Hs 34
by @legendspen
_Page 34_
"Umma na fito waje zan kira ku kenan kika kira, bara na fara kiran Yaya na faɗa mata duk ta damu, sai in shiga gidan."
"Hakane kuma Abdul kira ta, Allah Ya yi muku albarka."
"Amin ya Allah Umma." Ya faɗa tare da kashe wayar, sao da ya goge ƙwallan da ta sakko daga idonsa sanan ya tafi kiran Yaya Karima, kamar jira take kiran ya shigo dan bai gama ringi va ta ɗauka. "Hello Abdul ya ake ciki?."
"Yaya angansu duka."
"Kai Alhamdulilalh, amma sai na ci uban Bhatool wallahi, duk ta wahalal damu."
"Yaya tana asibiti." Ya faɗa kamar zai yi kuka. "Bangane asibiti ba, me take yi?."
"Yaya wai motane ya bige ta."
"Innullahi wa'ina illahir raji'un garin Yaya kuma, ya salam." Ta faɗa tana kuka. "Nima bans sani ba Yaya amma alamun sun nuna matsala suka samu."
"Eyh matsala suka samu tun safe ta faɗamun, yanzu wani asibiti kuke?."
"Zan tura miki live location ki duba, danni ma ban sani ba."
"Turumun yanzu, bara nasa ya kawo ni."
"Sannu bawan Allah." Abdul yaji an faɗa, ɗagowa ya yi yaga wane. "Nine na buge ƙanwarka, nazo hucewa yanzu naga kana waya." Miƙewa Abdul ya yi sanan ya ce. "Garin ya haka ta faru ɗan-uwa?."
"Wallahi bisa tsautsayi, ta tawo da gudu ne shi kuma wan can yana binta a baya, na yi duk ƙoƙarina amma haka Allah ya ƙadddara."
"Waye yake binta kuma?."
"Wan can mana da ya ce Mijinta ne." Ya faɗa yana nuna Senate. "Eyh Mijinta ne." Abdul ya faɗa. "Gashi wanan na yi payment na duk kuɗin da suka caza, sanan na ƙara musu dubu ɗari biyu ko zasu buƙaci wani ƙarin, zaka samun lambarka anan, zan dinga taɓa akai-akai in sha Allahu, yanzu zanje ɗakko mahaifina a filin jirgi ne."
"Ayyah ka bar shi kawai, hakan ma da ka yi mun gode sosai da sosai."
"A'a baza a yi haka ba ɗan uwa, kasamun dai lambar taka sanan Sunana Ahmad." Ya faɗa yana miƙama Abdul waya, amsa ya yi ya rubuta mai lambar sanan ya ce. "Sunana Abdul."
"Na gode, Allah yabata lafiya."
"Amin ya Allah." Abdul ya faɗa.
"Kagani ko Anas, wanan gayen akwai wani abu a ransa." Senate ya faɗa yana kallonsu. "Wane abu ne a ransa wai, mutumin da ya yi muku wanan abun kake cewa haka."
"To shi Abdul ɗin mene zai kulashi, har ya ba shi lambarsa."
"Kaga Senate bazan iya da wanan abun naka ba, gaka ga Abdul ɗinan kaje ka tambayeshi mana." Anas ya faɗa yana kiran lambar Mom. "Ban ce ka yi mun rashin kunya ba." Banza dai Anas ya yi masa ya mayar da hankali ga kiran Mom, sai da ya kira sau uku sanan ta ɗauka. "Anas na yi salla ne, kun gan su."
"Eyh Mom, gamu a asibiti wai mota ta buge Bhatool ɗin."
"Ya salam! Garin ya kuma."
"Wallahi banda masaniya."
"Turamun location ɗin inda kuke, gani nan."
"Tom." Ya faɗa tare da tura mata, zama suka yi jingun-jigun kusa mintuna goma sha biyar sanan Senate ya ce. "Ban card ɗinka, zan ayi payment." Miƙa mai ya yi ba tare da ya ce ko ƙala ba, shi kuma ya amsa ya huce wajen biyan kuɗin. "I'm sorry sir, your payment is already done." Abinda ma'aikaciyar wajen ta faɗa kenan. "Banagne ba, who paid it?."
"Someones named Ahamd." Ta faɗa, tsaki ya yi sanan yabar wajen ya koma ciki, lokacin Abdul ya tashi zai shigo da Yaya Karima da mijinta. "Abdul, me wan can gayen ya ce da kai?." Senate ya tambayeshi. "Nothing, kawai ya ce shi ya bugeta ya bada hakuri, sanan ya ce ya yi payment har ma da extra kuɗi ya bari."
"Mun ce mushi muna buƙata ne?."Ya faɗa a fusace. "Ƙila yaga kun yi kala da masu buƙatar ne." Abdul ɗin ya bashi amsa ya huce, tun da dai yaga ba ubansa ba ne shi dai zai zo yana mai tsawa, Senate kamar ya haɗiye zuciya haka ya ji. "Me wanna yake nufi?." Ya tambayi kan shi. "Yana jin haushinka ne, a kan abinda ya sami ƙanwarsa." Wani ɓari daga zuciyarsa ya faɗa masa. "To kuma nina ja?."Ya sake tambayar kan shi. "Ai kai ka biyo ta gudu, da kazo a nutse duk haka ba lallai ba ne ya faru." Tsaki yaja sanan ya ce. "Rubbish." Abdul kam a waje ya tarar da su Yaya Karima, kana ganin idonta zaka san ta ci Kuka ta gaji. "Ya salam Yaya mene yasaki Kuka haka?, jikin na ta fa da sauƙi."
