BARA A KUFAI

Page 5.

by @zeeykumurya

*BARA A KUFAI*


*Zeey Kumurya*


5.


BRIGHT PENS 2026

YOTA ID 003


Bismillahir rahmanir rahim.


Cikin tsantsar farinciki Umma Lantana ta miƙe ta dubi Zeenat ta ce. "Alhamdulillah! Lokaci ya yi ɗiyar albarka, in sha Allah ke ce matar wannan mutumin, ke zai zaɓa ki zama matar Alhaji a daina ɗaɗɗaga mana kai a gidan nan, ni ma nan da wasu ƴan watanni ki gyara mini ɗakina ki canzan kayan ɗaki mu siya mini suturu na alfarma." Murmushin rainin wayo Inno ta yi ta ce. "A yi dai mu gani idan tusa za ta hura wuta, ban da rashin sanin ciwon kai auren sadakar ake yi wa wannan murnar? Ai Lantana idan ma za ki buɗe ido ki ware toshashshiyar ƙwaƙwalwarki da miyar da kuka da daddawa suka toshe ta ki buɗe, ki nemo sana'ar kishinki da gasa a duniya amma ba ni Zulai ba, don na fi ƙarfinki, na wuce ajinki, na yi miki zarra ta ko'ina, ƴar tawa da kike ganin za ki aurar da wannan watsatstsiyar ƴar taki ta goga kafaɗa da ita haukanki ya sa kin manta ita mijin ne ya gan ta, ya ce yana so ba tallan ta aka kasa ya zo ya kwasa ba?" 

"Kuka dai yi masa asiri ya aure ta, mun san komai ai ba wata rufa-rufa da za a yi mana, kuma watsewa ke kike da ƴa mai yi gata nan a ɗaki amma ba dai ƴata ba."

"To idan fitsari banza ne kaza ma ta yi mana? Ke ki je ki yi asirin ki ga idan za ku samu ko wanda ya kama ƙafar mijin Laure ne, ai Laure ta riga ta zame muku ciwon ido sai dai gani daga nesa amma ba dai ku yi gogayya ba." 

Tsaki Umma Lantana ta je ta ce. "Kanki ake ji, ƴata dai ita za a zaɓa, ƴan baƙinciki sai dai su mutu, kuma..." Fitowar Baba ya sa ta haɗiye sauran maganarta, nuna ta kawai ya yi da hannu alamun gargaɗi, ƙunƙuni ta fara ƙasa-ƙasa tare da hararar shi ta gefen ido. 

Umma ya shiga ƙwala wa kira, ta fito kamar za ta kifa don sauri da ɗankwali a hannu ta tsugunna a gabansa, dubu ɗaya ya cilla mata ya ce. "Ga shi ku siyo gari ku kwaɗa, kar na je a cikin ƴaƴan naki zai zaɓa ta tafi da yunwa ta zubar mini da mutunci, ke da kullum sai dai ki jira sai miji ya ba ki, ba za ki yi koyi da ƴar'uwarki ki dinga ci da kanki ba ranar da babu." Kamar wanda ya bawa wata duniyar haka Umma ta shiga yi masa godiya jiki na rawa. 

"To ni kuma fa Malam na ga kana ƙoƙarin fita?"

"Tuwon da ake tuƙa miki yanzu daga gidan tsohonki kika zo da garin?" Ya yi maganar idanunsa akan Ahayan da ta zage ragowar ƙarfinta tana tuƙin tuwo, gudun kar a ce bai tuƙu ba. Ƙus Umma Lantana ta yi ba ta kuma magana ba, ya yi ƙwafa ya juya zai fita Inno ta ce. "Ba ka faɗi fa su waye za su shirya a cikin yaran ba, ko sai baƙon zo za ka tantance?" 

"Ummi da Husna da Zeenat, sai wannan agolar." 

