1
by @aishaangel
*MATAR BELLO.*
_The Bride Who Brought Chaos_
By Aysher Angel
Page 1
*When What Was Meant to Be Joy Became Trouble?*
WhatsApp ***
Amaryar Bello...
Fara ce sol har yellow fatarta take saboda haske, tana sanye da expensive Egyptian Abaya wacce ta matuƙar suiting dinta tayi matuƙar kyau kamar a sace a gudu, saidai hakan bai saka wautarta da kauyancinta sun gushe ba, kyawun da tayi daban, wautarta da kauyanci daban.
Duhu ne mamaye da falon, a hankali ta turo ƙofar ta turo kanta tana leƙe kamar wacce take tsoron leƙa ƙarƙashin kabari.
Ta tsaya cak ta ja lumfashi a hankali kamar wacce ta shigo gidan da yake cike da ifiritun aljanu, ta sake leƙawa Idanunta suna yawo a cikin falon, zuciyarta na bugawa kamar ana dukan gangar waka a tsakiyar taron bikin aure. Ta sake tura kanta kaɗan, ta ɗaga ƙafarta ɗaya, sai kuma ta dawo da ita baya.
"A’ah, idan wani abu ya fito fa?" ta raɗa wa kanta.
Ta ɗaga ƙafarta a karo na biyu, ta taka. Ƙarrrrr! ƙofar ta yi ƙara.
Ta zabura kamar an ce mata 'kama ta!..' Ta dafe ƙirji idanunta a waje.
"Na shiga uku, wannan ƙofar sai da ta tona min asiri," ta faɗa a zuciya.
Ta sake leƙawa, babu motsi, shiru kamar an zuba ruwa ƙasa ta shanye.
Babu zato babu tsammani ta ji wata ƙara daga kusurwar falon: ƙuuuu... ƙuuuu...
Ta tsaya cak ta zaro idanu tana tarababbi gashi kishirwa takeyi ba kaɗan ba ballantana ta juya ta koma dakinta.
Ta ƙara jin ƙara: ƙuuu... ƙuuu...
"Wayyo! Wannan murya ba ta mutane ba ce, mutanen ɓoye kuyi haƙuri ruwa kadai zan sha in koma inda na fito," Ta furta a hankali tana takatsantsan kada ta motsa domin a wannan lokacin motsin motsawarta kanshi tsoro yake bata.
Ta ƙara matsawa ciki tana tafiya da sanɗa kamar barawon da ya shiga sata gidan gardawan maza.
Tana tafiya, sai ta taka wani abu a ƙasa caaak. Ta yi tsalle sama kamar an jefa ta da spring.
"Na shiga uku! Wane irin abu ne wannan kuma?" Ta sunkuya da rawar jiki, ta taɓa, ashe takalmi ne.
Taja siririn tsaki, "Mtseew! Takalmi ya kusa sakawa in gudu in bar ƙafata a nan," ta ƙarasa maganar tana girgiza kai.
Sai ta sake jin ƙuuuu... ƙuuuu... amma wannan karon da ƙarfi.
Har tayi ready ta tattara rigarta da nufin ta koma ɗakinta a tamanin sai kuma taji shiru babu ƙarar.
Ta saka ƙafarta tana tafiya tana haskawa da touch, tana neman inda za ta samu fridge ta sha ruwa domin kawar da kishirwar dake ragargazar maƙoshinta.
Yadda take tafiyar kansa tako ne na wanda yake a tsoro ce, kafarta ɗaya gaba, zuciyarta uku baya.
Ta ɗaga touch ɗin sama, hasken ya haska bango, inuwarta ta motsa.
"Wayyo!" Ta fasa ihu ta juya da sauri, ashe inuwarta ce.
Ta girgiza tana faɗin, "Ke dai Bulkuma matsoraciya ce kina neman ki tsorata kanki da kanki."
Ta ci gaba da tafiya a hankali, tana baza idanu kamar mai neman zinariya a tumun dare. Kishirwa na ƙara matsa mata, makogwaronta kamar an shanyashi a rana.
"Wallahi idan na ga ruwa yanzu, ko daga robar aljannu ce sai sha," ta furta.