"Yanzu Abdul idan Umma ta ji ya za ta yi?." yaya Karima ta faɗa. "Ai baza ta ji ba in sha Allah."
"Kana nufin za'aɓoye mata ne?."
"Yaya likitan fa ya ce jikinta da sauƙi, bigewan bai mata komai ba kawai ciwon kai ne kuma wai dashi ta yini, ni haushin sakaran mijin nan na ta nake ji, duk shine ya ja komai."
"A'a Abdul, wai dan ya fita daɗe shine fa ta yi zuciya ta bar gidan." Yaya Karima ta faɗamai. "Mitchew Sakarar yarinya."
"Yanzu dai muje muga jikin na ta." Barrister ya faɗa. "Ai bacci take fa, kuma tana ta shi za'a tafi da ita gida." Abdul ya faɗa. "Gidan mijinta amma." Yaya karima ta faɗa. "Daman Yaya gidan mijinta, ina za'a kai ta da ya huce nan?." Abdul ya faɗa. "Yanzu ya za ayi da Umma?." Yaya karima ta tambayeshi. "Ta kirani na ce mata anganta, amma yanzu zan kira ta na ce na huce anguwa."
"Yawwa bara na fara kiranta." Yaya Karima ta faɗa sanan suka shiga ciki, Wajen Senate ta ƙarasa shima yana ganinta ya ta so. "Senate ya jikin nata?."
"Da sauki Alhamdulillah Yaya."
"Allah ya ba ta lafiya, ina likitan yake?." Nuna mata ofis ɗin ya yi, sanan ta ce. "Bara naje." Dai dai lokacin kuma Umma ta ɗaga wayar. "Hello Ummah."
"Na'am Karima."
"Umma mun yi waya da Bhatool ɗin, wai bazata kiraki ba sai da safe bata so ki yi mata faɗa."
"Aikuwa ko jibi zata kirani faɗane sai na mata, idan takama ma har gidan zan zo na ci ubanta."
"Ayi hakuri Mama, gata nan kamar ma ba ta da lfy."
"To ta ci kuka tum safe daman ya za ayi ta yi lafiya."
"Sai da safe Umma."
"Allah ya tashe mu lafiya." Yaya karima na sane ta katse wayar ganin ta ƙaraso ofis ɗin likitan.
Shigar Yaya karima babu daɗewa Mom ta ƙaraso asibitin, Senate na ganinta ya fara matse ƙwalla. "Kar ka yi mun kuka yanzu na tsinka maka mari a wajennan." Mom ta katse shi. "Haba Mom, yau na sha wahala sosai."
"Wahala ta huce wacce kajefa 'yar mutane a ciki, sabida baka da hankali ko?." Shiru ya yi ya shiga shafa kan shi. "Ta ina?."
"Har yanzu ba ta ta shi ba."
"Kariman fa?."
"Taje wajen Likita."
"Ina ne ofis ɗin?." Ta tambayashi, hannu ya nuna mata kamar yadda ya nunawa Yaya Karima.
"Babu wani abu da yasame ta, sanan a gwajin da muka yi ma tana ɗauke da jaririn ciki, wanda ko sati biyu bai yi ba."
"Ciki kuka likita, yau kwanansu goma sha ɗaya da aure fa?."
"To na ce miki cikin ko sati biyu bai yi ba."
"Aouho hakane kuma." Sallamar Mom ce ta katse musu maganar da suke yi da likitan, Yaya karima ce ta miƙe da faɗin. "Sannu da zuwa."
"Yawwa Karima ya jikin na ta?."
"Da sauƙi, yanzu ma ina tambayarsa idan da yadda za ayi su tafi ba sai sun kwana anan ba, sabida wallahi Ummanmu ƙarya mukayi mata batasan suna asibiti ba."
"To amma naji kamar ana maganar shigar ciki?." Mom ta tambaya. "Eyh, wai tana ɗauke da cikin da bai kai sati biyu ba."
"To Alhamdulillah, amma likita daman ana haka?."
"Anayi ranki yadaɗe, kawai dai ba'a gwada wane a wanan lokacin shi yasa ba a gani, amma da yawa zaki ga wasu suna cika wata tara cif da aure suke haihuwa."
"Eyh hakane kam akwai su da yawa ma." Mom ta faɗa, Yaya Karima kuma ta ce. "Likita za ayi ɓoye musu, sabida wallahi Bhatool sai ta gayawa ƙawayenta su kuma sai sun zagaya duniya da wanan batun, cikin da ko wata bai kai ba."
"Da gaskiyyarki kam Karima." Mom ta faɗa. "Eyh, zaku iya amma kun san akwai abubuwa da yawa da ya kamata mai ciki ta dinga kula da su."
"Zai a aika mata da mai aiki, sanan zan sa shi ya dinga kula da ita." Mom ta faɗa. "Shi ke nan hakan badamuwa."
Legendspen
***