Haka kawai Ahayan ta ji gabanta ya faɗi, duk da ta san har da ita Baba yake nufi tun ranar da ya zo da maganar amma furucinsa na yanzu ya sa zuciyarta dokawa har muciyar hannunta ta kusa suɓucewa ta faɗi. 

"Amma Yaya da an cire ta a lissafi gaskiya, saboda ka san ba kowa ne zai yarda ya auri mara asali da ba a san kowa nata ba, kuma tunda da kai ya ce yana son haɗa iri ai bai kamata ka sako bare a ciki ba ko?"

Caraf Umma Lantana ta ce. "Maganar gaskiya fa kenan Malam, kuma ita ma uwar tasu ai ba sanin kowa nata muka yi ba, a ƙa'ida ma Zeenat kawai ya kamata ta je su ga juna a yi abin nan a wuce gurin, don ita kaɗai ce ƴa mai daraja da asali na uwa da uba ga ta kuma ƴar cikinka." A fusace Baba ya ce. "To wa ya saka da ke? Idan muna magana da ƴar'uwata ban hana ki yi mana katsalandan ba?" Kallon raini Inno ta yi mata ta ce. "Kar ka biye ta, mu ci gaba da maganarmu kawai."  Baba ya ce. "Dukkansu ne za su je har ita ɗin." Don shi burinsa kawai ya samu su rabu da mutumin lafiya, saboda maƙudan kuɗin da yake bin shi da ya ce zai yafe masa, kowa ma ya zaɓa a cikinsu ba matsalarsa ba ce. Umma dai tana durƙushe ko tari ba ta yi ba, don ba ta da darajar saka baki akan duk wani tattauna batu da za a yi a gidan ko da kuwa akan ƴaƴanta ne. Inno kuwa ta ƙudirce ba za ta taɓa tura Husna ba, don da hankalinta ba za ta bari ƴarta ta yi wannan ƙasƙantaccen auren ba, su dai da ya haifa nasa ne ya yi duk abin da ya gama a kansu, amma ban da nata ƴaƴan, kuma ba ta san a zaɓi Ahayan saboda ta fi son ta gan ta kullum a cikin rayuwar ƙasƙanci da bauta, ko a mafarki ba ta fata Allah ya nuna mata Ahayan ta samu wani ci gaba a rayuwa. 

Sai da Ahayan ta kwashe wa Umma Lantana tuwon da ko ɗanɗana miyarsa ba ta isa ta yi a bakinta ba, ta kai mata har ɗaki sannan ta koma wajen Umma, dubu ɗayan da Baba ya ba ta ta cilla mata ta ce. "Ɗauki ki siyo mana gari da ƙuli, su Rauda sun je Islamiyya sun gaji ba za su iya fita ba." A ladabce ta ɗauki kuɗin ta saka cukurkuɗaɗɗen hijabinta ta fice daga ɗakin, Sabira ta ce za ta raka ta amma Umma ta hana ta, ta ce idan ta yi tafiya za ta ƙara galabaita da yunwa. 

Da bin bango take tafiya saboda jirin da ke ƙoƙarin kayar da ita, tsabar yunwa ko gani ba ta yi sosai, hakan ya sa ba ta san ta saka takalmi a baibai ba, ba kuma ta san mutum ya kawo kai a soro ba sai karo kawai ta ji sun yi.

"Subhanallahi! Ahlove?" Ya faɗa yana ƙoƙarin riƙo ta ganin tana shirin faɗuwa.

Ja baya ta yi da sauri ta jingina da bango tana mayar da numfashi, murmushin da ya fi kuka ciwo ta sakar masa, cikin ƙarfin hali ta ce. "Yaya Saif." Yawun takaici ya haɗiye, ya bi ta da kallo cikin matsanancin tausayin ta, murya a sanyaye ya ce. "Ba ki da lafiya ne? Kin ƙara ramewa, idonki ya koɗe, me ya same ki Ahlove?" Ƙwallar da ta tarar mata ta mayar ta ce. "Babu komai Yaya, idonka ne kawai yake ganin haka, amma...." Haɗa idon da suka yi ya harare ta ne ya sa ta yi ƙasa da kanta tana jin kamar ta fashe da kuka saboda abubuwan da suke danƙare a cikin ranta masu tsananin ɗaci da kaifi."