Sai ta ji ƙarrr... ƙarrr... daga wani gefe.
Ta tsaya cak.
"Mey kuma ne yake motsi a nan?" Ta tambayi kanta, murya na rawa.
Tuna tace ko a robar aljannu taga ruwa sai tasha ya saka cikinta ya bada sautin ƙu..lu...lu... zuciyarta na buga da karfi, da saurin tace, "Kuyi haƙuri bazan sha maku ruwa ba."
Taji shiru, ta ɗaga touch ta haska, sai ta ga labule ne yake motsawa saboda iska.
"Mtseew! Labule ya kusa sakani inci gudu kamar farar kura."
Ta sake matsawa gaba... sai kuma ta taka wani abu, ƙwac.
Ta yi tsalle kamar an jefeta da gungumen wuta. "Na shiga uku! Wannan gidan fa yau sai ya kasheni da tsoro!"
Ta sunkuya da sauri ta haska, ashe leda ce.
“Leda?!” ta faɗa da mamaki tana juya ledar a hannunta, "Leda ta kusa sakani shiga kundin tarihin matsorata."
Sai dai mi, tana zuwa tsakiyar parlour, sai bulb mai amfani da sensor ya fara kawo haske—tas!
Ta zabura kamar an ce 'riƙe ta!'
Ta saki ƙaramin ihu, "Wayyo! Aljannu suna dalleni!! Kuyi haƙuri, wallahi Allah ƙarya nike bazan sha maku ruwa ba, idan kuna so ni mai zuwa ce in ɗebo in cika maku bokitai!."
Da ta juya zuwa gabas, haske ya bita.
Ta koma yamma, haske ya bita.
Ta nufi kudu, haske ya bita.
Ta juya arewa, haske ya bita.
Su dai bulb duk inda sukayi sensing mutum haske suke dallawa.
Tayi wujiga-wujiga kamar wacce akayi dambe da ita, tana gudu haske yana binta.
"Ku kyale ni! Wallahi ban zo da faɗa ba!" Ta faɗa da muryar magiya tana roko.
Ta ɗaga hannayenta sama tana faɗin, "Na tuba! Duk wanda na taɓa yiwa laifi a cikinku ya yafe!! Nima na yafe!!."
Amma haske ko ince ajalin hasken yana nan yana biye da ita.
Bata san lokacin da ta durkushe tana fasa ihun ALJANNU ba
Ta fasa ihu da ƙarfi, "ALJANNU!!! KU BAR NI!!!"
Ta ƙara fasa wani ihun, "Wayyo Aljannu suna wasan kura da ni a parlour, mutanen gidan nan kuzo ku kawo min agaji tun kafin su kassarawa Gwoggota ni."
Ta rufe ido ƙam, tana jiran ko za a ɗauke ta sama ko a jefa ta ƙasa.
Amma Shiru. Babu motsi.
Ta ƙara fasa ihu, "Wayyo Aljannu suna wasan kura dani azo a kawo min taimako."
Amma shiru kakeji babu wanda ya kawo mata agaji.
Ta buɗe idanu a hankali, ta saurara, amma shiru kamar babu mai rai a gidan bayan kuma mutum ukku ne a gidan ita ta hudu.
Haushi ya turnuketa, "Lallai ma wato ni Bulkuma nice banza a gidan nan, wato nice banza wofi sharar tsakiyar kasuwa, ina ihun neman taimako amma aka yi min banza bayan ɗazu da nayi wa Bello fashin kwakwa a jelar tsakiyar wando, yana ihu suka fallo da gudu kamar waɗanda suke jira."
Ta ɗan tsaya, ta ɗaga murya kaɗan da ɓacin rai tana faɗin, "Amma ni da nike nan ina ihu ‘aljannu suna dalleni’ ko bera bai ce ‘me ke faruwa ba?'"
Ta naɗe hannuwa kamar wacce za'ayi faɗan dambe da ita.
"Wato Bello shine mai daraja, ni kuma banza ce ko?! Wato an mayar dani sharar tsakiyar kasuwa!"
Tabbas Yusrah ta ji ihun a lokacin tana zaune a tsakiyar gado da system a gabanta tana kallon english series, ga zazzafan shayi mai kauri a gefe yana tururi.
