BABAN KAWATA

Chapter 16

by @smauta

Wannan shine karo da farko dataji yayi mata magana mai dadi tun bayan kalma ɗaya daya fadamata wadda har yanzu take dawainiya da ita cikin ranta, _STAY AWAY FROM ME_ .......



Har lokacin manar na kwance idonta a rufe zazzabin data kwana dashi ya sauka,hamdala yayi a ransa sannan yace kiddo banza tayi dashi dan ta tsani yace mata kiddo din nan,wake up ga toilet nan ki shiga anyi sallah asuba kar lokaci ya kure maki,sai lokacin tace ni bazanyi sallah da wannan kayan na jikina ba...........




Satar kallon ta yayi kadan ya tuna kayan jikin nata sun sha wahala dafe kanshi yayi yace ni yanzu ina zan samo mata kaya 24/7 wata zuciyar tace masa da sauri ya mike tsaye yace 20mnt, parlour ya fito makullin mota ya dauka dake aje nan da sauri ya fice gidan da jijjifin asubar nan,duk abinda zata bukata ya hado mata gudu yake shararawa akan titinan abuja kamr zai tashi sama.........





Yadda yabar ta haka ya dawo ya sameta,gabanta ya ajiye ledojin tashi zaune ya iya cemata a hankali koda ta mike zaunen sabon kuka ta saka mashi,hey what's wrong bakinta na kyarma tace dan Allah ka kaini wurin kakata nasan sunacan hankalin su tashe tana cikin ciwo na taho nabaro su kar in rasa kaka dan Allah,kirrrr ya kura mata ido yanaso ya tabbatar da gaskiyar maganar ta ko karya take,kiyi wanka zansa a kaiki wurinta...............





Zaune take parlour tana shan tea zuciyar ta na suleja Dr ne ya shigo da a kalla zaikai shekara hamsin haka,dr ya kalli boss wannan ce patient din tawa? Bashida lokacin su da hannu ya nuna mashi ita kawai..........




Ina kafar?a hankali ta mike kafarta kallon kafar yayi ta gefen ido data fito cikin doguwar rigar ta fara tasss wani makoko yaji yana neman tokare sa ya danne,dr yace mata ya jikin fuskar ta itama a daure ta ansa da sauki.......




Bandejin ya warware ya shiga dressing kafar dakyar tabari aka idasa magungunan daya zo mata dasu ne ya bata ya kalli boss zanyi mata allura guda 2 for kafan nata da kuma zazzabi,baigama rufe baki ba tace wlh bazaaman allura ba ka gayama shi naji sauki wallahi..................




Tsaki yaja ya mike tsaye har gabanta yazo a hankali ya mikar da ita tsaye tana tsaye ta zubama sarautar Allah ido,hannu yasa ya daga rigar ta baya daga ƙasa zuwa sama jikinta ne yashiga rawa sosai fararan cinyoyinta suka masa sallama da bakin pant din ko underskirt babu kallo biyu yayiman wurin ya sakemata rigar ta,ka ajiye allurar zanyi mata..............




Kalmar karshe da yafada ta kara nanatawa waye zaiman allurar a hankali ta sulale ta zaune tattara komatsan shi dr yayi ya fice yabar masu parlourn.............




Ba mai cema kowa komai ga sanyin AC daya karade parlour sarai yagane AC ta mata yawa yaki ya rage,kasala ta rufe mata jiki a hankali ta kishingida gefen kujerar kamar jira take bacci yayi gaba da ita,wayar shi ta yi ringing kamar bazai dauka ba ya karata a kunne.........



Daddy muryar halim inata kira baka picking am not feeling ok ne,meke damunka daddy allergy dina ya taso ruwa ya bigeni jiya, subhanallahi Amma da sauki yeah alhamdulillah........




Ya cairo daddy cairo akwai dadi murmushi yayi sannan yace kina bukatar wani abu ne?a'a yaushe zakazo banida lafiya fa Egypt air kinsan bazasu daukeni a wannan condition din ba,but anytime na samu lafiya zaki ganni idan banzo ba kuma end of this month zamu hadu a China chill baby ya latse wayar............





Halim tayi murmushi tasan halin kayanta yadda ya katse wayar nan tana kara kira fada zasuyi number manar tashiga dailing har yanzu dai abu daya ake fadamata a kashe,kifar da wayar tayi a kasa tace Allah yasa dai lafiya 🥺🥺


       LAFIYA TANA KARKASHIN KULAWAR BABAN KI😂😂😂😂✌️


Kanta a langwabe daka gani kasan baccin wahala ne tsam ya taso daga inda yake ya dawo kan 1 seater da take ya dauketa ya dora akan kirjin shi lamo manar tayi kamar ta samu katifa ta cigaba sharara baccinta da kafar shi ya matso da centre table na parlour gefen shi yana aiki a system har kusan laasar manar bata farka daga baccin ba shima kuma bai sauke ta har bacci yayi nasarar dauki shi a haka..................





Mutsu mutsun manar ya tashe shi, kallon kanta tayi taga inda take da sauri ta duro kasa har saida kafar ta tayi dan kara ta kara kallon jikinta sannan tace me kayimani??????



Wata zuciya tazo mashi wannan karamar yarinyar me take ta maida shi?bakin kofar parlour ya buɗe sannan ya kalleta yace stay out of my house now👉👉abinda ya faru da ita daren jiya ya dawo mata sabo tsoro ya kara shiga zuciyar ta kafarta taja bata wuce ko ina ba sai dakin da ta kwana jiya tsaki yayi yafice gaba daya yabar gidan main house din shi ya tafi ko zai samu saukin bacin ran yarinyar can.......





Tun tana sa ran dawowarsa taji shuru bayan isha taji ana buga mata kofa a tunanin ta shine yasa tace wallahi ba zan bude kofar nan ba ka bude ka shigo,budo kofar akayi wata mata tagani da fararen kaya tashigo sannu mah boss ne yace akwai allurar da za'a miki,bakinta na kyarma tace eh eh sunacan parlour komawa nurse tayi ta kwaso harda magungunan ta dawo haɗa alluran tayi ta nufo ta ,tsaya dan Allah ki zubar da alluran nan dan Allah sai kice masa kinyi man........




Zaro ido nurse tayi tace a'a bazan iya ba ,ba zafi kiyi hakuri ayi maki da kyar tabari akai allurar nan harda kukanta haka nurse dai ta fice tabaro ta, lokaci take dubawa ko zataji shigowar sa amma shuru tun tana gyangyadi ta tashi har bacci mai nauyi ya kwashe ta da tunane tunane fal a ranta............