MATAR GIDA PAGE 11
MATAR GIDA 011
SHUUKRAN/022
P11
Zaune yake cikin office ɗinsa ya rabka uban tagumi tunani yake kan yadda zai yi da yaran,har cikin zuciyarsa ji yake bazai iya riƙe yaran shi kadai ba,yana buƙatar wanda zai taimaka masa wajen kula da yaran,daga ranar Lahadi zuwa yau talata gaba ɗaya ya galabaita da hidimar yara daga yammacin jiya littini zuwa safiyar yau talata ya fara nadamar sakin Amirah da ya yi,ya kuma jinjina mata wajen kula da yaran,kwanaki biyu da ya yi da yaran ya ji gaba ba zai iya ba,ina kuma ga ita Amirah da kullum take tare da su,sai yanzu ya gane gaba ɗaya Amirah bata da kazanta yaran ne ke yawan ɓata gida ita kuma tana iya bakin ƙokarinta wajen kula da gida,Amirah bata taɓa tafiya wajen aiki ba tare da ta gyara gidan ba haka zalika komai dare sai ta gyara ko ina kafin ta kwanta,ga damuwar yara kowanne da nashi damuwar Suhail yawan tambaya,Sudais mantuwa, Rayyan da Afef a kullum sai sun yi dambe sau biyar zuwa shidda,Ummu Abiha cin abincin makaranta a mota wani sa'ilin sai yi ta magana ita kadai,Sumayya tafiya makaranta da hijab biyu,ga kuma Fauziyya chewing gum,wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya tuna da maganar da Amirah ke yawan yi masa kan yaran kan cewar Sudais na ɓukatan addu'a saboda mantuwan sa ya yi yawa,Rayyan ma yana buƙatar addu'a saboda zafin zuciyarsa babu wuya ya yi fushi da ko ma waye dambe yake,sai Ummu Abiha da wasu lokuta ta zauna ita kaɗai ta yi ta magana,amma sai ya banzatar da maganar ta a ganinsa laifin ta ne ita ta maida yaran haka,a sanyaye ya dauki wayarsa ya yi dailing number plumber da ya saba masa aiki,bayan plumber ya amsa ne Ɗalha ya ce masa in ya samu lokaci zuwa karfe shidda ya zo gidan sa akwai gyaran da zai masa plumber ya ce babu matsala zai zo
Bayan Ɗalha ya gama waya da plumber ne kiran Ammi ya shiga,sai da zuciyarsa ta yi wani irin bugu nan take hankalin sa ya tashi, wani irin zufa ya feso masa,ya kafe screen ɗin wayar da ido har wayar ta tsinke bai iya ɗaga ba,yana shirin kiranta kira ya shigo wayar Ammi ce ke kira sai da ya saita nitsuwar sa kafin ya samu ya amsa kiran shiru Ammi ta yi ba ta ce komai ba,cikin rawar murya Ɗalha ya yi sallama nan shiru Ammi ta yi bata amsa ba,hakan yasa hankalin Ɗalha ƙara tashi,sosai Ɗalha ke tsoron Ammi,Ammi irin uwayen nan masu tsauri sam bata wasa kuma bata son wargi Ɗalha da Husnah sunfi sabawa da Abba kan Ammi tun suna ƙananu Ammi bata wasa dasu sam bata son a yi mata ba daidai ba,ba iya Husnah da Ɗalha ba kusan gaba ɗaya ƴaƴan dangi kowa tsoron Ammi yake kamar soja haka take,hakan ya samu asali ne daga wajen mahaifinta soja, kasancewar ita kaɗai ce ƴarsa hakan yasa ya reni ta kamar namiji tun daga primary har secondry dama jami'a duk na sojoji ne Ammi ta yi hakan yasa ta taso kamar namiji,sai da aka yi da gaske kafin mahaifinta ya hakura ya barta ta yi aure amma da cewa ya yi aikin soja zata yi,a wancan lokacin kuwa aikin soja ba na mace bane musamman musulma,jin shirun ya yi yawa yasa Ɗalha faɗin ''barka da safiya Ammi'' bata amsa gaisuwar da ya yi mata ba ta yi magana cikin karkausar harshe ta ce ''ka dawo da matarka?" handkerchief dake daure kan tebur ɗinsa ya dauko ya share zufa kafin ya yi magana cikin rawar murya ya ce ''har yanzu ina kan duba ta'' cike da ɓacin rai Ammi ta ce ''ban gane ba,kana nufin har yanzu baka san inda matarka take ba?" Ɗalha da hankalin sa ya gama tashi ya ce '' Allah ya huci zuciyar ki,ina iya bakin ƙokari na amma har yanzu babu labari'' wani irin murmushi Ammi ta yi ta ce ''kana wasa da ni Ɗalhatu'' Ɗalha na shirin magana Ammi ta kashe wayarta,a hankali Ɗalha ya cire wayar daga kunnesa ya aje kan tebur nan take Ɗalha ya ji ciwon kai da ya kwana ya tashi da shi ya ƙaro,jikinsa har rawa yake ga wani zufa dake ƙara feso masa,sanin kansa ne akan Amirah Ammi zata iya shiga mota ta zo har Kaduna ta yi masa rashin mutunci,a duniya daga Allah da Manzonsa sai Ammi Ɗalha ke tsoro,a hankali ya daura kansa bisa tebirin gaban sa yana nanata kalmar innalillahi wa inna ilaihi raji'un
Bayan Ammi ta kashe waya cikin tashin hankali ta kiran layin matar baban Amirah,kafin kiran ya shiga Ammi ta yi sauri ta katse kiran tunawa ta yi da halin matar baban Amirah ba wani kirki ne da ita ba,yanzu haka ƙila ma bata san abinda ke faruwa ba saboda gaɓa daya Amirah da ƴan uwanta basa gabanta rayuwata kawai take ita da ƴaƴenta cikin gidan,lokacin da Amirah ta haifi Ummu Abiha da Suhail dake aiki aka yi mata Abba ya ce Amirah ta koma gida a kula da ita,haka matar babanta me suna Hafsah ta nuna halin ko ina ga Amirah da ma abinda ta haifa,bata bawa Amirah abin kari sai sha biyun rana,wata rana Ammi ta kaiwa Amirah ziyara taga halin da Amirah ke ciki hankalin ta ya yi mugun tashin hakan ya sa ta dauki Amirah ta maida ta gidanta,layin Abba Ammi ta kira bugu biyu ya ɗaga wayar bayan sun gama gaisawa ne ta faɗa masa yadda suka yi da Ɗalha inda ta daura da ''Alhaji ina tunanin yarinyar nan ta yi fushi ne ƙila ta je gidan wani daga cikin ƴanuwanta ko cikin danginsu,kaga dai mu a nan babu inda bamu bincika ba kowa cewa yake bata gidansa,Alhaji ina tunanin zuwa in samu babanta mu yi magana ta fahimta in tana wajensu ne dan Allah su sanar mana dan hankali na ba a kwance ya ke ba'' Abba ya yi shiru yana sauraran Ammi kafin ya ce ''A'a Zainab kar ki yi haka da kaina zan je wajen mahaifinta da na tashi a office wannan maganar bata shafe ki ba ki bari zan yi duk wani abinda ya dace'' Ammi ta ce ''to shikenan Allah yasa tana can gidan nasu'' Abba ya ce ''Ammen''
Yayah Nasir ne zaune cikin parlour mahaifinsu daga gefinsa ƴan uwansa ne duka su shidda Muhammad Nasir, Muhammad Ahmad,Abdullahi,Yahuza,Ibrahim,sai autansu Muhammad Kabir,duk sun yi cirko cirko,daga can gefi kuwa matar babansu ce zaune hannunta riƙe da babyn ta ƴar watanni goma,hankali kwance take baiwa yarinyarta nono hannunta riƙe da waya tana kallon reals ɗin facebook amma ta rage murya sosai inda ita kadai ke jin muryar video ɗin,parlour ya yi shiru baka jin motsin komai sai ƙarar Ac da kuma video da anty Hafsah ke kallo mahaifin Amirah Alhaji Jibril Ahmad ne ya sauke wata ajiyar zuciya ya ce ''ku ka ce babu wanda ta je gidansa" duk suka amsawa mahaifinsu da ''eh'' Baba ya ce ''jiya na yi magana da Alhaji Abubakar ƙanin mahaifiyar ku ya tabbatar min bata wajen su,har ƴan uwan mahaifiyar ku na can ƙasar Chadi duk na yi magana da su su tabbar min bata can'' shiru parlourn ya yi na wasu ƴan sakanni a hankali Kabir ya fara magana ya ce ''ɗazu na hadu da wani abokin karatun ta wanda muka yi Sakandire ɗaya ni da shi da ita yayah Amirah,tare suka gama jami'a da ita yayah Amirah ajin su ɗaya,bayan mun gaisa ne na faɗa masa halin da muke ciki ya tabbar min lokacin da suke karatu Ɗalha ya raba Amirah da ƙawaye gaba ɗaya,bata da ƙawa ko ɗaya amma ya faɗa min zai sa maganar cikin group ɗinsu na makaranta ko Allah zai sa a dace'' Baba ya ce ''to Allah ya baiyana ta,abinda ya kamata mu yi shine mu dage da addu'a sosai duk inda take Allah ya bayyanar da ita Allah ya sa bata faɗa a mammunar hannu ba'' duk suka amsa da ameen