Ta ɗan ƙurbi tea ɗin a hankali, ta ɓata fuska kaɗan saboda zafi, ta ci gaba da kallonta tayi ɓarin mahaukaciya da ihun da taji daga falon wanda babu shakka muryar amaryar Bello ce.
Ihun ya sake tashi daga parlour, muryar amaryar Bello tana ihun, "ALJANNUUU!!!"
Yusrah ta ɗaga gira haɗi da taɓe baki, ta ce, "Hmm... babu inda zan je wallahi."
Ta sake ɗaukar kofin shayinta kakkaura ta kurɓa, "Shi da ya auri mahaukaciyar sai ya ji da haukanta."
Maimakon ta rage ƙarar volume sai ma ƙarashi da tayi tana faɗin, "Ba zan bar wannan episode din ba saboda ihun dare."
Tayi dariya tana maida hankalinta kacokam akan majigin kwamfutar dake a gabanta.
A ɗaya dakin kuwa, Zuhra da Bello sunyi nisa a duniyar farantawa junansu rai basu ma san ana ihun ba.
Haushi ya turnuke Bulkuma Amaryar Bello ganin har lokacin babu wanda ya fito kawo mata dauki, cikin ranta tace, "Dani kuke magana, wooh ni Bulkuma sarauniyar wauto, dukkanin wanda ya ci tuwo dani ko miyar bai sha ba, idan kun san wata baku san wata ba."
Ta kwara murya ta fasa ihun 'Ɓarawo!'
Faɗi take, "Ihu Ɓarawo! Bindiga! Bomb!."
Mai gadi yana jin haka ya wartsake daga barci ya miƙe zumbur yana neman hanyar gudu, yayi karo da bango ya saki ihun wahala, a tamanin yayi hanyar get ya kwabru da kofa, yayi zaman daɓaro a ƙasa amma jin ihun Bomb yana ƙara yawa ya miƙe ya buɗe kofa yayi waje yana gudu da iyakar karfinsa.
A cikin gidan kuwa...
Yusrah tana jin ihun Bomb ta zabura tayi wancakali da ruwan shayi saman kwamfutar da take kallo, a guje ta shige wardrobe ta kulle jikinta yana karkarwa, sau ukku tana sakin fitsari a wando, tana tuna yadda Bomb yake tarwatsewa ta saki fitsar mai haɗe da tusa, ta haɗa zufa tana wiki-wiki da idanu kamar beran da mage ta saka a corner babu hanyar tsira. Tuna yadda Bomb yake ragargazar katako ya saka ta fahimci wautar ɓoyewarta a wardrobe a guje ta fito tayi hanyar parlour daga ita sai daurin kirji.
A ɗaya dakin kuwa,
Bello da Zuhra suna jin ihun Bomb cikinsu ya ɗuri ruwa, ita dai Zuhra tasan ta janyo zani ta ɗaura a kirji, garin sauri ta janyo wandon boxer ɗin Bello ta yafa a saman kanta.
Shi kuwa gogan maimakon ya saka boxer ashe bujen Zuhra ne ya zura a kugunsa 🤣🤣🤣 suka yo waje a tamanin.
Zuhra da Yusrah sukayi arangamar kwara kai sukayi warwas a ƙasa suna ihun wahala kowace dafe da kanta.
Bello kuwa faɗi yake, "Ina barayin!? Ina Bomb ɗin!?"
Bulkuma ta kalleshi ta murguda baki tace, "Babu wani Bomb da ɓarayi, tun ɗazu aljannun kwan lantarkin nan suke wasan kura dani a falo, nayi mujiga-mujiga dani ina ihun aljannu amma kukayi min banza, amma yanzu da mukaji maganar Bomb da bindiga gashi kun fito a tamanin."
Ta wuce wajen fridge ta buɗe ta dauko ruwa ta kafa kai tana sha yayinda take jin sanyinsa yana ratsa mata har tsakiyar maƙoshi.
Yusrah ji take kamar ta fasa ihu saboda takaici, tana tuna yadda ta lalata system dinta mai tsaɗa da ruwan shayi ga kuma uban fitsarin da ta sharara a cikin kayan sakawarta.