"Ina za ki je?" Ya jefa mata tambayar bayan ya gama ƙare mata kallo, daga yadda ta saka takalman kafarta ya tabbatar masa a matuƙar galabaice take. 

"Gari da ƙuli zan siyo." 

Girgiza kai ya yi cike da baƙincikin yadda ake treating ɗinta a gidan ya ce. "Koma gida zan je na siyo miki." A tsoarace ta ware ido ta ce. "A'a don Allah, ka san..." Hannu ya ɗaga mata ya ce. "Amma kin san dai ko me zai faru ba zan bar Ahlove ɗita ta fita a wannan yanayin ba, ko so kike ki je ki faɗi a bar ni da ɗora hannu akai ina na shiga uku." Murmushi ta yi tana jin wani irin sassauci a zuciyarta.

"Oya koma ciki, zan dawo yanzu, ki kuma shirya za ki ba ni labarin duk abin da ya faru da bana nan, har wannan koɗewar idon sai kin faɗa mini dalilin ta, ko kwana kike kina kuka saboda bana nan?" Ya ƙarashe maganar da wata irin siga da za ta saka jin kamar za ta faɗi, kuzarin da ya rage mata ta tattaro ta girgiza masa kai. Ƙasa ya yi da murya ya ce. "Uhm, faɗa mini mana, na san kin yi kewa ta sosai, ko ba ki yi ba?" Juya masa baya ta yi ta ce. "Umma tana jira na fa." Kansa ya shafa ya ce. "Sorry, duk na zauce ne, kin san idan kina gabana mantawa nake da kowa da komai, bari na je na dawo, just 10 minutes in sha Allah." Da sauri ta ce. "Ga kuɗin to." Kallon da ya wurga mata ya sa ta yin murmushi, ta bi shi da kallo har ya fice ya bar ta da ƙamshinsa. Shi kaɗai ne, shi ne kawai kaf gidan take samun nishaɗi da farinciki a gurinsa, shi ne kawai yake darajata da ba ta ƙima irinta kowanne Ɗan'Adam.
Ba ta koma cikin gidan ba kamar yadda ya buƙata saboda tsoron kar ya kawo garin Inno ta gan shi, don daga ita har shi ta san sai sun kaɗe har ganyensu, a ƙofar gida ta lallaɓa ta samu dakali ta zauna tana mayar da numfashi, a ranta tana ayyana ba ƙaramin taimako Allah ya yi mata ba da ya jefo mata Saif, don sai a yanzu ta gane ba ta da ƙwarin zuwa kantin mai garin, don tabbas kamar yadda ya faɗa kafin ta je sai ta faɗi. 

Da ya dawo tun kafin ya ƙaraso ya fara yi mata mita.

"Yanzu don Allah mene na zama a bakin kwatar nan sauraye suna cizar mini ke? Ga maza suna wucewa suna kalle ki." Dariya kawai ta yi masa, a ranta ta ce. 'Ban shirya karɓar kwandon bala'i daga Inno ba ne.' Duk yadda ya so su shiga gidan tare ƙin yarda ta yi, a dole ba don ya so ba ya ba ta ledodin hannunsa da nauyinsu ya wuce na gari kawai, hakan ya sa ya fasa shiga gidan ya tafi masallaci don an fara kiran Sallah, shi kansa ya fahimce ta, ya san idan ta shiga da wannan kayan mahaifiyarsa ta ga ya biyo ta a baya to fa kashinsu ya bushe. 