Kamar yadda Abba ya faɗa bayan tashin sa a office bai tsaya ko ina ba sai gidan su Amirah dake G R A Kano state,nan parlourn Baba Abba da Baba suka zauna bayan sun gaisa ne Abba ya kwantar da murya ya fara bawa Baba hakuri kan abin Ɗalha ya yi,ya kuma nuna rashin jin ɗaɗinsa a kan hakan,Baba ya ce babu damuwa ƙaddarace haka Allah ya tsara babu wanda ya fi karfin ƙaddara,ita kuma Amirah ta yi kuskure da ba zo gida ba,yanzu haka ba'a san inda take ba,cike da mamaki Abba ke kallon Baba inda ya ce ''kenan kuma baku san inda take ba'' Baba ya ce ''wlh Alhaji har Chadi na bugawa ƴanuwan mahaifiyarta waya amma sun ce bata can ƴan'uwana dake nan Kano duk sun tabbatar min bata gidansu'' shiru Abba ya yi kafin can ya ce ''tabbas Ɗalhatu ya ƙure yarinyar nan,yarinyar da ko magana bata cika yi ba''Baba ya yi murmushi ya ce ''ko ma dai ya nene bai dace ta tafi wani wajen ba alhali duk muna raye'' Abba ya ce ''haka ne'' haka dai Abba da Baba suka yi ta tattauna batun Amirah daga karshe dai Abba ya yiwa Baba sallama
Karfe shidda da mintina goma Ɗalha ne tare da plumber cikin bathroom ɗinsu Sudais plumber na gayra yadda Ɗalha na tsaye yana yi masa hira,gyaran bai dauki lokaci mai tsawo ba plumber ya gama gyaran,har kofan gida Ɗalha ya yiwa plumber rakiya bayan ya biya shi ƙudi aiki,yau ma kamar kullum bayan shigar Ɗalha gida kitchen ya wuce ya daurawa yaran tuwo semonvita da miyar ɗanyar ƙuɓewa,yana aikin abinci yana wanke kwanuka,bayan ya gama wanke kwanuka ya shiga gyaran gida da ɗakuna ya fara in ya gyara nan su ɓata can da abin ya ishi shi bulala ya dauka ya nuna masu ya ce duk su zauna waje ɗaya duk wanda ya tashi zai zane shi,hakan yasa sun nitsu,Allah ya taimake Ɗalha kusan duka yaran suna tsoronsa Rayyan kaɗai ke yi masa taurin kai shima ba kullum ba,karfe goma da rabi Ɗalha ya gama yiwa yaran homework inda ya ce duk su dauki jakarsu su sa homework cikin jaka yana kallon su gudun kar wani ya sake manta homework a gida kamar yadda Sudais ya manta nashi yau,bayan ya tabbar sun sa homework cikin jakukkunan su ya wuce kitchen ya yi sarving ɗinsu tuwo,wani babban faratin ya dauko ya sa masu tuwo a cikin saboda ya samu sauƙin wanke wanke,daidai lokacin da ya dauki farantin da niyyar barin kitchen ɗin ne ya yi karo da Fauziyya dake manne da ƙafarsa bai san sanda ta biyo shi kitchen ba kafin ya ankare ya yi wata mammunar faɗuwa kasan tiles inda ya buga baki a tiles,Allah ya taimaka tuwo bai zuba ba,amma miyar dake cikin faranti ya wistilo ya ɓata kasan kitchen da bangon kitchen ɗin, lokaci guda kitchen ɗin ya hargiste kamar ba ɗazu ya yi morping ɗin kitchen ba,runtse idanu ya yi bakinsa na masa wani irin zafi murya can ƙasa ya ce ''wash'' kukan da Fauziyya ta fara ne yasa ya buɗe ido yan ƙare mata kallo ji ya yi kamar ya kama ta ya yi mata dukan tsiya,amma ya ƙasa har sannan yana kwance ƙasan kitchen ga farantin tuwo a hannusa,cikin hausarta da bai fita da kyau ta ce ''Dady goya ni inji balci'' Ɗalha na shirin tashi zaune Suhail ya shigo kitchen ɗin ganin Ɗalha kwance ƙasa riƙe da farantin tuwo Suhail ya ce ''me haka Dady?me ya faru? faɗowa ka yi? ina kuma za ka kai tuwon to?
SHUUKRAN