CHAPTER 4
AMARYAR GADO
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
AISHA SANI ABDULLAHI
Xayyeesherthul-humaerath
©️2026
Jan hankali: Wannan littafi ƙirƙirarriyar riga ce da aka saka wa kowace ƙaddara da ke cikinsa suna. Kada wani labari ko sirri da aka bayyana a cikinsa ya sa a fassara shi da rayuwar wani na gaske.
Gargaɗi: Haƙƙin wallafar littafin na marubuciya ce kaɗai. Ba a yarda a juye shi zuwa wani harshe, ko a canza shi zuwa sautin murya (audio) ba tare da rubutacciyar yarjejeniya ba.
SHAFI NA HUƊU
Sake-sake Farida ta fara yi a zuciyarta. Wata zuciyar na ƙarfafa mata gwiwa ta fita, abin da zai faru ya faru. Wata kuma na dakatar da ita, tana tuna mata cewa lallai idan ta fita, Abba Shuaibu zai iya aikata mata komai, domin tun da farko ya riga ya gargade ta.
Cikin tsananin fushi ta sake ƙofar da ƙarfi, ta koma ɗakinta, ta faɗa kan gado. Wani kuka na takaici ya fara ƙwace mata.
Shi kuwa Sufyan, dariyar mugunta ya yi a zuciyarsa, yana cewa, “Ai yanzu ma aka fara wasan.”
Ya tashi ya nufi ƙofar ɗakinta, ya tsaya a bakin ƙofar sannan ya ce,
“In ce kin manta cewa akwai buƙatar ki yi wa mijinki girki ne? Yunwa nake ji, ban karya ba, kuma kin san zan je school.”
Tana kwance tana kuka, cikin zafin murya ta ce,
“Ba zan girka ba! Ba zan yi ba! Indai ni zan yi girkin da za ka ci, sai dai ka mutu ba ka ci abincin ba.”
Sufyan ya ƙare mata kallo kafin ya ce,
“Ko? Okay, to mu zuba mu gani.”
Ya koma falo, ya ɗauki wayarsa ya kira number Inno.
Da Inno ta ga kiran Sufyan, cikin zakuwa ta ɗauki wayar ta kara a kunne.
“Assalamu alaikum, ango. In ce har hankalin ya ƙaru ne har an kira a yi mini barka da safiya? Ya amaryar ne? Kuna lafiya dai ko? Komai dai ba wata husuma ko?”
Sufyan ya katse ta da cewa,
“Cai tsohuwa, ni ba surutu na kira ki yi mini ba. Daman na ga kamar jikar taki ce ba ta san cewa yanzu akwai nauyi a kanta ba. Yunwa nake ji, ta ƙi tashi ta dafa mini abin karyawa.”
Inno ta zare ido ta ce,
“Ah, wannan ai akwai husuma! Wannan Faridatu na son gamuwa da rahamar Ubangiji kuwa? Ace har yanzu ƙarfe goma na safe ba ta ba wa miji abinci ba? Kar ka damu, yanzu kuwa zan sa a kawo muku abinci.”
Sufyan ya ce,
“A’a fa, Inno. Ai kar a saba mata haka. In ta ga ana kawowa, shi ke nan kullum ma haka za ta riƙa yi. Kin ga in ma ba ta iya ba, ba za ta koya ba kenan. Ni ma na fi zargin cewa ba ta iya girkin ne, don haka kawai ki zo ki sa ta a gaba ta yi mini girki. Ko ba haka ba?”
Inno ta girgiza kai ta ce,
“A’a, ka yi kyakkyawan tunani, Sufuyanu. Hakan za a yi domin a kauce wa husuma. Gani nan tafe yanzu.”
Tuni Inno ta tashi ta zura hijabinta a karkace, ta fita daga gidan. A bakin ƙofa kuwa ta yi karo da Kawu Hamza, wanda ke ƙoƙarin shigewa gidansa.