Har rinjayarta kayan suke saboda nauyi, a haka ta daure ta ƙarasa ɗaki ta zube su a gaban Umma wadda tun kafin ta yi mata bayani ta san daga hannun Saif suke. Banɗashen gurasa ne cikin leda, sai gari da ƙulin da suga. Hannu baka hannu ƙwarya haka duk suka rufu akan gurasar, sun ci fiye da rabi Umma ta ce. "To ki bar musu haka mana tunda ke ce babba, ki je ki haɗo mana kwaɗon garin." A daƙile Ummi ta ce. "Ba tana taƙamar saurayinta ne ya kawo ba ina za ta tashi?" Baki cike da gurasa Rauda ta ce. "To ba ɗan'uwanmu ba ne ba? Na ga Innon ƙanwar babanmu ce ba ta wani ba." Ita dai ba ta ce komai ba ta zare hannu ta miƙe, da sauri Sabira ta ce. "Aunty Ahayan ni zan rage miki, na san ba ki ƙoshi ba." 

"To uwar iya." Cewar Ummi tana hararar ta.

Garin ma wanda suka ci ya fi nata yawa, haka ta kora da ruwa ta yi sallah da ƙyar ta kwanta a wurin, wata irin gajiya ce take bin gaɓoɓin jikinta, ga kanta da ke sara mata da cikinta da ya ƙulle na wuni da yunwa, maimakon ta ji salama tunda ta ci abinci amma sai wani iri cikin yake yi mata, hakan ya sa take jinta kamar mai cuta.

Zeenat kuwa saka ta a gaba Umma Lantana ta yi ta shirya cikin wasu sababbin kayanta da sawa ɗaya ta taɓa yi musu, ta ba ta kwallin da Malamin da ta je gurinsa ya ba ta, ta saka, ta feshe jikinta da turare. Baki kamar gonar auduga Umma Lantana take faɗin. "Kin ga yadda kika yi kyau kuwa? Ga kwallin nan Malam ya tabbatar mini da zarar kun yi ido huɗu ke mutumin zai zaɓa." Fari Zeenat ta yi da ido ta ce. "To da ma Baba ne fa kawai yake son wahalar da kansa, ban da haka ƴaƴan Umma Karima har wani abin so ne? Ita Ummi ba ta gama zama cikakkiyar budurwa ba, Ahayan kuwa wa yake ta ita jiki duk ɗauɗa da gayyar talauci, ƙilama muna zuwa su tsugunna su gaishe ta saboda tunanin ko babarmu ce tunda sun gan ta kamar tsohuwa." Dariya Umma Lantana ta yi ta ce. "Ke! Ke ce fa mutumin nan zai zaɓa, ina jin hakan a jikina kuma Malam ma ya tabbatar mini da haka." Shiru Zeenat ta yi jiki a sanyaye, Umma Lantana ta ce. "Mene ne kuma?" 

"Yaya Saif na tuno, wallahi ina mugun son shi, ba yadda zan yi ne kawai saboda ina son kuɗi da auren mai kuɗi shi kuma ba shi da su." 

Tsaki Umma Lantana ta je ta ce. "Ke fa wani lokacin ba ki da hankali, ana sabgar arziƙi kina maganar tsiya, me za a yi da jinin Inno idan ba ƙaddara ba? Matar da ba wanda ta tsana a duniya sama da uwarki?" 

"To ai shi Yaya Saif yana da kirki fa Umma, kuma..."

"Dalla rufe mini baki, mu yi abin da yake gabanmu kawai mu bar wannan batun, ina cikin farinciki ba za ki ɓata mini rai ba." Duk tsagerancin Zeenat haka kawai jikinta ya yi sanyi, zumuɗin da take ji duk sai ta neme shi ta rasa.

