Hs 33
by @legendspen
_Page 33_
"Bhatool ki tsaya." Amma ta yi banza ta ci gaba da tafiya, tafiya take bata kallon gabanta shi kuma yana bin ta a baya da sauri da sauri, cikin rashin sa'a mota ta fito daga wani gida a guje kafin ka ce wani abu Bhatool ta yi sama ta dawo ƙasa, a ruɗe mai tuƙa motar ya fito yana faɗin. "Innullahi wa'ina illahir raji'un." Dai-dai lokacin Senate ya ƙaraso yana faɗin. "Bhatool! Bhatool." Wancan ne ya fara ƙoƙarin ɗaukan ta zai sa ta a mota, Senate ya kai masa wata mahaukaciyar cakuma sanan ya ce. "How dare you're, karka kuskura ka ce zaka kai hannu jikin matata."
"And so f**cking What dan tana matarka, ni na buge ta ni nake da right na kai ta asibiti." Gayen da ya buge Bhatool ɗin ya faɗa. "You're very stupid, bakasan abinda ake cewa mata ba?, she is my wife."
"Bayin Allah, ba cece-kuce zaku tsaya yi ba, ku kaita asibitin baku ga halin da take ciki ba." Wani mutumi da ya jiyo hayaniyarsu ya fito daga gidan da yake gadi ya yi musu magana, Senate ya sunkuya ya ɗauke ta shi kuma gayen ya buɗe masa motarsa, ba dan Senate ya so ba ya shiga motar suka tafi zuwa Asibiti. Kasancewar unguwar ta masu hannu da shuni ce babu nisa da wani makeken asibitin kuɗi, kai tsaye aka amshi Bhatool a a ɗakin gaggawa, tsyawa ya yi a bakin ɗakin yana ƙoƙarin daukan wayarsa, sai a lokacin ya tuna da cewa yabar wayar a gida. "Ya Allahu." Ya faɗa a fili, sanan ya kai kallonsa ga gayen da ya buge Bhatool. "Me wanan Bitch ɗin yake a wajen?." Ya tambayi kan shi, ƙarasawa ya yi inda yake sanan ya ce. "You can go." Kallonsa ya yi sanan ya ce. "Wai kasan me na yi kuwa?, mutum na buge, rai guda ana halim rai ko rayuwa amma sabida wani banzan kishinka zaka ce i can go, to bazan tafi ba ina nan." Tsaki Senate ya ja kawai, sana ya koma wajen da ya baro ya zauna.
Kusan mintuna ashirin suna zaman Doya da Manja, duk wanda ya kalli ɗan uwansa sai ya zabga mai harara. Likitan ne ya fito daga cikin ɗakin, a tare su ka taso su ka tare shi har suna haɗa baki wajen faɗin. "Doctor how is she?."
"Calm down! Yanzu za'ayi payment na dubu ɗari uku, sanan jikinta yana good condition, kawai sai zazzaɓi da ciwon kai da take fama da shi, wanda yana da alaƙa da damuwar da take ciki."
"Okay ina za'ayi payment?." Gayen da ya buge ta ya faɗa. "No you don't have too, matata ce zan yi da kai na." Senate ya tare shi. "Amma ai nina bugeta, haƙƙinane."
"Na ce karkayi." Senate ya faɗa a tsawace. "Sir ayi haƙuri bamasom hayaniya anan, muna da marasa lafiya." Likitan ya faɗawa Senate, sanan ya juyo ga gayen. "Tun da mijinta ya ce zai yi kabarshi, kai ka taimaka ta wani wajen." Banza ya yi da su daga shi har Senate ɗin ta huce. "Doctor please help me with your phone."
~~~~~Red bricks
Tun Mom na jiran kiran Senate har tagaji ta kirashi, ta yi matuƙar mamakin ganin taki kirashi bai ɗauka na, hakan yasa ta yi masa na biyu shima bai ɗaga ba, wasa-wasa sai gashi ta masa kira goma bai ɗaga ba nan-da-nan hankalinta shi ya ta shi, ta mayar da kiranta ga Anas. "Anas kuna tare da Senate?." Ta faɗa bayan ya ɗaga wayar. "No Mom." Ya bata amsa. "Kana ina yanzu?, je gidansa ka dubamun shi."
"Okay Mom." Ya faɗa tare da saita motarsa zuwa hanyar gidan Senate, dai-dai lokacin kuma Yaya Karima ta kira ta. "Karima ta zo?."
"A'a Momi ba ta zo ba wallahi, yanzu Umma ma ta ce ba ta zo ba."
"Innullahi me yake faruwa da yaran nan, shima kinga senate ɗin wayarshi baya ɗagawa tun ɗazu."
"Ya salam, To ko dai naje gidan nasu nagani?."
"Na tura Anas ya tafi."
"Innullahi, bara natura Abdul." Yaya karima ta faɗa sanan ta kashe wayar, ta shiga lalubar ta Abdul. Bugu ɗaya ya ɗauka da faɗin. "Yaya Karima yanzu Umma ke cemun wai Bhatool ba ta gidanta."
