa gwiwarsa. Kansha kamar kullin gashin daure da band dan karami. Wanda in ba ka lura ba ma ba za ka ganshi ba. Gaba daya surar jikinsa ta bayyana a cikin wannan kaya. Ya yi wani irin kyau na daukar hankali.
Tunani ya ke yi. Amma shi kadai ya san me yake tunani. Wanda kai in ba ka sani ba ma za ka dauka bacci ya ke yi.
Umair ne da Mahbub suka karaso gurin suka zauna a daya daga cikin kujerun wurin.
Duk da ya ji karasowarsu hakan ba sa ya dago ba.
Kafafun nasa masu matukar kyau da taushi. Mahbub ya sa hannu ya mintsina.
"Dama na san nan kawai za a same ka. Tashi magana na ke so mu yi." Mahbub ya fada yana daukan goran ruwan da ke kan tebur din ya bude ya kai baki.
Ko motsi bai yi ba. Kuma bai da alamar motsawar ma.
Umair ma bude baki yayi. Ya ce, "Seriously ka tashi dude. Ba mu san iskanci. Kai ta faman tsotsar lips kamar mai bukatar mace." Ya karasa maganar yana dariya.
"Mata maza na ke bukata." Ya ba su amsa yana harar su.
Dariya suka tuntsire da ita gaba dayansu.
"Yaro in abinda ka ke bukata ne ai kofa a bude take. Cikin kwana daya mun maka. Dan abinda muke ta fata kenan." Mahbub ya ba shi amsa.
"Ga ka waliyyi na ko?" Ya fada yana hararar Mahbub.
Shi kam dariya kawai ya ke yi. Dan ko mace ba za ta nuna wa Ayzaan harara ba. Shi kuma hararar ce take ba shi dariya.
Kira ne ya shigo wayarsa. Da jin ringing din ya san waye. Dauka yayi ya sa a kunnensa.
"Zaki naaa." Ta fada cikin matukar shagwaba.
"Chuchu." Ya fada kamar mai rada.
"Zaki naa ka zo ka daukeni. Ka ga yau ma ba ka niba da na tashi. Ammie ta ce ka ji sauki kuma na ji hakan a jikina. Yaya Mahbub ne ya kawo ni. Ni kuma kai na ke so ka daukoni."
"Tom." Ya fada yana shirin miƙewa.
"Lallai Annu na min iyakata. Ka ji wani munafurci a gurin yarinyar nan. Ni za a nuna wa wariyar launin fata? Ka ji maguomaciya fa." Mahbub ya fada yana kallon Umair.
"Aikuwa ba na kuma daukar ta a mota ta." Ya fada tunda sam ba a muku gwanin ta. Har ina cewa yarinyar nan fa in sun gama ta kira ni na zo na mai da ta gida. Tunda ba ta tafi da mota ba. Ashe ta nuna min iyakata.
Umair dariya kawai yayi ya ce, "Se ka tattara yan kafafunka mu tafi. Tunda wanda muka zo gurin sa ya manna mana hauka ya wuce."
Miƙewa suka yi kawai suma suka baro garden din na Ayzaan.