Saida Zuhra ta duba jikinta sannan ta lura ashe babban rigar Bello ce ta dauro a kirji, ta lalubi kanta taji boxer dinsa.
Bulkuma tana juyowa da nufin komawa dakinta ta hango Bello sanye da bujen mata. A take ta tsaya tamkar an dasata a wajen, ta ware idanu kafin wata irin dariya mai ƙarfi ta ƙwace mata.
"Hhhh buje!" ta fashe da dariya, ta durƙushe ƙasa tana riƙe ciki, hawaye na kwaranya saboda dariya. Ta kasa magana yadda ya kamata, tana nuna Bello tana ƙara tsananta dariya kamar wata zautacciya.
Zuhra da Yusrah suka maida dubansu akan Bello domin ganin abun da takeyi wa dariya, ganinsa sanye da ɗan bujen undy ya saka suka fashe da dariya.
Bello ya kalli kansa yaga bujen mata a kugunsa, ji yayi kamar ya nutse a kasa saboda kunya, ya yi yunƙurin ɓoye jikinsa amma lamarin ya riga ya tonu.
Yusrah ta riƙe ciki tana karkarwar dariya tana faɗin, "Kai Bello, wannan wane irin shiri ne haka?"
Zuhra kuwa jingina tayi da bango, dariya na ƙwace mata, har hawaye takeyi saboda dariya, "Wallahi yau mun sha kallo, wannan lamari sai wanda ya gani."
Falon gaba ɗaya ya cika da dariya, suna kallon Bello kamar wani wasan barkwanci. Shi kuma ya tsaya a tsakiya, yana jin kunya da takaici sun haɗu suna ragargazarshi a ciki, ji yake kamar ya rufesu da duka.
Yusrah tace, "Angon Bulkuma mai buje," ta ƙarasa maganar tana dariya har hawaye.
Yayi kanta tayi hanyar dakinta tana dariya. Zuhra kam faɗi take, "Ranka ya ɗaɗe bani bujena."
Ya fizge boxer dinsa dake a saman kanta ya zura ya cire bujen ya wurgar ya wuce dakinsa fuu kamar zai tashi sama.
Bulkuma tayi hanyar dakinta tana dariya har da durkushewa.
Zuhra da Yusrah kowace tayi hanyar dakinta, Zuhra ta zare babbar rigarsa dake a kirjinta ta shige bathroom ta sakarwa kanta shower tana wanka tana dariyar Bello mai ɗan buje 🤣🤣🤣
Yusrah kuwa kai tsaye wajen wardrobe ta nufa ta tattara kayan da ta ɓata da fitsari ta wanke ta shanya a bathroom, tana yi tana ɓaɓɓaka dariyar yadda Bello yake sanye da buje.
Ta wanke ƙasan wardrobe din ta goge, ta janyo system dinta ta gogeta ta ajiye da nufin washegari ta kaita gyara, daga nan ta shiga bathroom ta sakarwa kanta shower tana tuna yadda ta tsure tana wiki-wiki da idanu jin an kira Bomb, yadda ta rinƙa sakin fitsari mai haɗe da tusa, ita kanta dariya takeyi wa kanta yayinda a gefe guda bujen Bello yake bata dariyar da tafi waccen.
Mai gadi kuwa saida yayi gudun dogon zango yaga babu alamar tashin Bomb sannan ya dawo da baya yana tafiya yana haki ya buɗe get yayi wuff ya shige dakinsa ya saka sakata, barcin da bai koma ba kenan.
WASHE GARI
A tare Zuhra da Yusrah suka fito daga dakunansu kowace cikin shirin fita, ita Zuhra ta shirya domin zuwa makaranta yayinda ita kuma Yusrah fita zatayi kai system dinta gyara daga nan ta biya ta tasha ta amso kayan da aka aiko mata daga Kano.
Suka hango Bello zaune a dinning table ya haɗe fuska yana jiran su fito suyi karin kumallo, suna hangoshi suka tuna lamarin bujen jiya, a tare suka saki dariya.
Yana juyowa sukayi gumm, Yusrah tace, "Yaya Zuhra ina kwana?" Zuhra tace, "Lafiya lau ƙanwata. Kin tashi lafiya?" Yusrah tace, "Lafiya lau yayata ta kaina."
