JA DA BAYA...

The stubborn Inarah 😂

by @meelahbazata978

JA DA BAYA...
Book 1
Page 21✍️

***

Jauhaar ce zaune a falon Ammie, ta ɗan miƙe ƙafafunta, Inarah na gefe tana ɗan mammatsa mata ƙafafun da suka ɗan tasa.
Ammie na zaune tana haɗa mata kwadon zogale wanda ya sha kayan haɗi, sai kamshin abincin dake tashi.
Tun bayan samun wannan cikin nata, wanda aƙalla ya kai wata uku zuwa huɗu, da fari ba ta san tana da ciki ba. Sai daga baya, bayan Hajja ta gaya mata zuwan da ta yi, da ta gan ta sai ta ce mata ciki gare ta. Ita kuwa ta ce ba ta da komai.
Aikuwa ba a ja da nisa ba aka gwada ta. Cikin ikon Allah, gwajin farko ya nuna ciki.
Sun yi farin ciki sosai, bare ita Jauhaar ɗin, domin tana son yara sosai. Ko saboda ba su da yawa ne yasa take son ganin sun haifi yara da yawa.
Shiyasa ko planning ita ba ta yi ba. Shekarar Afeef huɗu kenan da aure.
Kuma ba ta jin wata alamar ciki sam. Shiyasa da ta san hakan sai ta yi murna sosai. Haka iyayen suka yi ta murna, kasantuwar a gidan aka mata gwajin, tunda likitoci suna da yawa a gidan.
Sai dai kamar cikin yana jiran kawai a san shi, shikenan sai laulayi ya yi mata sallama. 

Ba ta iya tabuka komai, kuma ba ta son komai. Mijin nata kuma baya garin, wani aiki ne ya kai shi Kaduna, sai kawai ta yi zamanta a gida.

Gata take samu ta musamman wajen Hajja da Ammie. Kai ba ma gurin su kadai ba kusan kowa Yana kokarin faranta mata.

Komai take so, yi mata suke. Hajja da kanta take shiga kicin ta dafa wa Jauhaar irin abincin gargajiya wanda za ta so, haka ita ma Ammie.
Shiyasa yanzu ma suke zaune a bangaren Ammie. Yawancin 'yan matan gidan suna can saboda Jauhaar akwai fara'a, shiyasa kowa yake sonta,haka itama tana son kannen nata sosai.

Zaune suke suna hira ana nishadi.
Afeef ya fita tare da Ayzaan, sun fita ne zuwa wani wuri a cikin estate ɗin, kasantuwar estate ne Mai girma,akwai gurare daban daban aciki.

Jauhaar na cin zogalenta, tana jin daɗin hirar da suke yi.
Inarah kuwa, sarkin tsokana, ta tsokani wannan ta tsokani wancan,sannan ita ana fara tsokanar ta se da fara rikicin nata.

Ta kalli Jauhaar sannan ta kalli cikin nata tace.
"Ohhh...yanzu Didi wannan Dan cikin naki fa mutun Zaki Haifa kamar Afeef ko?"ta fada cikin mamaki da zallar yarinta.
Jauhaar ta ɗago kai tana kallonta da dariya akan fuskarta,tace.
"Ehmana,lily?"
Inarah ta yi murmushi.
"Ni dai gaskiya Didi ina so ki Haifa yan biyu,se ki bamu daya ki rike daya,kokuma ki bamu duka biyun kinji didi."
Jauhaar ta yi dariya sosai tace.
"Yan biyu kike so na Haifa lily?"
"Kin san wahalar dayan ma kuwa bare biyu?Ammafa ni zanyi farin ciki ya kasance hakan ko uku ne ma ni inaso."
Ammie ta girgiza kai tana murmushi tare da jinjinawa jauhar da ta tsaya biye shirmen inarah,Bude Baki tayi tace

"Ke Inarah, kin fara ko,wai yaushe zakiyi hankali ne,girma fa kike"
"Ni fa gaskiya nake fada Ammie."

Jauhaar wacce ta cinye zogalenta ta tago ta Kalli inarah ta na cewa.
"To bari na haifi yara uku, sai na Baki daya ko biyu ni se na rike daya."
Inarah ta zaro ido,tace 
"Uku dai Didi🤔?"
Kuma da gaske za ki iya haifo ukun?
Jauhaar ta yi dariya sosai ta ce
"Eh mana. Ai kin san ina son yara."
Ammie ta katse su tana murmushi
"To Allah ya baki su, amma ki Kara kula da kanki jauhaar fatan mu Allah ya sauke ki lafiya."
"Ameen," Jauhaar ta amsa.

