MATAR GIDA 12
MATAR GIDA 012
SHUUKRAN
P12
Shiru Ɗalha ya yi yana ƙarewa yaran kallo,shi dai Suhail ya kafe babansa da ido yana jiran amsar tambayoyin sa,a hankali Ɗalha ya miƙe tsaye yana ciza baki,sosai bakin ke masa zafi,murya Suhail ya ji ya ce ''me ya sameka a baki Ɗady?" Ɗalha bai tanka sa ba kawai ya ƙara masu miya cikin tuwon daga haka ya fita zuwa parlour,bayan fitarsa daga kitchen ne idonsa ya sauka kan Sumayya dake wasa da jakar makarantarta inda take jefa jakar a sama,Ummu Abiha kuma ta kwaso takalmar Amirah tasa tana tafiya har wani yanga take,tana magana ita kadai kamar wani na gefinta,daga can gefi kuma Rayyan ne ya haɗe Afef da bango tare da shaƙe masa wuya,kallo ɗaya Ɗalha ya yi masu kafin ya ƙaraso cikin parlourn ya aji farantin tuwo nan ƙasan parlour,mayar da dubansa ya yi ga Sudais dake kwance yana wasa da motar wasa,ya ce ''tashi ka je ka wanke hannu ku ci abinci'' babu musu Sudais ya tashi ya wuce kitchen ya wanke hannu kamar yadda Ɗalha ya faɗa masa,a hankali Ɗalha ya tako har inda Rayyan da Afef suke ya daura hannusa kan hannu Rayyan,Rayyan na ganin haka ya yi sauri ya saki wuyar Afef,nan Afef ya kwanta ƙasa ya fara tari,shi kuma Rayyan ya sa kai ƙasa yana jiran hukuncin da mahaifinsa zai masa, kallonsa kawai Ɗalha ya yi kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce ''je ku wanke hannu ku zo ku ci abinci'' tun sanda Ɗalha ya shigo parlour Ummu Abiha da Sumayya sun shiga rigar nitsuwa tun ma ba Ummu Abiha ba,tuni ta cire takalmar Amirah ta ɓoya bayan kujera,ba tare da ya kalli inda suke ba ya ce ''go and wash your hands''duk suka wuce kitchen,waje Ɗalha ya samu kan kujera ya zauna yana jin yadda kansa ke sara masa,ya runtse idanunsa,Fauziyya dake tsaye cikin kitchen tun ɗazu ta fito parlour ganin babu wanda ya kulata yasa ta matso inda Ɗalha ke zaune ta tsaya kusa da kunnensa tana rera kuka,har cikin kwakwalwarsa yake jin sautin kukan nata,hakan yasa ya miƙo mata hannu har sannan idonsa rufe a hankali ya ce ''zo nan ya isa haka''Fauziyya kamar jira take ta wani haye cinyarsa ta kwanta a jikinsa,Ɗalha ya kai hannu bayanta yana buga mata baya a hankali alamar rarrashi,tunawa ya yi da maganar Ammi murya can ƙasa ya ce ''ya Allah'' nan ya fara tunanin yadda zai gano Amirah,yana cikin tunanin ne ya ji muryar Afef ya ce ''Dady kaga Rayyan ko'' a hankali Ɗalha ya buɗe idanunsa da suka yi masa nauyi sosai ya sauke su kan Rayyan lokaci guda suka haɗa ido mugun kallon da Ɗalha ya masa ya sa Rayyan sauke idonsa da sauri,har suka gama cin abinci Rayyan bai sake takalar wani ba,karfe sha ɗaya daidai duk yaran sun yi barci saida Ɗalha ya tabbar da kowanne su ya yi fitsari kafin ya koma parlour ya zauna yana mayar da numfashi yana jin yadda kansa ke sara masa,wayarsa dake kan doguwar kujerar parlour ta fara ƙara alamar shigar kira,da ƙyar Ɗalha ya miƙe ya dauki wayar Unaisa ce ke kira, tun karfe tara take kiransa bai ɗaga ba,ɗazu ya tura mata saƙo cewa ya gaji sosai da hidimar yara yanzu haka kansa ke masa ciwo ta yi hakuri suyi magana gobe,amma ta cigaba da kira,da fari ya yi tunani bata ga saƙon da ya tura mata bane sai kawai ya amsa kiran bayan ya amsa kiran sun gaisa bata yi masa ya jiki ba kawai sai cewa ta yi gobe tana son zuwa salon ya tura mata ƙudi,Ɗalha bai iya bata amsa ba kawai ya katse kiran ya cigaba da aikinsa,riƙe wayar ya yi yana ƙarewa screen ɗin kallo har kiran ya katse,bayan yankewar kiran ne ya kashe wayarsa gaba ɗaya,kan doguwar kujerar dake parlour ya yi kwanciyarsa da Fauziyya a kirjinsa