Suka nufi dinning table kowace na iyakar ƙoƙarinta domin ganin ta shanye dariyar dake ragargazarta a ciki.
Kowace taja kujera ta zauna, Yusrah tace, "Ina kwana ranka ya ɗaɗe?" Yana muzurai yace, "Lafiya." A dole kada su kawo mashi wargi.
Zuhra tace, "Barka da safiya your highness." Yana ɓata rai yace, "Barkanmu, tashi kije ki kira min amaryata."
Ta miƙe tana dariya ƙasa-ƙasa tace, "My pleasure ranka ya ɗaɗe angon Bulkuma."
Yana muzurai yace, "Miye na dariya a nan?" Tace, "Wani comedy na kalla a waya shine na tuna shine nike dariya."
A takaice yace, "Good, jeki ki kira min ita." Ta rusuna kamar da gaske tace, "An gama ranka ya ɗaɗe."
Saida ta laɓe a corridor tasha dariya sannan ta wuce dakin Bulkuma ta sameta ɗare-ɗare akan gado tana barci, bata yi yunkurin tayar da ita ba, ta juya ta koma saying, "Barci take, abar amarya tayi barci, kasan ita amarya bata laifi ko ta kashe ɗan masu gida."
Yusrah dai tana zaune shurum hannunta akan bakinta tana dariya ƙasa-ƙasa, yace, "Ke miye kike rufe baki, ciwo yake maki ne?" Tace, "A'a." Ta sauke hannunta tana mayar da dariyarta a ciki.
Suna tsakurar abincin suna faman danne dariya a ciki, Bulkuma ta fito daga dakinta tana buga hamma, ta hangosu suna cin abinci, tana ido hudu da Bello ta kwashe da dariya, dariya take har da riƙe ciki tana tuna yadda ta ganshi sanye da bujen undy.
Bello ya daka mata tsawa yace, "Ke uban meyy kikeyi wa dariya?"
Tana cigaba da dariya tace, "Buje!..."
Kanta tsaye tace, "Buje!..."
Zuhra da Yusrah suka kwashe da dariya, ya miƙe fuu ya fice.
Bulkuma ta gama dariya ta isa inda suke tace, "Ina abincina?"
Zuhra da Yusrah suka kalli juna suka taɓe baki, tace, "Ohhh ni kuke taɓewa baki, to wallahi duk wacce ta zageni sai mun dambace a falon nan, ni Bulkuma duk wacce tayi min kan kara sai nayi mata na itace ta shekara ta shekare tana amfana."
Ta wafce farantan da suke cin abinci ta hade waje daya, ta haɗe da na Bello ta wuce parlour tana ci tana kallon cartoon tana ɓaɓɓaka dariya.
Zuhra ta suri jikkarta ta fice domin tafiya school yayinda Yusrah ta koma daki ta ɗauko kwamfuta da jikkarta ta fice.
Bulkuma ta bisu da kallo tana mai taɓe baki, ta gama dabdalar cin abincin da saida ta zubar da rabi akan carpet, ta miƙe ta wuce dakinta tabi lafiyar gado.
*****
Tunda Bello ya fita ya rasa inda dosa, babu dama yaje kasuwa yadda yake kurin ya auri kwaila mai wauta maganin ciwon zuciya, idan Musa da Garzali suka ganshi a kasuwa ya boni da tambaya watakila har sai sun harbo jirgin abun da ya faru.
Idan kuma ya koma gida matan nan zasu fusatashi da dariyar da suke mashi, sun mayar dashi comedy.
Anya kuwa shi wautar nan mai maganin hawan jini ta karbeshi, Musa cewa yayi idan tayi maka wauta ka ɗagata sama kayi wa abunka tawai ko ka goya kayanka, amma shi a daren farko, fashin kwakwa tayi mashi a joystick saboda ya nemi hakkinsa. Bugu da ƙari ta sakasu a tashin hankalin da har ya fito sanye da bujen undy na mata ya koma laughing stock.