“Inno, ke ce da safiyar nan? Ina kika nufa?” ya tambaya.
Inno ta tabe baki tana tauna goro ta ce,
“Umm, Hanza. Faridatu ce ke son taɗa mana husumar fushin Ubangiji a danginmu.”
Cikin yanayin tuhuma Kawu Hamza ya bi ta da kallo ya ce,
“Kamar ya?”
Ta ce,
“E, ta ƙi tashi ta yi wa mijinta girkin karin kumallo saboda lalacewa. Zuwa zan yi in sa ta a gaba ta girka.”
Dariya ce ta subuce wa Kawu Hamza, ya ce,
“Ah, lallai kam, Inno. Akwai kau da husuma.”
“Kai dai sai na dawo kawai. Ka miƙa gaisuwa ga Hansatu in ka shiga.”
Da haka ta ƙarasa maganar tana ci gaba da tafiya.
Inno na tafiya tinkis-tinkis har ta isa gidan Sufyan da Farida. Da shiga, Sufyan ne ta fara cin karo da shi a falo.
“Ina Faridatun?” Inno ta tambaya.
Ya nuna mata ɗakinta da hannu.
Aiko, da Inno ta shiga, sai ta ga Farida kwance a kan gado. Dogon salatin da Inno ta fara rattabawa ne ya tabbatar wa Farida cewa ita ce ta shigo. Da sauri ta fara share hawayenta tana ƙoƙarin pretending cewa barci take.
“Husuma na binki, ke kuma kina barci. Aiko ta biyo ki har cikin barcinki, ku manne da juna.”
Mikewa Farida ta yi ta ce,
“Ina kwana, Inno?”
Inno ta galla mata harara ta ce,
“Da ban kwana ba ai da ba ki gan ni ba. Yoo, mu a zamaninmu, ko barci muna iya yi ne idan miji ya farka? Ai duk daɗin barci sai mun haƙura da shi. Mun fi bin miji, muna biya masa dukkanin buƙatunsa. Ke kuwa kin zo wata gandangandan, kin sheƙe a kan gado kamar doya, alhali mijinki na falo cikinsa na buga salatin yunwa. Maza, tashi mu je kitchen ɗinku.”
Farida ta rasa abin cewa. Tashi kawai ta yi yadda Inno ta umarta.
Da suka fito za su wuce kitchen, suka haɗa ido da Sufyan. Wani murmushin mugunta ya sakar mata. Ita kuwa ta yi masa tsaki tare da kawar da kanta.
Suna shiga kitchen, Farida ta ce,
“Wai me za mu yi ne, Inno?”
Inno ta ce,
“Gidanku, Faridatu, na ce gidanku. In ba girki ba, me kuwa za mu yi? Kin bar miji da yunwa. Maza, kunna abin hutar nan naku ki ɗaura ruwan ɗumi. Kin san ni ba iya amfani da shi na yi ba, kar ya je ya ƙona ni in shiga husuma.”
Haka Farida ta kunna gas ta ɗaura ruwa.
Inno ta ce,
“Yawwa. To yanzu, wani abinci kika san Sufuyanu na masifar mutuwar rayuwar son ci?”
Ta faɗi hakan a hankali kamar wata munafuka, wai kar Sufyan ya ji.
Farida ta haɗe rai ta ce,
“Ni ban sani ba.”
Inno ta ce,
“To yanzu dai lokaci ya ƙure. A dafa masa taliyar yara kawai. Maza, ki riƙa yin komai ina gani, don in tabbatar da iya girkinki.”
Farida na saka komai, idon Inno na kanta. Sai da ta zo saka Maggi, ta saci Inno ta zubar da shi bayan gas ɗin. Sannan ta yi grating ɗin zallan attaruhu ta zuba masa.
A ido dai kam, indomie ɗin ta yi kyau sosai, har za a yi mata kyakkyawan zaton cewa a baki ma za ta yi daɗi.