Bayan sallar Isha Baba ya shigo gidan da faɗa kamar kodayaushe, ya dinga ƙwala musu kira kamar sabon makaho, duk suka fito, ya tasa ƙeyar Ahayan da Zeenat da Ummi, don Inno ɓoye Husna ta yi a ɗaki ta ce tun rana ba ta gidan har yanzu kuma ba ta dawo ba, haka Baba ya saka su a gaba har soro inda baƙin suke, wani irin dokawa ƙirjin Ahayan yake yi mata, tsoro da wata irin fargaba suka shige ta, ga tunanin Yaya Saif da ya addabe ta, wanda bai shigo gidan ba har yanzu bare ta gan shi ta ji sanyi ko za ta samu sassaucin halin da take ciki.

***** *****

Wunin yau gabaɗaya da Tunanin Sheik Adnan Juraij ya yi shi, duk inda ya motsa sai komai da suka gudanar tare ya faɗo masa a rai, gefe guda damuwar ciwon Daddy ta hana shi sakat ita ma, hakan ya sa da ƙyar ya iya caccakalar abinci a cikin wanda Ramlah ta haɗo masa, saboda kiran da take ta yi masa da nacin tambayar ya ci abincin? Ban da messages da ta tutturo masa. 
Ƙarfe huɗu da mintuna suka hallara a conference room na headquarter ɗinsu dan yin meeting kamar yadda aka sanar musu, har lokacin kuma ba a sanarwa duniya batun rasuwar sheik Adnan ba. Shi ma tun bayan Malam bai ƙara faɗawa kowa ba, ya tsaya kawai ya ga iya gudun ruwansu.

Su biyar ne kacal masu meeting ɗin, daga Director sai DD sai shi sai CSO da Field officer. 

Bayan Director ya yi wasu jawaban ya ɗora da faɗin. "Na samu matsin lamba sosai daga Director General akan batun satar masu ƙusumbi da aka yi a gidan nakasassu watanni uku baya, saboda yana ganin kamar sakacinmu ne ya saka muka kasa gano mutum ɗaya da aka kama a cikin masu satar daga baya kuma ya gudu, ya so a yi wannan meeting ɗin da shi, amma wani meeting ɗin da suke da shi da Ministan tsaro ya saka bai halarta ba, but ya yi ta nanata mini na tabbatar an samu update a gurinmu a yau na yunƙurin da muke yi, that's why na tara ku don mu san ta inda za mu ɓullowa al'amuran nan, rashin tsaro da safarar miyagun ƙwayoyi kullum ƙara yawaita suke a ƙasar nan, don haka ya kamata a ce mun fi haka haɓɓosawa da dagewa gurin gano masu aikata waɗannan laifukan!" 

Numfashi DD ya sauke tare da bin su da kallo ɗaya bayan sannan ya ce. "Muna iyakar bakin ƙoƙarinmu ka sani Sir, amma abubuwan ne kamar muna tufka a cikinmu ana samun masu warware mana."

"No! Babu wannan maganar DD, don na tabbatar babu mai yin haka a cikinmu, muna buƙatar mu bayar da himma da ƙwazo ne kawai, zan ba ku lokaci wanda shi zan faɗa wa DG ni ma akan ya saurare mu, kafin lokacin ina son duk rintsi ku kawo mini information akan wannan mutumin ko da na sanin movement ɗinsa ne kawai." 

"In sha Allah Sir." COS Kamal ya faɗa cikin girmamawa. 

A hankali Juraij ya buɗe idonsa da suke lumshe ya dubi Director, fuskarsa babu walwala ya ce. "Akwai abubuwa da yawa da muke buƙata da za su taimaka mana mu sake kama shi cikin sauƙi, muna buƙatar ganawa da police ɗin da suka fara cafke ni kafin a kawo su nan, saboda mu babu wanda ya gan shi, abin da aka ce mana kawai sun tabbatar sun taho da shi har harabar nan, daga nan kuma aka neme shi aka rasa, su ne za su ba mu duk wasu bayanai na kamanninsa da wani abu da yake tattare da shi, may be a samu wayarsa ko wani abu makamanci haka a hannunsu, da zarar mun samu wannan kamar ya zo hannu ne in sha Allah!"