Shi da ya auro Kwaila ƴar wauta domin ta zame masa maganin hawan jini sai ta mayar dashi maganin hawan jinin har Zuhra da Yusrah suka tusashi gaba suna dariya, reshe ya juye da mujiya, kaikayi koma kan mashekiya.
Har ya fara hango damuwa a zamansa da wannan yarinyar, sai yanzu yake hango gaskiya akan magangun Malam Wada da yake mashi hannunka mai sanda akan Auren Bulkuma.
Akwai ridi da zai duba a wani kauye, ya sauya akalar motar zuwa hanyar kauyen.
******
Har Zuhra ta shiga school tana dariyar bujen Bello.
Class rep dinsu ne tsaye a gaban allo yana gudanar da tutorial akan wani course da zasuyi test dinsa sati mai zuwa, yana iyakar kokarinsa domin bayani akan wajejen da suke bukatar fahimta domin samun nasara a wajen test.
Dukkanin ɗalibai sun nutsu suna sauraro amma banda Zuhra wacce take zaune a benci na kusa da na karshe tana dariya a hankali cikin facemask dake fuskarta, har kafadunta na rawa. Tana iya kokarinta domin ta danne dariyar amma abun YA FI ƘARFIN KANTA.
Asiya kawarta da ke zaune kusa da ita, ta lura da yadda take ta faman ɓaɓɓaka dariya, ta dan matsa kusa da ita tana raɗa mata a kunne, "Ƙawata, miye kikeyi wa dariya haka? Ki daina mashi dariya mana, ba zai ji dadi ba musamman yadda yake iya ƙoƙarinsa domin ganin kowa ya samu sakamako mai kyau."
Ita Asiya a tunaninta class rep ne Zuhra takeyi wa dariya.
Zuhra ta girgiza kai tana dariya ƙasa-ƙasa, tace, "Ba shi nikeyi wa dariya ba, wani comedy na kalla a TikTok jiya da dare shine duk lokacin da ya fado min a rai sai in dara."
Ta dakata tana ƙoƙarin sarrafa kanta, amma inaa tuni dariya ta ƙara kufce mata tuna yadda Bello yake sanye da buje, ta ƙara fashewa da dariya kafin ta iya ƙarasa maganar da ta fara, "Na hango wani gardin namiji sanye da bujen undy."
Maganar ma bata kare ba ta sake fashewa da dariya.
Jin haka sai itama Asiya dariya ta kubce mata. Ta rufe baki da hannu tana faɗin, "Tab! Kunna min in gani mana."
Zuhra tace, "Meyy?" Asiya tace, "Kunna min in gani nima inyi nishadin nan."
Zuhra tayi tsuru-tsuru dama hausawa suka ce ramin karya kurarre ne, ko giyar hauka tasha bata isa tace Bello bane, ta ɗaure fuska kamar gaske, tace, "A can na kalla kuma na mance handle din."
Asiya ta kalle ta da ɗan shakku, amma dariyar da takeyi ta hana ta zurfafa bincike.
A gaban ajin kuwa, class rep ne yake cigaba da bayani, ya lura dasu, lokaci zuwa lokaci yana juyowa yana kallonsu da mamaki, yana zargin akwai wata magana a tsakaninsu.
Su kuwa, dariyarsu sukeyi ƙasa-ƙasa.
Bayan an tashi daga tutorial din, har lokacin dariyar abun da ya faru daren jiya bai saki Zuhra ba, the more ta tuna the more take dariya.
Ta samu waje ta zauna ta zaro wayarta ta shiga WhatsApp. Ba tare da ɓata lokaci ba, ta ɗaura bidiyon Bello da amaryarsa Bulkuma a status tareda saka wakar aure.
Ba da jimawa ba, Yusrah ta buɗe ta saka emoji na dariya da sticker ta dariya, tsaf ta gane inda maganar ta dosa.
Oga Bello kam yana hango bidiyon a status din Zuhra ya danna mata kira.
Tana ɗagawa bai jira tayi magana ba yace, "Zuhra! Laughing stock kike mayar dani kenan? Miye na ɗaura bidiyon nan?"
Zuhra ta kwashe da dariya kafin tace, "Ayyerh, na gaji da kishin hauka ne shiyasa nace bara in tayaku murnar aure, I wish you a happy married life, Zawāj Mubārak."