Inno ta ce,
“Yawwa, ’yar albarka. Ko ke fa ai haka ake. Duk wani abu da zai birge miji a faranta masa rai. Ba ki ga shi ya sa kakanku Alhaji Audu, masoyi har ya mutu bai ƙara aure ba? Tsabar kulawa da soyayyar da nake ba shi ne. Duk da ‘yan matan dangi sun riƙa kawo masa hari, amma ya ce a’a sam, ni kaɗai yake iya hanga. Na ishesa.Don haka ke ma so nake ki gaje ni.”
Farida dai sauraron Inno kawai take, amma ita kaɗai ta san baƙin rai da zafin zuciyar da suka tokare mata a ƙirji.
Inno ta ci gaba da cewa,
“Yanzu ɗauko faranti mai kyau ki juye masa. Ki fara kai masa, sai ki dawo ki ɗauki shayin ma.”
Bayan Farida ta zuba a farantin, ta je ta ɗungura masa a gabansa. Inno kuwa na labe tana lekensu.
Da ta koma kitchen, ta haɗa shayin ta kara satan idon inno ta zuba garin kanwa ciki,ta dauka kenan za ta fita.
Inno ta rike mata hannu ta ce,
“Amma ke dai an yi husumammiyar diya. Ke da za ki kai masa abinci kina murmushi, sai kika ɓata rai kamar fuskar bijimar saniya. Ga ki dama da wadatattun kumatu, ai sai ki razana shi. To, ahir ɗinki! Ɗauki shayin nan mu je tare. Murmushi za ki riƙa yi, kuma ki tafi a hankali. Ba wai kina tafiya kamar jikar Samudawa ba, jiki ba shauƙi. Yoo! To ta ina har za ki birge shi ma haka?”
Cikin fushi Farida ta ce,
“Ni don Allah, Inno ki bar ni. Wallahi na gaji, ba zan iya ba.”
Inno ta buɗe baki ta ce,
“Faridatu, ni kike faɗawa haka? To wallahi kamar kin yi da Haruna da Shuaibu ne.”
Ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin marairaicewa.
Tuni Farida ta riƙe ta tana ƙwaƙulo murmushin dole, ta ce,
“Haba, Innota! Wasa fa nake yi miki.”
Inno ta tabe baki ta ce,
“Da dai ya fi miki. Ni dai yanzu mu je. Lokacin sallar Walha ya yi, zan tafi.”
Ba don Farida ta so ba, haka ta ƙwaƙulo murmushin dole, tana tafiya a hankali har ta je ta ajiye masa shayin.
Za ta bar wajen kenan, Inno ta dakatar da ita.
“Ina za ki kuma? Ya Ilahil Alamina! Amma da uwarki Kulu ba ta yi mini adalci ba, domin ba ta koya miki yadda za ki yi zaman aure ba. Dawo nan ki zauna daf da shi har sai ya kammala cin abinci, kina yi masa hira, kina masa fifita saboda gudun zufa. Kin ga ba wutar ne fa, kuma ba aka riga aka sa muku wancan abin ranar ba da yake ba ya fitar da wuta ai ko?”
Tana ƙarasa maganar ta je ta ɗauko mafici ta miƙa mata.
“Maza, karɓa ki fara fifita shi.”
Ba yadda Farida ta iya, haka ta karɓi maficin ta fara masa fifita, shi kuwa ya washe baki.
Ganin hakan ya sa Inno ta ce,
“To yanzu ni dai bara in tafi. Amma dole in dawo in koya miki zaman aure da rayuwar aure, wanda Kulu ta gagara koya miki, domin kauce wa husuma. Na barku lafiya.”
Inno na faɗin hakan ta fice.
Tana fita, Farida ta jefar da maficin ta tashi, daidai lokacin da Sufyan ya kai lomar indomie baki.