"Good AD Juraij! Amma me ya sa tun a baya ba ku yi hakan ba?" 

Mayar da idonsa ya yi kan Field officer tare da yi masa alamar tambaya da ido alamun amsar tana gurinsa, da sauri ya ce. "I'll do my best Sir, zan yi kokari na samo dukkan bayanan da Sir AD ya faɗa." 

Ci gaba da tattaunawa suka yi har wajen 6 kafin suka kammala meeting ɗin.

A matuƙar gajiye Juraij ya ƙarasa gida, yana parking yaronsa Almu ya taho yana yi masa sannu da zuwa tare da ƙoƙarin karɓar briefcase ɗinsa, hannu ya ɗaga masa tare da yi masa alamar ya bar shi, yana kashe motar zai fito kira ya shigo wayarsa, tun kafin ya kai idonsa kan wayar ta sanar masa mai kiran, hakan ya sa ya ɗauko ya ɗaga da sauri. 

"Juraij! Jin ɗuriyarka kenan ko? Ka watsar da mu kwana biyu ba kira ba komai, ni kuma na kikkira many times ba ka ɗaga ba." 

Sai da ya jingina da kujera ya sauke numfashi sannan ya ce. "Abubuwa ne suka sha kaina Mami, I'm sorry."

"Haka ka iya ai kullum, ka zaɓi rayuwa a gefe daga kai sai matarka, da Ƴar'uwarmu tana raye ai ba ka isa ka yi mana haka ba, Juraij ka dinga zumuncin Allah, ka bar biye wa mace tana juya ka yadda ranta ya so tana hana ka yin abin da ya dace." 

"Mami..... Ramlah fa ba haka take ba, ba kuma ita ta hana ni zuwa inda kuke ba."  A fusace ta ce. "Ai da ma haka za ka ce, tunda ba ka ganin baƙinta, ba ka ganin kowa da gashi sai ita." Ta dinga faɗa da mita kamar za ta ari baki, shi dai ya yi mata shiru, sai da ta gaji don kanta sannan ta sassauta murya ta ce. "Ya jikin mahaifin naka?"

"Da sauƙi Alhamdulillah!"

"Allah ya ba shi lafiya ya tashi ƙafaɗunsa, amma ba zan fasa faɗa maka ba, barin jinyar shi a hannun matarka ba daidai ba ne, tana mace bai kamata ta yi jinyar ko da mahaifinta ba ne sai dai in dole, bare kuma naka, jinyar namiji sai namiji ɗan'uwansa fa." 

"Ni nake yi masa komai, magani kawai take ba shi idan na fita, tana kula da shi sosai fiye da duk wanda zan bawa ya kula da shi." 

Taɓe baki ta yi ta ce. "Ai shikenan tunda haka ka zaɓa, jikin nasa yana dai yin kyau sosai ko?"

"Alhamdulillah kawai za a ce Mami" 

"Allah ya ba shi lafiya ya ƙara sauƙi." 

"Amin ya rabb." 

Daga haka suka yi sallama ya katse kiran ya buɗe motar ya fita. 

Yana buɗe ƙofar parkour Ramlah ce abu na farko da ya fara gani, tana tsaye tana yi masa murmushi, ta ci kwalliya tana ta tashin ƙamshi.

"Sannu da zuwa, da fatan ka dawo lafiya?" Ta yi maganar tana yi masa side hug sannan ta karɓi briefcase ɗin hannunsa. 

"Daga ganin ka a gajiye kake sosai, mu je ka yi wanka ka ci abinci kafin lokacin sallah ya yi."

"Ya jikin Daddy?" Ya faɗa yana zare hannunsa daga cikin nata hango Marka durƙushe a ƙasan steps ta juya wa inda suke baya.