Karfe ɗaya daidai na dare Fauziyya ta farka tana faɗin ''Dady indomie'' a hankali ya buɗe ido kafin ya yunƙura ya tashi zaune,saida ya dauki a ƙalla mintina biyu zaune yana jin yadda kansa ke sara masa amma yanzu da sauki sosai ba kamar ɗazu ba,a hankali ya tashi ya wuce kitchen ya kunna wutar kitchen ɗin nan take haske ya gauraye kitchen ɗin gaba ɗaya idonsa ne ya sauka kan miyar da ya zuba ɗazu ƙasan tiles gaba ɗaya kitchen ɗin ya yi datti sosai saboda ɗazu su Sudais sun shiga wanke hannu sun zubar da ruwa kasan kitchen ɗin hakan yasa ruwan ya haɗu da miyar da ya zuba sai kitchen ɗin ya yi datti sosai kamar an yi sati ba'a share ba ko morping jiki babu kwari Ɗalha ya wuce pantry ya dauki indomie da kwai tare da wani karamin pot,ya tare ruwa a fanfon kitchen kafin ya daura pot ɗin kan gas tare da kunna gas ɗin,mopper ya dauko tare da buket ya shiga morping kitchen ɗin bayan ya gama morping ne ya goge bango inda miya ya zuba,karfe ɗaya da rabi Fauziyya ta gama cin indomie da ya dafa mata,ruwa ya bata ta sha ya wanke mata baki kafin ya wuce ɗakin yaran inda ya kaisu bathroom suka yi fitsari kafin ya wuce ɗakinsa tare da Fauziyya,bayan shigarsa daƙi ne ya shimfiɗa Fauziyya kan bed,daga nan ya wuce bathroom ya dauro alwala,bayan fitarsa daga bathroom ya shimfiɗa darduma ya tada sallah,nafila raka'a huɗu ya yi kafin ya daura da shaf'i da wutri,karfe biyu da rabi ya tashi daga darduma bayan ya shafe addu'a bai tsaya ɓata lokaci ba ya kwanta kan bed bayan ya yi addu'a ya tofawa Fauziyya shima ya shafe jikinsa da addu'a
Amirah zaune take cikin ɗakin hotel ta rabka uban tagumi,tunanin ƴaƴanta cike cikin zuciyarta,kwanaki uku da tayi bata tare da yaranta ba ta ji kamar shekaru uku ta yi ba tare da su ba,a hankali ta sa hannu ta share hawaye da ya gangaro mata,murya can ƙasa ta ce ''ya Allah ka kara min hakuri da juriyar rashin ƴaƴana kusa da ni'' ta kare magana tana share hawaye da ya gangaro mata,jiki babu kwari ta tashi ta wuce kitchen ɗin da dake hotel room ɗinta ta yi worming jollof pasta da ta siya tun ɗazu,bata wani ci sosai ba ta wuce bathroom ta yi wanka,bayan fitar ta daga bathroom shirya kanta ta yi cikin wata doguwar riga abaya green colour ta yi rolling kanta da wata farar karamar gyale,sunglasses ta sa daga haka ta dauki farar hand bag ta fita daga ɗakin,bata tsaya ko ina ba sai harabar hotel wajen swimming pool,inda ƴan mata da samari ke zaune kan kujera suna hira,waje ta samu can nisa inda babu mutane sosai ta zauna ta shiga bin wajen da kallo tun zuwanta hotel ɗin sai yau ta zauna a wajen swimming pool abinda ke fita da ita daga ɗaki siyan abinci da ta siya zata koma ɗakinta
SHUUKRAN