Wato dai ta maida komai kamar wasa.
A ɗaya ɓangaren, Bello ya yi shiru na ƴan daƙiƙu. Kalmar da ta fito daga bakinsa kaɗai ita ce, "Yayi kyau."
Kyit ya tsinke kiran.
Lokacin da za su shiga lecture, Zuhra ta tsaya a wajen lecture theater din na ɗan lokaci, ta ɗora hannu a ƙirji tana jan lumfashi a hankali, tana ƙoƙarin daidaita kanta. Ta sani sarai idan ta shiga a wannan halin, dariya na iya kufce mata a tsakiyar aji, ayi waje road da ita.
Ta matse baki tareda ta gyara facemask dake fuskarta, tayi kamar wacce ta manta da komai amma deep inside dariyar tana ragargazarta a ciki. Da wannan ɗan ƙoƙarin ne ta shiga cikin ajin.
Ta zauna a cikin nutsuwa kamar sauran ɗalibai, amma lokaci zuwa lokaci sai ka ga tana mazewa, ta sunkuyar da kai kamar wacce take rubutu, alhali kuwa dariya take ƙoƙarin mayarwa ciki. Wani lokacin har kafadunta na ɗan rawa kaɗan, sai ta daure ta gyara zamanta da sauri.
Duk wanda ya kalleta sosai, zai gane cewa akwai wani abun da take ɓoyewa.
A haka ta cigaba da fama da kanta a tsakanin san ta natsu da kuma dariyar da ta ƙi barinta har ƙarshen lecture.
*****
A bangaren Yusrah yadda dariya take cinta ya saka ta tsaya ta sayi facemask domin kada ta kece da dariya akan santa ayi mata ɗaukar mahaukaciya, saida ta fara zuwa tasha ta amso sakon sannan ta biya shagon gyara ta kai system dinta ta tsaya a gyara mata ta wuce da ita.
Tana cinikin masu kayan kitchen online, matar tana yi mata voice note amma ita ta gagara voice note saboda yadda dariya take cinta saida typing takeyi.
Matar dake kusa da ita ta fusata tace, "Hajiya lafiya zaki tusani a gaba kina min dariya!" Yusrah ta nuna mata wayar dake hannunta tace, "Hira nikeyi da ƙawata ko kina da matsala da hakan ne."
Matar ta taɓe baki ba tareda tace komai ba, daga nan Yusrah ta kama kanta tun kafin azo ana wallahi tallahi da ita.
******
A bangaren Bulkuma amaryar Bello kuwa ta gama barci ta samu gida wayam, tace, "Tab wato ni ɗaya suka bari a gidan kamar wata gantalalliya to nima bazan zauna ba."
Ta koma dakinta ta duba cikin kuɗin da tazo dasu ta zaro dubu ɗaya ta fice compound ta tarar mai guard ya zagaya, ta buɗe kofa ta fice tana tafe tana kalle-kalle, akan layi ta hango mai rake ta saya ta amso canji ta dawo tana tafe tana wafkar rake tana dariya.
Ta hango wasu yara suna jan mahaukaciya ta tsaya tana ɓaɓɓaka dariya, mahaukaciya tayi bi, a guje ta yanki layi, Allah ya taimaketa da tayi corner ta tsinci kanta a kofar gidan tayi wuff ta shige tana maida lumfashi.
Mai gadi ya taso da sandarsa yana fadin, "Ke lafiya? Wacece a nan?"
Kanta tsaye tace, "Amaryar Bello." Ta bangajeshi ta wuce ciki tana tafe tana kwaftar rake, ya dubi yadda ƙafafunta sukayi budu-budu da ƙasa, ga yadda ta fita babu ko mayafi, ya riƙe haɓa yana mamakin wacce irin amarya ce haka mai gidansa ya auro.
Ta shige parlour ta kunna cartoon tana kallo tana dariya, cikinta ya fara kukan yunwa abunka da wacce ta saba da ƙara cin abinci a tsakanin kalacin safe da abincin rana, ta dafe ciki tana ɓata fuska gashi gidan babu kowa sai ita ɗaya.