"Jiki Alhamdulillah yana ta yin kyau." 

Wani yawu ya haɗiye a hankali, amsar da yake ba wa kowa ce idan an tambaye shi jikin Daddy, ba don kuma yana samun sauƙin ba, suna faɗa ne kawai don hakan ne ya dace, amma ba don ana samun ci gaba yadda suke so ba.
Ƙoƙarin rungume shi ta yi ya janye jikinsa ya nufi sama yana faɗin. "Bari na gano jikin nasa." Ba ta ce komai ba ta nufi ɗaki da sauri sannan ta ajiye masa briefcase ɗin sannan ta dawo ta bi bayansa.

Ni'imtaccen ƙamshi ne ya fara yi masa maraba a ɗakin, kamar kullum Ramlah ta gyara shi fes, ga karatun Alkur'ani ta kunna a speaker, wata irin nutsuwa ya ji ta saukar masa, ya saki sassanyar ajiyar zuciya sannan ya ƙarasa ya tattaɓa fuskar Daddy, hatta bargon da yake lulluɓe da shi ba wanda ya tafi ya bari ba ne, ta sauya wani kuma ta turare shi da ƙamshi mai daɗi. 

A hankali cikin lallaɓawa ya ɗago hannun Daddy ɗaya ya riƙe shi a cikin duka hannayensa ya ɗora fuskarsa akai, a haka ya fara karanto addu'a yana tofa masa. 

A haka Ramlah ta shigo ta same shi, ta jira har ya ida sannan ta janyo maganin Daddy na rubutu ta nuna masa. "Ya kusa ƙarewa, ya kamata ka samu lokaci ka koma gurin Mai-maganin nan ka sake karɓo masa, na ga idan aka ba shi jikinsa yana nuna alamun yana jin daɗin maganin.

"In sha Allah!" Ya faɗa idonsa akan fuskar Daddy.

"Na gode Ramlah, na gode sosai, ban san da me zan iya saka miki da wannan sadaukarwar da kike yi mini ba."

Kamar za ta yi kuka ta ce. "Na faɗa maka bana son wannan godiyar, kuma akan Daddy kake cewa ba ka san da me za ka saka mini ba? Da ma mutum yana jiran tsammanin sakayya ne a abin da ya zamar masa dole? Ka daina wannan maganar don Allah bana jin daɗi." Ta ƙarashe maganar a shagwaɓe. Murmushinsa mai kyau ya yi mata ya ce. "Allah ya saka miki da gidan aljanna." 

"Amin mijina abin alfaharina." 

Bayan sun koma ɗakinsa yana rage kayan jikinsa ta dube shi ta ce. "Su Kawu sun zo fa yau, sun duba Daddy." Da sauri ya kalle ta, jinjina masa kai ta yi ta ci gaba da magana. "Sun yi faɗa sosai kamar yadda suka saba, sun ce dole sai an mayar da Daddy asibiti tunda nan ɗin ma ba ci gaba, na yi ƙoƙarin fahimtar da su ciwon ba na asibiti ba ne, amma sun ƙi saurarata, sun ce za su dawo su same ka." 

Runtse idonsa ya yi yana jin kansa kamar zai fashe, kamar matsalolin cikinsa sun yi masa yawa shi kaɗai, da me zai ji ne? 

Ƙarar shigowar saƙo wayarsa ya saka shi buɗe idanunsa da suka yi masa nauyi, Ramlah ta riga shi ɗaukar wayar ta miƙa masa, ya karɓa ya buɗe ya duba, video ne daga guri mai muhimmanci a gare shi. 

Ya san ya buɗe ya fara kalla, amma bai san ya aka yi ba, sai jin ƙarar wayar ya yi ta faɗi a kan ƙafarsa ba tare da ya san lokacin da ta zame daga hannunsa ba saboda tsabar gigita da kaɗuwa.



#Zeey Kumurya 
#***