Inarah ta ɗan matso kusa da Ammie tana kama sannun ta tace.
"Ammie wai da gaske zata iya haifar guda uku?
Bansani ba ke ban ciki da shirmenki ni, Ammie ta fada tana cigaba da abunda takeyi
"Didi! gaskiya ina son ki sosai Amma hakanan Sena ji nafi kaunar wannan cikin na jikinki,Allah yasa ki haifo ma ta mace ta fada cikin jin dadi sosai,tace Allah Didi dama nice ke."
Dariya sosai Didi ke yi Allah kadai yasan farin cikin da takeyi inta tare da inarah domin tana Shan dariya daidai misali,dakyar ta tsagaita dariya tace
"Me yasa?"
"Saboda yanzu kin zama sarauniyar gidan nan. Kowa sai yayi tacewa ke,yanzu duk sunfi sonki akaina ta fada tana turo baki .
kowa se ya tambayi ya kika tashi me kika ci, me kika sha,me kike so,Ina ga Didi har wanka ma fara yi Miki za'ayi."
Ammie ta yi dariya sosai tace Allah dai ya shirya min ke inarah
 Ciki ba wasa bane dole kowa ya lallaba ta "
Jauhaar ta ɗan yi murmushi tana kallon Ammie tana Jin kaunar ta har zuciyarta.
Kallon Ammie inarah tayi sannan tace"Ammie yanzu kenan nima innayi ciki haka Zaki dinga min duk abinda nake so?
Dariya duk sukayi.
Hibba tace sosai kuwa har da goyo ma Zaki dinga samu.
Itama zaitoon haka ta Fadi suna dariya.
"Wow Allah ya saka hakan,ai da Dena tafiya zanyi Allah duk inda zani ko bayi ne sedai a goyani,har abinci na dena taunawa se dai a tauna abani,hohhh ni inarah,ta karasa maganar tare da gwada yadda zatayi.
Dariya suke Yi sosai cikin nishadi da walwala hadi da farin ciki.
Gaskiya Ammie kina shagwaba Didi Allah,inji hibba ganin yadda take bare gyada dafaffa tana ba Didi.
Ba ruwanku atoh,kinsamin Ido yarannan inji Didi tana musu harar wasa, Ammie sa Ido suka zo Yi mana,ki barsu kici gaba da bani kulawa.
"Ba kulawa kawai ba jauhaar,kome kikeso zan Miki Inshallah ,ke Idan kika ce kina son mangwaro da tsakar dare ma, zan tashi na nemo miki, Ammie ta fada cikin sigar wasa"
Dukkansu dariya suka fashe da ita.
"Yanzu fa nima haka zan dinga cewa inason abubuwa da yawa innayi ciki ko?inarah ta fada bilhakki da gaskiya"
"Ki gwada mana inji zaitoon,ahaka ma ya mu kabkare da ke,wai hmm zaa ga shirme agurin mata"
Dukkansu suka yi dariya.
Didi to wai cikin akwai wuyane,nifa inason cikin gaskiya Amma bari na fara Jin in akwai walaha se na hakura.
Inbaki rabani da zancan cikinnan ba jikinki ya gaya Miki inarah, Ammie tafada tana jefawa inarah follow din hannunta.

 babu wanda ya lura da Ayzaan wanda yake dauke da Afeef Wanda ke bacci a kafadar sa.
 tsayawa yayi yana kallonsu na ɗan lokaci Wanda tunda inarah ta fara zancan ciki yana jinta yadda ta kuke tana misalta yadda zatayi besan ya danyi murmushi ba ,sedai Jin sautin murmushin yayi kafin ya Tako a hankali cikin izza.
"Dariya bata Miki wuya haka kuka"yafada Kuma ya fuske kamar ba shine ya ce ba.
Inarah ta waigo da sauri Yana kallonsa tace"Kai Zaki na kayi kyau sosai,shine baka jira mun fita tare ba.

Ayzaan ya yi murmushi kawai ya karaso ya kwantar da Afeef a kujerar Wanda yake baccinsa hankali kwance.
"Didi ya jikin?"
"Alhamdulillah, bobo ya kake?"
zaunawa kusa da ita yayi, yana kallon yadda Ammie ta bare mata gyadar a Wani Dan bowl me kyau.ga sauran abubuwan da ta cibwasu ma bata Kara sa ba
"Didi duk ke kadai kika ci wannan.?"
Dariya tayi tace ehmana bobo
"Kin cika ci da yawa Didi,yafada Yana tabe fuskarsa."
Ammie barka da gida mun dawo .
Barka dai Zaki sannu da dawowa. 
Jauhaar ta kalle shi tana murmushi sannan ta waiga ta Kalli Afeef da ke bacci Wanda Ayzaan din yayi wa gyaran gashi irin nasa,Wanda yayi matukar Yi masu kyau
"Ka ga yadda kayi kyau kuwa sosai bobo Kaida Dan naka,kowa da yake gurin SE da ya dago ya Kalli irin kyawun da sukayi.
Yaya Allah kayi min kyau sosai,Dama baka fita ba,yakarasa magana idanun ta na yawo ajikin jikin nasa.
Zaki na, nace idan Didi ta haifi yara biyu ni ce zan zama mai kula da su ko."
Kafin ya bata amsa jauhar tayi caraf tace"
"Ke dai lily ki fara koyon yadda ake riƙon jariri,Dan naga ko rike jarirai Baki iyaba,maga da yadda.zaki iya ,kiyi rainon jaran"
Inarah ta turo baki.
"Ni na fi ki iyawa ma kika didi."
Dukkansu suka sake fashewa da dariya.