Ta shiga kitchen ga komai da komai akwai saidai bata iya kunnawa, karshe ta koma dakinta ta ɗauko naira ɗari biyar ta fita bakin layi ta sayi shinkafa da wake da mai da yaji ta zauna a gefen hanya tana ci tana jan tsaki tana mita, tana amaryarta mai capacity amma saboda cin amana Bello ya barta tana cin abincin gefen hanya, koda yake takamar yayi fushi ne don tayi dariyar saka buje, ai kuma buje tayi wa dariya kuma ba ita tace ya saka bujen ba, ita ihun Bomb da bindiga kawai tayi saboda aljannun haske suna wasan kura da ita tana neman taimako sunki taimaka mata, ai ba ita ya kamata ya ji wa haushi ba, kanshi ya kamata ya ji wa haushi, duk abun da ya samu gafiya jelarta ce ta janyo mata.
Ta koma gidan ta cigaba da kallon cartoon, wajen karfe ɗaya na rana Yusrah ta dawo tayi turus ganin yarinya tana kallo a parlour, tace, "Ke daga ina?"
Haushi ya turnuke Bulkuma tace, "Ban sani ba, kije matambayu gidansu tambai ki tambayo masu tambaya, koda yake bara in baki amsa, nice Bulkuma amaryar Bello wacce jiya ta sakaki gudun ceton rai watakila har guntun kashi kika saki a wando."
Yusrah tayi mata banza ta wuce dakinta ta ajiye kayan da ta shigo da su, tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga marar nauyi ta fito parlour ta shiga kitchen ta girka shinkafa tareda shayi mai kauri ta dawo parlour tana ciniki tana cin shinkafa da miya tana korawa da shayi.
Bulkuma wacce take jira a bata kasonta taji shiru ba'a ce mata ga naki ba, ta miƙe ta isa gaban Yusrah tace, "Ke Malama ina abincina?"
Yusrah ta dubeta tana mamakin tsaurin idon yarinyar, ta murtuƙe fuska tace, "Abincinki kuma? Miye hadina da abun da zaki ci ko kuma a yarjejeniyar aurenki da Bello ance in ciyar dake ne? Dalla matsa ki bani waje, kije ki girka da kanki."
Bulkuma tace, "To ai ban iya amfani da kayan madafarku ba."
Da gatse Yusrah tace, "Sai kije kiyo icce kamar yadda kika saba a kauye, sai kuma ki nemo sabara da kalgon da kika saba ci a kauye, mudai Bello bai kyauta mamu ba, ya je ya auro mamu jaraba da bala'i."
Bulkuma ta nuna kanta tace, "Ni kike kira jaraba da bala'i aikuwa zakiga jabara da bala'i ganin idanunki."
Yusrah ta taɓe baki tace, "Get out of my site you stupid girl."
Bulkuma da bata san abun da aka ce ba tace, "Ba dai uwata ba saidai uwar mai zagi." Yusrah tace, "Oh ashe fa har da ciwon jahilci ne yake damunki."
Takaici ya kama Bulkuma ji take kamar ta fasa ihu, har ita za'a kira Jaraba ace mata jahila aiko sai ta nunawa matar nan samfurin jahilci da jaraba ta gani ganin idanuwanta, sai ta koyawa matar nan hankali fiye da yadda ta tumurmusa zukatan ƴan kauye da suka kulla mata tsiya, bata cuta amma bata yafe cutarwa, idan kayi mata sharri sai ta aikata maka domin kaji daɗin faɗa da hujjq.
Ta fita ta bazama neman bola ta tattaro riguna da zannuwan da aka zubar, saida taje daidai window ɗin dakin Yusra sannan bankawa kayan wuta ta ɗaura girkin doya jolof, dama tagar Yusrah a buɗe take aiko hayaki yayi ta afkawa ciki, ta ɓata bangon wajen, yadda dakin Yusrah ya turnuke da hayaki kai kace a cikinsa ne tayi girkin, tana gamawa ta saka leather manya ta toshe window din domin kada hayaƙin yayi saurin ficewa.
Ƙaƙara Ƙaƙa...Hhhh... Turkashi 😅😅🤣🤣😂
Muje zuwa😁😅🤣🤣😂
Taku Har Kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)