"Eyh wallahi Abdul, mijinma kaga ana kiran wayarsa baya ɗagawa ko zakaje gidan nasu ne?."
"Yanzu abinda Umma ta faɗamun kenan."
"To katashi kaje, duk yadda akayi kafaɗamun kafin ka fara faɗa mata."
"Toh shikenan." Ya faɗa tare da kashe wayar, motarsa ya ɗauka ya nufi gidan Bhatool ɗin sai dai a bakin gate yaco karo da Anas, fitowa ya yi daga motarsa suka yi musabaha sanan ya ce. "Suna ciki?."
"Basa ciki fa, yanzu ma naga wayarshi a ciki da tarin Missed calls ni ina tsorom ma faɗawa Mom."
"Itama Bhatool ɗin wayarta tana ciki, tun da idan an kira bata ɗauka mu shiga aduba." Abdul ya faɗa. "Okay mu shiga."
Wayar Abdul ya fara kira tun da suka shiga gidan, can suka juyo ƙarar ta a cikin bedroom, ita ma da tarin missed calls sosai, Anas ne ya kalli Abdul sanan ya ce. "Me kake tunani?."
"Ni wallahi duk kaina ya kulle, amma an ce Bhatool ɗin ce ta fara fita, ina tunanin shi bai yi nisa ba ya shiga Anguwa dubawa ko zai ganta."
"To mu ta shi mu shiga Anguwan muma." Anas ya faɗa, Abdul ya ta shi suka shiga zaga Anguwan. "Kana ganin ba zamu fara tambaya ba?." Abdul ya faɗa ganin sun zaga Anguwan sosai. "Mu fara, amma wanan abun na Bhatool ne." Ya faɗa yana tsugunnawa ƙasa, braclet ya ɗakko wanda yasan yaƙin da sukayi da Bhatool a kan shi. "Mu tsaya anan muyi tambaya to." Anas ya faɗa. "Wa zamu tambaya ko ina babu mutane."
"Bayin Allah lafiya." Mai gadin da ya yi wa su Senate magana ɗazu ya faɗa. "Dan Allah Baba muna cigiyar 'yan uwan mune mata da miji, yanzu anan mukaga abun hannun matar."
"Ayyah, ɗazu macen ta tawo tana kuka shi kuma mijin na binta a baya, cikin rashin sa'a yaro ya fito daga gidan da kuke tsaye a mota ya buge matar, amma sun tafi kai ta asibiti."
"Innullahi, Baba wani asibiti?." Abdul ya faɗa kamar zai yi kuka. "Nima bana ce ba, amma nasan asibiti mafi kusa zasu je."
Wanne ne mafi kusan?." Anas ya faɗa. "Akwai wani a farkon Anguwan nan. "Abdul calm down, everything will be okay." Anas ya faɗa ya taɓa Abdul ganin ya shiga damuwa sosai. "Bhatool fa amanace a hannuna." Abdul ya faɗa ƙwalla na zubowa daga idonsa. "Ka yi haƙuri kazo muje mu duba." A hankali ya fara tafiya yana bin Anas a baya har suka isa inda motar Abdul ɗin take, kasancewar ta Anas na cikin gidan. "Ina key ɗin ka?." Anas ya tambayeshi, hannu yasa a aljihu ya fito da shi ya miƙa mai.
A hankali Anas ke jan motar, zuciyarsa cike da tunanin me ya faru da Bhatool da Senate har ya kai ga ta fito waje yana binta, a haka suka ƙarasa asibitin. "Mu fara duba emergency." Anas ya faɗa, bayan sun fito daga motar. "Tom." kawai Abdul ya faɗa suka nufi emergency ɗin, dai-dai lokacin da Likitan ya miƙama Senate wayar da ya tambayeshi.
"Senate!." Anas ya kira sunanshi, juyowa Senate ya yi kalleshi a take ya miƙa ma Likitan wayar tare da cewa. "Thanks you."
"You're welcome." Likitan ya faɗa tare da hucewa. "How is she?." Abdul ya faɗawa likitan. "Tana cikin ƙoshin lafiya." Likitan ya faɗa. "Me yasa me ta?."
"Kai kuma mene alaƙanka da ita?." Likitan ya tambaya, dam shi abun ya fara ɗaure masa kai, wan can ya ce mijinta ne, wan can ya ce shi ya bugeta. "Ɗan-uwanta ne na jini, yayanta ne."
"Okay bata da wani rauni sosai, hasali ma bugewar bai wani taɓa ta ba daman dai tun farko tana cikin damuwa ne."
"Damuwa kuma wane kala?."
"Wanan mijinta zaka tambaya kuma." Likitan ya ba shi amsa tare da hucewa. Waje Abdul ya samu ya zauna, dai-dai lokacin da wayarsa ta fara ringi.
Sai da ya fara sai ta nutsuwarsa, sanan ya ɗaga wayar da faɗin. "Umma anganta suna tare da mijin." Ajiyar zuciya Umma ta sauke sanan ta ce. "Kai Alhamdulillah, ba ni ita."
Legendspen
***
Follow for more update